BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


Wannan page naki ne Gimbiya Rahama group admin Hausa novel Novel facebook ina Alfahari dake da mutanen gidan ki Allah ya bar kauna♥️👌

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----10 

Tun Ranar Mubarak ya shiga bincike akan Suhail cikin Nasara ya samu duk wasu bayanai a kanshi a wunin ranar ya sami malan a kofar gida bayan ya sallami masu ɗaukar karatu.

Mubarak ya ce"dama Malan akan aikin da ka bani ne naga ma binciken kaf a kan Suhail dan gidan Alhaji munnir,a duk binciken da nayi ya tabbatar min da Suhail mutumin kirki ne,kuma mutun ne mai gaskiya akan aikin sa ya sha banbam-banbam da sauran abokan aikin sa mutun ne ,mai tausayi da kuma taimakon na ƙasa dashi tun da na fara gudanar da bincike banji wanda ya faɗi aibun saba ina ganin wannan mijin ya dace da Iman"

shiru Malan yayi yana sauraren Mubarak har ya kammala masa bayanin daya kawo shi Malan ya ce"Masha Allah,nima tun a daren ranar na fara isthikara kuma Alhamdullilah naji hankali na ya kwanta,Amman matsala ɗaya ce Iman da mahaifiyar ta"

Mubarak ya ce"Malan ka bar komi a hanuna zanyi ƙoƙarin fahimtar dasu"

Jinjina kai Malan yayi cikin gamsuwa.

“Allah yayi maka albarka Mubarak”

“Amin” ya amsa kafin ya miƙe ya shiga ciki 

A tsakar gida ya tarar da Iman zaune kan tabarma tana danna sabon wayarta sanye take da Doguwar rigar atamfa peach color

ganin Mubarak yasa ta ɗago kai tana murmushi "yaya sannu da zuwa"

gefenta ya zauna yana kallon wayar hannnun ta 

"ke dai baƙi da wani aiki a wayar nan sai game"

zaro ido tayi cike da yarinta ta ce"yaya to ai shi kadai na iya dama inaso idan ka samu lokacin ka bude min whatsApp mu rinƙa gaisuwa da aunty zaituna da kuma hafsat harda sauran kewayena"

"to shikenan zan buɗe miki"

"Iman"  ya kira sunanta a yanayin da ya kirata tasan serious issue hakan yasa ta ajiye wayar ta maida hankalin ta wajen sa 
"na'am" yaya

"Idan muka tabbatar Suhail mutanen kirki ne zaki Amince ki aure sa"

Murmushin dake kan fuskarta ne ya ɗan gushe daidai lokacin zuciyar ta buga da ƙarfi hawaye suka cika idanun ta cike da rauni ta ce Yaya ni bana son gidan masu kuɗi  kaga yadda masu kuɗi ke rayuwa ni bana son inda za’a rinƙa kallona kamar ban isa ba"

Shiru Mubarak yayi yana kallon kanwarsa.

Cikin sanyin murya ya ce,
“Iman kin yarda dani ko?”

Kai ta jinjina masa

“To kisa a  Ranki bazan bari a cutar dake ba Kuma matukar ina raye bazan taɓa bari a wulakanta min ke ba kin fi ƙarfin duk wani abu Iman Ke ba talaka bace Ke yarinya ce mai ilimi,hankali ga nutsuwa wanda hakan ya kwaidata masu  ke har suka ji suna so ki zama cikin ahalin sa"

iman bata ƙara magana ba Mubarak ya miƙe ya ce"Ammi bata dawo bane"

kai ta ɗaga masa ya shige dakin sa tagumi ta rafka zuciyar tunkushe da. tunani kala-kala 

a daren Ranar Malan Abdallah ya sheda Alhaji munnir Amincewar su  akan maganar  da sukayi Kamar yadda Mubarak ya faɗa masa ya gama da Iman kuma ya tabbatar ita ma Ammi zata amince din.

Alhaji munnir ya jima bai shiga farin ciki irin na ranar ba duk wanda yake tare dashi zai fuskanci hakan a daren ranar ya tattara Alhalin sa kaf a babban palorn sa Mami,hajiya fauziya tare da Suhail.

gyaran murya yayi ya ce"Abinda yasa na tara ku anan,ina so na shaida Maku na samo wa Suhail matar da zai aura kuma kuma cikin watan nan nake so a daura auren"

tuni Suhail ya dago idanun ya kalli Abba ji yayi maganar ta yi masa kama da saukar aradu aure kuma shi?.

