TALES OF THE WAZEERIS

The crown prince nd d princess

by @surayyahms

25...🦋🦋🦋

SURAYYAHMS

Tales of the wazeeris

mai machine yayita yima ushna hirararki amma ganin bata ko amsashi ba yasaka yagaji yay shiruu sai bai kara cemata uffan ba..

dagata dayan bangaren kuwa tun kafin convoy din Sultan Shamsan wazeeri ya samu isowa cikin kananan hukumomi dake yankunan Dala axis labarin dawowar san tuni ya gama zaga ko ina gulma yagama yaduwa cikin kauyuka da garuruwa dasuke nan yankunan dala har zuwa fadar zamkora.

Tun bayan tafiyar sarki murad Areesha ta saka servants din gidansu agaba akai ta kimtse kimtse tay wanka taci kwalliya na musammn tasaka doguwar riga kalar ja da ruwan gwal da aka masa saqa da zaren sarauta dawasu shegun gwalagwalai masu nauyi da tunanin cewa dole ne yariman tharim vale yakaraso tafadar zamkora dmin duba yanayin garin da kuma talakawarsu tun da dai yankinsu na zamkora akarkashin masarautr dala yake.

dake mahaifinta baya nan kusan itace take yanke hukunci akan komi, she has invited few palace elders nd her grandparents daga sashen uwa da uba.

hakanan ta ɓoye duk wani xumudi da kuma obsession inta tasaka kowannensu yafaraji aransa cewa zasu kare martaban zamkora ne ayayinda mahaifinta baya gari musmn idan yariman tharim vale yaxoshi cikin zamkora.

tun daga kakanninta har manyan hadiman fadar zamkora suna mata kallon gwarzuwa ce, yarinya me nisan tunani da son kare martaban mahaifinta da kuma darajar garin zamkora gabaki daya.

yau inda ace Arisha namiji ne da tuni an bata matsayin sarki me jiran gado sbd babu wani mahaluki agarin da baya mata kallon yarinya kamila kuma jajirtaccya wnda tay gadon jarumta irin na sarki snn awajensu arisha kusan yarinya ce datariga tasan abunda yakamata.

lokacin ruwan sama na sauka ahankali dan tun safe akeyinshi har yanzu da yamma yay bai gama tsayawa cak ba anadan yayyafi ssai kasa tajike sharkaf da laka dan ruwan da suke taruwa ahanya sun cike waje harma babu hanya mai kyau na wucewa.

duk da haka mutanen yankunan babu wanda bai fito kwansa da kwarkwatansa ya fito cikin tsantsan zumudi ba,mata sun fito da yaransu a bayansu ga dattawa,samaruka na rike da wayoyi suna recording shigowar hadaden convoy na motocin yariman dala yara kanana sunata ta guje guje da ihu cikin farin ciki “Yarima ya dawo...yarima ya dawo

manyan royal black SUVs convoy daga masarauta da suka daukosa tun daga Airpot sunkai goma sha biyar da suka doso cikin yankunan dala suna ratsawa ahnkli cikin muddy roads na kauyukan Rimkasa, Falwade, Karzumi da Dambishir ayayin da securities masu yawa ke kokarin controlling crowd din dake kkrin cike bakin hanya.

duk inda motocinsa suka ratsa saiyaga cinkoson mutane na daga masa hannu cikin tsananin murna kamar wani shugaban kasa wasu ma harda kuka...

jama'ar kauyukan basu taɓa ganinsa koda a hoto ba amma sun sha morar ayyukansa for years dan shi yasa aka gina musu asibitai da makarantu ingantattu duk akan kyauta, gashi ko wani shekara yana aiko musu maganin gona na zamani da taki da kuma tallafi ma manoma da mata thru his charity fndations.

sann shekaru da yawa babu wani dan sarauta ko billionaire dayake aikowa dan aduba masa rayuwar ire iren forgotten villages din domin yaga halin da suke ciki face shi.

hatta Sarauniya arisha na zamkora datake zagowa taimako,ihsani daga wajenta baya wuce na abinci kwano kwano, ruwan sha irin na gora ko leda, da kayan sawa, shima kuma bata zaga kan kowa da kowa dashi dake tanayi ne yawnci ma manyan gidajen gari da nakasashu datasan zasu barbaza sunanta dan asan da ita bama kowa da kowa ba.

