RAGAYAR DUTSE

Official thriller

by @nanahaleema11

*RAGAYAR DUTSE.*

*Nana Haleema*

*Official Thriller*

*A 2026 Novel.*



*Daga marubuciyar, KWANTAN ƁAUNA, BAYA DA ƘURA, KIRAN RABO, MAI ƊAKI....*


***



"Are you out of your mind? Duk bathrooms ɗin da suke apartment ɗin nan, you could'nt find one to use except the public one in the main palour?. What kind of nonsense is this?."


Islaha ta ɗago ta kalle sa jin yadda yake yi mata magana cikin kaushi da zafi, bata taɓa jin muryarsa a haka ba, bata taɓa ji ya yi magana mai ƙarfin wannan ba. Ko yaushe magana yake yi cikin steeze, yana yi yana basarwa. Amma yau ta ji akasin haka, har yana shouting.


Bata motsa daga inda take ba, duk kunya ta gama mamaye mata idanunta ta ce, "don Allah ka bani waje in shirya, bana so kana shigowa inda nake  anyhow. Ka san dai ni ba muharramar ka bace, zuwa inda nake without permission haram ne."


Tsabar takaici bai san ya riƙo hannunta ya miƙar da ita tsaye ba. Bata yi zato ba zai yi hakan ba ko kaɗan, ta yi saurin riƙe towel ɗin jikinta, jin zai kwance.


Ya ce, "baki ji me na ce miki ba? Ina yi miki magana akan shirmen da ki ka yi kina yi min maganar na shigo ɗaki without permission?." 


Islaha ta bi sa da kallon mamaki, ita dai bata ga abin ɓacin rai haka daga wajansa ba, ita ta yi tunanin bazai ji haushi ba, ita ce zata ji haushi, tunda jikinta aka gani ba nasa ba. Meye dan wani ya ganta tana wanka zai ɗaga hankalinsa haka, kamar ya ga matarsa ko wata ƴar uwarsa?. 


Ita kunya take ji ta rufe ta, daga ita sai ƙaramin towel a tsaye, ga kanta ko ɗankwali babu. Ta ɗan juya baya da nufin ta ɗauko hijjab, ya finciko hannunta ya dawo da ita ta baya. 


Kafin ta ce wani abun ya ce, "dan kin saba yin hakan a wani wajan, shiyasa za ki yi a nan?." 


Bata yi niyar tanka masa ba, amma jin abinda ya ce sai ta kawar da duk abinda take ji, ta danne duk wata kunya da firgici ta ce, "tunda ka san na saba meye na zuwa ka same ni kana yi min shouting? Yau wani ya saba ganina ina wanka, ko ka manta har ta ya ni wankan ana yi?."


Duk da babu haske sosai a ɗakin, tana iya ganin yadda fuskarsa ta canja kamar ba shi ba. Ita wallahi mamaki yake bata, ko ina ruwansa oho.


Ta cire hannunsa da ya riƙe hannunta ta ce, "kar ka sake riƙe hannuna na faɗa maka, ka daina ƙoƙarin taɓa jikina. Ina ruwanka dan ya ganni ina wanka? Kai ya gani kana wankan, ko matarka ya gani, ko ƙanwarka ya gani da zaka damu har haka?."


"Na ga dai Islaha ya gani tana wanka ba kai ba ko, to meye na damuwa har haka?. Ai ba yau na saba ba, ka manta na saba zama dashi, ko ka manta kafin shi akwai maza da yawa da suka ganni a irin yanayin da ya ganni?."


"Meye naka, abu ne da na saba wannan ba komai bane a wajena. In na ga dama zan kwance towel ɗin jikina in fita kan titi, rayuwata ce ba taka ba, jikina ne ba jikinka ko na matarka ba. Kaf mutanen duniya in na yi niya zan iya nuna musu jikina, kuma bai shafe ka ba, tunda ba aurena ka ke yi ba."


Ka bani waje don Allah, ka kuma daina yi min ihu. Babu ruwanka da duk abinda zan yi, rayuwata ce ai ba rayuwarka. Ka je waje!" Ta faɗa bata yarda sun haɗa ido ba, tana nuna masa ƙofar da zai fita daga ɗakin.


