SARTSE COMPLETE

23

by @legendspen

“Ya salam! Me ya faru Sardauna?” 


Wasu hawayen ne suka fara fitowa daga idanunsa, waɗanda suka ƙara ɗagamin hankali, ya riƙe hannu. 


“Nana nagaji, ina danne zuciyata ina sonki, bana son abinda zai cuceki, amma Hajiya ta dage wai tana son ganin jikokinta, Nana ko zuwa gidan Hajiya bana son yi, bana so na ji an soke ki ko anci mutunciki, Nana bana son zaluntarki, bana son cutar da zuciyarki, bazan iya ƙara aure ba kwata kwata, karki ga yadda ake zancen nan a family house kamar akaina aka fara shekara uku da aure ba haihuwa. Hon haihuwar nan dole ne?.”


Wani irim tausayinsa neya ratsamin zuciyata, sai na ji dama ni ce nake shiga wannan matsin ba Sardauna ba, dama nice nake wannan kukan ba Sardauna ba, bazan iya jure ganin hawayen Sardauna ba, suma azabatar da rayuwata. 


“Ka yi haƙuri, haihuwa ba dole ba ce, amma tabbas a idon iyayenmu gani suke dole ne, Sardauna a yanzu ma da ka zo maganar muke da Bilkisu amma taƙi fahimta ta duk da nasan zata fahimta in sha Allah. Ina tunanin idan ka yarda zanje gidansu gobe mu sake magana da ita. 


“Hon ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, rayuwa ta yi min baƙi mutuncina yana watangarirya. Na yarda ki je da kanki, kisan yadda zaki yi da ita ta amince, Hon ki durƙusa mata a ƙafa, ko ni naje na durƙusa mata kawai Hon, da mutuncina ya zube a idon duniya, gwanda na yi haka, ko menene zan iya yi mata wallahi indai zata aureni.” 


“Ya zaayi kaje ka durƙusa mata? Haba dai. Ka barni da kaina zanje gobe, zan yi magana da ita ta yadda dole zata amince, ka sa haƙuri a ranka dan Allah.”


“Nana idan ba ta amince ba ina cikin tashin hankali, ni dake Nana bamu da wata mafita.” 


Ji na yi kamar na tashi a cikin daren na je gidansu Bilkisu amma ba hali, daƙyar na lallaɓa Sardauna ya nutsu amma bai iya cin abinci ba, haka muka kwanta duk ranmu ba daɗi. Washe gari lokaci ɗaya muka fita dashi, ya yi ofis ni kuma na yi gidansu Bilkisu ta hanyar kwantancen da ta yi min tun kwanaki. A bakin gate ɗin na tarar da wata mata mai kama da Bilkisu na shirin fita, ƙasa na tsugunna tare da faɗin. 


“Ina kwana?” 


“Lafiya.” 


Ta amsamin a daƙile, sannan ta ce. 


“Wa kike nema.”


“Bilkisu.”


“Tana ciki.”


Ta faɗa tare da hucewa, na kusa minti biyar a tsaye ina faman tunanin ta yadda zan fara da Bilkisu, bana son ta tirjemin kamar yadda ta yi jiya. A hankali na tura ƙofar falon na shiga, zaune na tarar da su 'yan mata ne sun kai su biyar da alamu ma wasu ƙawayenta dan ba 'yan gidansu ba ne, duk da nima wannan ne zuwa na na farko gidansu. cikin wani irin yanayi kamar na isgili haka ta tarbeni. 


"A'a Nana kina ƙaraso." 


Na yi mata murmushi sannan na ce. 


"Eyh wlhi, ya gida?" 


"Muna lafiya." 


Zama na yi sannan na kalli sauran matan dake ɗakin, sannan na ce. 


"Sannunku." 


Bansaniba ko sun amsa ko basu amsa ba, nidai abinda ke gabana shine kaɗai ke damuna. 

Gaba ɗaya tunanin maganganun da muka yi da  Sardauna ya cika min ƙwakwalwa, bana iya tuna komai sai muryarsa. 


