NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)

CHAPTER 21 ( Getting to know him)

by @deejasmah

Had'e fuskarsu guri d'aya yayi cikin fitar hayyaci, ya shiga aikata duk wani abunda zuciyarshi ta raya masa. Duk mutsu-mutsun k'wacewar da takeyi ya hanata hakan don duka k'arfinshi ya sanya wurin rik'etan, tun tana da k'arfin kokawar har ya ci k'arfinta ta tsaya cak tana karb'ar sak'onninshi batun ma bata da tsarki ta manta shi.



Sosai lamari yayi nisa don d'aukarta yayi zuwa cikin bedroom, hijabinta ko da nightienta tuni suka fice da mugun sauri. Cak ya dakata da abinda yake yi jin tudun pad, idanuwansa da suka gama juyewa ya bud'e a wahalce don dubawa ai ko dai shi ne har ma ya karkace saboda azaba. Wani irin rawa jikinshi ya soma yayinda ya zura mata idanu yana mai binta da kallon takaici don ya riga da ya kai k'ololuwar buk'ata, muradi da kuma sa rai. Sai kuma ya janyota jikinshi yana mai k'ank'ameta kamar zai b'allata gida biyu hawayen wuya suna gangarowa daga idanunshi, k'ara ta sanya jin yadda ya fisgeta ya kuma cukwuikuyeta kamar ya samu takadda ko wata mara k'ashi a jiki.




Ba ta da k'arfin janyewa daga jikinshi musamman ma yadda zuciyar shi take bugawa da sauri, kamar zata b'alla k'irjinshi ta fito na tan ma kusan da irin na shi yake gudu a lokaci ɗaya kuma jininta yana zuwa kamar an koro shi. Lafewa kawai tayi a k'irjinshi cikeda tausayi, sun d'auki kusan 30 minutes kafin ya janyeta daga jikinshi yana sauka daga kan gadon.




Haske ya kunna nan take ko ya gauraye d'akin sakamakon bulb da ya kunna, kifa cikinta tayi ta juya baya. Ko kallonta bai yi ba saboda takaicin abinda tayi ya wuce toilet, ruwan sanyi ya juye ma kansa idanuwan nan a lumshe. Sai da ya d'auki time mai tsayi a k'asan shower d'in har sai da ya samu relief na abinda yake ji kafin ya d'aura towel ya fito, har lokacin tana a yadda ya bar ta sai duvet da ta ja ta duk'unk'une a ciki.





Yanzun ma bai kalleta ba ya nufi mirror, goge jikinshi yayi ya shafa cream kafin ya nufi closet pajamas ya ciro mai gajeren hannu da gajeren wando farare tas ya zura bai ko sa buttons d'in rigar ba ya nufi gado bayan ya maida towel d'in toilet.



Kwanciya yayi ba tareda ya ja bargo ba ya tsura mata idanu, sai kuma yayi gyaran murya yana mai cewa " ai sai ki tashi ki bar min d'aki tunda dai babu amfanin da zaki min ko?". A hasale da d'aga murya yayi maganar juyowa tayi ta kalleshi, sai kuma ta kawar da kai da sauri tana zama a kan gadon har lokacin duvet na k'irjinta.



Tsaki ya sake saki yana cewa " ban buk'atar maimaita kaina, ina son inyi bacci ki tafi ki bani wuri!!". Kai ta gyad'a kawai don ta lura yayi fushi sosai a hankali tace " i'm sorry".



"Riƙe kayan ke, ke kenan kullum sorry-sorry? Baki gajiya da fad'inshi bayan kina sane kika yi abinda kika yi, wulak'anta ni kika so yi kuma kin yi hakan meye kuma amfanin dawo da shi baya?". Ya furta kamar zai kai mata mangari.


Cewa tayi " tun ɗazu na so gaya maka sai dai baka bani damar hakan ba, wata riba zan ci idan na wulak'anta ka Yaa Islaam? " ta k'arashe a hankali, cikin ko in kula yace '' in ba wulak'anci ba ne me kika yi? Kin kyauta ai ribar da kika so samu kuma kin sameta da fatan kin ji daɗi?". Girgiza kai tayi ganin ba wani amfanin yi masa bayani a yanzu tunda ya riga ya hau dokin na k'i, sauka ta fara k'ok'arin yi daga gadon tana adduar Allah ya bata ikon ganin rigar baccinta ko hijabi.



K'wafa ya kuma saki wato ga mahaukaci yana mata magana tayi banza da shi ko? Ko da yake ba laifinta ba ne ai, na shi ne shi da ya nuna har tana da wani abu da zata iya jan hankalinsa gareta da bai nuna ba da duk haka ba ta faru ba. 'Da kuma yanzu kana shirin barin duniyar ai, kuma ai ma ba k'arya ba ne ta ja hankalin naka kanta you gotta deal with that' ya bawa kan shi amsa yana mai cije baki, d'an satar kallonta yayi ya ga tana ta cuku-cuku da blanket ya bud'e baki kamar an masa dole yace " ohh fita zaki yi ba tareda kin bani hak'urin ba ko?".



