BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----7



Bayan an gama gudanar da walimar cikin nasara jama’a suka cigaba da tururuwar fita yayin da wasu ke tsayawa suna taya Malam Abdallah da iyalan sa murna akan baiwar da Allah yayi wa diyar su Khadija.

ciki kuwa hadda Alhaji munnir mahmud wanda shima ya taya sa murna Haka suka gaisa da malan abdallah kamar sun san juna

Mahaifiyar ta Hajiya Maryam ce ta rungume ta cike da murna ta ce",
“Allah ya sanya Alƙur’ani ya zama haske a rayuwar ki duniya da lahira diyata.”

Khadija ta sunkuyar da kai cikin ladabi ta ce,
“Amin Ammina”

Yayan ta mubarak na wajen ya karaso yana murmushi ya ce,
“malamarmu yanzu kin zama celebrity kenan ko?”

Dariya duk suka yi yayin da Khadija ta turo baki ta ce,
“Yaya Mubarak ni ka bari”

hannun sa ya haɗe waje guda alamun haƙuri ya ce"an bari Hafiza Iman"

Mubarak ya kasance mutum mai tsananin kaunar kanwar sa tun tana karama, Mubarak mutun ne mai haƙuri yana bakin ƙoƙarin wajen sa ganin ya kula da iyayen sa da kuma kanwarsa Iman Yana daga cikin wadanda suka fi kowa murna da nasarar Iman da ta samu.

Bayan sun gama karbar baki suka shiga mota suka nufi gida.

kofar gidan cike yake da ɗaliban Mahaifinta wanda suka zo taya su murna 
Tun kofar daga gidan har zuwa tsakar gida an kawata su da kujera lulluɓe da farin yadi a cikin gidan mata ke ta ai kawo na aikin abincin Aunty zaituna wanda ta kasance kanwa ga Ammi ta nufo iman cike da murna Iman ta rungume ta ce"Aunty na"

shafa kanta tayi tace ƴan harda Allah ya miki albarka ya albarka ce ki da samun miji na gari"

taɓe baki iman tayi dan a rayuwa ta idan akwai abinda ta tsana shine ayi mata zancen aure duk yadda ta gai ga farin ciki sai kaga ɓacin rai a fuskar ta aunty zaituna dake kallon ta ganin ta haɗe rai ta ce"maza kije ki shriya kafin mutane su fara shigowa"

Dakin ammin ta koma ta bude wadrope din ta, ta dauko wani royal blue lace dinkin riga da siket ta saka dinkin yayi zauna dass a jikin ta kasance khadija na da ɗan jiki amman ba sossai ba tana da hips kirjin nan ma ya cika yayi fam tamkar zai fara riga Masha Allah ,Allah yayi hallita domin kuwa iman irin mata nam ne masu diri tayi kyau sossai mayafi ta dauka da jaka wanda suka shiga da laces din tayi light make up wanda ya fito da bakar fatar ta ,Iman ba fara bace kuma hakan bazai sa ka kirata da baka  ba tana da round face bata da dogon hanci sosai tana da karamin lips  tare da sexy eyes wanda ya cika da lashen tamkar an dasa mata su girar nan a cike har tana shirin game wa.

daurin dankwali tayi ta yafa mayafin tun daga samar kai ta dauko jaka da takalmi ta saka ta fito.

matan dake tsakar gidan keta yaba kyawun ta yaya ta ne Mubarak ya shigo hannun sa rike da kwallin waya  kirar Samsung A07 ya mika mata wani tsalle ta buga ta rungume sa ta ce"Thank so much yayana"

sakin ta yayi ta nufi Ammi dake kaiwa masu aikin abincin maggi ta fara nuna mata wayar da mubarak ya siya mata Murmushi Ammi tayi ta ce"Angode Allah ya saka da Alkhairi"

nan fa ta nufi ƙawayen ta ,ta fara nuna masu suma sun taya da murna dan duk cikin su iman ce kadai ke riƙe keypad.

anyi taro lafiya an gama lafiya kowa ya watse ya rage saura yan gida kawai sai aunty zaituna da yake daga Katsina tazo kuma zata kara kwana biyu zuwa ukku kafin ta koma.

daren Ranar Iman na zaune dakin mahaifin ta da ya saka yayanta Mubarak ya kira ta akan maganar kudin da ta samu wajen sauka 
"Abba ni ba abinda zanyi dasu kawai ina ganin ka riƙe zaka fini bukatar su "

murmushi Abba ya yi dan ya san Iman bazata taɓa amman naira daga cikin kudin nan dan tun a filin saukar ta damƙa masa su Mubarak ya ce " Abba kamar yadda Iman ta faɗa kawai ka barsu a wajen ka din"

Abba ya ce"to shikenan"

Mubarak ya ce"Abba ina roƙon alfarma a wajenka ka bani dama na maida iman Makarantar boko"

"Mubarak ba wai na hana Iman karatun boko bane dama inaso bayan ta gama haddata sai a sama mata wata ta cigaba dan bana so ta hada makarantar isilamiya data boko ne amman tunda yanzu ta gama sai a nema mata wata ta cigaba"

Mubarak ya ce"Nagode Abba"

anan Iman ta tashi ta barsu da mubarak suka cigaba da hirar su ta ɗa da mahaifi a kullin Abba godewa allah yake da ya basa nagarttun yara masu ladabi da kuma biyayya.


Iman na fita daga ɗakin Abba ta koma Dakin Ammi zaune ta same su da Aunty zaituna suna hira wanda duk akan iman ne har ga Allah hankalin Ammi yafi karkata Ga iman tayi aure fiye da karatun boko dan a yanzu tana da shekara goma sha takwas aunty zaituna ta ce"yaya iman din da ko mane mi bata dashi ki duba kiga yadda take korar samari  Mahaifinta na mara mata baya tunda kinga bata shirya auren ba ki bar tayi karatun Allah ya fito mata dana gari" suna wannan hirar iman ta shigo ta same su zama tayi ta fara fito da kyatuttukan data samu