Namiji Ƙanin Ajali (Book 01)

Chapter --- 12

by @amdeeytejjdunique587

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Namiji Ƙanin Ajali

By

Amdeey Tejj d'Unique

Page --- 12.


A cikin hirar ne yake bani labarin yadda ya kasance bayan rabuwarmu,"amma ke Haula kin samo wani abu awun barar taki?" Na'amsa masa da "eh ba laifi", kafin na sake magana yace"hmmmm mu kam dai sai a hankali,sai mutane ƙalilanne kawai masu tawakkali da sanin ya kamata,duk inda naje sai kiji mutane suna cewa waini da ƙarfina bazasu bani sadaka ba,dama sun saba ganin mutane irinmu da za suzo suna ƙarya suna karɓar kuɗin mutane, kuma waya hanani inje in nema suma da basu nema ba sun zauna barane da banzo ina nema a wajensu ba, ke dama maganganu makamantansu kowa da abin da zaice,sam bansan meyasa mutane basa la'akari komai ƙaddara ce ba,kuma komai da silarsa"nidai shiru nayi na rasa mai me zance sauraronsa kawai nakeyi ni bama wani fahimtarsa nakeyi sosai ba,dan tun daga farkon bayaninsa na farko a cikin kaina tunanina yayi nisa dani, ajiyar zuciya nayi sannan nace''Allah ya shige mana gaba dan duk abinda kaga ya faru jarabtace kuma Allah yana jarabtarmu ne dan ya gwada imaninmu, sai dai muyi addu'ar Allah yasa muci jarabawar,dan duk tsanani yana tare da sauƙi"na faɗa kawai batare da na faɗa masa tawa matsalar ba gudun kada ya ta hankalinsa tashi, dan ni tausayima yake bani wlh, kuma bana jin zan iya taɓa kuɗin nan dan yin wani register suma da zasu haɗa min da nasu da karɓa zanyi,yo karɓa zanyi mana abincima tun na safe idan naci ban sake ci sai ruwa shima dan dolene yasa, kuma ni da ba jimawa zanyi ba me zaikaini yin wani register nasan daga yau zuwa gata dai mun bar musu garinsu, kuma ina fatan kafin mu bari Allah ya kawo mana ɗan arzikin da zai ɗauki nauyin aikin nan, idanma bamu samu ba abin da muka haɗa da wanda za'a samo acan ma roƙi likitocin suyi aikin in yaso daga baya a cika musu,sam nidai ban kawo komai raina ba,haka nayita saƙe-saƙe ni kaɗai a raina........

Washe Gari.

"Salamu alaikum"nayi sallama a wani gida aka amsa min muka gaisa da matan gidan,"dan Allah bayin Allah sadaka nake nema mahaiyatace ba lafiya za'ayi mata aiki,kuma bamu da halin biya dan Allah ku taimaka mai biyar mai goma a taimaka mana"ɗaya daga cikin matan da suke cikin gidan ne ta ɗauki jakarta ta zaro dubu daya tace

"Gashi baiwar Allah, Allah ya bata lafiya"tayi maganar tana miƙo min kuɗin sabo dal dashi.

Na ƙarasa na kai hanu zan karɓa sai naga ta ƙureni da kallo,Naja da hannuna baya dan kallon da take ya ban tsoro,da wani mamaki a muryarta tace"wannan ba Haula bace ɗiyar..."

Da sauri na katseta gaba yana faɗuwa kuma a ɗan rikice jin za'a ɗaukoni tun daga tushe nace"ba ita bace baiwar Allah ni sunana zaliha,ina ga kamace kawai"daga haka ban tsaya karɓar kuɗin ba,na juya zan fice,

Sai naji tace"anya kuwa, amma in kuma kamar ce to tayi yawa gaskiya dan Haula ko a cikin ƴan uwanta ita kaɗaice mai kama da mahaifinsu"

Nanma ban kulata ban kuma tsaya ba dan in na sake juyawa tofa za'a gano ni,dan duk yadda akayi wannan matar tayi min farin sani, ta sake cewa "to baki karɓi sadakar ba"batare da na juyo ba nace"Allah shi karɓa''na fice daga gidan dan burina kenan.

Sauri sauri nake tafiya dan karta ta biyoni,sai kuma da na tafi nayi dana sanin ƙin karɓar kuɗin dan hakan shi zaisa ta ƙarfafa zarginta akaina, amma ya wuce dan koda kuɗi bazan koma wancan gidan ba tunda na fito,haka na hau tafiya inayi ina waige dan kada a biyo bayana, hankalina bai kwanta ba saida na bar layin gaba ɗaya,na cigaba da bin gidaje ina bara na kamar yadda nakeyi sai dai yanzu inayi ina ɗari ɗari ba kamar dazu ba,fitowa ta kenan daga wani gida naci karo da wata mabaraciya,ta tsareni da ido tana kallona gabana ya faɗi,a ɗan diririce sakamakon kallon da take min nace"sassannu mama"saboda tsohuwa ce,

''Riƙe gaisuwarki, dan ba ita nake da buƙata ba, dama irinku ne masu ɓata mana suna ko? To waike waya gaya miki haka kawai ne zaki shiga yin barar,kawai daga kinji kina sonyi sai ki kama yi" zanyi magana ta daga min hannu sannan tace" tunda baza kije a sanda da zamanki a cikinmu zamu ɗauki mataki, dan bazaki ɓata mana sana'a ba"

Nidai mamaki sai kasheni yakeyi to dama suna waɗanda basa cikinsu ko a hanya kuka haɗu ana ganeka?kodai dama tana nan ne jiya aka koreni,to amma.......