Gabaɗaya ta kashe masa baki, ya kasa magana sai kallonta da yake yi. Bai san abinda ya saka yake jin zuciyarsa tana zafi akan kalamanta ba, ya san dai gaskiya ta faɗa, ta saba wanka da maza, shi shaida ne akan hakan, amma bai san dalilinsa na jin haushi ba. 


Daƙyar take iya jurewa take komawa mara kunya a gabansa, tunda a haka yake kallonta bata so ta canja masa tunani, shine ya saka ta zama haka ta ƙarfi da yaji, bata so ta canjawa mutum tunanin da yake yi a kanta. Tunda ita ƴar iskace a idanunsa, aje a hakan.



Maganarta ce ta dawo da dashi daga duniyar tunani, ya ta ko ya zo kusa da ita daf da daf, yana kallon fuskarta ta ƙaramin hasken ɗakin ya ce, "mazan kan titi zasu iya ganin ki, haka ki ka ce ko?." 


Yadda ya yi maganar sai da gabanta ya faɗi, gashi ya matso kusa da ita daf da daf, ga shi daga ita dai towel. Ta ɗan ja baya kaɗan ta ce, "zasu iya, kowa ma zai iya. Babu ruwanka."


"Kowa ma zai iya!" Ya furta yana cize bakinsa, cikin wani irin yanayin da bai taɓa jin irinsa ba. 


Ya ɗan girgiza kai yana kallonta, kafin ya yi ƙasa da muryarsa, cikin soft vioce ya ce, "tunda kowa zai iya ban ga amfanin rufe jikinki ba. I can also see you without a towel" ya faɗa yana zagawa da hannunsa bayanta, ya asaka hannunsa a inda ta ɗaure towel ɗin ta baya, ya ja shi da ƙarfi ya zare shi gabaɗaya.


*******


Ya ce, "Yauwa. Za ku kawo kuɗin ko mu kashesa? Baza mu ƙara mu ku lokaci ba, in dai ba a kawo kuɗin nan ba, sunan ɗanku gawa!."


Baffa zai yi magana Islaha ta firgita ta fizge wayar, cikin kiɗima da tashin hankali ta ce, "Kar ku kashe sa, zamu kawo mu ku in sha Allah. Kar ku kashe Hamma. Ku ƙyalesa zan nemo kuɗin na kawo." 


Islaha ta cillar da wayar, jikinta yana rawa kamar wacce aka jonawa wutar lantarki. 


Ta gyaɗa kai tana kallon Baffa ta ce, "Baffa zan nemo kuɗin, zan yi komai saboda Hamma." 


Baffa ya riƙe kafaɗunta ya ce, "ba ki da hanyarsu Islaha, ba naira dubu tamanin aka ce ba, ba dubu ɗari takwas aka ce ba, ba miliyan takwas aka ce ba. Miliyan tamanin suka ce. Miliyan ɗaya sau tamanin, baki da hanyar da zaki samu. Ki karɓi ƙaddara kawai. Ba a kansa aka fara kashe mutane ba, shima ki bari su kashe shi ya fi alkhairi."


"Bazan iya ba Baffa, zan nemo kuɗin a ko ina ne, na yarda zan yi ko me ye indai zan samu kuɗin fansar rayuwar Hamma!" Ta faɗa tana fita a guje.


Baffa ya ce, "Sadik bi bayanta don Allah." Da sauri ya bi bayanta, ya samu zata fira daga gidan, ya yi sauri ya cimma mata. Ya ce, "ina za ki je?."


Murya tana rawa tana kuka ta ce, "zan je na samo kuɗin ne."


"A ina zaki samu? Baki da hanyar da zaki samu wannan kuɗin." 


Sai ta fashe masa da sabon kuka ta ce, "haka zan bar Hamma kenan a kashesa a banza, haka zan bari Hamma yana neman taimako na ƙyalesa?. Ni bazan iya ba, wallahi bazan iya ba" ta faɗa tana rufe fuskarta da hannunta tana kuka sosai.


