Chapter 22
🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 22
Hannun da ya mare ta da shi ya bi da kallo na 'yan sakanni bayan sun kurewa ganinsa, cikin mutuwar jiki ya nemi guri ya zauna dan ƙafafuwansa sun kasa daukarsa “Mene ne haka Ahmad? Me ka aikata haka? Ina tunaninka ya tafi? Wannan babban zunubi ne... Wannan babban zunubi ne.“ Abin da yake ta maimaitawa kenan a can cikin zuciyarsa, yana jin kamar ya fashe da kuka ko zai samu sassauci, amma shi kansa yasan ba abu ne mai sauƙi ba, abinda zai saka shi hawaye a yanzu dai, to lallai ya gawurta. Zabura ya yi kamar wanda ya tuna wani abu mai muhimmanci, ya jawo waya cikin sauri ya shiga lallatsawa, gajeriyar saƙo ya tura ma wata lamba da ya yi saving da Fav kafin ya ajiye wayar akan cinyarsa ya kureta da kallo kamar mai neman jiran tsammani wani abu daga cikinta. Ya dade a haka kafin lokacin guda ya saki wata kyakkyawar murmushi bayan ya tuno abinda ya aikata.
Kai tsaye Ussy wajen da motarsa ke fake a compound ɗin gidan kusa da ta AA ya nufa, tana biye da shi a baya kamar jela ,duk da rana ta fadi duhun magriba ya fara shigowa, tsakar gidan tamkar safiya saboda wadatar haske. Kofar baya ya bude mata, babu musu ta shige, ta zauna ta dafe kanta da take jin ya yi mata bala'in nauyi kamar zai rikito. Sai da ya mayar da murfin motar ya rufe kafin ya zagaya ya shiga ya zauna a mazaunin direba, yayinda Jarumi dake cikin motar yana jiransa ke zaune a gefen hagunsa, da hannu Ussy ya yi masa wata inkiya, gyaɗa kai ya yi alamar ya gane, sai kuma ya ɗan juya ya saci kallon Aysha, da shesshekar kukanta ke ratsa kunnensa, dai dai lokacin da Ussy ya fisgi motar a tsiyace suka fice daga harabar gidan.
Sosai Ussy ke sharara gudu a hanya cike da kwarewa a iya sarrafa sitiyari, cikin kankanin lokaci suka iso kafar gidan ba tare da wani daga cikinsu ya tambayeta ko da sunan unguwar ba ne. Jin sun yi parking baisa ta dago ba, sai da ta ji kakkaurar Muryar Jarumi yana bata umarnin sauka. A wahalce ta ɗago don ganin inda suka kawota, ganinta a kofar gidansu ya bata matukar mamaki, sai dai yana yin da take cikin bai bari mamakin nata ya yi tasiri ba, dakyar ta iya miƙa hannu ta buɗe motar, haka kafin ta ja jiki ta fita sai ta kusa kwashe minti ɗaya saboda yadda jikin nata yake babu kwari. Tana sauka suka yi wani irin ribas na garari, daidai saitinta suka tsaya Ussy ya cillo mata yar jakarta kamara data fadi a motar tun lokacin da suka dauko ta, kafin suka figi motar a tsiyace suka bar layin.
Wannan karar ita je ta janyo hankalin Salman Salmah, da Ammie da suke tsaye a compound cirko cirko cike da damuwa, fuskokinsu kadai ka kalla za ka shaida halin tashin hankalin da suke ciki. Kasancewar basu baro gidan su Suraj ba sai bayan la'asar, yasa basu tarar da Ammie ba, don duk da kasancewar Asabar da Lahadi babu aiki, takan shiga asibiti idan tana da patient da yamma ta duba su, rashin ganin Aysha bai sa sun kawo komai a rai su ba, sai zaton ta bi Ammie asibiti don su kan yi hakan a wasu lokutan, dawowar Ammie ita kaɗai shine ya ganar da su wautar da suka tafka, nan da nan suka fayyace mata halin da suke ciki, hankalin Ammie ya fi nasu tashi, domin da fada ta rufe su da fari kafin kuma ta zari mayafinta da ta ajiye a kan kujerar da makullin mota ta sake fitowa suna biye da ita, a bakin motar take gaya musu Police station za ta je ta kai report, a dai dai wannan lokacin ne suka ji karar motar su Ussy.
