BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----9 

Shiru ne ya mamaye ɗakin bayan Alhaji Munnir ya gama maganar sa.

Malam Abdallah ya sauke numfashi a hankali yana kallon Alhaji Munnir cikin nutsuwa kafin ya ce"Alhamdulillah naji daɗin wannan karamci da ka nuna min Kai babban mutum ne da kowa ya sani da mutunci Amman kafin na yanke hukunci sai naji ta bakin mahaifiyar da kuma ita Imam din,duk da a iya sa  ni na  bata da samari amman zanji ta bakin ta duk hukuncin da muka yanke zan sanar dakai"

Alhaji munnir ya ce "Babu matsala hakan ma yayi"

Nan suka ɗan cigaba da hira kafin daga bisani Alhaji Munnir ya miƙe zai tafi.

Har bakin mota Malam Abdallah ya raka shi 

Bayan tafiyar sa Malam Abdallah ya koma ciki.

A tsakar gida ya tarar da Ammi tana shara ta ɗago tana kallan sa "malan baƙo kayi ne"

"Eh idan kin gama sharar ki same ni a ɗaki"

da sauri ta gama sharar dan taƙosa taji maganar dake bakin mallan a ɗaki ta same shi waje ta samu ta zauna Malan Abdallah ya ce"Alhaji munnir Muhammad ne"

maimaita sunan take cikin zuciyar ta kafin ta ce"Alhaji munnir ma dai dana sani"

kai ya daga mata alamun "eh"

"to mallan miya kawo sa"

Malam Abdallah ya rasa ta ina zai fara wa Ammi bayanin abinda ya kawo sa cikin dakiyyar murya ya ce"Yazo nemawa ɗan sa auren Iman"

dandanan bugun zuciyar ta ya ƙaro ta ce"malan kana nufin Iman"

"Ita"

kai ta girgiza ta ce"Anya malan ba ɓatan hanya yayi ba a ina ma yaransa nasa yaga iman din da har zai zo nema auren ta"

murmushi Malan yayi irin nasu na dattawa, ya shiga ba Ammi labarin yadda Alhaji munnir ya ga iman ranar sauka ta sannan yana ɗaya daga cikin mutanen da suka bata kuɗi a ranar"

Cike da raunin murya ta ce"Malan Gaskiya ni dai ban Amince ba,Ni bana son a kai min ƴata gidan da za’a rinƙa wulaƙanta ta saboda talauci ko asalinta ka barta ta samu mijin da yazo dai-dai da Rayuwar ta"

Malan  ya ce"a iya sa nina Alhaji munnir mutumin kirki ne"

"naji mutumin kirki Amman kasan ya matarsa take? iyalansa tare da saura a halinsa"

malan ya girgiza kai "ban sani ba amman suma ina kyautata masu zato"

"Allah ya tabbatar da Alkhairi"

Tashi tayi zata fita mallan ya ce"kije kiyi shawara dan ban riga na faɗa masa hukuncin da muka yanke ba"

fita tayi ba tare da ta bashi amsa ba daki ta koma aunty zaituna ce zaune a falo tana haɗa kayan ta dan gobe da sassafe zata wuce Katsina.

Kallon Ammi tayi ganin Lokaci guda ta sauya ajiye kayan dake hannun ta tayi ,ta koma kusa da ammi dake zaune kan kujera ta dafe kan ta ta ce"Yaya lafiya miya same ki"

Ɗago idanun ta tayi da suka chanza lauyi ta soma yi mata bayanin kiran da malan yayi mata.

Aunty zaituna ta ce"yaya wannan ai abin farin ciki Iman zatayi aure a babban gida irin gidan Alhaji munnir mahmud"

Ammi ta girgiza kai 

"zaituna kenan ana ruwa yaci maƙadi kina ganga ta jiƙe ba wannan  na ke dubawa ba, bana son iman taje idan za'a takura mata ko a nuna ita tallakka ce ki san halin masu kuɗin basa san hada inuwa da talakka gani suke Tamkar zasu shafa musu talauci Iman yarinya ce mai haƙuri da nutsuwa kuma irin sun fi shiga damuwa idan aka fara gallaza musu "

murmushi Aunty zaituna tayi ta ce"Wannan shine kike tunani kar ki manta su suka zo neman aurenta bawai tallar ta aka musuu ba ki kawar da damuwar nan taki ki mata addu'ar fatan Alkairi kawai"

Ammi ta share hawayen ta aunty zaituna ta cigaba da bata kalaman da ta tabbatar zasu kwantar mata da hankali.
Washe gari tun da safe Aunty zaituna ta fara haɗa kayan ta ta musu sallama zata wuce Mubarak ya samo mata adaidaitar da zata kai ta tasha.