'Nana nagaji, ina danne zuciyata ina sonki, bana son abinda zai cuceki, amma Hajiya ta dage wai tana son ganin jikokinta, Nana ko zuwa gidan Hajiya bana son yi, bana so na ji an soke ki ko anci mutunciki, Nana bana son zaluntarki, bana son cutar sa zuciyarki, bazan iya ƙara aure ba kwata kwata, karki ga yadda ake zancen nan a family house kamar akaina aka fara shekara uku da aure ba haihuwa. Hon haihuwar nan dole ne?.'


"Allah Sarki Mijina." 


Na faɗa a zuciyata, a fili sai kuma na kalli Bilkisu na ce. 


"Dan Allah magana nake so mu yi dake, ina son mu shiga daga ciki." 


Dariya ta yi ita da mutanen nan nata sannan ta ce. 


"Haba Nana kamar ba wise ba." 


Ɗaya cikin ƙawayen ta ce. 


"Baiwar Allah kizo ki ganmu tare sannan ki ce wai ta tashi ku shiga ciki a wane dalili?" 


Baki sake nake kallon ikon Allah. 


"Nana waɗannan ƙawayena ne duk wani sirri zan iya yi dasu, dan haka ki faɗi abinda zaki faɗa." 

Ji nai na yi wani irin muzanta, kamar bata san maganar da zamuyi ba, to ma wai 'ƙawayenta ƙawayena ne?, ko da ƙawaye na ne kowacce magana yakamata na yi a gabansu?.


"Hon ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, rayuwa ta yi min baƙi mutuncina yana tangarirya Hon, na yarda amma ki je da kanki kisan yadda zaki yi da ita ta amince, Hon ki durƙusa mata a ƙafa, ko ni naje na durƙusa mata kawai Hon, da mutuncina ya zube a idon duniya, gwanda na yi haka." 


Kalaman Sardauna suka dawo kunnuwa kamar yanzu yake faɗinsu. 


"Bazan taɓa bari ka hulaƙanta ba in sha Allah Mijina." 


Na faɗa, sannan na kalleta tare da tasowa zuwa inda take, na sanya gwiwoyina a ƙasa sannan na ce. 


"Maganar mu ta jiya, ki taimaka ki auri mijina." 

Wata shegiyar dariya na ji ƙawayen na ta sun kice da ita, kamar daman jira suke na yi magana.


“Bilkisu wannan mahaukaciya ce?”


Ɗaya cikin ƙawayenta ta faɗa, tana wata irin dariya. 


“Bana ce ba, ni yadda nasanta lafiya ƙalau take, amma daga jiya zuwa yau gaba ɗaya ta canja.” 


“Bilkisu kinsan komai, wannan abun mafita ce gani da ke.” 


“Nana ki saurareni, na gama magana fa wai ma idan aure ne macece zata nema masa aure? Ke awa da zaki nema masa aure, ba zai zo da kansa ba? Kinga kenan kece kika aureni bashi ba.” 


“Ba haka ba ne Bilkisu, kusancin dake tsakanina dake ne yaja haka, amma da kin bashi dama zai zo da kansa Bilkisu.”


“Ke amma kin rako mata wallahi, bantaɓa ganin ballagaza marar kishin kai ba irinki, mijin naki kike yawo da shi a haka? Kina neman a aure shi? Sannu Saratu ba ki yi wa kanki tanadi ba wallahi, bama alfahari dake.” 


Wani irin ɗaci na ji ya tsayamin a maƙogwaro zuciyata ta fara wani irin raɗaɗi. ‘Ko Bilkisu ta kawo waɗannan ƙawayen na ta suci mutunci na ne?.’ Na tambayi kaina, ban kai ga samun amsa ba na ji wata ta ce. 


“Ni yau na fara ganin asara irin wannan ba, amma dai duk da yadda aka yi mijinne baya sonta, shine ya bata dama ta kawo mai wata ko ya rabu da ita.” 


Suka tuntsire da dariya, Bilkisu ta ce. 