Hajiya fauziya ta ce"Masha Allah"

Mami ta washe baki dan duk a tunanin ta Abba a cikin ɗiyan abokan  sa ya sama wa Suhail mata.

cike da fara'a ta ce"Alhaji diyar governor ce ko dan majalissa"
harara ya wurga mata ya ce"to ba Abinda kike tunani ba diyar wani baban Malami ce"

dogon tsaki taja ta ce"Haba Alhaji ka rasa inda zata nema wa ɗan ka Aure sai gidan malamai wannnan zubar da mutuncin kai ne ma wallahi kuma. hadda kimar Suhail din yaro kyakyawa  mai ilimi irin suhail ace ya kare a gidan malamai to ni sam ban Amince ba ni ka barni da kai na zan samo masa matar da zai aura na tabbatar ko diyar shugaban kasa Suhail zai iya neman auren  ta mi za'ayi da diyar Malamai kaii  ala dole sai kun haɗa irin da talakka"

Murmushi hajiya fauziya tayi dan tasan sarai da ita take

Abba da zuciyar ke tafarfasa  jin kalaman mami ji yayi kamar ya tashi ya wanke ta da mari control din kansa yayi ya ce"Naji din ai diyan talakkan sun fi  da yawa daga cikin masu kudin tarbiya da sanin darajar dan adama kai Allah ya wadaran Gidan da aka tara dukiya babu tarbiyya"

maganganun Alhaji suyi wa mami zafi tashi tayi ta ce"Nagode, Alhaji dama ka shirya Wannan zaman ne dan ka cimin mutunci Amman ka sani na isa da yarana wallahi Suhail bazai taɓa auren diyar  Malamai ba"

tana kaiwa nan tayi fuuu ta fice daga ɗakin Abba ya dawo kan Suhail dan tun maganar da Abba yayi ta farko ta daskarar dashi a wajen

"Suhail"

dago idanun sa yayi da suka ƙaɗa sukayi jajir ya ce" na'am abba"

"did You have something to say"

so yake ya faɗa wa Abba yana da wacce take san shi kuma yayi mata Alƙawarin aure amman ya ƙasa, ji yayi ba zai iya ja da maganar Abba ba , ba Tun suna yara mahaifin su ke kula da su ya basu Ilimin addini da na zamani Abba Mutun ne mai tsayawa iyalensa da badan shi ba da bai zama yadda yake a Yanzu ba ya samu ingantaccen ilimi da yake alfahari dashi yau yan ganin Amincewar zata zama kamar ya saka masa da kwatan-kwacin abinda yayi masa a rayuwa kuma yana da yaƙinin mahaifinsa bazai zaɓa masa abinda zai cutar da shi ba"

ji yayi hawaye naso zu zubo masa da sauri yasa tafin hannun sa ya goge cikin karyayyar zuciya ya ce"Abba na Amince"

shi kansa yasan ya fada ne amman ba har cikin zuciya ba dayan bangaren zuciyar sa na tuno masa sa zeenah da yake ganin kamar ya ci Amanar ta

murmushi ya faɗaɗa a fuskar Abba ya ce"nasan baza ka taɓa watsamin ƙasa a ido ba Suhail ,kai da Zarah Ina matukar alfahari daku ban taɓa yanke hukunci a kanku kun musa min ba a gidan nan ko yayi maku dad'i ko akasin haka Allah yayi maku albarka gaba dayan ku"

Aunty Fauziya ta ce"Amin"

Suhail da Zarah sun fita daban cikin yaran Hajiya laila basu dauko halayen mahaifiyar su ba suna da haƙuri ,Duniya da abinda ke cikin ta baya gaban su , Zarah ce babba duka cikin su tana aure wani Babban attajiri a abuja  yaran ta biyu Amatullah yar shekara biyar sai junaid dan shekaru ɗaya daga Suhail sai kanwar su Naima tana auren kanin governor din Jigawa suna zaune a dutse tana da yarinya ɗaya Ayla.

Suhail da kyar ya iya kai kasan ɗaki wani irin jiri ke dibar sa lokaci guda zuciyar sa na tuna masa da zeenah da wani ido zai kalleta ya mata bayanin abinda ke faruwa ayyah zata fahimta kuwa?"


KU BIYO NI A PAGE 11 
like, comment and share