Dafe kai tayi tana mai duk'e jikinta don Allah ya ba ta ikon ganin hijabi, sai da ta zira kafin ta d'ago tana cewa " toh ka yi hak'uri please". Cike da shakiyanci yace " ai ba wannan hak'urin nake so ba, ɓata min rai kika yi ki zo ki saka na daina yin fushin" yana mai kashe idanu, kasak'e tayi tana mai mamakin halayyar Islaam yanda ka san wani hawainiya ya juya a sanda ya so ya kuma sake sauyawa a sanda ya so.



Tace " ta ya zan iya goge maka ɓacin ran?". Zare idanu yayi sai kuma ya k'ank'ancesu yana mai cewa " ohh really, baki sani ba? Zo nan in nuna miki". Daskarewa tayi a wurin ta kasa ko motsi, shi ko ko a jikinshi sai ma hannuwanshi da ya mik'o mata alamun ta kama. 




Yanda tayi ne ya tunzura shi don bai wani cika son jan rai ba, doguwar tsaki ya ja yana cewa " kin san me? Fita kawai ". D'aga k'afa tayi da niyyar zuwa inda yake tana cewa " sor.......". Dakatar da ita yayi ta hanyar d'aga mata hannu da daka tsawa da dukkan muryarshi yace " OUT!!" Ai ko da sauri ta juya ta fice daga d'akin, tsaki ya sake ja yana mai cewa a fili " don taga ina janta a jiki zata wani kawo min iyayi, da wani busasshen jikinta kamar cray fish in ba ma kwad'ayi ba miye a wurin da zai wani ɗaga maka hankali?".




Abun dariya wai yaro ya tsinci hak'ori ka san ba abun da zaa tsinta a jikin nata ne ka susuce har da fita hayyaci a kanta? Ai size doesn't matters da babba da k'arama da chubby da siririya in dai har balbela zata biya buk'ata ai ungulu sai dai ta koma gidanta na tsamiya.



Ko da ya kore tan ya sha zai samu salama ne, amma kamar yadda ya saba kwana tunaninta yau ma hakan ce ta kasance ko ma fiye tunda yau ya ganta zahiran d'inta. Wanda ba k'aramin taimakawa yayi ba wurin tunzura hauhawar buk'atuwarshi a kanta ba, har mantawa yayi da shi ya koreta ba wani ba. Damuwar da ya shiga a daren ya ninka na kullum, kuma ya k'ara farashin haushinta a ranshi kai har haushin kanshi ranar sai da yaji haka ya kwana juyi da imaginations na scene d'in d'azu yau ko arzikin barcin bai samu ba sai da yayi sallahr asuba tukunna ya d'an kwanta cikeda d'acin rai.




Ita ko tana komawa d'akinta wanka ta sake don tana buk'atar hakan, ta chanja pad cikeda mamakin mai ya kawo period d'in ta yau da gudu har haka. Allah ne ma ya taimaketa da bai ma tab'a wandonta ba da sai ya b'ata masa gado, fitowa tayi dafe da mara wanda ba haka ta saba ba tana yin ciwon mara amma bai kai wanda take ji ba a yanzu haka. Magani ta kuma sha ta kwanta a gado da bathrobe d'in , ita ma juyi ta dad'e tana yi don marar ta matsa mata ga kuma pad d'inta da yayi ta cika sai da ta canja sau biyu kafin asuba da sanyinshi ne ma ya sa ta bacci bai tsayi.




Ba ita ta bud'e idanu ba sai 8 da sauri ta dira daga gadon toilet ta shiga ta sakin ma kanta ruwa ta sa pad ta fito, ta nufi sashenshi turawa tayi ta tardashi a gark'ame alamun ya fita. Murmushin gefen baki tayi wato fushin na shi da gaske ne, gyad'a kai tayi ba ta ma koma ciki ba ta fara ayyukanta na cikin gida a cikin kitchen ta iske kwanukan da ta sa masa abincin daren jiya. 10 ta shirya cikin top da skirt ta zumbula dogon jilbab Maroon a sama bak'ak'en sneakers ta sanya da handbag d'inta ita ma bak'a ta vinci ta fita bayan ta kulle gidan.



Yau dai aiki ya mata yawa don suna shirin yin Ramadhan discount na kayayyaki saboda bayan sallah za ayi sababbin zubi ga kuma Ramadhan special package da suke yi na turarukan wuta na muhalli da kayan jiki, ga kuma kyaututtukan da suke bayarwa na dabino, counter, carbi da alk'urani mai girma ga customers d'in su. Wanda daman ta kanyi hakan duk shekara tana kaiwa makarantun islamiyya a can cikin unguwannin masu k'aramin k'arfi har ma da littafan addini da na rubuta, shirya kayayyakin promon tayi ta rubuta su tsaf da kud'ad'ensu. Content ta so yi amma ba time don 3 har tayi kuma 4 take tafiya, sai kawai ta d'auki hotunansu da niyyar in ta je gida sai tayi voiceover.



Tattara komai tayi ta maida shi wurinshi sannan ta tarkata jakarta zuwa gida, sallama tayi da staffs d'inta ta sauko k'asa. Suliem ta lek'a nan tarda Zulfaa kwance shame-shame kamar wadda akaiwa duka, dariya ta sanya mata tana cewa " wai meye haka kike ta wani zare idanu kamar wacce take nak'uda? Tun abun bai zo ba har kin sare ga kuma azumi yana tafe ".