Sadik ya ce, "haƙuri za ki yi, babu abinda za ki iya a kai" 


Bata ce komai ba sai kuka, sai da ta ga ji sannan ta ta kalle sa ta ce, "ina da mafita, ban sani ba ko za ka bani goyan baya akan hakan." Ya kalle ta ya ce, "indai hanyar bata saɓawa addini ba zan amince, ina jinki." Ta ja numfashi ta sauke, ta rufe ido ta buɗe tana kallonsa cikin jin nauyin abinda zata ce.



********


Jikinta rawa yake yi, ga sanyin a.c da ya yiwa yanayinta yawa, ta cure a waje ɗaya tana kuka mai tsuma zuciya.


"Na shiga uku, na shiga uku. Ina zan saka kaina, me na aikata haka, ya aka yi na bari hakan ya faru?......" ta sake fashewa da kuka, ta riƙe bedsheet tana ji kamar ta shige ciki saboda rashin sanin abinda zata yi, ta juya kai ta ce, "My dignity gone for no reason. My life is a mess already, my life is scattered.......me na yi, me na aikata, What i have done to deserve all this, Why!" Ta faɗa tana kuka sosai wanda sautinsa yake fita. 


Wani irin juyi take yi tana kuka, zuciyarta tana bugawa sosai. 


"Na yiwa Hamma alƙawari, na ce zan riƙe masa kaina, amma kasa cikawa, na kasa. Ka yi haƙuri Hamma, ka yi haƙuri! Ba a son raina bane. Na yi duk saboda kai, saboda kai ne Hamma!" Ta kuma faɗa kamar yana gabanta tana kuka mai tsuma zuciya.


*******


Daidai lokacin da hawaye ya sakko daga idanun Islaha, muryarta tana cracking ta ce, "Hamma!." 


Ya lumshe ido yana jan numfashi daƙyar, ya buɗe ido ya sake kallonta ya ga tana kuka sosai hawaye wani yana bin wani.


A hankali ya ja da baya, zai rufe ƙofar ta yi hanzarin tarewa ta hana shi rufewa, tana girgiza masa kai ta ce, "Hamma ka tsaya ka saurare ni, kar ka yanke min hukunci cikin fushi. Ka tsaya ka ji abinda zan faɗa maka, na san na ɓata maka rai amma ka tsaya ka ji uzurina, na tabbatar zaka fahimce ni. Don Allah Hamma ka dakata, kar ka riƙe ni a ranka. Wallahi saboda kaine, saboda ceton rayuwarka ne!."


Kasa rufe ƙofar ya yi, ya lumshe ido yana jin yadda take magana cikin kuka da rawarta tana murya. 


Ya buɗe ido bai kalle ta ba, ya sake ƙoƙarin kulle ƙofar ta buɗe ƙofar da ƙarfi, ta shiga ta tsaya tana kallonsa. 


Ta haɗe hannayenta guda biyu ya ce, "na san na yi kuskure, na san kana jin zafi a ranka, amma don Allah ka yi haƙuri, ka tsaya ka ji abinda zan faɗa maka, na tabbatar zaka fahimce ni."


"Ba na faɗa miki ki bari su kashe ni ba, meyasa ki ka sadaukar da rayuwarki a kaina, Islaha!."


"Bazan iya bari a kashe ka ba Hamma, zan iya sadaukar da raina a matsayin a kanka! Shiyasa...shiyasa..shiyasa...kawai na amince.....na karɓi.....kuɗin......"



"Babu abinda za ki ce min Islaha! Kin ɓarar da yarda da na yi miki, kin lalata amincewar da na yi a kanki! Ki fita ki bani waje, bana son ganinki!" Ta faɗa cikin murya mai amo yana nuna mata hanya.


Safeera ta goge idanunta, ta dafa kafaɗarta ta ce, "tashi tsaye Islaha." 


Ta miƙe a hankali ta kalli Safeera ta ce, "Na faɗa miki daman ni ba ƴar halak ba ce, jikina yana bani a......" 


