24
by @legendspen
“A sake komawa? Wajenta kenan?”
“Eyh Nana, aganina a sake komawa mai nema ai yana tare da samu, kuma muke nema bai kamata mu yi zuciya ba Nana.”
Shiru na yi ina faman tunani, tabbas zancen Sardauna gaskiyya ne, wanda yake nema ba ya taɓa fushi amma tabbas abinda Bilkisu ta yi min abu ne da yake nuna zallan rashin mutunci, amma ya zanyi tun da Sardauna yana so.
“Shikenan gobe zan sake zuwa ko?”
“Yawwa Nana, ki bi duk wata hanya da zaki bi kinji ‘yar Aljanata.”
“Ina son gobe zanje asibiti, ina yawan jin jiri da ciwon kai sosai.”
Na faɗa ina lumshe idona.
“Okay tom daga gidan nasu sai ki je asibitin, da mota zaki fita?”
Na girgiza masa kai tare da cewa.
“A’a.”
“Tom, me aka dafa mana?”
Na girgiza kai.
“Banyi komai ba, amma muna da gurasa.”
“To aban na sha da tea.”
“Tam.”
Na faɗa tare da miƙewa, anan falon na kawo masa ya ci bai ji dinning ɗin ba. Bayan ya gama ci na kwanatar da kaina akan cinyarsa.
“Yaushe zanje na gaida Hajiya.”
“Wace Hajiyar? Taki ko tawa?”
“Duka biyun.”
“A’a Hajiya ta dai ba yanzu ba, yadda take wannan fushin, sai da Hajiyarki, ita ma ba yanzu ba.”
“Sai yaushe?”
“Mu gama da abinda yake gabanmu Nana.”
“Eyh hakan kam gaskiyya.”’
“Yawwa ko ke fa.”
“Ya zancen tafiyarmu Turai? Gashi kuma Maulidi ya tawo ka ce Umarar Maulidi zamu.”
“Nana, turai ba yanzu ba dan Big Daddy ma ya hana, sai dai Umarar.”
“Shikenan yanzu an fasa?”
“Ko za a je ba kusa ba.”
“Shikenan yanzu karatuna fa, gashi ‘yan anjimu on 11 this month zasu yi resuming level 300 zasu shiga.”
“To Nana ya zaayi? Haka Allah Ya ƙaddara amma ki kwnatar da hankalinki kin ji Nana.”
“Alhaji ya mutu da burin na yi karatu, akwai alƙwarinshi akaina fa.”
“Nana mene haka wai? Da matsalal da take gabanmu zamuji ko kuma da wacca kike shirin kunno mana?”
“Ni ba matsala nake son kunnowa ba.” Na faɗa ina goge ƙwallar dake idona, ban ƙara ko minti biyar ba na tashi na shige ɗaki na kwanta, ina jinsa har ya shigo ya gama gyaran muryarsa ban ce ko ƙala ba, ya jawoni jikinsa.
“Nana nah, me na yi?”
“Babu komai.”
“Bangane ba komai ba, gashinan kina wani yi min banza.”
“Ni ba banza nake ma ba, kaina ke ciwo ne.”
“Tom, na ƙyaleki kike so ki ce ko?”
“Jiri nake ji.”
“Uhm, shikenan.”
Yana faɗin haka ya cikana ya juya ya kwanta, haka kawai yau na ji ni bana wani marmarinsa ko magana ma ban son yi da shi.
“Bazaki kulani ba ko?”
Matsowa na yi kusa da shi sannan na ce.
“Ka yi haƙuri.”
“Nana kullum baki da aiki sai ayi haƙuri, amma kuma ko an haƙura ba kya fasawa.”
“In sha Allah za a gyara.”
Daga haka ya muka kwanta.
******
Yau ma kamar jiya tare muka fita da Sardauna, na yi gidansu Bilkisu ya yi ofis, yau ma na ɗan jima a ƙofar gidan kafin na shiga, ko dame zata zo yau oho? Sai da na ƙarewa gidan kallon, su Bilkisu sun fi mu kuɗi sosai da sosai ko unguwar da suke ma kaɗai ya isa tabbatar min, ga gidan masu ya tsaru da tsaruwarshi. A hankali na tura ƙofar falon na shiga sai dai babu kowa a ciki, haka na tura kai na shiga tare da yin sallama, sai da na yi sau biyar sannan aka amsa min.
“Nana! Me ya dawo dake kuma? Kar dai ki ce baki haƙura da wannan zancen ba.”
“Bilkisu kenan, ai kya tsaya mu gaisa.”
“Tom zauna mana.”
Na sami waje na zauna ita ma ta zauna.
“Ina ina saurarenki.”
“Bilkisu dagaske kike akan maganar da kika faɗan?”
“Wace magana?”
“Ta wajen mahaifinki.”
“Nana zan miki ƙarya ne?”