Iman ta ce"Aunty sai yaushe zaki dawo"
murmushi tayi ta ce"sai bikin ki zan muzo gaba ɗaya harda su Hafsat"

ido ta zaro ta ce"tabb Ashe zaki ɗa de baki dawo ba kuwa" Ammi murmushi kawai tayi har kofar gida suka raka ta ta tafi bayan sun dawo malan ya ce "gaba ɗayan su same sji a ɗakin sa"

Iman ta kalli Mubarak dan malan baya kiransu haka kawai sai da dalili haka suka ɗunguma gaba ɗayan su zuwa ciki.

malan yayi gyaran murya "jiya munyi baƙo wanda ba kowa bane illa Alhaji munnir"

iman ta dago idanun ta tana kallan Malan idan bazata manta ba wannan sunan yana ɗaya daga cikin baƙi na musamman da aka gayyata ranar saukar su 

abba ya cigaba da magana "yazo nema wa dan sa auran Iman"

İman ta tsaya cak tana kallon su kamar bata gane maganar ba 

Mubarak yace"Abba wata iman din"

Abba ya ce"Akwai wata banda wacce ke zaune kusa da kai"

Nan take kunnenta ya fara ɗaukar ƙara zuciyarta na bugawa da sauri, a hankali ta sauke kanta ƙasa.

Ammi ta ce"Iman ki nutsu babu wanda zai tilasta maki"

ɗago idanunta tayi da suka cika da kwallah ta ce"Abba ni Ba Yanzu zanyi aure Makaranta nake so in cigaba kuma yaya Mubarak yayi min alkawari zai samo min admission"

kallon Mubarak tayi cike da damuwa ta ce"ko Yaya"

kai ya jinjina ya ce"Amman iman aure ai baya hana Karatu idan har mijin ki ya Amince zai barki ki cigaba"

hawaye masu zafi suka fara sauka daga Idanun ta Malan ya ce"kije kiyi shawara dan ban riga ma amince masa ba"

ganin tana shirin fashewa da kuka Ammi taja hannun ta suka bar ɗakin 
Malan ya kalli Mubarak ya ce" ina so kayi min bincike sosai akan yaron"

kai ya daga ya ce"in sha Allah malan"

tashi yayi yabi bayan su Ammi na kai Iman ɗaki ta fashe da kuka da kyar Ammi ta shawo kan ta tayi shiru ta ce" shi kukan na minene keda ba ari ance an bada ki zaki dora wa kanki damuwa"

ɗago jajayen idanun ta yi ta kalli Ammi ta ce"Ina tsoro kin san hali Malan Ammi ni kuma tsoron masu kudi nake wallahi ni ban saba da Rayuwar su idan ma aure yake so yamin ya zaba min wanda Rayuwar tazo ɗaya amman Ammi banda gidan masu kuɗi"

shiru Ammi tayi dan a wannan gabar Iman ta fisu gaskiya kuma tun farko itama abinda ta koka kenan Iman nada wani irin hali ba kasafai ta fiya shiga harkar masu kuɗi ba ko cikin abokan ta ta iya kanta bata san Abinda duk sai ja mata gori ko wulakanci.

Mubarak ya shigo Ammi ta shiga daki ta barsu anan,sai da yasan yadda yayi ya dawo wa da Iman farin cikin da yake nema ya gushe mata cikin ƙankanin Lokaci Ammi na daki tana jiyo Dariyar ta.

Murmushi tare da yiwa Allah godiya daya ba Iman Mubarak a Matsayin yaya ko a labari Bata taɓa jin irin yayan da ke nuna kanwarsa soyayya irin Mubarak ba.

Mubarak tun  Iman  na ƙarama yake bata kulawa da kariya tamkar amanar da Allah ya bashi Ko yaushe idan ya dawo daga makaranta ko wajen aiki abu na farko da zai fara nema shine ita Saboda tsananin shakuwar dake tsakaninnsu

Tun iman na yarinya shi yake mata wanka ya shirya ta ya sha rakata wajen kitso da kunshi ya jirata har sai an gama masu su dawo tare duk wata Hanyar da zabi wajen ganin Iman tayi farin ciki ya santa ko guda baya son ya taɓa nasa kanwar nan tasa.

Ko ammi keyi mata faɗa sai dai ya bar gidan dan baya jurar ganin ɓacin ranta hakan na sa Ammi alfahari sossai tare da godewa Allah ya haɗa kansu waje guda tasan ko bayan ransu Mubarak zai tsaya wa Rayuwar Iman.

Gaskiya idan bakwa comment zai daina maku posting anan na cigaba da wa masu comment da like kawai