Ban haɗa ɗaya da ɗaya ya bani amsa ba naji ta hau min kwarmato wai na ƙwace mata kuɗin bararta, da farko turus na tsaya na kasa komai, kasancewar anguwan masu hali ce yasa bai cika hayaniya ba,ba majalisu da kantuna yasa ba mutane sosai a layin sai jifa jifa yawancinsu ma a abin hawa suke, da a anguwar ƴaƴan malam Shehu ne nasan wannan kururuwar da takeyi da yanzu sai dai wata Haular ba wannan ba, tunanina bai gama kaiwa inda nake so yaje ba na jiyo sauti da kururuwar mutane da bama fahimtar me suke cewa nakeyi ba, koda na kai kallona wajen sai naga dandazon mutane suke da alama dai suma mabaratanne dan da gani ba saika tambaya ba, da farko ban fahimci meke shirin faruwa ba sai da naga sun dumfaroni nan wani tunani ya haska a cikin kaina, dan farko tunanin na tsaya na wanke kaina nayi, amma ganin yadda suka tunkaroni nasan ba saurarona zasuyi ba,na damƙe jakar kuɗina dan shine abinda ya fara zuwa kaina,dan nasan muddin na bari wannan tawagar tayo diran Yesu akaina to sai dai wani labarin, ganin da gaske sukeyi na ari na kare na saitawa kaina hanya.

Gudu kawai nakeyi batare da nasan inda nake jefa ƙafata ba,nayi gudu sosai dan nidai bazance ga sanda suka daina bi na, kuma da yake inda nake zuwa ba cikin mutane yasa gudun nawa yayi nisa dan yanzu ma wata anguwa nake da alama sabuwace,dan yawancin gine-ginen ba a ƙarasa ba waɗanda aka gama ma ba sufi a ƙirga ba,har na tsaya a jikin wata bishiya sai naji hankali bai kwanta da wurin ba,kar ace suna nan basu koma ba,na tashi na shiga wani kango dake kusa dani ina haki numfashina har wani sarƙewa yakeyi tsabar gudun da nasha gashi ba sabawa nayi ba,yaraff haka na zube na jingina da jikin wani dutse ina mai da numfashi,na kai wajen minti talatin kafin tunanina ya fara dawowa daidai,na buɗe idanuna dana lumshesu tun zamana a wajen sakamakon hancina da ya fara jiyo min warin sigari,sai sautin magana ƙasa-ƙasa daga can cikin kangon,kasa kunne nayi ban kai ga jiyo mai suke cewa ba naga sun fito, wuf ɗaya daga cikinsu yaje ya tare ƙofar shigowa cikin kango,da sauri na miƙe akan diga-digaina zuciyata na tsallen baɗake a ƙirjina na sake damƙe jakar kuɗina da kyau dan ni a tunanina abin farutarsu kenan,wani daga cikinsu ne cikin muryar mashaya yace"a'a ƴammata kada ki damu ,mu baza mu ƙwace miki kuɗinki ba muddin kika bamu wanda yafi kuɗin"a zahiri nidai ban fahimci me yake nufi ba duk da yaci ace na fahimta me yake nufin,amma tsoro da ruɗani sun cike kai ɗin ba abinda na fahimta.

Cikin wata murya da nake fatan suji tausayina nace"dan Allah kuji tausayina,wlh mahaifiyatace ba lfy na fito yin bara dan na sama mata abin da zamu siya magani da abinci dan Allah kuyi haƙuri"

Ɗaya wanda da alama shine jagoransu,bakin nan baƙi ƙirin ido yaji kwalli kaman boka"ahh'ahh ƴammata mun gaya miki ay ba kuɗi zaki bamu ba,ɗaya abun zaki bamu"yana magana yana zuƙar sigari yana taune baki.

''Dan Allah kuyi haƙuri me kuke so to?"na tambaya dan ni kaina gaba daya a kulle yake nama kasa tantance fari da baƙi.

Bai ce komai ba ya dumfaroni yana min wani irin kallo yana lashe baƙaƙen laɓɓansa,jina da nayi naci karo da bangone yasa nayi masa tambayar da bansan daga bakina ta fito ba dan a tsorsce nake"memme zakai min?"nayi maganar a rarrabe

"Zamu hutane kawai ƴammata"

"Dan Allah kayi haƙuri wallahi ni matar Aure ce"

Wani dariya sauran biyun suka tuntsure dashi suma,shi kuwa bai fasa tunkaroni ba.....

Mu haɗu a Page na gaba....

Ku cigaba da kasancewa da

Amdy Tejj d'Unique Writer 📖✍️

Nagode 🙏🙏🙏