22
by @legendspen
‘Sardauna baya son karatu? Bilkisu har aiki take yi, shin Bilkisu za ta iya barin aikinta sabida Sardauna, ko kuwa Sardauna zai iya haƙura ta yi aiki, ya ce kuma yana da kishi ba zai iya jurar matan shi na yawo a titi ba suna cakuɗuwa da maza, amma tabbas Bilkisu za ta dace da zamanmu a wannan ƙadamin, tun da itama mahaifinta ya bata lokaci kamar yadda Hajiyar Sardauna da Big Daddy suka ba shi?’
“To Nana hakan ba matsala?” Na ji wani ɓari na zuciyata ya faɗa a fili kamar wani daga wajene ya faɗa. ‘Sardauna yana sona, kuma Bilkisu tana sa ilimi zata zauna da ni da Sardauna lafiya, ni bani da wata matsala indai Sardauna na nan kuma yana kallona a matsayin mata ina ƙarƙashen inuwar aurensa.’
Waya ta na ɗauka na kira Bilkisu amma ba ta ɗauka ba, ƙila bata ƙarasa ofis ba sai kawai na tura mata text.
“Bilkisu dan Allah ki kirani, akwai mafitar da nake tunani wacca za ta kawo ƙarshen komai in sha Allah.”
Na tura mata tare da emoji na kuka da na roƙo, ina turawa na nemi lambar Yaya Rumaisa dan tabbas sai na sanar da wani nawa. Bugu ɗaya ta ɗauka tare da faɗin.
“Manya yau a gari?”
“Ina wuni Yaya?”
“Lafiya ƙalau Nana, ya gidan?”
“Alhamdullah Yaya, dan Allah wata magana zan faɗa miki amma bana son Hajiya ko wani ya sani.”
“Wace magana ce haka Nana?”
“Ki yi min alƙwari dan Allah.”
“Nana ya za ayi na yi alƙwari akan abinda bansani ba?”
“Dan Allah ki yi min, ba wani abu ba ne na cutarwa kawai labari zan baki.”
“Shikenan Nana na yi miki.”
Na sauke ajiyar zuciya sannan na ce.
“Zan ƙarawa Sardauna aure.”
“Bangane abinda kike nufi ba.”
“Yaya a gidansu aka bashi zaɓi guda biyu, tun da ni bana haihuwa mahaifata ba ta gama ƙwari ba ko ya sake ni su aura masa wata ko kuma ya ƙara aure.”
“Ke bana son rashin hankali, uban waye ya ce miki ba kya haihuwa?”
Ta faɗa cikin jarababbiyar muryarta.
“Munje asibiti sabida na yi ɓari har sau biyu, shine aka ce ba ta yi ƙwari ba.”
“To da zai sake auren shine ke zaki ƙara masa?”
“Yaya ya bani zaɓi ne akan na nema masa matar.”
“Wannan shine kuskure na biyu da zaki yi a rayuwarki da Sardauna, na farko kin zaɓi miji sama da kowa, sai da ya raba ki da ‘yan uwanki da duk wasu mutane a kusa dake shine zai ƙara aure? Nana wai uban me kike sha?”
“Yaya Umarni ne daga gida, shi ya sa ma ya bani damar zaɓa masa wadda zai aura.”
“Lallai Nana mahaukaciya ce ke? Dan mun yi alƙwarin bazamu sake shiga al’amuran gidanki ba, amma dai sai na zo har gidan na ci ubanki na ci uban mijin, banza marar hankali wace yarinyar kika zaɓa masa?”
“Wata maƙwafciyar mu ce.”
“Jaka! Nana bansan ki lalace ba sai yanzu.”
Tana faɗin haka ta katse kiranta, ni nama manta da halin faɗa irin na ta har na kira ta, gashi ta zageni ta zage mijin nawa gaba ɗaya, ita daman bata da haƙuri ba abinda ta iya sai faɗa a rayuwarta.
“Mitcheww.”