Salman ne ya fara takawa da gudu ya nufi get shi da Babangida megadi da ya riga shi fita wajen, Salmah da Ammie, suka rufa masu baya.
Taku ɗaya biyu ta yi ana ukun ta gaza, saboda jirin da ke kwasarta, tana shirin durkushewa, suna fitowa, Salman da ke gaba shine ya fara isa gareta ya tarota, sai kawai ta narke a jikinsa, ta lumshe ido numfashinta na fita dakyar. bakinta ya bushe raƙauu kamar me azumi, “ Innalillahi wa Inna ilahi raji'un!” Ammie ta furta, ta yo kansu ta rikota, Salmah kam tuni ta fara kuka, motarsu Ussy da ke daf da ficewa daga layin Ammie da Salman suka bi da kallo, sai kuma suka kalli juna zuciyoyunsu na rawa. Jijjigata Salmah ke yi tana faɗin, “Aysha, Aysha me ya faru, me ya same ki?” “Kamata Salman mu shiga ciki.” Ammie ta bashi umarni, “Zan iya.” ta furta a hankali, tare da girgiza kai, “A'a Aysha bari ya taimaka miki.” Ammie da ta riga ta yi wa karfin halinta farin sani ta yi saurin faɗa. Hakan yasa bata sake musawa ba, Salman ya gyara mata riko Salmah ta taimaka masa suka saka a tsakiya suka shiga da ita ciki har falon ƙasa, akan dogon kujera suka zaunar da ita, Salmah da har lokacin hawaye ta ke yi, ta zauna kusa da ita tana taɓa jikinta da ya ɗauki zafi zauu alamar zazzaɓi ne a jikin “Jikin ki zafi Sister baki da lafiya, meya faru dake, ina ki ka je, ki ka barmu cikin tashin hankali da damuwa?” “Ruwa. Zan sha ruwa. Ki bani ruwa Salmah, ina jin ƙishi.” a hankali ta yi maganar da yanayin da ya kara tabbatar musu tana jin jiki sosai. Salman da ke tsaye ne ya yi saurin nufar kitchen ya dauko ruwan baban gora da cup, Ammie ta amsa ta tsiyaya mata ta bata a baki.
Yadda ta karbi ruwan ya kara ɗaga musu hankali, har tana riƙe hannun Ammie da kyau tana kara tura kofin a bakinta , kafin sakan biyar ta shanye, ganin haka yasa Ammie ta kara mata, nan da nan ta kuma shanyewa, karshe sai ta kafa mata goran a baki, sai da ta ga bayanshi, sannan ta shiga sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri. Duk ido suna zuba mata kowannensu zuciyarsa na bugawa. Sai da ta ɗan shiga natsuwarta, Ammie da dauriya kawai take yi tun ɗazu ta sake cewa “Mene ne ya faru Aysha? kin barmu cikin zulumi?”
Ɗagowa ta yi ta zubawa Ammie kumburarrun idanuta da suka koɗe suka rine tsabar kuka, kwarjini Ammie ta yi mata, ta kawar da kai da sauri, bakinta ya fara rawa, fuskarta ya kwaɓe alamar wani sabon kuka na shirin kwace mata, cikin rawar murya ta ce, “ Am...mie, Ba..ban..gi.” sai kuma ta datse zancen ta fashe da wani irin kuka, mai tayar da hankali.
