SARTSE COMPLETE

21

by @legendspen

Da ƙyar na iya lallaɓa Sardauna ya fita ofis, amma da ya ce wai bazai iya fita ba sabida kowa ya ganshi zai san yana cikin damuwa. Sai da na yi masa daɗin baki sosai na nuna masa babu wanda zai gane yana cikin damuwa, sannan ya fita. 

Tun bayan tafiyar Sardauna na shiga aikina na kullum, amma sai dai na yau zuciyata tafi nuna min wa Sardauna zai aura, wani irin zama zamuyi shin zai so ta kamar yadda ya so ni, ko ma zaifi sonta, za ta yi masa biyayya irin yadda nake yi? Ko za tafi ni? Dole fa na dinga raba mata kwana da Sardauna, duk da hakan bai dameni ba amma tabbas ina jin ba daɗi. 

Har yamma ina ta faman tunani, da kuma tsoron me Sardauna zai dawo da shi, zai sami matar ne ko sai gobe?

"Ya Allah ka sa wannan auren ya zama ƙarshen duk wata wahala, da wani tashin hankali." 

Knocking na ji ana yi min, na tashi a raina ina addu'ar Allah Ya sa Bilkisu ce, sai ina buɗewa na ga Turaki. 

"Ina wuni?" 

"Lafiya ƙalau Nana." 

Ya faɗa yana kallona, ganin shirun ya yi yawa na ce. 

"Bayan nan." 

"Nana komai lafiya a gidanki?" 

"Lafiya ƙalau." 

"Kinje wajensu Hajiya?" 

"Na je." 

"Amma Ra'is ya ce kin fi watanni baki je ba, me ya sa?" 

"Ina zuwa." 

"Nana yakamata kije ki yi magana da Hajiya, ki faɗa mata duk wata matsala da take damunki." 

Yana faɗin haka ya juya ya shige ɓangarensa, haka na dawo ciki duk jikina babu daɗi, ni shikenan kullum rayuwata a babu daɗi, zaman ba daɗi, gidan ba daɗi, ni narasa wace irin rayuwar aure ma nake yi. 

Waya ta na ɗauka na kira Hajiya, na yi sa'a kira ɗaya ta ɗauka. Bayan mun gaisa nake ce mata bani da lafiya ne kwana biyu. 

"Me yake damunki?" 

"Hajiya na yi ɓari ne."

"Allah Ya ƙara lafiya."

"Amin Hajiya, ya mutan gidan?" 

"Nana kowa yana lafiya, Ra'is ya ce kun yu waya kwanaki, Nana duk wanda na ce ya zo gidanki sai ya ce bazai zo ba mijinki, sai  da wancan ɗan Albarkan Turaki ya zo na yi masa magana, nasan yanzu ma shi ya yi miki magana ko?" 

"Eyh Hajiya shine." 

"Nana ki dinga addu'a kin ji." 

"In sha Allah Hajiya." 

*****

Wayar da na yi da Hajiya ta rage min wani abu daga cikin damuwar da nake ciki, yamma lis sai ga Bilkisu ta zo itama a kiɗime, al'amarin mahaifinta ya ta azzara akan auren da ya ce  zai yi mata. 

Itama gaba ɗaya ta yi wani sukuku, ta fita hayyacinta. 

"Bilkisu to ke ki duba cikin masu zuwa wajenki mana."

Na faɗa dan dai nasan Bilkisu ba zata taɓa rasa masu zuwa wajenta ba, domin dai tana da kyanta yadda yakamata, ga ilimi kuma yar gayu ce sosai da sosai. 

"Nana bazaki gane ba kwata kwata, duk masu zuwa wajena ba na aure ba ne, burinsu na basu haɗin kai su ɓarar mun da mutunci su cuceni."

"Ya salam, Allah Ya tsare ki."

"Amin amin, ku yanzu kun sami matsaya?" 

"Eyh mun samu, aure kawai Sardauna zai ƙara kamar yadda suka umarta."

"Allah Sarki Nana gaskiyya kinyi namijin ƙoƙari Allah Ya baki haihuwar nan." 

"Amin Bilkisu, Allah Ya kawo miki mafita." 

Itama ta ce Amin, nan muka zauna kowa na jajantawa kowa har Sardauna ya dawo ya sameta, sai bayan ya dawo ta tafi. 

A yanayin Sardauna na yau dai babu wata sabuwar matsalal, kuma na ji daɗin hakan sosai da sosai, haka washe gari ma babu wata matsalal. Al'amuran kamar sun sauƙaƙa wajen kwana biyar, sai ranar kwana na huɗu Sardauna ya dawo cikin tashin hankali, Hajiyarsa ta ce lallai lallai ya sake ni idan har bai fito da mata ba cikin kwana biyu, a kiɗime na ce. 

"To baka ce musu kana dubawa ba ne?" 

"Nana wa zan duba, har yanzu fa ban ga wata da na ji zan iya haɗa ta dake ba, Nana mata basu da kama ko kaɗan, bazan iya auren wacca zata hulaƙanta ki ba ko kaɗan Nana." 