saidai shi Sultan duk da tsananin darajarsa da karfin mulkinsa yau ya iso nigeria amma koda aka ce masa talakawa sun taru a titi suna son ganinsa bai musa ba sai gashi nan yazo...

gabaki daya mutanen yankunan awaje guda akaxo aka taruuu kai zaka dauka filin yaqi ne sbd ture ture da akeyi dan agansa kowa yana kiran sunansa da murna

a hankali motar dayake ciki ta tsaya a tsakiyar garin Karzumi saboda duka anan aka taru, kaf manyan elders din yankuna sun taho each representing his district kowa yana tsaye acikin yayyafin ruwan saman suna jiran saukar yarima

kauyukan kowani yanki suna da jagora amma banda zamkora dan ko mutum daya daga cikin zamkora ba a aiko ba sbd umarni ne da sarki murad ya bayar tun kafin ya wuce mali yace bai amince wani dan zamkora yajeshi gaban yarima jinin tharim vale yana ihu yana bauta masa ba sbd har yau ji yake kamar duk duniya baida maqiya kamarsu

anan take security suka bude ma sultan kofar bullet proof suv dinsa..

lokacin da ya fito cikin yayyafin gaba daya wajen yayi shiru for some scnds aka zuba masa idanu yuu sbd yadda yake nan dogo kyakkwan gaske gashi hadadden kayn royalty dake jikinsa takaramai wani irin tsananin kyau da daraja kagansa zaka dauka sarki ne dakan sa a tsaye.

yayyafin ruwa dan kadan yake sauka akan shoulders dinsa yana kara masa wani irin masculine royal elegance, kamshin hadadden turarensa tuni ya gama gauraya da sanyin ruwan sama yadan zuba cloudy grey eyes dinsa yanata kallon irin cinkoson mutane manya da yara dasuka fito daga cikin garuruwrsu dominsa

acikin nitsuwa da kasaita ya tsaya tare da zuba manyn idonsa akan su inda fadawa da wazeeran fada da kuma profesional body gurds dinsa suka rufa masa baya.

atake dattawan kauyukan duka suka rusuna qasa suna masu fadanci tare da gaidashi cikin daraja da girmamawa

maroka da yan zagage kowa yana miko kirari da gaisuwa

“Allah ya taimake yarima

"Allah kara daukaka ranka ya dade...

"Allah ya kara maka daraja dan masu daraja..

"gwarxo uban gwarzaye..

xaki uban zakuna...

"maqiyanka fadawarka yarima..

"Allah ya shi albarka yarima.. jinin daraja, da mulki dakansa..

"shugaba, jikar shugaba, dan shugaba...

"jagora uban tafiya....

ahankali shamsan ya daga musu hannunsa da alaman kaf su mike tsaye, da rawan jiki da ture ture kowa ya tashi kusan kaf dinsu elders din sun haifesa dan tsofi ne sosai wasunsu sun sha ruwa babu laifi yan kadan dinsu ne dattawa

batare da wani hayaniya ba yatsaya yanamai sauraron matsalolinsu da kansa

yasan bazai iya daga muryansa sama har yay wani dogon bayani ba, danhaka maza maza wani hadiminsa ya matso kusa yana tayashi comunicting dasu..

within less than 30 min ya juya ya kalli daya daga cikin executives dinsa cikin calm voice dinsa dake fita kasa kasa ya bada umarni cewa within two weeks yakeso ayi registrng kauyukan for good road Reconstruction dan haka engineering teams zasu zo sufara shigewa cikin kauyikan domin a gyara musu hanyoyi da kwalbeti snn yakara odan food supply trucks wanda yace lallai su shigo gobe da sasaafe a raba, in angama gyara musu hanya kowani yanki za'a bude musu entrepreneurship cnter fully funded for the youths to create more job openings under Prime Real Estate charity organisation

da tallafin tsabar kudi na musmamn domin mata, yara, da tsofi da marayu sbd kara jari da kuma dogaro dakai agidan mazajensu...