Ya Salam! Idan ka kalli fuskokin, Salman Salmah, da Ammie a lokacin sai ka tausaya musu, “Babangida?” A ruɗe Salman ya faɗa cikin sigar tambaya kamar ya san wa take nufi. Ta gyaɗa masa kai. Cikin tashin hankali Salmah ta ce “ Kin gan shi ne, me ya yi miki?” “ Wane ne kuma Babangida? Ammie ta furta ita ma. Ɗagowa ta yi ta kallesa duk sai suka bata tausayi, maimakon ta basu amsa sai ta sake kife kanta a jikin Salmah ta saki kuka, “Don Allah ki yi magana Aysha.” Ammie ta faɗa muryarta a raunace, “Ku barta!” Su ka ji muryar Abie yana faɗa cikin bada umarni, duk daga kai suka yi inda suka jiyo sautin, shine yake saukowa daga upstairs jikinsa sanye da jallabiya, da alamar ba yanzu yake a cikin gidan ba. “Ku rabu da ita, kada wani cikin ku ya kara takura mata da tambaya, tunda dai ta dawo lafiya shikenan Alhmdlh.” Ya sake fada bayan ya gama sakkowa. Yadda ya yi maganar cikin tsare gida yasa ko Ammie bata iya kawo masa wargi ba balle su Salmah, sai dai ta dinga binsa da wani irin kallon tuhuma wanda shi kaɗai ya fahimci mai take nufi, sai ya dauke kai ya ki bata damar hada ido da shi, kallon Salman ya yi ya ce, “ Mu je.” Ba musu Salman ya bisa a baya suka fice daga falon domin zuwa Masallaci, su sallaci sallar magribar da har an tayar a wasu wuraren. Kallon Salmah ammie ta yi ta ce, “ Ku je ɗaki, ni ma bari na yi sallah.”
Dakyar Aysha ta iya karasawa dakinsu, har sai da Salmah ta tallafa mata, suna shiga ta sulale ta zauna a bakin gado, ita kuma Salmah ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, a kwance ta same ta ta kudundune tana rawar sanyi, da hanzarin ta karasa, ta na faɗin “ Subhanallahi, jikin ne?” ta miƙa hannu ta taɓa wuyanta, da sauri ta dauke saboda zafin da ta ji, “ Ya Salam! Sannu Sister, bari na kira Ammie.” riko mata hannu ta yi a wahalce ta ce, “ Ki lulluɓeni ina jin sanyi.” fankar dakin ta kashe, sannan ta dauki bargonsu na kwanciya ta ninka shi ta lulluɓa mata, kafin ta fice daga ɗakin a gurguje, ta isa dakin Ammie bata idar ba, don haka sai ta dauki dadduma itama ta shimfida ta tayar da tata sallar, kusan tare suka idar da Ammie wanda ta daura da nafila bayan ta sallame farillah. “Ammie jikin Aysha ya yi tsanani.” ta ɗaura da labarta mata yadda ta barota. “ Ya Salam!” Ammie ta furta tare da miƙewa. A tare suka koma ɗakin, tana nan yadda Salmah ta barta a kwance.
Ammie ta ƙarasa bakin gadon da sauri, ta zauna gefen Aysha tana kallonta fuskarta dauke da damuwa, cike da ƙwarewa akan aikinta, ta dora hannu a goshinta, sai ta ɗan lumshe ido na wasu sakanni alamar tana tantance yanayin zafin jikin.
“Zazzabi ne mai tsanani…” ta faɗa a hankali.
Ta juya ta kalli Salmah da ke tsaye cike da tashin hankali, “Ki ɗauko min thermometer daga drawer na ɗakina, sannan ki kawo towel da ruwa mai ɗan sanyi.”
Ba ɓata lokaci Salmah ta juya da gudu.
Ammie ta dawo da hankalinta kan Aysha, a hankali ta ɗaga kanta ta ɗora akan cinyarta, tana shafa kanta a hankali kamar ƙaramar yarinya.
“Aysha… ki kwantar da hankalinki… kina tare da mu…” ta faɗa cikin sassanyar murya mai cike da tausayi.