"Kar ka damu Sardauna, ni zan iya zama da kowace muddin kana nan kuma kana ganina a matsayin da kake ganina yanzu, Sardauna ka auri duk wacca ta yi maka." 

"Nana anya kuwa kina kishi na?" 

Kallonshi na yi, sannan na kalli ƙasa. 

"Tayar maka da hankali shine kishi? Sardauna indai sai na ɗaga maka hankali na saka a damuwa bayan wacca kake ciki shine kishi to ni bana kishi, hasali ma babu zuciya a tare da ni, ina sonka a kowanne irin hali, zan ci gaba da sonka a kowanne irin yanayi Sardauna." 

"Nana bana jin zan iya neman wacca zan aura, ina neman alfarma a wajenki guda ɗaya dan Allah." 

Ya faɗa yan goge ƙwallar da take idonsa, bai bari na yi magana ba ya tsugguna a gabana, tare da riƙe min hannuna. 

"Nana! Dan Allah, dan girman ma'aiki ki ta ya ni duba wacca zan aura, Nana kowa kika kawo indai kin aminta da ita to zan aura Nana, dan ke zan yi auren kuma ina so ki nema min waccan zan aura da kanki da hannunki Nana." 

Wani irin nauyi na ji ya danne ni kamar an ɗauramin gungumen dutse. Tabbas wannan alfarmar da Sardauna ya nema a wajena da girma take, ta ina zan fara? 

"Nana dan Allah, mutuncina da darajata duk suna hannunki a yanzu ki tallafa min Nana." 

"Ka tashi zaune dan Allah." 

"Nana ki yi min wannan alfarmar dan Allah." 

"Tom na yi ka tashi zaune ka ji."

"Na gode Nana."

Ya faɗa tare da zama kan kujerar, ya ƙureni da ido sannan ya ce. 

"Nana!" 

"Na'am." 

"Na ga kin rame kamar bakya cin abinci?" 

Kallon jikina na yi, ni banga wata rama ba amma tabbas nasan a jikina ina jina falai falai kamar wata takarda. 

"Nana kamar ba kya cikin ni'imar aure, matar Ta Ambo ce a haka Nana?"

"Ba wata rama da na yi fa, kawai strees ne."

"Name?" 

"Abubuwan da suka dagule mana, komai ya rincaɓe." 

"Nana ai komai yazo ƙarshe ko? Komai zai yu sauƙi tunda a yanzu za ayi auren kuma ai shikenan ko?" 

"Eyh shikenan in sha Allah." 

"Yawwa Nanaty, zan ci abinci." 

Tashi na yi ma nufi wajen dinnig ɗin, shi kuma yana biye da ni a baya, alkubus da miyar taushe ne na yi, ya zauna ya ci sosai nima kuma ya matsamin sai na ce, yadda ya ci haka na ce. Ko majalisar ma baije ba ya kwashe ne muka yi ɗaki, duk ranar da Sardauna ya ɗaukeni da kansa ina shan wahala har nagane, shi ya sa bana so ya ɗaukeni nafi son mu tafi ƙafa da ƙafa. 

Tun daga wannan lokaci Sardauna ya sani a wata duniyar ta daban, kullum aikina tunanin wace za ta da ce da Sardauna, dan ya zama dole na nema masa a ƙasa da kwana ukun da ya ambata. Ƙawayena Malaika ta yi aure tana kano, Fauziya ta yi aure, Amina Aminu ma ta yi aurenta daman su kenan, Yaya Radiya kuma Yayata ce babu aure a tsakaninsu, Anty Adiza kuma matar aure ce, ni kuma su kaɗai ne mutanen da nasani, sai dai ko Bilkisu ita kuma aure ne ba ta so a yanzu. 

"Ni fa ina ganin can yaje danginsu ya nema, zai fi mana sauƙi." 

Na faɗa a fili kamar ina magana da wani ko wata, ko da ya dawo ma baiyi min maganar ba kuma nima bance komai ba, washe gari ma haka na yi ta faman tunani, sai gab da yamma na shirya naje gidan kitso wanda daman na tambayeshi, tun zuwana unguwar gidan kitson kawai nake zuwa shima sai na yi wata nawa banje ba. A hanya na yi ya kallon 'yan mata ko akwai wacce za ta da ce da Sardauna, amma bansamu ba. Haka a gidan kitson ina zaune ina kallon mutane sai hira suke, a ɗauko gulmar waccan a sauke a ɗauki ta waccan har layi yazo kaina ni dai ban tanka musu ba. 

"Baiwar Allah a wane gida kike?" 

Wata mata ta tambayeni. 

"Nan baya." 

"Ina ne baya ko ba anan kike ba?"

Wata daban ta yi tambayar.

"Eyh ina Takur Site C ne." 

"Eyh kam da dan nisa gaskiyya, amarya ce?" 

"A'a na shekara biyu." 

"Allah Sarki Allah Ya sanya alheri." 

"Amin." 

Na faɗa daga nan ban sake ce musu komai ba har aka gama yi min na tashi na tafi, a raina na ce. 

"Ina fita zaku hau yi dani." 