“To amma me ya sa baki amshi mafitar da nazo da ita ba.”
“Nana! Wai ta ya zan auri wanda baya sona? Da auren mijinki da auren wanda Abbana zai ban duk ɗaya ne tun da duk ba sona suke ba.”
“Bilkisu baki bawa Sardauna dama ba ne, amma yana sonki kuma zai nuna miki soyayya, Bilkisu dan Allah ki gwada ba shi dama.”
“Wace kalal dama?”
“Ya zo ku yi magana, ko tattauna ko fahimci juna.”
Shiru ta yi sai kuma can ta ce.
“Shikenan ya zo yau.”
Har cikim zuciyata na ji daɗi, kuma na kasa ɓoye jindaɗina.
“Na gode miki sosai Bilkisu.”
“Karki gode min Nana, dan ba cewa na yi na amince zan aure shi ba.”
“Nasan ma zaki amice, daga hakan in sha Allah.”
Na ɗan zauna a gidan nasu har wajen ƙarfe goma sannan na ta shi na nufi asibiti, dan har zanje wajen Dr Ɗan Adala, kawai na yanke shawarar zuwa asibiti mafi kusa.
Duk da kasancewarsa asibitin gwamnati amma ma’aikatan ciki sun kasance masu matuƙar kirki, tun daga zamana har layi yazo kaina ban ji sun hantari wani ko wata ba.
“Wacece Nana.”
“Ni ce.”
Na faɗa ina miƙewa.
“Ki shiga ciki.”
Godiya na yi mata sannan na ta shi na shiga
Likitar babbar Macece mai mutunci, Dr Na’ima Daƙayyawa. Shine sunan da naga an rubuta a jikin tag ɗin ta, kallo ɗaya ta yi min ta ce da ni.
“Mrs Ta ambo, gaba ɗaya shekarunki nawa? Me yake damunki da zai haifar miki da Low Bp a wannan ƙarancin shekarunki?”
“Low Bp Dr.”
Na faɗa a hankali, ta gyaɗa min kai sannan ta ce.
“Yeah! Low Bp ma’ana jininki ya yi ƙasa fiye da tsammani, ya kamata ki cire duk wata damuwa a ranki, ke yarinya ce ƙarama. Baki kai matsayin da abu zai dameki ba.”
“Yanzu mene abun yi?”
“Ki cire duk wata damuwa a ranki, ki miƙa al’amuranki ga Allah, komai ya yi farko yana da ƙarshe.”
“Tom.”
“Matsalal gidan aure ce ko? Ki yi haƙuri muma dukkanmu haƙuri muke, rayuwar gaba ɗaya haƙuri ake da ita, kin ji?”
“Tam na gode, amma dan Allah likita na tambayeki.”
“Allah Ya sa Nasani.”
“Zuwa shekara nawa ne mahaifar mace take yin ƙwarin da zata ɗauke ciki?”
“Bangane ba.”
“Ina nufin zuwa shekara nawa mace take iya fara ɗaukan ciki?”
“Shekarun da ta girma mana.”
“To wasu da mahaifarsu ba ta da ƙwari fa?”
“Mrs Ta Ambo am sorry bangane abinda kike son faɗa ba, can you please open your mind and talk?”
“Shikenan zan dawo wata rana.”
Na faɗa tare da tashi.
“Okay Allah ya ƙara lafiya.”
Har na fita na dawo, “Dan Allah zan iya samin numberki?”
Kati ta ɗauko mai ɗauke da sunanta address ɗinta da lambar wayarta ta ba ne, na amsa tare da yi mata godiya na fice.
Kai tsaye gida na dawo, bayan na sha magunguna da aka bani na kwanta bacci ya ɗauke ni wanda ban tashi na sai gab da la’asar, a gurguje na yi ayyukana na gama, yau Sardauna zai je gidansu Bilkisu Allah Ya sa su fahimci juna, ayi ayi auren nan kowa ya huta da ko zan sami nutsuwa jina na ya dawo daidai.
Lokacin da ya saba dawowa ya dawo, da farin ciki na tarbeshi kamar yadda nasaba yi masa a farko, da mamaki yake kallona, har ya kasa ɓoye mamakinsa ya ce da ni.
“Nana me ya faru?”
“Ka fara wanka ka shirya sai mu yi magana.”
“A’a kinsan ni bana son irin wannan kawai ki faɗa min.”
“Bilkisu ta ce dai ta yarda ka je ku yi magana ku fahimci juna.”
“Ma sha Allah, na gode miki matata abar alfaharina, Allah Ya biyaki.”
“Amin amin, yanzu je ka yi wanka ka shirya sai ka tafi.”
“Tom, yadda kika ce haka za ayi Hajajju, ko tare zamu je.”
Ya faɗa yana shigewa ɗaki, na yi dariya sannam na ce.
“Ni wa? A’a dai.”