20
by @legendspen
“Sardauna! Me ya faru? Me ya faru da kai?” Na faɗa muryata tana rawa, hankalina ya gama tashi.
Bai ce mini komai ba, ya ƙaraso cikin falon ya zube a kan kujera, ya rufe fuskarsa a cikin tafin hannunsa, kuka yake yi mai taba zuciya, yana girgiza kai tamkar wanda aka yi wa rasuwa. Ban san lokacin da nima hawaye suka fara wanke mini fuska ba, na durƙusa a gabansa na kamo hannunsa.
“Don Allah Sardauna ka yi magana, ka tsoratar da ni. Ko wani ne ya rasu a gidan?”
Ya ɗago idanunsa waɗanda suka rine suka yi ja, ya kalle ni da wani irin tausayi, sannan ya fara magana cikin muryarsa wadda ta dashe sabida da kuka.
“Nana... gara ma mutuwa ta ɗauke ni na huta da wannan mummunar kaddarar. Nana, Big Daddy da Hajiya sun sanya ni a gaba sun ce lallai sai na ƙara aure. Wai saboda har yanzu shiru ba ki samu juna biyu ba. Kuma matsalal daga gareki take Nana, su kuma ba za su iya jure hakan ba, tun da ba asan zuwa lokacin da mahaifar taki za ta yi ƙwari ba Nana, ina cikin damuwa gwanda mutuwa ta ɗaukeni da wannan abun.”
Wani irin jiri na ji ya kwashe ni, na ji numfashina yana shirin ɗaukewa. Aure? Sardauna zai ƙara aure?
“Sun ce... sun ce idan ban yi ba, to za su cire ni daga cikin komai na gidan. Nana, na yi kuka, na roƙe su, na ce musu ke kaɗai kika isa ki zama uwar ’ya’yana, ke kaɗai nake so Nana ke kaɗai nasani a cikin duka matan duniya amma sun ƙi saurare na. Wai ko dai na sake ki ko kuma na yarda na ƙara aure, idan lokacin da suka ba ni ya cika to za su aura mini wata ko wace.”
Ya sake fashewa da wani sabon kukan, ya jawo ni ya rungume ni yana kuka a kafaɗata, ni kuwa kamar mutun-Mutumi haka nake jina, ba na gane komai.
“Nana, ba zan iya rabuwa da ke ba, amma kuma ba zan iya saɓa wa magabata na ba. Ina son ki Nana, amma kaddara tana shirin raba mana farin ciki.”
Nima kukan nake yi kamar raina zai fita. Ganin yadda Sardauna yake zubar da hawaye saboda ni, ganin yadda yake nuna mini yana cikin matsanancin hali, sai na ji duk duniya ba ni da masoyi kamarsa. Na ji tausayinsa ya mamaye mini zuciya, har na manta da zafin kishin da yake shirin shiga rayuwata.
“Ka yi haƙuri Sardauna,”
na faɗa cikin dasasshiyar murya.
“Idan har hakan shi ne zai kawo maka kwanciyar hankali a gida, to ka bi maganar su. Ba na son ka shiga matsala da iyayenka saboda ni.”
A daidai wannan lokacin, na lura da wani ɗan gajeren murmushi da ya gifta a fuskarsa ba tare da na fuskanci ma’anarsa ba. Sai na ga ya ɗago ya kalleni, ya sake murmushin.
“Nana kina da hankali? Kinsan me kike cewa? Na je na yi auren haka kike cewa Nana wa zan aura, wa na sani? Kin taɓa ganina da wata mace? Kin taɓa kamani da wata mace? Nana ba kya kishina ne ko me?”
Da sauri na girgiza kai sannan na ce.
“A’a ba haka ba ne, amma ina ganin bamu da wata mafita a yanzu da ta kai hakan, babu ita dole ne mu yi biyayya, idan muna son kasancewa tare.”
Kuka ya sake fashewa da shi, tare da tashi ya shige cikin ɗaki. Yana tashi na bi bayanshi har zuwa cikin ɗakin, nasan dole a yanzu ni zan tausashi Sardauna, tabbas yana cikin damuwa mai girma nina sani. Zama na yi akan gadon kamar yadda ya yi.
“Kai daina tagumin nan dan Allah.”
“Hhhm! Nana idan banyi tagumi ba me zanyi? Ina da abun yi ne? Wai baki ji abinda na ce miki ba aure fa, aure suka ce na sake nan da two weeks ko zasu bani wacca suka ga dama kuma na sake ki.”
“Nasan sun yi fushine, amma ka bi komai a hankali nasan Hajiya za ta sake fahimta dan Allah.”
“Nana kina nufin na je na yi musu wani bayani? Kina tunanin akwai abinda ban faɗa musu ba? Nana kin raina girman soyayyarki a zuciyata ne?”