Safwera ta rufe mata baki ta ce, "kar ki ƙara faɗar haka. Allah ya san zuciyarki, nima na san silar abinda ki ka aikata, Sadik ma ya san dalilin yin. Mu mun san rayuwarki ki ka sadaukar saboda Saheer, shima kuma zai amince ki, amma na faɗa miki sai ya nutsu sosai."


Islaha ta kwantar da kanta a kafaɗar Safira ta ce, "Ko magana yaƙi ya yi min, yaƙi ya kalle ni. Na yi dansani ya fi cikin kwando Safeera." 


Ta ɗan tapping bayanta ta ce, "ki yi haƙuri, ki daina kuka. Allah yana tare dake." 


Ta goge hawayenta bata ce komai ba, ta ɗauki handbag ɗinta, sai kuma ta dafe kanta saboda yadda ya sara mata. Ta ce, "Kaina yana ciwo, mumfashina baya fita daidai."


Safeera ta ce, "babu lafiya kam. Tun ƙarfe bakwai da rabi tana unguwar nan, ta zo wajan Saheer amma ya gaza fahimtarta." 


Sadik ya ce, "Islaha Saheer bazai fahimce ki yanzu ba, Saheer ba a nutse yake ba kwata-kwata, yana buƙatar lokaci kafin ya gane abinda zaki faɗa. Abu ɗaya yake kallo a yanzu, kin ci amanarsa, kuma su Mama suma sake ɗora shi akan hakan. Dole sai kin sake haƙuri na wani lokaci. Ke kin san halinsa, na tabbatar zai amince dake da zarar ya nutsu yadda ya kamata."


Safeera ta ce, "amma ni ya bani mamaki, ai ya san wacece ita ko? Ya san duk a kan karɓo shi daga hannun masu garkuwa da mutane ta aikata abinda ta aikata."


"Ba goyan bayansa nake yi ba Safeera, amma ina so ki tuna abinda ta aikata saboda shi. Yana jin zafi a ransa, yana jin haushinta, ni dake ne kaɗai muka san abinda yake faruwa shi bai sani ba. Ku bashi dama ya huta tukunna, in ya huta zan yi masa bayanin komai daki-daki."


*******


Baƙin ciki ya mamaye mata zuciya, ta miƙa masa wayar, ta miƙe tana zaga falon cike da tunanin mafita. Ta rasa yadda zata yi da Rehaan, kuɗin da ya kamata ace ƴaƴanta ne suka yi shine yake mallakarsu. Hakan yana taɓa zuciyarta, yana sakawa mata baƙin ciki da hassada. 


Mama ta ce, "ya aka yi haka yake faruwa, Ya aka yi abubuwa suke jagule mana ne Sameer?. Rehaan fa, kai kanka ka girmesa da shekara ɗaya. Ya aka yi yake samun ɗaukaka, bayan ku ne manya a cikin gidan nan?." 


Sameer ya ce, "wallahi zamansa a england babbar illa ce a gare mu, ni ban yarda ba dukiyar Abba ce a hannunsa ba. Ta ya yaro ƙarami ace ya mallaki abinda mahaifinsa bashi dashi, Hamma Zayyad da yake babba bashi dasu, mu ma da muka biyo baya bamu dashi. Kina jin wannan kin san haɗawa aka yi, gabaɗaya dukiyar Abba tana hannunsa, mu muna nan an haɗa mu da ƙananun abubuwa na banza. Babu damar mu yi magana sai ace ai shi a nan ya girma ba, shi a a can aka haifesa, a can yake kasuwancinsa da sauran shirme. Mama in muka zuba ido, kaf dukiyar Abba da take can zata zama haram a gare mu."


Mama ta girgiza kai ta ce, "ya aka yi hakan yake faruwa, ya aka yi abubuwa suke lalace min ne?. Meyasa na kasa ɗaukar mataki akan Rehaan, meyasa yake shigar min hancina na kasa fato shi?." 


Sameer ya ce, "dole a san abinda za a yi, bazai yu kina babba a gidan nan, muna manya a gidan nan, ace komai yana hannun Rehaan ba, dole ki san yadda zaki yi ya dawo nigeria, in ba haka ba wallahi muna ji muna gani komai zai fi ƙarfin mu."


