18
by @legendspen
"Su waye baka yarda da su ba?"
"Nana kenan? Ni wannan ma duk da ba wani kallo na yi mata ba amma tabbas tafi ƙawayenki da yayyunki da yawa kalal nutsuwa."
Haka kawai na ji ta kwantamin a raina, sakamakon abinda Sardauna ya faɗa, daman kuma tabbas zaman ni kaɗai ɗin ya isheni na gaji da zaman.
"To yanzu ba matsala kenan?"
"Eyh! Ba matsala kam amma dai ba ko yaushe anyhow ba gaskiyya kinsan tsarina."
"Tom shikenan na gode."
Na faɗa ina ci gaba da cin abincin, shima ya ci gaba da ci bayan mun kammala ya kalleni sannan ya ce.
"Na yi wasu abokai anan baya, suna da majalisa ina tunanin zan fara zama ina rage dare kafin mu saba da yanayin unguwar."
"Eyh hakan yana da kyau kam gaskiyya, Allah Ya taimaka."
Na faɗa shi kuma ya tashi ya shiga ɗaki, can ya fito bayan ya ƙara gyarawa ya fice.
Daga wannan rana kullum Sardauna sai ya fita majalisar nan bayan ya dawo, sai goma ta gota yake dawowa, tun bana jindaɗin zaman har nasaba, Bilkisu kam ba ta sake zuwa ba tun ranar ba gaba ɗaya na damu, har na fara tunanin ko sardauna ne ya dakatar da ita sai kuma na tuna kwata kwata basu haɗu ba tin da ya shiga ɗaki bai fito ba sai da ta tafi. Sai da aka yi sati biyu sannan ta sake zuwa, ranar na yi murna kamar na cinye ta, haka itama ta dinga biya min mun hira sosai kuma na ji daɗin zama da ita sosai da sosai, tun daga wannan lokacin ta fara zuwa duk da ba ko yaushe ba, babban abin daɗin Sardauna bai taɓa yi min ƙorafi akan zuwa na ta ba, duk da wani lokacin su kan haɗu.
Na yi mata maganar rashin haihuwata, ta ƙara ƙarfafamim gwiwa tare da ba ni hakuri akan hakan, da cewa na dage da addu'a, babban abinda ya burgeni da Bilkisu shine karatunta ta yi degree a yanzu ma ta ɗaura masters sannan tana yin aiki, mace mai ilimi daban ce, komai na ta gwanin ban sha'awa akwai tsari, ban taɓa zuwa gidansu ba, amma ina yawan ce mata zanje idan na fita.
A ɓangaren Turaki har yanzu auren shiru, sai dai kawai na ji mostintsa idan ina falo amma bai taɓa shigowa ba kuma ko a waje bamu taɓa haɗuwa ba, da muka yi magana da Ra'is ta wayar Hajiya ya ce da ni wai Turakin nema yake nemansa a waya lokaci zuwa lokaci ya ji lafiyarsa da ta mutanen gidan.
A tsakanina da Sardauna abubuwa suna tafiya yadda suke, kawai dai kwana biyu ya ƙulla sabuwar abota da wayarsa da kuma zuwa majalisa, wanda a yanzu ya ɗan rage bai cika fita kullum ba.
****
Yau tun safe na kammala aikina, dan mu yi da Bilkisu zan koya ma ta yadda ake Samosa wrap, ta ce tana so kuma ta ga ina yi yawan yi tasan dole maza suna so.
Ina tsaka da aikin gida ta shigo, daman ta ce yau gudun wajen aiki za ta yi, murmushi na sake sannan na ce.
"Har kin ta so?"
"Na dai gudu, ai yau sai na koyi abin Samosar nan, har da wasu kayan fulawar tunda nima na kusa aure."
Murmushi na sakar mata sannan na ce.
"Ke ce muna da shan biki."
"Ke ba wanda nake kulawa, kawai na faɗa ne."
"Wai daman ina ta so na tambayeki me ya sa bakya kula maza ne, ba ayi miki zancen aure a gida?"
"To Nana ai aure lokacine, bazan iya biyewa namiji ba inda ba na aure ba, dan ba duka ba ne suke da kirki, yanzu zai yi miki SARTSE a rayuwarki indai namiji ne."
