SARTSE COMPLETE

19

by @legendspen

Gaba ɗaya Sardauna ba walwala ya yi komai har ya fice, a yanzu ba ni da kowa na kusa sai Bilkisu ita kaɗai nake magana da ita, itama sabida mijina ya zaɓe ta, kiranta na yi a waya duk da nasan tana wajen aiki, har ta ƙaraci ringing ɗinta ba ta ɗauka ba, sai da na kira sau uku sannan ta ɗauka. 

"Hello Nana, ya aka yi ina ofis ne." 

"Bilkisu akwai matsala ne babba ba ƙarama ba." 

"Ta mece? Me yake damun Sardaunan?" 

"Matsalal daga gidansu take, akan zancen haihuwa ne." 

"To ai Nana ba ke ce me matsalal ba ko? Kamar kince min kin taɓa ɓari ko?" 

"Eyh na taɓa, nice me matsalal, wai mahaifata ƙarama ce, shi ya sa jariran basu fiya zama ba." 

"Innullahi yanzu Nana mene abun yi?" 

"Wallahi Bilkisu bansaniba, duk na shiga damuwa, mussamman ganin Sardauna da na yi a cikin damuwa sosai." 

"Ai ba daɗi irin haka, ki lallaɓashi ki ji ko akwai wata mafita da yake gani, yau bazan shigo ba sabida zani unguwa amma zan zo a satinan." 

Daga haka ta kashe wayarta ta barni cike da damuwa. Ina nan zaune na rasa abinda ke min daɗi, kawai na kira Ra'is bayan mun gaisa na ce da shi. 

"Ra'is akwai matsala a gidana." 

"Ta mece ba dai mijinki ba." 

"Shine Ra'is."

"Lallai Nana, ke kenan bamu da amfani sai matsala ta taso tsakaninki da mijinki shine muke da rana, ba kyajin kunya sai ki tunkare mu idan kuma kuna cikin soyayya babu 'yan iska sama damu ko? To wallahi kisani babu wanda zai ƙara shiga al'amuranki tsakaninki da mijinki tun da kin zaɓi mutumin da ya haɗu dake ta haƙwaranki talatin da uku, kin bar wacca ta raini ki a cikinta har kika fito duniya, ta yi ɗawainiya dake, kin bar wayanda suka raine ki, su ka so ki, su ka baki farin ciki, su ka tsoraci kukanki Nana, duk akan wani mutumi guda ɗaya, ki je rayuwar duniya ce." 

Yana gama magana ya kashe wayarsa, kuka na fashe da shi, tabbas nasan maganarsa gaskiyya ce, kuma ya faɗa min abinda nake buƙatar a tinasar da ni, amma ya zanyi da Sardauna Allan da ya hallice ni shi ya sanya mini soyayyarsa. 

Daga wannan lokacin na ƙudiri aniyar bazan sake kiran kowa a gidanmu akan damuwa ba sai dai gaisuwa kawai. 

Bayan sati biyu. 

Tun lokacin da maganar nan ta fito gidanmu ya canja daga gidan farin ciki zuwa damuwa, daga gidan walwala zuwa na ƙunci, babu wani abu mai daɗi a gidan, kullum muna neman mafita amna taƙi samuwa, haka ta ɓangaren gidansu Sardauna, kullum matsanta masa ake yi, an hana shi sakat. A yanzu Sardauna har baya son zuwa gidan Hajiyarsu ko Family House, kullum daga gida sai Majalisa yanzu ma da mota yake fita majalisar, ni kam bana iya komai banda tunanin mafita. A ko yaushe cikin saƙe saƙe nake, na yi baƙi na rame gaba ɗaya na fita hayyacina. 

Gashi Bilkisu ba ta sake zuwa ba, tun ranar da na faɗa mata matsalal ta ce zata zo a cikin satin, idan ma na kira ta sai ta ce ba ta gari ma baki ɗaya.  Jiya da muka haɗu da Turaki sai da ya tsareni da tambayar me yake damuna, me ya faru tsakanina da Sardauna, amma na ce da shi komai lafiya. Daga ƙarshe ma ya fara yi min nasihohi masu ratsa zuciya akan haƙuri da rayuwar aure, sannan ya dinga jaddadamin na dinga yi wa mijina biyayya, har sai da na yi mamakin me ya sa ya yi haka.