“Ba fa haka ba ne, ni bansan mene asalin matsalal ba kamar haihuwa ne ba ta yi.”


Wani zafi na ji a zuciyata, wai Bilkisu ke hulaƙantani, tana shela da ni haka, kamar ba ta san komai ba. 


“Ai kuwa babbar matsala ce, dole ta fito ta nema masa aure kafin ya kaɗata, dan ba kowa zai iya jurar mace daga ci sai kashi ba.” 


Ƙwalla na ji tana zirara daga idona, a fili na furta. 


“Ya Allah Ka na ji ka na gani.” 


“Nana idan zaki tashi ki tashi, babu abinda zai sa na auri mijinki, gwanda ma ke nemi wata mafitar.” 


“Ji ta ballagaza.” Wannan ita ce maganar da tafi ƙonamin rai, ba shiri na miƙe a raina na ƙudiri cewar zan nemawa Sardauna wata ba dole sai Bilkisu ba, tun da daman ba sonta yake ba. 


“Na gode Bilkisu.” 


“To Nanan Sardauna, ki gaida gida sannan ki canja shawara.” Bilkisu ta faɗa, wata cikin ƙawayen ta ce. 


“Ki canja tunani kam, kuma a dage a rage ci tun da ba haihuwa za ayi ba.” 


Ban kai ga ƙarasa fita ba, na ji sun kece da wata irin dariya, haka na tawo ina haɗa hanya sakamakon matsanancin jirin da nake ji, fuskata ta jiƙe shargab da hawaye, wannan cin mutuncin har ina? Lallai Bilkisu. 


A haka na shigo cikin gidan, daidai lokacin da Turaki ya fito daga ɓangarensa, da sauri na yi ƙasa da kaina sabida kar ya ga fuskata. Ba ni da damar yin sauri sabida jirin da nake ji, hakan yasa na tafi a hankali. 


“Nana!” 


Ya kira sunana, ta dole na tsaya ba tare da na juyo ba. 


“Kuna waya da Hajiyarki?” 


Na gyaɗa kai, ba tare da na yi magana ba. 


“Good.” Ya faɗa tare da fara tafiya, jan hanci na yi tare da wata shasheƙa da ta ƙwacemin ba tare da na shirya ma ta ba ya sa shi dawowa. 


“Nana! Meke damunki? Kuka kike?”


“A’a.” 


“Ƙarya zaki yi min, Sardauna ne ba lafiya?” 


“A’a.” 


“To me ya sa ki Kuka?” 


Ya faɗa yana matsowa inda nake, girgiza kai na yi bance komai ba. 


“Me ya saki Kuka!” 


Ya faɗa a tsawace.


“Ba komai, ka yi haƙuri, zan faɗa ma.” 


“Haƙurin me Nana? Me ya ta ɓa ki haka?” 


“Ka yi haƙuri, zan faɗa ma.” 


Na sake maimaitawa gaba ɗaya na ruɗe.


“Nana kina da damuwa ne? Duk kin ruɗe kin fita hayyacinki, are you okay?” 


“Yes! I’m okay.” 


“Hhhm.” 


Kawai ya faɗa tare da sa kai ya fice, ni kuwa har da harɗe ƙafa sabida sauri na shige ciki, ina shiga na faɗa kan kujera na fashe da kuka, mai tsuma zuciya. Kuka nake yi mai ƙarfi har sai da na fara jin ɗaci a maƙwogarona. Kukan da ya haifarmin da wani ciwon kan wanda ya haɗe da jirin da nake ji gaba ɗaya na ji duniyar ta fara yi min zafi, abubuwan sun har gitsemin sama ta juye ƙasa. 


Daƙyar wani wahalallen bacci ya ɗaukeni marar daɗi, ina yi ina firgita, ina zabura kamar wacca za a taɓa, cikin barci na fara jin hayaniya sama sama. A hankali na buɗe idanuna sa suke jawur, wani irin sarawa na ji kaina ya yi, amma a haka na dafe kan na miƙe sabida jin kamar cacar baki. A hankali na leƙa ta window Sardauna da Turaki ne. 