Illai kuwa ko ƙarasa fita ban yi ba na ji muryar wata ta ce. 

"Wai ita matan Takur sai wani shan ƙamshi ake." 

Murmushi na yi na ƙarasa ficewa ta, ba su san ɗimbin damuwar dake damuna ba ne shi ya sa ma suke wannan zancen. 

Har na ƙaraso gidana ina kallon 'yan mata hanya sai dai Allah bai sa na ga wadda zata da ce da mijina ba, haka na dawo gida shiru. Nan dai na yanke shawarar tamnbayarshi na ji ko akwai wata yarinya da yake burgeshi haka, ko yake yawan ganinta. 

Banyi masa maganar adawowarsa ta farko ba, sai da ya dawo daga Majalisa sannan na ce. 

"Na yi tunani a iya matan da nasani, amma kafin nan kai babu wata yarinya da ka sani ko kake ganin tana da hankali." 

"Nana bayan ke bansan kowa ba."

"Ko a wajen aikinku, ko a family?"

"Nana bayan ke bansan kowa ba." 

"Ka na ji, ko a unguwarku da kuna ƙanana?" 

"Nana unguwar da na taso ba irin Yalwawa ba ce, Unguwa ce da ba ruwan kowa da kowa, unguwa ce ta masu arziƙi babu talaka ko ɗaya a unguwar dan haka babu 'yar wanda nasani Nana, ba kamar ku ba cike da yara wani gidan na cin wani gidan, yara su shiga wancan gidan su fita wancan, mu duk ba haka muke ba."

A maganar sai na ji kamar gori, na yi mishi murmushin yaƙe sannan na ce. 

"Ba haka nake nufi ba ranka ya daɗe, irin ko a makaranta haka?" 

"Nana, zaki yi min ko bazaki yi ba? Idan bazaki yi ba just tell me, ba sai kina haɗani da ƙazamar rayuwa marar daraja ba, rayuwata ba irin wannan ba ce Nana. Ina ga har yanzu bakisan su waye Familyn mu ba Nana."

"Ka yi haƙuri, baka fahimce ni ba." 

"A'a ba wani ban fahimce ki ba Nana." 

"Ka yi haƙuri." 

Ta shi ya yi ya shige ɗaki ba tare da ya ce dani ko ƙala ba. 'Oh ni yau me yake damun Sardauna ne?.' Na tambayi kaina a zuci. 

Washe gari ma haka ya tashi yana faman cicin magani ko breakfast ma cewa ya yi wai ba zai ci ba. 

"Dan Allah me ya faru?" 

"Nana kinfi kowa sanin duk abinda ya faru."

"Bansan sani ba, bansan wani abu da ya faru wanda yasa ka canja baki ɗaya."

"Hhm! Nana sai na fito fili na faɗa miki cewar ki nemo min aure?"

"Ai akan wannan maganar muke kai kuma ina kan dubawa." 

"Su wa kika duba?" 

"Duk cikin ƙawayena kowacca ta yi aure." 

"Duka babu marar aure kenan?" 

"A na kusa dai babu, shi ya sa nake so kara faɗa tunanina don bincikawa." 

"Nana yau ne fa ranar ta ƙarshe da Hajiya ta bani." 

"Nasani kuma in sha Allah yau komai ƙare." 

"Nana ki yi duk abinda kike tunanin zaki iya, dan Allah." 

"In sha Allah, to muje ka yi breakfast ɗin." 

Muka nufi dinning ɗin, muna cikin breakfast ɗin Sardauna ya ce. 

"Nana! Ko zan samu ki wanken kayana ko guda biyu ne, na ji daɗin wancan da kika yi min." 

'Ashe Sardauna ya kula na yi masa wanki? Amma ko a ido bai taɓa nuna min ba, ko da yake gashi yanzu ya faɗa.' Murmushi na yi masa sannan na ce. 

"Babu damuwa, ko ban yi yau zanyi gobe."

"Me ya sa sai gobe."

"Idan ba mafita na samu akan wannan maganar ba bani da nutsuwar da zan iya yin wankin da zai burgeka ya yi maka kyau." 

"To shikenan, Allah Ya yi miki albarka Nanaty." 

"Amin amin." 

Tin fitar Sardauna nake tunanin inda za a sami mafitar ƙarshe, kwatsam Bilkisu ta kirani a waya, bayan na ɗaga muka gaisa na ce da ita. 

"Ya Abban naku?" 

"Nana ya ƙaramin one week ɗazu, na ji daɗi sosai wallahi Nana zan duba yanzu duk wanda yazo zan bashi fuska." 

"Ma sha Allah Bilkisu, Allah Ya kawo na gari."

"Amin Nana, na gode miki da nuna kulawa, zan je ofis mu yi magana anjima." 

Bayan ta kashe wayar kawai tunanin haɗa ta da Sardauna ya faɗomin. 

"Zaman Sardauna da Bilkisu zai yi ɗaya kuwa? Tsakanina da Bilkisu akwai fahimtar juna, akwai soyayya to amma Sardauna fa?" 

Legendspen
***.