koda aka gama daukar abunda yarima yace a rubuce, kusan bayyane aka hau karanta ma jama'ansa dan suji da kunnensu, take wajen ya kusa cakukewa da farin ciki da ihu dattijai suka fara masa addu’a kamar zasu rushe da kuka iyaye mata daga nesa suna ta kokawar miko masa albarka da addua yarima Allah ya saka maka da gidan aljannah, Allah ya kare mana kai, yarima dama kaine gatan mu..

duk da haka fuskar shamsan babu wani canji dan baya son mgna baya murmushi saidai kaga ya daga musu hannu ko ya dan gyada musu kai to look more humble nd kind.

cikin kasaita ya koma cikin motarsa sbd ya gaji yana shiga mota convoy dinsa yafara tafiya ahnkli ahnkli sbd yawan ruwan laka da dandazon cinkoso na mutane

gaba daya hanyoyin sun cika an hada dogon traffic saboda yadda kowa ke kokarin ganin yazo kurkusa da motar yariman dala ko taɓawa suyi suji dadi

ata dayan bangaren kuwa tun lokacin da suka iso wajen ushna ta sauka daga kan machine din saboda tsabar taron mutane

shikasan mai machine din bai tsaya karban kudinta ba taga yabi zuga anata yarima yarima..

wanda sukay ma yarima rakiya suna watsa kudi yan dubu dubu a iska jama'a na kokowar kwashewa

ran ushna ya gama baci sosai har tana huci dan babu wani abunda take matsatsin bukata ayanxu sama da ta ganta a gida..

kayan dake jikinta duk yajike shartaf da diso dison yayyafin ruwan sama musmn ma da iskan machine yariga yagama sauka ajikinta

hannunta rikeda trolley dinta jikinta na rawa rawa tanata kokarin wucewa ta tsakiyar cinkoson cikin wahala

kamar zatay kuka take cusa kanta cikin tarob tanamai cewa excuse me pls...hey dan Allah kudan bani hanya,toh harshen hausar ma bai gama zama abkinta sosai ba duk magiya da roko datakey wa mutane..amma inaaa

babu ma maijinta kusn kowa hankalinsa yana kan yarima ne

dakyar ta iso ta gaba gaba inda ake tsananin turereniya da ake na son karasowa kusa da convoy din, lokacin Ushna ji take kamar ta fashe da kuka saboda tsabar takaici, gajiya, da tsananin tsoro.

she was so frustrated it seems like tunda ta dawo nigeria babu wani abunda ya tafi mata dai dai, gashi yanzu ta makale cikin laka da taron jamaa anata tureta kamar wata yar gudun hijira.

tana kkrin safce high hls dinta daya makale acikin laka lokaci guda wata buguzumar mata ta turata kasa da karfi

atake Ushna ta zame kasa tsiii trolley dinta ya wani kwace daga hannunta yay gefe guda nan take kayan jikinta gaba daya ya turmusu cikin wani brown muddy water dake gefen hanyar

ita kanta batasan sanda kuka mai rauni ya kwace mata ba she felt soo soo angry nd embrassed, jikinta na rawa rawa ta kalli tafin hannunta da ya gama baci da laka.... kayan jikinta duk ya dauki uban datti for seconds bata iya motsi ba dan gaba daya wajen is so disoriented kanta taji yana juyawa dan ihu da hayaniyar mutane kawai take ji akanta.

tana kuka ahankali ta daure ta hawo trolly in tana kokarin mikewa tsaye dede lokacin ne kuma daya daga cikin black SUVs din convoy din yarima ya ratsa da wani irin speed ta nan gefenta kan kace wani abu ruwan laka mai datti ya tashi tassss yawanke gaba daya jikinta daga kai har kasa

Ushna ta tsaya cak for a while bata iya motsi ba idanunta a rufe jin

fuskarta harna diga da ruwan datti, jacket da grey veil dinta was complty drenchd veil din harya manne da gefen fuskarta sosai

kara fashewa da kuka tay hannunta dake kan rawa rawa har yanzu na rikeda handle din trolley dinta tightly ta na ji kmar zata suma da baqin ciki,atake taji numfashinta na sama sama saboda tsananin humiliation da yanayin takaicin datake ciki.