Harararta tayi tana cewa " dariya ko? Ai da yake kema naki yana tafe za kuma ki ji mai kowa yake ji, gwara kowa ma da ke mai shegiyar raki ". Gwalo tayi mata tana cewa " ai yanzu rakin naki ne ya riga nawa bayyana Madam". Girgiza kai tayi tace " hehehe, ni ai ba biye miki zan yi ba don lokaci zai gaya miki wannan uban glowing d'in da kike yi kullum ai ba a banza ba ne ki. Laulayi ma kad'ai ya isheki ki gane Allah d'aya ne".


Suliem ce tace " bar ta dai, yarinya kwana nawa ne zaki ji maza iya maza? Gwara mu a tare muka yi ke kuwa sanda zaki yi na ki duk mun juye sai dai muyi ta miki sannu ". Zulfaa tayi caraf tana cewa " sai dai in kece zaki yi mata sannu, amma ni ai tuna mata da baya zanyi in rama tsokanata in more ". Turb'une fuska tayi tuno abinda ya kusan faruwa jiya, da fa yanzu tana da tsarki da k'ila ma har ta samu ciki ko?. Cewa tayi '' wannan dai mugun fata ne kuma babu kyau, ni kun ga ma tafiyata Allah ya baku hak'uri ya kuma raba lafiya ''. 





Ta k'arashe tana mai juyawa, me zasu yi in ba dariya ba ganin yadda ta rud'e kamar wacce aka ce wa ga wani shahararren abin tsoro. A nasu tunanin zancensu ne ya tsoratata ita kuwa nata tsoron mai zaman kan shi ne, Suliem ta tashi ta biyo bayanta har ta kai stairs saboda sauri. Kiran sunanta tayi ta tsaya tana waigowa cewa tayi " haba Lele ya da gudu haka?" Kumbura fuska tayi tace " ai naga kamar ba shirin tafiya gida kuke yi ba, ni kuma na riga na fito kar bawan Allah ya dawo gida ba na nan". Matsowa Suliem tayi gabanta a hankali tace " amma yanzu ai komai ya daidaita ko?" Don kaf familyn itace ta san wani abu a zaman nasu, tun da tun fari da ita aka hau amsa ta bata da " in shaa Allah, don yanzu yana nuna d'an kulawa a kaina matsalar shi ne kamar dai ita soyayyar ne har yanzu babu ita ".



"Ai in dai akwai kulawar toh ita ma gab take da samuwa, musamman ma in yana nuna son kasancewa dake wannan kuwa k'atuwar dama ce da zaki gina rayuwarku tare ta hanyar sanya shak'uwa mai k'arfi a tsakaninku kin san ita shimfid'a sirri ce mai k'arfi dake gyarawa ko lalata zamantakewa wanda ya dogara da yadda kike kula da buƙatun sa akwai cigaba ta nan d'in kuwa?".



Ajiyar zuciya ta sauke tana mai cewa " tabbas akwai amma ban so in sakin masa jikina bai bai fara so na ba, kenan zai same ni a bulus". Girgiza kai tayi ta dafata tana cewa " ko d'aya wannan ne ma mataki na farko na samun zuciyarshi a tafin hannunki, shin kina tunanin babu son ne a ranshi har da zai so kusantarki? Hmm mutum irin Ya Islaam ba kasafai zai so had'a jiki da wacce bai so ba, don in da zai zo haka da tuni ya wuce wurin tunda ai ba yau bane a kayi auren amma sai yanzu ya fara nuna miki hakan so ki kwantar da hankalinki ki bashi abinda ya so har ma da k'ari. Ki fetsare idanunki ki ba shi abinda ba zai taɓa mantawa da shi ba " ta k'are tana sakin dariyar shakiyanci, baki ta bud'e za tayi magana Zulfaa da fitowarta kenan daga cikin shop d'in tace " wai me ake gulmatawa ne a waje aka barni ni d'aya a ciki kamar wata tsinkakkiyar silifas ". 



Waigowa sukayi a tare ganinta jingine da k'ofar shiga shop d'in ya sanya su sakin ajiyar zuciya a tare, Lelen ce tace " me za a tsegunta, wani batu ne na nemi k'arin haske akai ta kuma bud'e min shi tsaf ". Cewa tayi " ni shi ne ba a bud'e hasken da ni ba? Saboda wariyar launin fata ku a dole sirikai ko?".



Dariya suka saki dukansu Suliem tace " ke ma ai sirika ta ce, matso kema ayi dake meye a ciki na zafi?". Tura baki tayi tana cewa " ba wani nan, ni za ai wa dad'in baki toh ba yarda zan ba". Nadeefah tace " ki matso mana matar Alhaji Farhaan, dama ai tallafin nan sai da manyan Hajiyoyi irinku maganar foundation d'ina ne fa. So nake this time su ma su Baba su shigo ciki Allah ya had'a mu a ladan, shi ne muke maganar yadda zan musu magana ke ma ai zaki kawo naki contributions d'in ko?".