“Ko kaɗan ba haka nake nufi ba wallahi, ina nufin mu nutsu mu sami mafita a hankali.”
“Kina da mafita? Dan Allah Nana na faɗa min.”
“A yanzu dai babu, amma dole na yi tunani na sami mafita domin matsalalka matsala ta ce.”
“Allah Ya bamu mafita Nana, ki yi haƙuri kin ji ko?”
“Dame? Me ka yi min haka? Kai zan bawa haƙuri Sardauna.”
******
Washe gari Sardauna bai fita ko ina ba, yana gida gaba ɗaya babu abinda yake iya zuwa, ni ke ta ɗawainiya da shi kamar ƙaramin yaro, kuka kuwa ya yi yafi a ƙirga. Gaba ɗaya bai bani wata dama da zan yi wani tunani ba, gashi a yadda ƙwaƙwalwata ta toshe ina buƙatar isashen hutu kafin na yi tunani, nasan matsala ta babba ce amma har yanzu naƙi yardarwa kaina matsalar babba ce, gani nake akan Sardauna komai zan iya yi.
Sai wajen ƙarfe biyar sannan ya shirya ya fita, bai daɗe da fita ba na kira wayar Bilkisu, ina kira ta ɗauka, cikin muryata dake cike da damuwa na fara magana.
“Sister kin daina zuwa kwata kwata, abubuwa duk sun caɓe mini.”
“Ba haka ba ne Nana, nima ayyuka sunyi min yawa ga wata matsala da ta fara kunnomin kai a gida.”
“Ya salam, ni kaina abubuwam sunyi yawa daga gidansu Sardauna.”
“Nana tun da gidansu Sardauna ne ai da sauƙi, nifa akan kaina nake magana, Nana kinsan Abbanmu ya bani sati ɗaya na fito da mijin aure ko ya auramin wani abokinsa, Nana dattijo ne ya kai kusan shekara 70, gashi kinsan ni babu wanda nake kulawa, Nana ina cikin damuwa.”
“Allah Sarki ‘yar uwa, muma makamanciyar matsalalki muke fuskanta.”
“Bangane ba?”
“Gidansu Sardauna sun matsa mishi akan ya ƙara aure.”
“Saboda me to?”
“Rashin haihuwa mana.”
“Nana kika ce kin yi ɓari har sau biyu, kuma kince mahaifarki ce ba ta yi ƙanƙanta ko?”
“Hakane.”
“To ai zaki haihu Nana, ki yi musu bayani mana.”
“Bilkisu ba zaki gane ba, a yanzu dole Sardauna sai ya ƙara aure ko kuma ya sake ni.”
Na faɗa ina fashewa da wani irin Kuka, bana son kalmar sakinan ko kaɗan a rayuwata.
“Idan har haka ne mafita Nana ki amince masa, tun da kina son sa, kina son farin cikinsa, farin cikin iyayensa ai shine nashi, Nana ke kika ce kina son Sardauna sama da kowa sama sa komai, to ki nuna masa a wannan lokacin, ki nuna masa soyayya ki dage ki danne ki barshi ya yi auren.”
“To ai ba anan matsalal take ba.”
“Nana ga Momy nan mu yi magana anjima.”
Ta faɗa tana kashe wayarta, bayan wayar ta mutu ta barni cikim tunani. ‘Idan da gaske nake son Sardauna yanzu ne lokacin da zan nuna masa soyayyar ta hanayar ƙarfafa masa gwiwa kenan? To amma Sardauna baya kula mata ba ruwansa.’
Wani ɓari daga zuciyata ya ce da ni. ‘Ko a wajen aikinsa ba zai rasa ba, ko a ‘yan uwansu.’
‘A ‘yan uwansu fa?’ Na tambayi kaina.
‘Kai a’a gaskiyya a gari kawai ya nema ya aura, zanyi haƙuri zanyi biyyaya in sha Allah.’
Wannan ita ce shawarar da na yanke akan Sardauna, ita ce mafita guda ɗaya da nake ganin za ta fiye mana daga ni har shi. Sai wajen ƙarfe tara ya dawo, ina zaune a falo ya shigo.
“Sannu da gida Honey.”
“Yawwa sannu da dawowa.” Na amsa masa, kasancewar ba shigar ofis ba ce yasa ban cire mai takalmi ko wani abu ba.
“Ga abinci.”
“Honey ba ni da nutsuwar cin abinci, ni kaɗai nasan abinda nake tun kara Honey, ni kaɗai nasan abinda nake ji.Hon ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, rayuwa ta yi min baƙi mutuncina yana watangarirya.”
“Ka yi haƙuri, komai ya yi tsanani sauƙi yana tafe, a yanzu na yi tunani kuma na fitar da wata shawara da nake ganin kamar ita ce mafita Hon.”
“Mecece? faɗamin dan Allah.”