"Ƙarya ne wallahi, yadda ku ka kasance manya a gidan nan babu wanda zai samu ɗaukaka sama da ta ku, dole a dakusar da ɗaukakar Rehaan, dole Rehaan ya dawo ƙasar nan.."



"Ɗaukaka ta nawa kuma Mama? Sunan Rehaan da labarin Ray ina ne bai shiga ba a faɗin ƙasar nan?. Sai dai a kiyaye gaba, amma wannan ya riga ya faru. Kai tsaye ki samu Daada da wannan maganar, dan ita kaɗai ce zata zama silar dawowarsa ƙasar nan har abada."


Ta girgiza kai cike da gamsuwa ta ce, "yanzu nan zan je na same ta, indai a kan ganin bayan ɗaukakar Rehaan ne babu abinda bazan yi ba Sameer, zan iya sadaukar da duk abinda na mallaka dan ganin Rehaan ya dawo ƙasa, ku kun hau sama."


Sameer ta miƙe ya fita cikin gamsuwa sa kalamanta. A ganinsa ta ya ya suna manya a gidan, ƙaraminsu wanda ya zama shine namiji ƙarami a kaf gidan, ya zo ya fi su ɗaukaka.


 Mama kuma ta dafe kai cikin rashin mafita, a bayyane ta ce, "Rehaan! Rehaan! Rehaan! Ka shiga rayuwata, ka hanani sakewa Rehaan, ka hanani cika burina....."


Ta girgiza kai ta ce, "Baka isa ba wallahi, baka isa ɗaukakarka ta disashe ta ƴaƴana ba, yadda na kasance gaba da kowa a matan gidan nan, dole ƴaƴana su kasance gaba da kowa a yaran gidan nan. Babu wanda ya isa ya sha gabansu, su ɗin su za a kalla aje ace su bayar, ba kai ba. Tun kana yaro ka ke bani wahala, amma a yanzu bazan barka ba Rehaan, bazan taɓa barin ka ba."


******


Maimakon ta bashi amsa sai ta fashe da kuka. 

Baffa ya ce, "ki bar kuka Islaha."


"Baffa ni ban san yaushe aka yi min video ba, wallahi ban san an yi ba."


"Ki daina kuka, Hamman ki ya faɗa min an shigar da ƙara, za a nemo wanda ya yi wannan aika-aikar." 


Hawaye ya zubo mata ta ce, "kowa maganata yake yi, ana ta tsine min Baffa. Kowa ya ga tsiraicina a duniya, kowa a fanko yake kallona Baffa. Zuciyata zafi take yi min."


"Ki yi haƙuri Islaha, ki daina kuka, Allah yana tare dake a ko yaushe. In ma an yi wannan abun da a tozarta ki Allah bazai bari ki tozarta ba, zai baki kariya in sha Allah."


"Baffa ai na tozarta, an gama tozarta ni a duniya. Baffa ji nake kamar na kashe kaina na huta, so nake na daina numfashi ko zan ji daɗi Baffaaaa!" Ta ƙarasa faɗa tana jan sunansa cikin kuka. 


Hamma da yake kusa da Baffa ya ce, "Islaha ki nutsu, komai zai warware. Ni na tabbatar ba ke bace." 


Ta ce, "Hamma ni ce, ni ce fa Hamma. Ni na san wannan jikina ne, ban san yaushe na aikata zina har aka yi min video ba. Shikenan an gama wulaƙanta ni Hamma, an cuce ni Hammaa!."


"Ya isa haka, ki daina faɗar wannan kalaman babu daɗin ji. Ki nutsu, zuwa nan da gobe komai zai zo ƙarshe." 


Islaha ta ce, "Safeera nuna min video nan don Allah." 


Safeera ta ce, "babu amfanin ganin Islaha, zai sake ɓata miki rai ne."


"Ina so in gani, ki bani."


"Bazan bayar ba, ki zauna." 


Islaha taƙi zama ta ce, "In kina ƙaunar Allah ki bani."


"To meye abin gani a video?."