within that exact moment of extreme frustration ne kuma taji wani irin sanyi na daban yana ratsata

tanakan kuka tafara lalume cikin jakarta ta jawo karamin hanky tafara goge dan ruwan dattin a fuskrta ahnkli ko kadan bata lura ba,... motar da Sultan Shamsan yake cikin ne yake tahowa ta inda take tsayen ahankali

he was trying to pick a call sai kwatsam yaji gabansa yay mugun fadi wayarsa ta zame daga hannunsa tayi gefe batare da ya lura da hakan sosai ba

naturally ya dan dago cloudy grey eyes dinsa yadasasu ta window din motar kai tsaye sai idanunsa suka sauka akanta and immidietly he looked at her...time just stopped for him for a moment.

gabaki daya noise din wajen ya disapearing daga kunnuwansa sai

bai kara jin komai ba

motarsa is being driven too slowly sbd dandazon jama'a dan haka yasamu isashen dama ya kalleta da kyau tun daga sama har kasa,yaga yarinyar sai kukar shagwaba kawai takeyi ahnkli tanata share fuskrta with deep frustration kamar wata broken angel da ta fado daga sama...

gashi veil dinta ya dan zame kadan jikkken dogon bakin gashinta yawani mannu da gefn kyakwar fuskrta

hawayenta na zuba bt within one second ya faraji kamar anahuda cikin kirjinsa ne directly sai kuma numfashinsa ya dauke grey eyes ball dinsa na akanta daga gani kasan sosai ta dauke masa hankli

tsabar ta jike da ruwa har wani rawan ɗari dari takey kananan lips dinta na rawa ahankali

kallo maicike da nazari yake mata tamkr bai taba ganin mace me sanyin kyau kamar ta arayuwarsa ba she was not an ordinary beauty to his eyes,

she looks soft nd special har cikin kokon zuciyarsa yakejin wani strange feelings yana bugawa da wani irin karfi akanta kai tsaye.

he has seen beauty queens, international models, royal women,

billionaire daughters

amma bai taɓa jin irin wann strange pull din dayakeji ynxu akan wata ya mace ba, its just feels like kamar rabin ransa yake kallo acikin yayyafin nan a tsaye ba yarinyar data gama lalata jikinta da ruwan datti da laka ba.

motar tasa na cigaba da wucewa ahankali kwayar idanunsa suna kanta har lokacin data gama goge hawayenta ta kara bude idanunta ahankali ita kanta kirjinta bugawa yakeyi da masifar karfi kmr zai ballo waje...

tana dago kai dede lokacin ne idanunsu suka kusa haduwa ta cikin rain stained glass din motarsa she lookd at his tinted window direct tanajin jikinta na wani irin sacewa yana mai kara mutuwa wani abu mai ƙarfi kmr sihiri yasaka ta kasa dauke idonta akan motar

shi yana iya kallon kyakkwan fuskrta ta tinted dinsa tsar tsar amma itakam bata gansa ba..

alkacin batajin komi face wani irin bugun zuciya datakeji mai masifar karfi,gabanta na faduwa,sanyi kuma kmr zai haukatata

...and something inside them completely shifted...

sultan yasaka hannu ya jawo wayarsa data zamen yaga abokinsa itban ne ya kirashi sai baiko kula missed call din ba ya rubuta dan karamin text messge wa personal body gurd dinsa dake tahowa a motar dake daf dashi

har motarsan ya wuce ushna bata iya dauke idonta akan motarsan ba sai can after like 5 min taji dirar wani murya a bayanta.

sallama aka mata mai sanyi tayi saurin juyowa ta kalle mutumin dake tsaye a gefenta sanye da bakin suit ajikinsa.

sallamarsa kawai ta ansa cos she was too embrassed to talk...

cikin dakika ya kare mata kallo snn ya daga text din sultan ya kalla yaga yadda yayi masa full describtion inta excatly babu wani kuskure aciki.

da girmamawa a yanayinsa yace excuse me ma'am..if u don't mind i wll like to know ur full adress so i can delivr you to your home safely..

da kunya da tsoro tsoro a yanayinta tace "no sir, its okay..i can manage...nagode

kai tsaye yace "its an oder ma'am. idan ban kaiki gida cikin koshin lafiya ba i may loose my job.

da mamaki tace" nd who gave you those oders? isit my mum or my sister

yay shiru....sai can yaxoshi kusa ya amshi trolley inta a hannunta da girmamawa da soft voice dinsa yace "shall we???

ganin idon mutane sun fara dawowa kansu kuma dama tanajin tsananin kunya da takaicin yadda tariga tayi dukun dukun da ruwan datti sai kawai ta gyada masa kai tafara binshi har gaban wata royal SUV yakaita da ko a london inma bata taɓa cin karo da irinsa ba ya bude mata gidan baya ta shiga ta zauna aciki.

yana zama a driver seat ahnkli yace mata ur address ma'am??