Na ja tsaki na kwanta akan kujera, banda rainin hankali irin Yaya Rumaisa mutumin da baya son auren ƙarshe ma yaban zaɓi shine za ta ce wai ya rabani da kowa shine zai ƙara aure. Duk sai da na yi danasanin kiranta, daman ita ba a fiya yin abun arziƙi a kwashe duka da ita ba, haka na yi ta faman ɓacin rai har yamma, yau indomie na yi wa Sardauna dan ba abinda zan iya sabida wani irin ciwon kai da na tashi dashi bayan na kwanta da yamma.
Fuskarsa babu yabo babu fallasa haka ya shigo cikin gidan.
“Sannu da zuwa.” Bai amsa ba ya ajiye jakarsa, yanayin da nake ji ma bazan iya tashi na bishi ba, yanda ya shiga ɗakin haka ya fito.
“Baki da lafiya ne?”
“Jiri nake ji.”
“Sannu, bama ki yi girki ba kenan?”
“Na yi.”
“Bari na ci.”
“Tom, akwai magana.”
“An samu?”
Na gyaɗa masa kai.
“Faɗamin to.”
“Ka fara cin abincin.”
“A’a faɗan.”
Sai da na tashi zaune na riƙe hannunsa.
“Kasan dai bazan zaɓa ma abinda zai cutar da ka ba, dan Allah ina son ka amshi zaɓin da na yi maka da hannu biyu biyu, kuma kasa a ranka alheri ce a garemu duka.”
“Nana duk jikina ya yi sanyi, wace ki faɗamin dan Allah.”
“Bilkisu! Wannan ƙawar ta wa ta kake ɗan ganinta.”
Shiru ya yi sai kuma can ya ce.
“Wata fara haka?”
“Eyh ita.”
“Anya Nana?”
“Dan Allah karka ce a’a.”
“Nana zan yi shawara.”
“Tom, amma da matsala guda fa?”
“Kinji ko? Wace matsalal?”
“Tana aiki.”
“Wane kalal aiki kuma?”
“Aikin Ofis, kuma ka ce ba zaka iya jure ganin matarka na cakuɗuwa da maza ba, shine nake so dan Allah ka yi haƙuri ka barta.”
“Nana sai na yi tunani gaskiyya, bari na ci abincin.”
Yana faɗin haka ya tashi ya nufi dinning ɗin, da kanshi ya zuba ya ce kuma bai yi magana akan indomie ɗin ba, ko da yaga ban jindaɗi ne?
*********
Yau Sardauna bai fita majalisa ba, da na tambayeshi sai ya ce bani da lafiya dole ya yi jinyata kuma gashi yana son ya yi tunanin akan al’amarin nan. Haka dai na yi bacci na barshi yana faman tunane tunane.
Washe gari bayan munyi breakfast zai fita ya ce da ni.
“Nana na yi tunani duba da yanayin da muke ciki na matsi Hajiya da Big Daddy na amince zan barta ta yi aikin na ta, amma gaskiyya bana so.”
Har cikin raina na ji daɗi.
“Alhamdulillah, Allah Ya sa albarka, yanzu sai na yi mata magana nasan zata amince itama.”
“Wannan ya rage naki.”
Ya faɗa yana ficewa, ni kuma na koma kan kujera na zauna, na ɗau wayata na fara kiran lambar Bilkisu, amma bata ɗauka ba, gashi message ɗin na jiya ma ba ta dawo da amsa ba. Sake kiranta na yi har ta gama ƙarar ta ba ta ɗauka ba, haka na ajiye wayar da tunanin an jima zan sake kiranta idan ba ta kirani ba. Har yamma ba ta kirani ba kuma nasake kira ba ta ɗauka ba, na yi ta addu’ar Allah Ya sa lafiya dai. Da ddaddare na faɗawa Sardauna na ce ya bani wayarsa na kira ta sai ya ce na sake kiranta dai. Ina kira kuwa ta ɗauka.
“Nana ki yi haƙuri, yau na yi busy da yawa wallahi, ina ta ganin kiranki ban sami zama ba.”
“Ayyah ba komai Bilkisu, ya gida ya aikin?”
“Alhamdullilah, ya mai gidan?”
“Lafiya ƙalau, na ce ya ake ciki da maganar Abban naku an da ce kuwa?”
