BARRISTER SUHAIL
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️----8
Alhaji munnir ne zaune a palorn sa tare da hajiya Fauziya yana bata labarin abinda ya faru wajen saukar da aka gayyace sa a yau.
hajiya fauziya duk da bata ga Iman ba amman ganin yadda ta birge mijinta ta san tayi abinda za'a yaba mata ne.
Suna tsaka da hira Mami ta shigo sanye take da wata hadaddiyar Atamfa ta kamfanin holland anyi mata dinki doguwar ruwa ta shigo cike da takun ta na ƙasaita wani kalo ta watsa wa Hajiya fauziya wanda a kan idanun Alhaji munnir kalllon arziki baya haɗa ta da matar sa sai na tsiya zama tayi,kan kujerar da Alhaji ke kai sum-sum Hajiya fauziya ta tashi ta bar ɗakin ganin ba arziki tattare da fuskar Mami.
Kallo Alhaji tayi da ya hade girar sama da ƙasa ta ce"Allaji kuɗi nake so ka bani"
Alhaji ya ce"har nawa"
"5 million ne ba yawa zanyi ordern kayan da zan saka da bikin diƴar hajiya turai "
Alhaji ya ce"har millon biyar kuma haba laila ke miyasa komi zai kin cika ruwa a al'amuran ki,baki san da wahala ake samun kudin bane"
a fusace ta ce"haba Alhaji,kai miyasa duk sanda nazo da buƙatar kudi duk ƙanƙantar su sai kayi ƙorafi idan da waccen juyar matar taka ta tambayeka kana rawar jiki zaka bata dadin abin nima na haifa ko baka bani ba ina da wanda zai ban aikin banza kawai"
tashi tayi tana ɗingisa kafa ta fita Alhaji Munnir ya bita da kallo kullum al'amarin laila gara girmama yake tana girma amman tana cin ƙasa wayar sa ya dauka ya kira Suhail
Suhail ne zaune a office din sa hannun riƙe da cup din coppe wanda har ya zame masa al'ada kullin idan bai sha ba baya jin dadin wayar ta soma Ringing sunan Abba ya bayyana kan screen din da sauri ya Daga ya ce"good morning Abba"
"morning Suhail kana ina"
"Abba ina office,wani abu ne"
"no ba komai mahaifiyar ka zata kirata zata tambayeka ka kuɗi kace mata baka dasu ko baka ji ba ita kullum bata da aiki sai na a bata ta san wahalar ake samu ita bata san tattali ba"
shiru Suhail yayi yana, sauraren mahaifin nasa har ya gama fadan kafin ya kashe wayar
murmushi yayi ya ce"Abba kenan"
Sameer ne ya shigo ya zauna kan kujera yana kallon cup din da suhail ke shan coppe murmushi yayi ya ce"Suhail ya kamata fa kayi aure ka huta da shan coffe a office kaga kullin sai dai kasha abinda daga gida amman kullum ace sai kazo office ka ke breakfast haba suhail kayi wa haka faɗa mana duk cikin friends din mu , kai kadai ne baka da aure mi kake jira You have all the qualities da mace ke nema kana da kyau, kudi, ilimi haka suhail kayi wa kanka faɗa Lokaci na tafiya ka duba cikin abokan mu daga mai yara biyu sai ukku ko mu ƴan baya baya gashin ina da baby you need to think gaskiya"
Suhail ya kalli sameer ya ce" na dauka ana aure idan ka samu wacce kake so tana sanka ko to Sameer ni ban samu ba"
zaro ido Sameer yayi ya ce"what of zeenah"
gyara zama Suhail yayi ya ce"nasan Zeenah tana sona Sameer Amma ni kaina ban san irin abinda nake ji a kanta ba kwata-kwata Zeenah bata cikin tsarin matan da nake so Idanun zeenah sun gama buɗewa da duniya"
sameer ya ce " kana nufin All this while basan ta kake ba"
"Ba wai bana sonta bane kawai duk lokacin da nake tare da ita bana jin nutsuwar da nake tunanin mutum zai ji idan yana tare da matar da yake son aura "
Sameer ya ci gaba da Magana
“Amma gaskiya Zeenah tana sonka sosai Duk wanda ya ganta tare da kai yasan hakan"
Kai Suhail ya jinjina.
“Nasan tana sona, Kuma bana son na cutar da ita ne yasa bana son na yi mata alkawarin da zuciyata bata gama yarda dashi ba”
Sameer ya gyara zama yana kallon abokin nasa cikin fahimta.
Sameer ya tashi ya ce"bari naje office akwai aikin da zan karasa"
Washe gari.
malam Abdallah ne zaune a Kofar gidan sa yana yiwa daliban bitar karatun la'asar wata baƙar mota ce ta shigo Layin ta faka kofar gidan tuni kallo mutanen wajen ya koma kanta dan ba kasafai motoci irin haka ke shigo cikin Layin ba iya Rururin da motar keyi kadai abinda burgewa ne bayan driver yayi parking ya bude kofar sa Alhaji munnir ne sanye cikin farin babban riga mai tsada da hula zanna dara wacce ta ƙara fito da kwarjinin sa.
ya nufo inda Malan Abdallah ke zaune tare da daliban sa gani wajen sa aka so ya sa ya sallami ɗaliban akan zasu cigaba da karatu bayan sallar magariba.
cike da fara'a malan Abdallah ya tarbi Alhaji munnir dan ya sheda fuskar sa tun a ranar saukar Iman dai-dai lokacin yana bude kofar seating room din sa suka shiga ciki.
Bayan shiga Malan Abdallah ya ba shi wajen Zama suka gaisa cike da girmama juna Alhaji munnir ya ce"na san ba lalle ka shaidata fuskar ta ba"
murmushi Malan yayi ya ce"haba Alhaji na gane ka mana sabuwar gaisuwa ta biyo baya"
Alhaji munnir yayi gyaran murya ya ce"Sunana Alhaji munnir Mahmud"
cike da mamaki Malan ke kallan sa dan a bai taba tunanin shine Alhaji munnir din da yake jin labarin saba idan bazai mantaba ya sha taimakawa a masallaci da yake limanci dan har yanzu fankokin dake cikin masallacin duk shi
ya saka su amman ko a hoto bai taba ganin sa ba sai yau.
malan yayi ƙasa da murya ya ce"Alhaji Allah sai dai ba laifi mukayi ba"
murmushi yayi ya ce"ko ɗaya nazo neman alfarma a wajen ka"
"Alfarma kuma,haka Alhaji mu almajirai har muna da alfarma da zamu iya yi wa manyan mutane irin ku"
shiru kai Alhaji yayi ya ce"tabbas kuwa kuna da ita,nazo nemawa dan na auran ƴar ka Khadija idan har ba Maganar wani akan ta ,tun Ranar da na ganta wajen walima na yaba da tarbiyyar da nutsuwar wanda duk wanda ya sameta a Matsayin suruka haƙiƙa yayi dace da sirika ta gari"
GA ZEENAH GA IMAN
NIDAI YAR TEAM ZEENAH CE KUFA READERS