Numfashin Aysha na fita da sauri, jikinta na rawa kaɗan-kaɗan, wani lokaci kuma tana motsa leɓɓanta kamar mai son magana amma kalmomin na makalewa.
Salmah ta dawo da kayan da Ammie ta nema, cikin sauri Ammie ta amsa ta saka thermometer a bakin Aysha, sannan ta karɓi towel ɗin ta tsoma shi a ruwan sanyi, ta matse shi sannan ta fara goge goshinta da wuyanta a hankali.
“Zazzabin ya tashi sosai…” ta faɗa bayan ta duba thermometer.
Ta miƙe kaɗan ta buɗe jakarta da Salmah ta dauko mata ta ciro magani, ta ɗauko cup ta zuba ruwa kaɗan.
“Salmah ki taimaka ki ɗaga ta kaɗan.”
Suka haɗa kai suka ɗaga Aysha, Ammie ta saka mata maganin a baki a hankali tana cewa, “Ki haɗiye Aysha… zai rage zafin jikin…”
Da ƙyar ta iya haɗiyewa.
Bayan ta mayar da ita ta kwantar, Ammie ta ci gaba da goge jikinta da towel ɗin sanyi, lokaci zuwa lokaci tana duba numfashinta da bugun zuciyarta.
“Ba zazzabi kawai ba ne…” ta faɗa a hankali kamar tana magana da kanta, “akwai firgici da tashin hankali a jikinta…”
Ta juya ta kalli Salmah, “Kada ki sake tambayarta komai yanzu. Abinda ta fuskanta ya girgiza ta sosai.”
Salmah ta gyaɗa kai tana share hawaye.
Ammie ta ɗan yi shiru kafin ta sake cewa, “Zan zauna da ita yau. Idan zazzabin bai sauka ba, sai mu kai ta asibiti da safe.”
Ta koma ta zauna kusa da ita, tana riƙe da hannunta a hankali, tana jin yadda zafin jikinta ke raguwa a hankali.
Wani irin kakkarfar ajiyar zuciya Aysha ta saki, sai kuma laɓɓanta suka buɗe a hankali ta furta “baa...shi...ba... ne. Na.. ga.. ni.. da.. ido...nahhh....”
Ta yi maganar a rarrabe, amma hakan bai hana Ammie da Salmah fahimta ba, da sauri suka kalli juna.
Dai dai lokacin Salman da Abie suka shigo ɗakin, dakyar suka iya jira har aka isar da Isha kafin su ta so, gabaɗayansu hankalinsu na kan Aysha, “Dacta Jikin ne? ” Abie ya furta muryarsa a raunane, “E zazzaɓi ne mai tsanani, sannan akwai firgici sosai a yanayinta, kamar wanda ya ga wani abu mai razana.” Numfashi ya furzar kafin ya sake cewa
“Ta faɗi wani abu?”
Ammie ta ɗan tsura masa ido kafin ta ce, “Eh… amma ba a fili ba.”
Salman ya matsa kusa da Aysha yana kallonta da tausayawa ya ce “Me ta ce Ammie?”
Salmah ta kalli Ammie kamar tana neman izini, sannan a hankali ta ce,
“Ba shi ba ne. Na gani da idona…”
Duk shiru suka yi kowa na nazari kafin Abie ya kashe hakan da faɗin, “Allah ya ba ta lafiya ya kawo mata haske a cikin rayuwarta, hakika ta ga jarabawar rayuwa kala kala, ina fatan gobenta ya yi kyau fiye da zaton mai zato.”
Idanu Salmah ta lumshe ta bude a hankali, tana mai jinjina kalaman Abie domin bayan shi ita ce mutum ta biyu da tasan hakikanin wacece Aysha. Yayinda Ammie da Salman suka amsa da Amin............
Shin wai wacece Aysha, me ya faru da rayuwarta, da gaske AA shine Babangida ko kuwa dai ya abin yake?