Murmushi ta saki yana cewa " in shaa Allah, kuwa ke dai duk aikin ladan kin bi kin kwashe mu kin mana wayau. Shiyasa kowa yake son ki, ni ma dai ina kishi maganar su Baba ai kawai ki samu Hajjah kin riga da kin gama zancen sai dai ki jira ganin kuɗi na shiga". Cewa tayi " nima ai ina son ki fiye da kowa Zulfaa, sweetheart ke ma zaki iya da ɗan abinda yake hannun ki ki bawa wanda ya fiki buƙata ke ko iyayenki kika mawa sai ki ga Allah ya d'aga ki don kin san ma a sadakar fa kafin ki je ga wasu Allah sai da yace " qul ma anfaqtum min khairin fa lil walidaini, wal aqrabina wal yatamaaa wal masakinaa wab nis-sabeel, wa ma taf'alu min khairin fa innallaha bihi aleem".


Nisawa tayi tana mai cewa " ma'ana ka gaya musu yaa Rasulullahi ( S.A.W) duk wani abu da zaku bada na daga alkhairi to ku bawa iyayenku guda biyu, da makusanta, da marayu, da miskinai da wainda ba su da shi. Lallai kuma duk wani abun alkahiri da kuke aikatawa toh Allah shine masaniii". Ajiyar zuciya Zulfaa ta sauke tana cewa "ai wannan ma ya saka ina jin kishin ki sosai Habibtie komai kin haɗa Ma Shaa Allah, ina so in zama ke idan na girma ".



Harararta tayi tana cewa " abegg, maganar serious muke ban da iskanci". Suliem tace " actually babe mu ma serious muke yi, Allah ya sa bayan cikin nan in na samu wani in haifi mace don sunanki zan saka da fatan Allah ya sa ta gaji halayen ki". Zulfaa tace " toh ai na rigaki Madam, har da kyan nata nake son tayi wallah". Dafe kai tayi tana cewa " toh na barku da halinku, sai anjima zan je in wa mijina tuwo ". Dariya suka sanya, Zulfaa ta rufa mata baya tana cewa " ni ma muje in tafi kin ji, nima zan yi girkin ". Suliem ta rik'e k'ugu tana cewa " eh, lallai masu miji ni ma ai ba kwana zan yi a nan ba dukda nawa mijin yayi tafiya ai na je in huta a gida ko dai gidan Lele zan tsaya kwad'ayi ne?". Jan ta Zulfaa tayi tana cewa " kar ki yarda, tun da ke da naki mijin yayi tafiya ta kawo miki abinci ne halan?". Dariya suka sauka suna yi, ita Lele ta wuce wurin motarta, Zulfaa kuma ta shiga eateryn nata ba wani dad'ewa tayi ba ta fito don wucewa gida kusan tare suka fito da Suliem don ita Nadeefah tuni ta riga da ta wuce gida.



San da ta isa bai ma dawo ba, jakarta da hijabi ta ajiye kawai ta cire sneakers d'in ta ajiyesu a shoe rack ta sanya slippers masu taushi ta fito. Kitchen ta shiga da k'arfinta ta fara girki don tun da safe take kwad'ayin fried rice, ba ta siya a Yerwa's cuisine ba tafi son ta dafa kayanta. Yanka kayan girkin ta yi da yanka chicken, kidney da sausage tana girkin cikeda nishad'i da 'yan wak'ok'inta.



Da yake ba mai yawa tayi ba ya sanya ta gama lokaci k'ank'ani, zubawa tayi a flasks ta had'a salad mai apple da pear da ya ji mayyonaise sosai da madara. Jera masa tayi a kan tray normal pineapple da cucumber drink ta had'a ta zuba a cikin jug ta ajiye akan dining wanke kayan da ta b'ata tayi ta wuce d'aki.



Wanka tayi ta zura wani three quater mai fad'i na kaki da top da ta lafe a shafaffen cikinta tana fitowa abincinta taci ta k'oshi kafin ta dawo parlorn waya tayi da Ummu da ta iso yau da yamma sun d'an jima kafin suka yi sallama ta zauna zaman jiran tsammani. Ba shi ya shigo gidan ba sai kusan k'arfe 9, key ya sanya ya bud'e k'ofar part d'in shi ya shige ciki ko da yayi wanka ya sanya pj zama yayi a cikin kujera yana mai jin kamar ya fito amma girman kan shi yana hana shi.



Ta ji shigowarshi amma ba ta taso kai tsaye ba don ta riga da ta haddace abubuwan da ya kanyi a dai-dai lokacin, sai da ta kintaci lokacin da ya kammala komai na shi kafin ta koma cikin d'akinta. Turare ta k'ara kad'an tana kallon kanta gashinta da ya kwanta sosai, ya ji gel ga color da ta sanya ta cakud'a kan da shi yayi 2 colors dark brown da gold. Lips gloss ta goga tayi murmushi ta fito trayn ta d'auka ta nufi d'akinshi, knocking tayi yana daga zaune ya k'i bud'ewa.



Har ta fara tunanin ko ya kuma fita ne taji ana murd'a key d'an matsawa baya tayi ya bud'e fuskar nan a cunkushe, kallon sama da k'asa yayi mata yana mai sake d'aure fuska yace " lafiya?".



Yawu ta had'iye a d'an tsorace tace "ammm abincinka na kawo...".



"Ohhh saboda ga mayunwaci ko? Toh ki tafi da kayanki ban ci ". Ya k'arashe da niyyar komawa a d'arare tace " i'm sorry ba haka bane ".