“Hon, rayuwa tana bamu zaɓi da dama, wani abun da muka tsara da kanmu, wasu kuma sukan afku ba tare da muntsara su ba, kamar yadda bamu taɓa tsara zamu san juna ba kafin nan, haka bamu taɓa tsara zamanmu zai zo da wata tangarɗa ba bayan munsan juna, Honey ubangiji ne ya dasamin sonka a zuciyata, na yi imani da Allah na yi imani da soyayyar da kake min Hon, dan haka ni dai a ganina kawai ƙara auren ne mafita agaremu dukkanmu. Duk son da nake yi maka, duk ƙaunar da nake yi miki ba ta da wani amfani a ranar da narasa ka, a ranar da nazama ba mallakinka ba, duk wata iriyar soyayyarka da nake ji ba ta wata rana. Idan har ina son ka me zai sa ba zan so ma farin ciki ba? Me zai sa bazan so ma ladan biyayya ga iyaye ba? Menene wata riba a duniya da ta wuce ta biyayya ga iyaye Sardauna?”
“Nana wai kina nufin kema kin amince na ƙara aure?”
Wani irin zafi nake ji a zuciyata a duk lokacin da Sardauna ya ambaci ƙara aure, amma ya zanyi ƙaddara ta riga fata, dole ne na goyi bayansa akan yiwa iyayensa biyayya.
“Na goyi bayan ka yi biyayya ne Sardauna, domin kasami rabauta da tsira a duniya.”
“Nana bazan iya ba, bazan iya ba, bazan iya ba wallahi, na yi miki kishiya fa Nana, wa zan aura to? Wa nasani ma bayan ke?”
“Ka duba zaka samu in sha Allah.”
“Cikani.”
Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa.
“Ka fahimce ni dan Allah, idan fa baka yi auren ba rasani zaka yi, zasu ce ka sake ni.”
“Nana su faɗa, ai ba lallai ba ne na yi musu biyayya.”
“A’a Sardauna, idan ka neman albarka dole ka yi wa iyayenka biyayya, ni dai ka fahimce ni.”
“Nana kenan, wace kalal fahimta zan miki? Zancen ki anan babu abinda yake nunawa sai zallar rashi Kishina, Nana kalamanki tsaf zasu yi wa zuciyata Sartse mai raɗaɗi.”
Kuka ne ya ci ƙarfina, ni a yanzu ai angama yi wa zuciyata Sartse gaba ɗaya, domin duk lokacin da na ji a raina wai Sardauna zai ƙara aure sai na ji wani raɗaɗi daga cikin zuciyata mai haɗe da ya ji, amma yana iya? Dole na so farin cikin mijina sama da komai a wannan rayuwar.
“Ka yi haƙuri Sardauna.”
Na faɗa ina jawo shi jikina, ya rungume ni iya ƙarfinsa kamar zai mayar da ni jikinsa, ina jin yadda yake shasheƙar kuka.
“Ka yi haƙuri ka ji.”
“Ya zanyi Nana?”
“Ka yi tunani ta ina ka haɗu da ni, har ka tun kare ni, nasan zaka samu zaka samu wacca zaka iya aura.”
“Nana bana so su bani a dangi, bana so su ce na rabu dake Nana, bazan iya ba.”
“A waje zaka samu.”
“Hhhm, Nana kenan.”
*******
Har dare Sardauna ya kasa fahimta ta, ya kasa fahimtar inda zance na yake son nufa, a haka muka haƙura mu ka kwanata, sai dai fa ni bacci yaƙi zuwa idona, tunani nake anya zan iya kasadar barin wata kusa da Sardauna, babban abinda yafi bani mamaki, ban ji mahaukacin zafi a cikin zuciyata ba akan zancen ƙarin auren, zafin da fi ji shine na rabuwa da ni, ko dan maganar sake ta shigo ita ce ta cire min raɗaɗin kishin? Amma kwata kwata ban ji ina mugun kishi ba, ko a baya ma bana iya tuna kishin da na yi akan Sardauna ba.
Ƙarfe uku na dare na tashi, bayan na yi nafila raka’a biyu na yi addu’o sosai, sannan na dawo na kwanta, sai a lokacin bacci ya ɗauke ni.
Washe gari ma haka muka tashi da Sardauna yanayin babj daɗi, na yi masa bayani yafi sau cikin carbi amma amsa ɗaya yake ba ni.
“Honey bazan iya ba, Honey ban da ita.”
Ya koma kamar wani ƙaramin yaro ba abinda yake iya ganewa, abinda ya ƙaramin tausayin Sardauna kenan, gaba ɗaya ji nake duk ni ce na ja masa komai ma, ko kuma na ji dama akaina waɗannnan abubuwan suke faruwa ba akan Sardauna ba, domin duk damuwar sardauna guda ɗaya, sau dubu nake jinta a zuciyata.
Legendspen
***