"Amma nikam Alhamdulillah wallahi, miji dai na yi da ce."
Na faɗa ina shiga cikin kicin, bayana ta biyo tana faɗin.
"Ga alamu nan dai, muma idan mun sami irin nakun sai mu aura, amma wa'yanan samarin shawon ba dani ba."
Na tuntsire da dariya sannan na ce.
"Lallai fa Samarin Shawo."
Haka muka shiga ina yi tana kallo tana 'yan tamnayoyinta har muka kammala. Daga nan muka dawo falo muka shiga hira tana nan har yamma sannan ta tafi.
Haka rayuwata ta yi ta tafiya, yau daɗi gobe akasin haka, abubuwa suna tafiya wasu yadda aka tsara wasu kuma ba yadda aka tsara ba, tsakanina da Sardauna kullum sabuwar soyayya, sabuwar biyayya, a kullum Sardauna yana farin ciki tare da yin alfahari da ni. Yana yawan ce min.
"Nana kin yi min komai a rayuwa, Allah Ya bani ikon faranta miki rai."
Ni kuma a kullum duk wata sabuwar na'uin biyayya yi wa Sardauna nake, wani abu ni a kaina na kan ji kamar ya zarci hankali, dan a yanzu takai idan Sardauna yana kan kujera ni a ƙasa nake zama, sai ya dage min nake zama akan kujerar ko na ga ya sauko ƙasa.
08:30pm.
Zauna nake a falo, hankalina yana kan wayata dan nasan Sardauna yanzu ba lokacin dawowarsa ba ne.
"Hon!"
Kamar daga sama na ji muryarsa.
"Kawo min abinci."
Ya faɗa yana nufar kan dinning a tsorace na tashi gabana ya na faɗuwa, me ya sami Sardaunana haka?
zama ya yi akan dinning ɗin bai ce ko ƙala ba, na zuba masa ina binsa da ido, a yanayinsa ma kamar cusa abincin yake dan kamar baya jindaɗi.
"Me ya faru dan Allah."
"Bakomai."
Ya faɗa yana ci gaba da abincin, yana cikin ci ya tashi ya shige ɗakinsa, ba shiri nima na bishi ciki amma kafin na je ya kulle ɗakinsa.
"Innullahi wa'inna illahir raji'un, me ya faru dan Allah, Ya Allah Ka kawo wa Sardauna na sauƙi."
Na faɗa ina komawa falon, sai dai gaba ɗaya na rasa abinda zan yi tunaninma na kasa, halin da Sardauna yake ciki ya dameni, Whatsapp na duba naga Bilkisu na online, na tura mata message
" 'yar uwa da matsala." Na haɗa mata da emoji na kuka, cikin ƙasa da minti ta dawo min sa amsa.
"Sisi me ya faru?"
"Sardauna ne ya dawo gida da damuwa."
"Me yake damunshi?"
"Bai faɗan ba wallahi."
"To me kike da baki tambayeshi ba, Nana kije ki tambayeshi mana, a shawarar da nake baki a kullum ina faɗa miki ki mayar da damuwar mijinki taki."
"Ya kulle ɗakin."
"Toopa, gaskiyya wannan babbar matsala ce, ko dai zuwan da na yi ɗazu ne?"
"Anya kuwa, Sardauna baya son mutane su zo amma ke bai taɓa min magana akanki ba."
"Ikon Allah."
Ta haɗo da emoji na mamaki.
"Yanzu mene abin yi?"
"Abin yi kije ki tambayeshi mene, ki yi amfani da duk wani ikon da ƙarfinki wajen ganin kin magana ce mai damuwar tasa."
"Na gode 'yar uwa."
Daga nan na kashe data ta na kwanta, ina ta faman saƙe saƙe har bacci ya ɗaukeni, washe gari da safe bayan na yi duk wani abu da nasaba, amma Sardauna har wajen ƙarfe tara bai fito ba, ina nan zaune akan a falo ya fito da shirinsa, da sauri na tashi tare da faɗin.
"Ina kwana?"
"Lafiya, ya kike?"
"Alhamdu Lillah, ga abin breakfast nan."
"Nana bazan iya cin abinci ba, ina cikin damuwa ki yi haƙuri."
"Me yake damunka dan Allah, ka faɗa min ka ji."
"Nana ina cikin damuwa kawai, ki yi haƙuri."