"Ki rik'e kayanki ban nema ba". Yana fad'in haka ya buga mata k'ofar a fuska har sai da ta tsorata, dafe baki tayi yoh dama yaya lafiyar giwa ina ga tayi hauka? A banza ba a tab'o shi ba ma yayi masifar balle a yanzu da ya hau dokin zuciya. 



Sauke trayn tayi a gaban k'ofar ta koma kan kujera ta zauna, wayarta ta d'auka ta lalubo numbershi. Message ta tura masa kamar haka " kar ka bari b'acin rai na ya hanaka cin abinci please Yaa, in haka ta faru toh ba zan tab'a yafewa kaina ba nima d'in na san nayi laifi ka yafe min ka san fushin miji kan matarshi masifa ne. Ga abincin nan a k'ofar parlornka please" ta k'arashe da emojin hawaye a k'arshe.



Zurawa message d'in idanu yayi yana mai sake karantawa a karo na kusan uku, a kullum Nadeefah tayi masa message ya kan tsaya masa a rai har ya kasa daina karantawa. Kalaman ta ba wasu masu tsada ba ne ko wasu manyar kalaman soyayya ba amma suna d'auke da sak'onnin da ke nuna girman so da kulawarta a gareshi, haka na yau ma wato ita mai wayo ko ?.



Samun kan shi yayi da murmushin da ba kasafai aka cika samu a fuskarshi ba, yana sake karanta message d'in. Shafa gemunshi yayi don shi ma sosai yake jin yunwa saboda ko breakfast bai yi ba ya fita gida, tea ne kawai ya samu ya sawa cikinshi a office shi ma ba wani da yawa ba ne ya sha don bakinshi bai son taste d'in wani abinci ko abin sha in ba nata ba "Please Yaa" ta sake tura masa.



Tashi yayi ya bud'e k'ofar a k'asa ya ga abinci, ita kuma tana daga kan kujera. Kallonta yayi yaga yanda ta marairaice fuska kamar za tayi kuka. Bud'e baki yayi a d'an sakin fuska yace " zo nan " bai ko d'auki abincin ba ya juya ya koma in da ya fito.




Tasowa tayi cikin shagwab'a ta d'auki abincin, bin bayanshi tayi cikin d'akin ajiyewa tayi a kan centre table ta fara serving d'in shi a plate. Salad d'in ta sa masa a gefe zuba masa pineapple juice d'in duk ta ajiye, kallonta yayi ita da abincin cikin marairaicewa ta kuma cewa " please Yaa".



Lumshe idanu yayi ya bud'e yana nuna mata gefenshi, sai da ta d'an d'auki lokaci kafin ta dawo wurin. Zama tayi tana mai sake cewa " zai fa yi sanyi Yaa". Sai taji saukar hannunshi a kan gashinta, shafawa yayi daga farko zuwa k'arshe a d'an bazata taji yace " meye wannan kike shafawa gashinki?".



D'an daburcewa tayi ba na tambayar but na yanda yake tura yatsarshi wurin massaging gashin nata, "uhmm?" Ya sake tambayarta. A hankali cikin sark'ewar yawu tace " hair color ne". Sake cewa yayi " meyasa kike shafawa tohm?, baki son ainihin kalar gashin ki ne?".



"Aa kawai dai yana birgeni ne" ta bashi amsa, cewa yayi " saboda gayu ko? Uhmm yayi miki kyau ".


"Yaaa Abincin fa" ta furta cikin son gocewa, cewa cire hannun nashi yayi ya tashi. Dining d'in sa ya nufa ya wanko hannunshi a wash hand basin, kana ya dawo wurin da taken bai sake magana ba ya fara cin abincinshi. Tass ya cinye wanda ta saka masa ya ture plate d'in, drink din ya sha da kuma ruwa ya ja tissue yana mai goge bakinshi. Kallonta yayi yana cewa " yayi daɗi sosai, Allah ya miki albarka" kallonshi ita ma tayi da mamaki nan ko idanuwansu suka hard'e cikin na juna, wani irin abu take hanga a cikin bak'i da farin idanuwan shi masu girma da suka had'a da rigima rikici da kuma wani kwantaccen abu da ba ta tab'a ganin kalarshi ba a cikinsu.



Hakaza shi ma wani nau'in so ne mai nauyi dake dank'are a cikin zuciyarta, yake fita daga cikin brown ɗin k'wayoyin idanunta da kalar madara shanyayyu masu girma ba sosai ba da kyawawan mak'yaftai masu d'auke da zara-zaran gashin idanu. Lumshe idanun tayi don abinda take gani sun fi k'arfinta, wanda yayi dai-dai da saukar bakinshi a kansu. A hankali yayi kissing d'in su kana ya gangara kan abinda yafi komai d'aukar hankalinshi a fuskar tata.



Ya d'auki kusan tsawon lokaci yau yana aikata abinda ya fi so, sai dai yau bai nemi wuce iyaka ba tun da ya lura da shi zai na shan wuya ba kowa ba. Sai da yayi maishinshi kafin ya janye, cusa kanta tayi a cikin k'irjinshi tana mai saurarar bugunta da ta sauya completely a kunnenta ya rad'a mata " shi wannan abun kwana nawa yakeyi bai tafi ba?".