ɓakinta na rawa rawa tay masa bayanin masarautar zamkora

kai tsaye ya saka sunan wajen a device na gaban motar da zai na nuna masa hanya

suna fara tafiya taga ya danna wani abu kmr room heater yanamai buso mata dumi me dadi....

lumshe idonta tay for a bit tanata tunanin to waye ya aiko a dauketa

duk sai ta saka rai ko mamanta ne ko kuma arisha hala ko sunga sakonninta ne

hankali adan kwance aka tukota har cikin masarautar xamkora

wanda tun daga nesa taga yadda gidan nasu ya dan lalace kamr ba gidan sarauta ba...

koda shike Arisha tasha gaya mata cewa babansu yana cikin matsala, snn sunakan struggling basuda kudi but she dint expect it to look dis much.

har gaban gate na fadansu ya kawota yay horn kawai sai taga an dakatar da su atake masu gadi da tsaron kofa suka wani fito suna hargagi badon komi ba saidan ganin

karamin tutar tharim vale da kuma plate number na motar masarautar dala.

Driver yay parking baice ma ushna komi ba yasauka yaje har bakin katon gate din ya samesu tareda musu bayanin cewa shi oder kawai aka bashi akan ya kawo wnn matar har gida..

suka ce masa sammm shi spy ne suka fara masa barazana..

ushna dake kallon su ta tinted atake ta bude kofar SUV din ta sauko

tasha mamaki da ko ganeta gurds din gidan basuyi ba dake tun da can ita batay kama da kowa ba da kakan kakan kakanta wato sarki imamu waxeeri daya asalin hada jini da tharim vale take mugun kama shiyasa tsananin kyanta da iliminta ya fito daban

ta lura royal gurds na gidansu are very rude ko kadan basu iya furta magana ba they are hot headed nd very arrogant kusan kamar halin babanta, dan tana musu magana ma kamr bajinta sukeyi ba

tsabar an cusa musu tsana akan duk wani mutum ko abu daya fito daga tharim vale

anan ne ma ta dada fahimtar cewa bafa mamanta ko addarta bane suka aiko da motar nan wani mutum ne daban gashi driver yaqi sam ya furta musu sunan wanda ya aikosa ya kawo ushna gida..

karshe itace ta bashi hakuri ta sallamesa bayan ya dauko mata trolly inta har inda take snn ya tsaya agefe har saida yaga tagama musu bayanin kanta snn masu tsaron kofar sun barta tashige ciki

kafin nan taga shima ya shiga motarsa ya koma masarautar dala

Tana shiga dataga yanayin gidan nasu yadda aka mance da ita kwata kwata saida taji hawaye ya kara tuluwa acikin kwayar idonta

can wata servant taxo ta karbe kayanta zata wuce mata dashi main building sai kawai taji bazata iya xuwa ba kai tsaye ta canza hanya tanufi sashen kakansu ummu hareera kirjinta na tsananin bugawa dan batasan ko tana raye koma ta rasu ba dan rabonsu da juna tun shekara goma sha biyu da ya wuce.

tana shigewa sashen kuwa ta hangota acn a zaune duk ta motse ta tsufa sosai, muryan ushna na rawa rawa tace "grandma???...

da wani irin razana tsofuwar ta miƙe tsaye dan sosai tasan sautin muryan ushna dan ushna itace favourite grand doter na mijinta marigayi sarki saleem imamu ..

kakanta saleem din kuwa yasota sosai dan dayake raye shine ma kadai yake nuna mata tsantsan soyayya snn yake yawan karba mata yanci agidan nan musmn awajen mahaifinta sarki murad.