Da na dawo ɗaki ma na yi ta faman tunani maganganun Turaki me suke nufi, yanayin maganar kaman faɗa da nasiha yake min daga baya kuma ya dawo shawara. 

“Allah Ya sa alheri ne.” 

Na faɗa, sai kuma can na yi tunanin ko akan maganar da ta ɓullo ne ta haihuwa shi ya sa. 

“Innullahi wa’inna illahir raji’un, ya zan yi ni Nana?”

Na tambaye kaina tare da fashewa da kuka, sai da na yi mai isata na ta shi na shiga ɗaki, zaman gidanma ya isheni tun da na zo gidan ban taɓa fita ba ko sau ɗaya, a yanzu an kai wata uku zuwa huɗu amma ban taɓa fita ba ko gida ban je ba, sai gidan kitso da naje sau ɗaya.

Kwanciya na yi akan gadon na shiga tunanin rayuwa, da irin abubuwan da Sardauna ya sadaukar akaina, gashi kuma yana ƙara fuskantar wasu. 

“Lallai Sardauna ya cika sadauki, Allah Ka ƙara mai lafiya da arziƙi, Allah Ka ƙarawa Sardaunana haƙuri da juriya akan abubuwanda suke tun karoshi, Allah Ka sani ina son bawan nan naka, Allah Ka so shi, ka yarda da shi, ka amince masa akan duk abinda ya sa gaba.” 

Cikin ikon Allah wani bacci ya ɗaukeni, wanda kiran sallar magariba ne ya tayar da ni, ina tashi na ɗaura alwala na yi sallah, dan yanzu Sarduna a waje yake magariba, idan aka yi isha kuma ya fita, tara da rabi zuwa goma yake dawowa. 

Ina idar da sallah na shiga haɗa masa abinci akan dinning, ina cikin haɗawa ya shigo, fuskarsa kamar kullum amma yau ma tafi raunana, ajiye abinda nake na yi tare da tawowa inda yake. 

“Sannu da zuwa Mijina.” 

“Yawwa Nana.” 

“Ya ofis?”

“Nana rayuwa babu daɗi, abubuwa duk sun kacame.” 

“Innullahi wa inna illahir raji’un, me aka sake cewa kuma?” 

“Mene ma ba a ce ba Nana, mene ba a ce ba? Kinsan yau kwanakin da Big Daddy yaban zasu ƙare gashi babu wata mafita da muka samu.” 

“Ya baka kwanaki ne?” 

Na tambaya cike da mamaki, ya gyaɗa kai kawai, sai kusan minti biyar sannan ya ce. 

“Big Daddy ya ban 10days akan na fitar da mafita, na ce ya ƙara min zuwa sati biyu to kinga yau anyi sati biyun.” 

Hawaye na ji suna gangaromin a fuskata, da sauri na gogesu sabida kar Sardauna ya gani, ni da zan ƙarfafa masa gwiwa bai kamata na raunana ba. 

“Nana bansan abinda Big Daddy zai ce ba.” 

“Ni kaina kwana biyu na dage da addu’a sosai da sosai, abinda nake gudu kenan tun farko akan rashin haihuwar nan ka ce kai ba komai, yanzu ga shi komai ya juye.” 

“Nana ni kaina matsamin aka yi a gida, shi ya sa kuma wallahi nauyinki nake ji Nana, ina jin kunyar yi miki magana akan haihuwa Nana.” 

“Nasani, duk wannan matsi da takurar da muka shiga akan haihuwa ba ra ayinka ba ne, na kasance me yi maka uziri a ko yaushe Sardauna, ina sonka son da na yarda da kai fiye da kowa fiye da komai, na yi imanin har abada ba zaka taɓa cutar da zuciyata ba Sardauna.” 

Na kama hannunsa, ya ɗago ya kalle ni. Idanuwansa fal da damuwar da ta dame ni. 