"8 days" ta furta ai da sauri ya janyeta a k'irjinshi yana cewa " 8 days?,kuma yaushe ne ya zo ?". A hankali ta bashi amsa da " jiya". 


"Ki kashe ni kawai ki huta mana, yayi yawa ai ". Dariya ne ya kusa k'wace mata jin yadda ya furta cikeda damuwa kamar wani wanda aka shaidawa ranar mutuwarshi kusa,saurin had'iye shi tayi sai dai 'yan ƙananu da suka fita a k'irjinta. Kallonta yayi jin girgizan da jikinta yayi alamun tayi dariya sai ya ga fuskarta fayau, cewa yayi " Allah ya kaimu ranar amma gaskiya da kwai k'ura". Yana sake rungumeta a cikin k'irjinshi, ita ko tayi luf cikeda fatan su dawwama a haka.



Ba ita ta bar part d'in ba sai kusan 11 suna zaune ba magana, sai TV dake aiki ita d'aya sai ita Nadeefahr dake ta kallon TV ba tareda tana fahimtar rabin abinda ake yi a cikinta ba. Sai da ta fara gyanyad'i kafin ya sallameta, traynta ta d'auka sai da ta wanke kayakin don duk abinda zai kawo mata kyankyaso ba son shi take ba shi ko barin kwanukan abinci ba wanki ba k'aramin kyankyasai yake kawo wa mata ba.



Tana gamawa ta goge su ta maida komai tsaf inda yake, sannan ta kashe wutar kitchen d'in ta fita. Wutar parlorn ma ta kashe ta shige cikin, shirin bacci tayi ta kwanta. Yau dai ba ta d'auki time mai tsayi ba kafin tayi baccin ba, don akwai bacci sosai a idanunta wanda ta san har da na jiya a ciki. 


Shi ko kamar yadda ya zama cikin kwanakin nan haka ya gagara bacci sai da ya gama tunaninta, har ji yayi kamar yaje can wurinta su kwana tare ko ya rage jin kewar da yake damunshi sai kuma yayi tunanin ko ta rufe k'ofa kuma knocking k'ofarta ai tamkar zubewar kimarshi ne a idanunta.

Da safe da wuri ta tashi har kuma ta gama ayyukanta bai tashi ba, kallon agogo tayi tana mamakin rashin tashinshi. Har ta nufi d'akin na shi don ta tashe shi sai ta tuna ai yau Friday bai kuma fita da wuri, tale baki tayi don tana son fita da wuri. Zama tayi cikin kujera ta fara creating videon da ta so yi jiya ba tayi ba, voiceover ta fara na tallar kayansu da kalar discount d'in da sukayi. Ta gama voiceovern kenan tana editing ya fito, bai ko yi shirin fita ba a yanda ta ganshi.



Zama yayi a gefenta fuskar shi ba yabo ba fallasa, ajiye wayar tayi tana gaishe shi da kulawa ya amsa yana mai cewa " ya kika tashi? Yau ba zaki fita ba ne?". Cewa tayi " Alhamdulillah, eh ba zan je office ba gidan Ummu zan je sun zo jiya sai kuma gidan Hajjah da Umma na kwana biyu ban je ba ".





"Uhmm ki ce yawo dai zaki sha yau d'in " ya furta yana jingina da bangon kujerar, d'an murmushi tayi tana cewa " ya zamuyi tohm, ai zumunci za mu sada ". 



Cewa yayi " ok, ki shirya sai in sauke ki a can d'in ".


"Ok Yaa" ta tashi so excited da nufin shiryawa, rik'o hannunta yayi yana cewa " ba yanzu ba madam ko fa abinci ba kina saurin ki je yawo". Shagwab'e fuska tayi tana cewa " auu toh a dining zaka ci ko nan za a kawo?". Mik'ewa yayi bai tanka ba alamun a can d'in zai ci, serving d'in shi normal breakfast na kunun gyad'a da puff-puff tayi sai gizzard pepper soup da ta had'a don shi mayen nama ne duk wani abinci in babu shi ganinsa yake lami.


Sosai ya sha kunun in da ta nan tafi gane in abu yayi masa ko akasin haka, baya wani yaba abinci na jiya ma Allah ne ya k'waci maganar a bakinshi har ya furtan ba tareda ya sani ba. Yana gamawa yace thanks a hankali yana wucewa cikin d'akinshi, gyara wurin tayi itama ta wuce room d'in ta don shiryawa.



A cikin getzner bak'a mai k'yalli ta shirya wanda aka yi masa ado da zare gold mai sauk'i ba mai colorn nan sosai ba, d'inkin Senegalese har k'asa da straight skirt akayi mata mai tsagu sosai ya kuma kamata tsam. Amma saboda zubin rigar sai ba a gane hakan ba don ma an mata tsaga itama a gefe da gefe an kuma ci bakinshi da zare gold d'in shima. Gold costume tayi ado da su har da abin hanci da anklet duka gold, ba tayi make up ba a fuskar banda 'yar foundation da ta murza don rage hasken nata da yayi fayau sosai. Taje gashin girarta tayi ta zizara kwalli a k'wayoyin idanunta sai lashes d'in da ta jasu da maskara suka kuma sawa suka mik'e sosai, lip balm kawai ta sa a bakinta ta sanya turare dai-dai kafin ta fito hannunta d'auke da bag golden color. 