“Turaki ina so ka sani, ni Sardauna na yi maka nisan da har abada ba zaka taɓa kamoni ba, Turaki duk abinda zaka yi tsakaninka da ni sai da ido. Kasani abinda Sardauna ya taɓa har abada ya yi maka nisa.” 


Turaki ya saki wani murmushi, sannan ya dafa kafaɗar Sardauna ya ce. 


“Alfahari da fariya na ƙarya kake yaro, ni lokacin da zan zauna na yi wannan maganar marar amfani ma ban da shi, sannan ina tunasar da kai cewar Ajuri zuwa rafi, wata rana tulu zai fashi. Shashasha.” 


Yana faɗin haka ya wuce yabar Sardaunar a wajen, da sauri na koma kan kujera na kwanta, na rasa mene asalin wannam faɗan dake tsakanin Sardauna da Turaki. Da ƙarfi ya saki ƙofar bayan ya shigo, na runtse idona sabida wani irin bugu da na ji zuciyata ta yi. 


“Nana! Nana! Nana!” 


Na buɗe idanuna na kalleshi. 


“Me kike yi a kwance.”


“Bakomai.” 


Na faɗa ina miƙewa zaune. 


“Me ya shigo da wannan ɗan iskan bangarena?”


“Waye?” 


“Karki rainan hankali mana, waye banda Turaki.” 


“Bai shigo ba.” 


“To aina ya ganki?” 


“A parking space ne, bayan na dawo daga gidansu Bilkisu.” 


“Hhm, har ni zai cewa wai na dinga yin adalci, me kika ce masa?” 


“Babu abinda na ce masa, to me kake yi min da zan faɗa masa?” 


“Nasan mike, nasani ko kin yi min wani sharri.” 


“Uhm.” 


Kawai na faɗa tare da sake komawa na kwanta, kallona ya yi sai kuma ya sha jinin jikinsa. 


“To kawai yana ganina ya wani hau yi min magana, ni da ba shiga sha’aninsa nake ba, tun muna yara Turaki yake son shiga rayuwata, yana baƙin ciki da ni a rayuwarsa, ni kuma ko magana ma bana son naga ta haɗani da shi, ina kishin naga nasan abu Turaki ya san shi, shi ya sa ma duk family na bar masa, na ja rayuwa ta na yi gefe, ranar da na ga ya yi miki magana a family meeting wallahi Nana ji na yi kamar an watsamin tafasheshen ruwan zafi a zuciyata, na ji zafi fiye da yadda kike tsamanni.”


“Hhhm, to yanzu ni me zai haɗani da shi da har zan hau yi masa magana akanka.” 


“Ki yi haƙuri to.” 


Ya faɗa yana kama hannuna. 


“Bakomai.” 


“Ya kuka yi?” 


Tashi na yi zaune duk da jirin da nake ji yana ɗibana, na kalleshi sannan na ce. 


“Akwai matsala fa.” 


“Wace irin matsala?” 


“Babu wani nau’in rashin mutunci da kasani da Bilkisu ba ta yi min ba, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, abun babu daɗin ji.” 


“Ita Bilkisun?” 


“Ita fa, ni kaina har mamaki na yi, kamar ba ta sanni ba.” 


“Innullahi wa’inna illahir raji’un, to yanzu Hon ya zaayi?” 


“Ina ganin kamar a ƙyaleta a nemi wata kawai.” 


“A nemi wata kuma Hon?” 


“Eyh a nemi wata, tun da ita ba yarda za ta yi ba.” 


“Nana haka zamuyi ta zagaye mutane muna faɗa musu matsalalmu, suna ƙin amincewa shikenan mun tonawa kanmu asiri?” 


“To ya kake gani zaayi? Mene mafita a ganinka?” 


Shiru ya yi na tsahon mintina sannan ya ce. 


“Ni fa da har ta kwantamin a rai, Nana ki sake komawa.” 


Legendspen

***