“Tun da ya ƙaramin sati ɗaya bamu sake maganar ba, kuma kamar naga saƙonki ko? Kince kin sami mafita?”
“Eyh Bilkisu na samu wacca nake ganin za ta yi amfani wa ni dake.”
“Nana ai matsalal mu ba ta da alaƙa da juna.”
“Eyh Bilkisu sai dai kamanceceniya, Abbanku ya matsa miki, nima Hajiyar Sardauna ta matsa me zai hana Bilkisu mu haɗu a rufawa juna asiri, ki auri Mijina.”
“Nana kina da hankali? Kinsan abinda kike faɗa kuwa? Na auri mijinki Sardauna?”
“Is for the best Bilkisu Please.”
“Nana bazan iya ba, a yadda kike son mijinki na shiga ciki? Ki rufan asiri Nana.”
“Bilkisu ke ce last hope ɗina, aure na ma tangarɗa yake ki taimaka.”
“Lallai Nana, dan Allah ina so ki a ranki bamu taɓa wannan maganar ba dan Allah.”
Tana gama faɗin haka ta kashe wayar, na kalli Sardauna da yake zaune yana sauroro.
“Nana akawai wata bayan ita?”
Na girgiza kai sannan na ce.
“Ita kaɗai ce.”
“Nana to ya za ayi?”
“Ita ɗin dai, nasan za ta fahimta in sha Allah.”
“Nana banga alama ba, ki na ji ta ce yadda kike son mijinki ba za ta iya shiga tsakaninku ba.”
“Hhhm, idan ba ta shiga ba rasa ka zanyi gaba ɗaya.”
“Nana ki daina wannan tunanin ba zaki taɓa rasani ba, Nana a yadda nake jin ki a rayuwata idan babu ke nima ai babu ni.”
“Nima nasan ba zan rasa ka ba, amma biyayya ga iyaye dole ce idan muna neman albarka a rayuwa.”
“Nana bari na je gidan Hajiya na gara kiranta yanzu.”
“Tom Allah Ya tsare hanya.”
“Amin Ya Allah.”
Ya faɗa yana tashi, yana fita na sake kiranta a waya amma bata ɗauka ba, message na hau rubuta mata.
‘Salam, Bilkisu dan Allah ki fahimceni, ina so ki aure mijina Sardauna sabida ki tsira daga auren dole da zaayi miki, shima ya tsira daga auren dolen da za ayi masa ki fahimta dan Allah.’
Na tura mata amma har Sardauna ya dawo ba ta yi min reply ba, washe gari da safe ma na sake tura mata wani amma shima ba ta ce dani komai ba.
“Honey ya kuka yi da yarinyar?”
Kallonsa na yi sannan na ci gaba da haɗa mai tea ɗin, sai da na gama sannan na ce.
“Ba ta sake cewa komai ba, amma dai zan ƙoƙarta zan sake magana da ita.”
“Shikenan Nana, nasan zaki iya, Allah Ya yi miki albarka.”
“Amin Amin.”
Bayan mun kammala breakfast ya tafi, na dawo na ci gaba da kiran wayar Bilkisu amma bata ɗauka ba, ganin ba zata ɗauka ba na shiga fito da wankin kayan Sardauna na hau yi, da ƙarfi nake dirza kayan sabida ina son su fita su yi haske yanda zai ji daɗi, sai wajen la’asar na gama wankin na shanya su s abun shanyar mun na bayan kitchen, ina dawo na ga missed call ɗin Bilkisu, jikina har ɓari yake na ɗau wayar na kira ta, ina kira ta ɗauka, cikin rawar baki na fara magana.
“Bilkisu!”
“Na’am Nana.”
“Bilkisu kinga messages ɗina?”
“Nagani Nana, ni bansan abinda zance miki ba shi ya sa ma ban miki reply ba, kina magana kamar wata ‘yar ƙwaya.”
“Hhm Bilkisu ba zaki gane ba ne, amma dan Allah ki taimaka, ki taimakeni ki taimaki mijina.”