"Yanzu akwai damuwar da bazaka faɗan ba a matsayina na matarka dan Allah?"
"Ba haka ba ne Nana, ki yi haƙuri zuwa na dawo kinji."
Yana faɗin haka ya fice, ya barni tsaye kamar wacca aka dasa, na kusa minti goma sannan na sami waje na zauna, haka na shiga damuwa gaba ɗaya ko breakfast ɗin nima ban iya ba, sai wajen sha biyu na rana na iya sa abu a bakina, daga nan na dawo kan kujera na ci gaba da zaman damuwa, sai ƙarfe biyu Bilkisu tazo bayan ta dawo daga ofis, ta yi mamakin ganin yadda na rame ma fige duk a iya rana ɗaya.
"Nana haka kika damu da Sardauna? Duk akansa kin wani canja haka ji fa?"
"Bazaki gane ba Bilkisu, wallahi ina son mutumin nan sama da kowa, sama da komai a wannan rayuwar, bana so na ga wani abu guda ɗaya da zai dami Sardauna a duniya, bana son shi wallahi."
"Lallai Nana, to yanzu me ya ce miki yana damunsa?"
"Ya ce sai ya dawo."
"Allah Ya sa alheri ne, Allah Ya sauƙaƙa al'amuran."
"Amin amin."
Haka tai ta yi bani shwarwrin hamyoyin da zan bi na yi maganin damuwar tasa da yanda zan kwantar mai da hankali, na nuna komai zai zo da sauƙi, sai yamma ta tafi kamar ko yaushe.
Tana tafiya na yi wanka na gyara gidan, bayan na yi sauƙaƙƙen abinci na dawo na zauna, ina nan zaune na ji hayaniyar mutane. Labule na ɗaga na buɗe Turaki na gani yau ma kaya ake shigo masa da shi, da alama yau ya dawo dan dama na ji alamun baya gidan, komawa na yi na zauna akan kujera na ci gaba da tunanin yadda zanyi kwantarwa da Sardauna hankali yana dawowa.
Sai wajen tara sannan ya shigo gidan, babu damuwar a fuskarsa kamar jiya, amma bayan na shiga ɗaki na fito na ganshi ya haɗa kai da gwiwa, da sauri na ƙaraso inda yake tare da cewa.
"Sardaunana, jarumina, Honey me ya faru?"
"Nana! Bansan ta inda zan fara yi miki bayani ba, amma tabbas akwai matsala."
"Wace irin matsala ce haka dan Allah?"
"Nana su Big Daddy da Hajiya ta sun matsamin wai suna ganin jikokinsu na wajena, wai shirun ya yi yawa, Nana duk bayanin da yakamata na yi musu, amma su kasa fahimta, faɗi kawai suke duk inda matsalal take na nemo to na yi maganinta, Nana na shiga damuwa matuƙa na rasa abinda zan yi shi ya sa kika ga na damu kwana biyu."
Shiru na yi nima kaina na rasa abinda zan faɗa, matsalal daga ina take, me ya kawo duka wannan zancen?
"Kinji abun wani kala ko?"
Na gyaɗa kai, sannan na ce.
"Yanzu mene abun da za ayi?"
"Ni kaina bansaniba, ina ta faman tunani."
"Allah Ya sauƙaƙa mana."
"Amin Honey nah."
Haka muka zauna jigun jigun gaba ɗaya na rasa abinda ke mun daɗi, me ya kai 'yan uwan Sardauna wannan zancen? Su da suke wayayyu, 'yan boko masu ilimi, amma zasu zo da wannan zancen?
"Kar ki sakawa ranki damuwa kinji Hon, komai zai zo da sauƙi."
"Nasani." Na faɗa tare da yi masa murmushin yaƙe, sai yanzu na ji ina ma ina da halin kiran su Hajiya na faɗa musu, gaba ɗaya rabona da su an kusa wata guda, Sardauna duk ya hanani.
Ko da muka je bacci ma haka kowa ya kwanta, ransa babu daɗi, ni barcin ma rabi da rabi na yi, Sardauna ne daman shi duk girman damuwa ba ta hanashi bacci, ni kuwa ko ya damuwa take mussamman ta al'amarin Sardauna to ba ni da wata nutsuwa akai.
Legendspen
***