“A ko da yaushe ina miƙawa ubangiji Amanarka Sardauna, ina miƙawa Allah ragamar kula da kai, nasani Allah zai amss addu’a ta, ba zai taɓa ɗoramin abinda zaifi ƙarfinka ba, a ko da yaushe ina sonka zan kasance mai sonka Sardauna har numfashi na ƙarshe.”

Ji na yi ya jawo ni jikinsa ya rugumeni tare da faɗin. 

“Nana, bani da wata kalma guda ɗaya da zan iya godewa kan alherin soyayyarki agareni, Nana nasami damarmaki masu yawa sanadiyar soyayyarki, na gode Nana, nima ina sonki.”

Haka mu ka yi ta lallaɓar juna, ina ƙara nunawa Sardauna girman soyayyarsa a zuciyata, har na samu ya ci abinci ya shirya ya fita Majalisa.  Sai goma ya dawo gida, ina nan inda ya barni ina ta faman saƙe saƙe dan yanzu babu abinda na ƙware da shi kamar damuwa, ina saƙa wancan na since wancan. 

“Honey baki yi bacci ba?” 

Ya faɗa yana zama. 

“Ban yi ba tukunna, har ka dawo?”

“Eyh na dawo Honey, kin ga.”

Ya faɗa yana buɗe ledar da ya shigo ita, kwalin wayar iphone, ya miƙomin. 

“Nana take.” 

Na sa hannu na amsa ina mai jindaɗi. 

“Buɗe mana.” 

Na fara kici kicin buɗewa, iphone 16normal ce pink kala mai kyau. 

“Na gode sosai mijina, Allah Ya ƙara arziƙi lafiya da wadata.” 

“Amin My love.” 

Ya faɗa tare da ɗaukana zuwa ɗaki. 

Washe gari Sardauna bai fita ko ina ba, muna gida gashi ba weekend ba, da na tambayeshi sai ya ce. 

“Bana som fita ofis, zan haɗu da Big Daddy. Kuma kinga yau kwana goma sha huɗu ta cika.” 

Kamo hannunsa na yi, sannan na ce. 

“Wane irim hukunci kake tunani kake tunanin zai yanke?” 

“Nima bansani ba, amma bana son ya bani hukunci mai tsauri Nana.” 

“Duk tsaurinsa bai zai yanke ma hukuncin da zaka rasa rayuwarka ba, Sardauna nasan ba zai yanke ma hukuncin da zai cutar da lafiyarka ba, to ina ganin duk wani hukunci da ya biyo bayan wannan mao sauƙi ne a wajena da kai, ni zan ta ya ka karɓar kowanne irim hukunci ne Mijina.” 

“Na gode Nana, Na gode amma bana son wani hukunci da zai cutar da rayuwarmu, ko wani hukunci da zai sa mu yi abinda ba zamu ji daɗi ba, Nana ke nake so ke kaɗai a duniya, ban damu da ‘ya’ya ko rashin su ba Nana, amma tabbas ina jin ba daɗi idan na ga Hajiya ta a cikin halin damuwa, na kan ji zafi idan na ga Alhajina a cikin damuwa, duk akan yara.” 

“A kullum kaine mai cemin haihuwa da rashinta duk na Allah ne, akan wannan na tashi, akan shi na ɗaura yarda ta, kuma nasan suma sun san da haka, dan haka nasan ba zasu yanke maka hukuncin da zaka kasa ɗauka ba.” 

“Nana ki yi haƙuri, na yi miki laifi mai girma.” 

A tsorace na ce. 

“Wane irin laifi kuma?”

“Nana, na sanar da Hajiya asalin matsalal rashin haihuwarmu, a tunani za ta fahimta ko ta yi mana uziri, kuma nasan ta sanar da Big Daddy.” 

Shiru na yi na rasa me zance, yanzu tun da sun san matsalal daga wajena ne zasu iya cewa ya sakeni? A fili na furta. 

“Innullahi wa inna illahir raji’un.” 

“Nana calm down kin ji, ko mai zai zo da sauƙi, kece mai faɗin haka.” 