“Nana babu wata hanyar taimako da zan ia yi miki bayan wannan? Gaskiyya wannan abun yafi ƙarfina, ki barni da matsalal Abbana kawai.”
“Bilkisu dan Allah ki biyo ta gidana mu yi magana.”
“Nana bana jin zan sake zuwa gidanki, tun abinda kike son ƙullamin kenan? Ace na zo gidanki na aure miki miji, duniya ta yi ta zagina.”
“Haba Bilkisu ya zaki ce haka? Dan Allah kizo ko ba zaki aureshi ba nasan akwai shawarar da zaki ban.”
Shiru ta ɗanyi na ‘yan mintina sannan ta ce.
“Shikenan, bari na zo yanzu.”
“Tom Bilkisu na gode sosai.”
“Sai na zo.”
Ta faɗa tana kashe wayar, na koma na zauna. ‘A halin da Bilkisu take ciki na yi tunanin zata amshi wannan tayin hannu biyu biyu? Ko dan mafita da take nema, amma taƙi! Lallai Bilkisu ta cika mutuniyar arziƙi.’
Ta shi na yi na duba kayan Sardauna dana wanke, na fara kawahe waɗanda suka bushe na shiga dasu ciki, ina fitowa itama ta shigo ɗakin, ban bari ta zauna ba na fara mata magana.
“Haba Bilkisu, ahalin da kike ciki na yi tunanin wannan mafita ce a garemu duka?”
“Nana mafita ce mana, amma da ace wani ne ba mijinki ba, Nana da wane ido zan kalli duniya? Da wani ido zan kalli mutane zan kalli makwafta, zan kalli ‘yan uwanki, ace ina ƙawarki na zo na auri mijinki, zagin da zan sha Nana ba ƙarami ba ne, Nana tsinuwa zan sha a bakin jama’a, ta yanda babu yadda zaayi na kare kaina, tun da gani a gidan naki, Nana a dinga duba ana saran gatari.”
“Bilkisu mu zauna.” Na faɗa ina kama mata hannu, zaman ta yi sannan na ce.
“Ina ruwanmu da surutun wani? Waye zai sani? Waye zai san mi dake ƙawayene, Bilkisu ko sun sani mene a ciki? Ba dai mu muna zaune ba, nasani Bilkisu zaki zauna tare dani cikin aminci, mu kula da mijinmu, to ina ruwanmu da zancen mutane? Su yi ta yi kar su daina.”
“Idan ke kunnenki zai iya jurewa, to ni nawa ba zai ya jurewa ba. Nana bakisan mene bakin mutane ba, idan suka sa ka agaba wallahi duk wata albarka dai ka nemeta ka rasa, Nana idan ke kin fahimta ina ‘yan uwanki zasu fahimta?”
“Kishiya ce fa Bilkisu! Kuma ba Kaina farau ba ko karau? Mijina ne kaɗai ya taɓa ƙara aure?”
Hannuna ta kama sannan ta ce.
“Nana, ki yi haƙuri abar wannan maganar, kamar zata fi amfani Nana, idan duk na ce na ji nagani shi mijin naki fa? Yana sona? Zai soni? Zaman alfama Nana bazan iya ba dan Allah.”
“Salamu alaikun.”
Muyar Sarauna ta ratsa ɗakin, ban maji ko warn ɗinsa ba, kawai sallamarsa na ji.”
“Sannu da zuwa.”
“Yawwa sannu.”
“Sannu da zuwa.”
Bilkisu ta faɗa kanta yana ƙasa.
“Yawwa sannu.” Yana amsawa ya shige cikin ɗakin, bai ƙara sa shigewa ba Bilkisu ta miƙe tare da faɗin.
“Nana, zan tafi.”
“Bilkisu bamu gama magana ba.”
“Nana ni dai nagama yanke hukuncina.”
Tana faɗin haka ta fice, hannuna na ɗora a goshine tare da faɗin.
“Hhhm, Ya Allah.”
Ɗakin da ya shiga na bi shi, ina zuwa na tarar da shi zauna a kan gado, idanunsa sunyi jawur alamun ya ci kuka ya gode Allah.
Legendspen
***