mutuwar kakansu saleem dinne ma yajawo har Arisha taci nasarar yin makirci daya jawo aka tura ushna nesan duniya yin karatu tasan da yana raye da duk hakan bazai taba faruwa da yar jikansa ba

tana juyowa suka hade ido da ushna da already wasu zafafan hawaye sun fara xubo mata daga cikin idanunta ahnkli tana sakin huci me cike da bacin rai da takaici..

cos for a moment ta dauka daga gidan ne aka aika a daukota amma kuma sai tagane ba haka bane, nd it hurts soo much da hatta masu gadin kofar gidan ubanta saida suka titseyeta da tambayoyi na walaknci kafin nan suka kyaleta ta shigo

gabaki daya yanayin gidan yasaka ta gane kamar fa sun mance da ita ne gaba daya...

akangare ummu hareera ta kalle ushna yadda ta girma ta kara azaban kyau sosai

koda ta tabbata ita dince atsaye wani irin kuka mai rauni ne ya kwace mata ta taho da sauri sauri cikin dingishi ta jawota jikinta sosai tadan rungumeta tana kuka...

hannunta da suka riga suka tsufe ta tantame ushna dashi tanadan shafa mata bayanta cikin rawar murya tace

“....ya Allah...ushna?...

ushna yanxu kece wnn da gaske ko mafarki nake?Allahu akbar, Allah ya jikan ka mai martaba saleem ko jiya saida yazo min acikin mafarki yanata tambayana ke..

ushna bata iya furta komi ba sai kuka kawai takeyi sosai tanamai manne ajikin tsohuwar kamar wata karamar yarinya data jima a prison batare taga wani jininta ba .

duk wani takaici, gajiya da tarin humiliation da tasha tun daga airport har zuwa kofar gidan nan lokaci guda taji suka taru suna dawo mata akai

ummu hareera na zubda ruwan hawaye tareda dudduba jikinta tana cewa“ waye ya barki kika shigo haka acikin ruwa? kunyi hatsari ne..waye ne ya kawoki? yaushe kika dawo nigeria..

ahankli ushna ta dago kanta sama lkcin kirjinta na bugawa da rauni kwayar idanunta dasukayi jawur saboda kuka

muryarta na rawa tace

“grandma...kina nufin you didn’t know i was coming? wai dagske ne kowa baiga kirata da sakona a gidan nan ba..?

atake tsohuwar ta tsaya cak da wani irin yanayi tace...ushna anya kuwa nan gidan kika kira?dan wallahi bansan zaki dawo ba yau da safe babanki ya tafi mali nide babu wani wanda ya sanar dani komai game da zuwanki...

adame ta kara duba yanayin jikinta tace dan Allah ki gayamin meye same ki haka? ko hatsari kikayi ne a hanya

wani irin shiru ushna tay tanata kallon fuskr kakartan brain inta is busy trying to fully understand the real situation

duk dama tariga taga gaskiyar acikin pure shock da confusion in dayake cikin yanayin kakansu amma bata wani amince wai har familynta zasu iya walakntata haka ba musmn ma da tasan sun jima basu ganta anan gidan ba

atake taji zuciyarta ta wani irin nutsewa can kasa kamar an cinna mata wuta mai zafi akan kirjinta...

slowly ta ja baya daga jikin tsohuwar hawaye na zuba daga idanunta cikin wani irin sanyin murya tace..“...so they are all around, nd nobody care to read my text or pick my call

cikin tashin hankali ummu hareera tace ke nide wallahi bansan komai ba kuma fa mamanki da addarki kaf suna nan atare da su daxu mukai ma mahaifinki sallama snn muka ci abinci aida sun san zakizo da tuni mun shirya tarbanki..

ushna tay shiru batace komii ba,jikin tsohuwar na rawa rawa ta jawo hannunta tace toh zoki zauna anan auta bari na aika akiramin su...

kafin ta budi baki sai kawai taga ushna ta fashe da kuka tanamai girgixa kai da alaman batason ganin kowa..

SURAYYAHMS

***

ENJOY UR WKEDNS

COMENT

SHARE

TOH FA YARIMA YAGA USHNA SHIMA🤭🤩😁😁😁😁😁

snn ME KUKE TSAMMANIN YAKAMATA USHNA TAYI A WANN YANAYI

LETS coment duk inda kake....tell yr friends to read this amazing book

SAI MONDAY IN SHA ALLAH ZAMU CIGABA

***