Golden d'in medium hills ta sanya sai chantily veil shima haka, ta fito tsaf kamar ka saceta. Tana fitowa shi ma yana fitowa daga part d'in shi, brown colored shadda ya sanya shi ma getzner ba ai mata aiki ba ko d'igo ya haɗa bak'in hula da takalmi palms har da agogo na fata shi ma hakan.



Kallonta ya tsaya yi kawai ita kuma ta kawar da kai don jinta take wani iri a kaf Yerwa in dai aka ce kwalliya ne da iya hawa sutura babu kamarta ga uwa uba kyawun da ko makaho ya shafata ya san tana da shi. Muk'ut ya had'iye yawunshi yana cewa " mu je?" Kai ta gyad'a tana kinkimar basket guda a cikin ukun da ke ajiye a dining ta nufi waje, tayata yayi da sauran biyun ya fito shi ma ita ta rufe k'ofar lokacin har ya fiddo motar da zai fita da ita mai tinted don ko bai son wani ya ganta a yanda tayi kyan nan ba kowani namiji bane zai iya kawar da kan shi daga kallon ta ba, ba zai tab'a yiwuwa ayi mata kallo d'aya ba a sake waiwayawa an mata na biyu ba.



Sai da suka hau titi ne ya dubeta yana mai cewa " wai ke baki gajiya da wannan abincin da every week sai kinyi shi ne? Kuma ma suna da masu aikin da ko mai suke so zasu had'a musu miyasa sai kin damu kan ki?". Murmushi tayi ta kalleshi tace " albarka nake nema ba komai ba, kuma ma ai ba wani abu mai yawa ba ne ". Ok oo ya furta bai sake magana ba har suka isa gidan Umma.



Tarba ta musamman da bai saba gani tana wa Khaleesah matar Yaa Hafeez da take duniyar Allah har Lagos ba shi tayi mata, kai zai iya cewa irin ma wacce take wa su Ya Budu da Fadwaah mai bin shi bai kai kwatankwacin wacce ake mata ba. Tun ma kuwa kafin ayi aurensu take mata hakan, yanzu ko sai abunda ya k'aru akan na da shi dai na shi ido. Sanda ko ta gabatar da abincin shi ma ko ta sha albarka yafi cikin kofi, ranar har ma dashi mai cefanen sai da ya samu na shi rabon. 



Kamar kowacce rana basu dad'e ba suka wuce gidan Hajjah da yau can ya ga damar sauketa, ciki ya shiga suka gaisa da Hajjah sosai fiyeda yanda suke a baya. Bai wani dad'e ba ya musu sallama ya tafi nan suka b'alle sabon babin hira da Hajjahn inda duk hirarsu bayan bikin nan ba ta tab'a bibiyar yadda zamantakewar ta su take ba don tace ba huruminta ba ne ko a baya ma da take ganin da matsala balle yanzu da suke tunanin daidaitar komai a tsakaninsu.


Sai after 2 ta wuce gidan Ummu amma ba kai tsaye ta wuce can d'in ba sai da ta lellek'a su YaMara da Ya Madari suma ta ajiye musu abinda ya samu saannan ta k'arasa gida. Sosai Ummu ta ji dad'in ganinta musamman ma yanda ta k'ara kumari fiyeda last ganin da tayi mata, a baki da zuciya ta dinga shi wa Burhaan albarkar kula mata da sanyin idaniya da yakeyi. Yau gabad'ayansu sukayi dinner a parlorn Abbu har da shi da ya zo da niyyar su tafi, su Abbu su kayi masa ya jiki don su basu zo ba ciwon da yayi sai a waya suka gaisa. Saboda dad'in ba su suka bar gidan ba sai 10 na dare kafin su k'arasa gida kuwa 11 tayi hakan ya sa suna zuwa kowa wanka yayi ya nemi wurin Kwanciya.


Saturday meeting a kayi inda aka tattauna akan shirin azumi da sukeyi da masu tafiya umrah, in da har da su Nadeefahr a ciki sai kuma foundation d'in ta da Hajjah ta gabatar a wurin kowa ya sa abinda ya sawwak'a da fatan Allah ya had'a su a ladan banda doguwar adduar sa albarka da ta samu daga iyayen nasu don karon farko kenan da wani ya fara bud'e gidauniyar tallafin gajiyayyu da marasa k'arfi shi ɗaya a familyn. 





Kowa ya fi dogara da wanda suke da shi na family gabad'aya, ita ko na ta ya kai kusan 4 years tun farkon dawowarta Nigeria bayan kammala MBA d'inta amma ba wanda ya san dashi in ka d'auke 'yan gidansu sai Suliem, Zulfaa da Hajjah. A haka aka tashi meeting cikeda annashuwa yayinda aka bar Burhaan da yak'e a lokacin da ake yabawa support d'in shi ga Nadeefahr wanda inda yana da kunya toh ita ya kamata ya ji amma ko a jikinshi don shi mutum mara son shiga harkar da ba a kasa da shi ba har ji yayi kamar yayi mata magana sai kuma ya fasa don a ganinshi matsalarta ba tashi ba.