Gaba ɗaya na tsorata idan babu Sardauna ina zan sa rayuwata ni Nana, ina zan kalla na ji daɗi, ta ina zan iya numfashi bayan babi Sardauna a kusa da ni, na shiga uku ni Nana. 

“Ki nutsu ba zasu yanke hukunci mai kamar wanda kike tunani ba in sha Allah.” 

Cikin muryar kuka na fara magana. 

“Wallahi cewa zasu yi ka sake ni wallahi, me ya sa  ka faɗa musu haka?” 

“Nana baza su ce haka ba kwata kwata, in sha Allahu.”

“Sardauna.” 

Na faɗa tare da tsugunnawa a ƙasa.

“Na’am Nana.” 

“Dan Allah, dan Annabi da girman iyayenka Sardauna kar ka sake ni, ko mene zai faru, wallahi ina sonka, ina sonka ban da wanda nake so bayan kai, Sardauna idan ka rabu dani bani da wata rana a rayuwata, ka yi min alƙwari dan Allah.” 

“Tashi Nana, tashi ki zauna.” 

Ya faɗa yana kamoni na zauna. 

“Nana, ina sonki fiye da yadda kike tunani, na yi yaƙi mai girma kafin na aureki, sabida haka zan yi wani yaƙin akan na rayu da ke.” 

“Tabbas Sardauna idan ba kai ni gawa ce.” 

“Nasani Nana.” 

“Sardauna kai ne dalilin da yasa nake numfashi, Sardauna kai ne dalilin da murmushi yakw fitowa a fuskata, ka tausayamin dan Allah.” 

Rumgume ni Sardauna ya yi sannan ya ce.

“Nana, na yi miki alƙwarin duk tsanani dui wuya ba zan taɓa rabuwa dake ba, ko da ke ce kika buƙaci haka, Nana wallahi ina yi miki kishin da bazan iya numfashi ba muddin na ga wani namiji a tare dake, ko da ɗan gidanku ne, Nana a ƙarƙashin ikona zaki rayu, anan zaki mutu na yi miƙi alƙwarin hakan Nana.” 

Duk wasu kalamam Sardauna daɗi suke mim a rayuwa, babban buri na shine na rayu na kuma mutu a ƙarƙashin auren Sardauna. Yinin ranar bai fita ba sai dare, haka washe gari ma wai duk akan big Daddy, sai da ya kwana uki a gida sannan ya yanke shawarar zai fita, shima dai duk a tsorace yake. Ni kuma wani tausayinsa ne yake taɓa min zuciya, Allah Ya gani bana son wani abu da zai dami mijina ko kaɗan, bayan ya fita na yi ayyukana na kwanta bacci. 

*****

06:30pm

Yamma ce mai cike da sanyi, ina zaune a falo ina jiran dawowar Sardauna. Tun safe bayan ya fita na ji zuciyata tana bugawa, wani irin nauyi nake ji wanda na kasa fassara shi.  Ko da na yi bacci wani irin mafarki na yi marar daɗi, amma abinda ya kwantar min da hankali shine ba Sardauna ba ne a mafarkin ni ce, ni kuma nasan ina zaune anan babu wani abu da zai sameni, duk da a mafarkin ganina na yi ina kuka a zaune a falon nan, amma yanayin kujeruj falon su sauya kuɓa duk hotona na da suke falon babu su, nasan dai wannan duk mafarki ne. 

Ina zaune ina ta faman addu’a Allah Ya sa alherine, duk da al’amuran gidansu Sardaina sun dame ni sosai da sosai, gashi rabon Bilkisu da gidan nan an kwana biyu, sai dai ta waya da muke magana. Ina jin ƙarar motarsa, na tashi da sauri don na tarbe shi kamar yadda na saba.

Ina buɗe ƙofar, na gan shi tsaye, amma yanayin da na ganshi ya sanya na sandare a wajen. Sardauna ne, amma ba wannan Sardaunan mai takama da izza ba. Idanunsa sun yi jajir, fuskarsa ta kumbura alamar ya sha kuka, har lokacin hawaye suna zirara a kumatunsa.

Legendspen
***