Cikin kwanakin akwai wata kalar zaman lafiya da shak'uwa mara fasaltuwa a tsakaninsu,ba wai hira suke yi mai tsayi ko wasanni ba. Amma suna da wata fahimtar juna mai yawa tsakaninsu musamman ma ita da ta gama nak'altarshi da abinda ke b'ata masa rai ko saka shi farinciki, ta kuma san cewa off everything in this world yana matuk'ar so da girmama abinci. 



Miskili ne ainun sai son girman da kowa ya sanshi da shi ko ba a magana, bai da naci amma akwai kafiya akan abu. Akwai muguwar aji wacce ake d'aukarta a matsayin girman kai da kuma kamewa wacce ake ganinta a faɗin rai. Ba a tursasa shi kan abu in kuma yaso yin abu duk wahalarshi sai yayi, bai da wani hak'uri sosai amma yana da kawaici akan wasu lamuran. Ya tsani jan rai amma ya na son jan aji da natsuwa, bai da rowa amma kyautarshi hab'o ce bai kuma yi don wani yace yayi yana da kirki fiyeda sanin mutum shi ma sai yaso. Yana da muguwar kishi don ko Safwaan ba wani sakewa fuska yake akan zuwa gidanshi ba.



Yana son gayu amma bai cika son k'yale-k'yale tayi yawa ba, bai son gaggawa amma bai cika son shiririta ba. Yana da natsuwa mai tarin yawa ga kwarjini da haiba, bai kuma cika hanzari a lamura ba. Akwai taurin kai ga wuyar tank'waruwa musamman a abinda ya shafi rayuwarshi sai dai yana da tausayi in yaso, yana son kulawa bai kuma fiye son a dameshi da yawa ba. Ya kuma tsani mutum ya aikata wani abu don shi ya gani ko yaba ko ya samu attention d'in shi, shi yasa yake respecting Nadeefah saboda duk abinda take yi ba ta tab'a nuna wai neman shiga take yi a wurinshi ba Aa halittarta ne hakan da duk wanda ya santa toh da su ya santa kamar dai shagwab'arta, yawan murmushinta da kuma kulawa da mutun bakin rai bakin fama. Kwalliyarta, ko hair color da take shafawa ya san ba dan kowa take yi ba shiyasa bai tab'a d'ad'a shi da k'asa ba and most importantly he's very romantic wanda ba lallai ko shi ya san da hakan ba sai ita da Allah ya had'ata zama da shi.


A kaf kwanakin nan a takure yake sosai don ya kai juriya iya jurewa akan abinda yake ji musamman ma da ya dad'e da ajiye drug d'in da yake sha tunda ya lura ba wani aiki da yake masa, ga kuma had'uwarsu ta kullum sake zafafan halin da yake ciki yake yi duk da ya kan rage zafi ko yace k'ara zafi don in dai ya rab'eta da k'yar yake iya bacci amma hakan bashi yake hanashi da ya d'an lafa masa ya sake rarumota ba. Bai kuma jin kunya a koina ne ba parlorn shi ba, ba sitting room ba kai har a kitchen shisshige mata yake yi ita ko tana biye masa sai hankalinshi ya kai k'ololuwar tashi ta bar shi. Sai yayi ta mita ai mugunta take masa ita ko tayi ta k'umshe dariyarta,a gefe guda kuma tsoro da fargaban duk ranar da zata fara sallah takeyi. Hakan ya sa ko da ta samu tsarki kafin cikar kwanakinta ba ta nuna masa ba, cigaba tayi da sa pad shi ko bawan Allah yana nan har da ƙirga kwanaki.


Ran da kwana na 8 d'in ya cika har da saurin dawowa gidan amma sai cewa tayi ba ta fara sallah ba, tsayawa yayi yana kallonta sai tace " da ma ya kan rage kwanaki ko ya k'ara, but bai wuce 2 days zai tafi gabad'aya ".


Cewa yayi " anya akwai lafiya a abun naki kuwa? Abu yana yin 8 days a k'aida ya kuma k'ara kwanaki goben nan zaki ga likita in sha Allah". Da sauri tace " ai na tab'a ganin doctor, tace ba wani abu ba ne in kuma ya wuce 15days ne shine za ai min pelvic scan saboda a san kalar maganin da za ai min and bai ma kai ba balle har ya wuce hakan ya tafi ". Shiru yayi yana jinta don ya san gaskiya ta faɗi don ya karanta komai, duk da ba duka ba tunda ba medicine yayi ba.

Da kallon tausayi ta raka shi don ta hango sa rai a idanunshi k'uru-k'uru wanda ke ƙara tsorata ta don ba ta gama shiryawa karb'arshi ba, ko da ta kira Suliem ta bata labarin yanda sukayi rufeta tayi da fad'a akan meyasa take son wasarere da damar da Allah ya bata. Kuma meye wani amfanin jan rai tunda ko ba jima ko ba da'de dai sai an je wurin, bayan haka ma kanta zata taimaka ba wani ba. Shiru tayi tana saurararta tana gamawa ta yanke wayar, ajiye wayar tayi tana mai tunani a ranta game da zancen Suliem d'in shin ta amince d'in ko ta kafe akan ra'ayinta?..................


Deejasmah ✍🏼