NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)
CHAPTER 24 ( getting along or getting apart?)
by @deejasmah
Idanuwansu ya rufe ruf ba su ji kuma ba su gani, sai abinda zukatansu suke raya musu akan lokacin. Sai da tafiya tayi nisa tayi ana shirin sake kusantata da azabar da ta fuskanta a daren jiya kuma ba wai ta warke daga na jiyan ba ne, ya sanya ta fara k'ok'arin janye jikinta.
Ture shi tayi a rikice sannan ta ja duvet ta lullub'e jikinta tana mai maida numfashi, hannu ya kai da niyyar sake janyo ta cikin fitar hayyaci don yau ma ya kai gejin da ba zai iya jurewa ba. Sake k'ank'ame jikinta tayi shi ma ya sake matsowa jikinta yana maida numfashi, shiru sukayi shi da ita kowa yana sauraron bugun zuciyar d'an uwanshi na mintoci sai da ya d'an samu natsuwarshi ta d'an dawo amma har lokacin babu mai kuzari a cikinsu bud'e idanunshi da har sun canja kala yana cewa " Awiro? (Me yasa?)".
"Tiy ni kuttu, (Ban da lafiya)" ta amsa a shagwab'e,hannu ya kai ya dafa kanta yana cewa " me yake damunki?".
"Ka sani mana".
Zare idanu yayi yana sake shige mata yace " shi ne baki gaya min ba? Mu ga wurin". Zare idanu tayi tana cewa " kaiii!! Haba Yaa" cewa yayi " meye a ciki, bud'e in gani ".
Da mugun sauri ta janye jikinta daga gareshi, tana shirin dira daga gadon ta ma manta ba riga jikin ta shi ma towel d'in an yar da shi a toilet cikin zafin nama ya rik'ota kan gadon ya dawo da ita yana cewa " ashe ma kin warke kenan, na ga har ƙarfi kike da shi sosai".
"Ni ban warke ba ai" ta furta tana kwab'e fuska, cewa yayi " shi ne sai kin ji ma kanki ciwo, ko ki fama na jikin ki?". Shiru kawai tayi ba ta tanka ba sai duk'ar da kai da tayi, d'an murmushi ya saki ganin yanda ta tsume yace " in ta ni ne ba sai na duba ba, na bari ok? Hope ciwon ba sosai ba ne ko mu je asibiti?".
"Ba sai mun je ba, zai wanke in shaa Allah".
"Alright " ya furta yana mai tsura ma jikinta idanu, sai lokacin ne ta tuna ba ta da riga ai ko da sauri ta duk'e a cikin gadon tana sake jan bargo har kan ta, tab'e baki yayi cikin son danne dariyar shi komawa yayi gefenta ya kwanta haske ya kai hannu ya kashe bai kuma sake tab'a ta ba har bacci ya kwashe shi a wurin. Jin numfashinshi yana sauka a hankali ya sanya ta sauka daga gadon, da wayarta ta haska ta nemo wata sleeping dress ta zura toilet ta shiga ta gyara wurin alwala ta sake d'aurawa kafin ta fito shigewa tayi jikinshi ta lumshe idanu a haka har bacci ya d'auketa.
Tun daga ranar bai sake nemanta ba duk da a d'aki d'aya suke kwana wato d'akinta ko na shi amma tsakaninshi da ita wasanni ne, don in dai yana gida hannun shi yana jikin ta amma bai tab'a ƙetare iyakar shi da ita don ya fi son ta warke sosai kafin ya k'ara ziyartan ta.
Ya jure na tsawon kwana biyar inda ita a tun rana na uku ta koma office don tana jin ta normal, har girki ranar tayi musu ai ko a ranshi kamar ya goyata amma ko a fuska bai nuna ba sai kwasar girkinshi da yayi ya cika ciki. Ta sha ko zai nemeta a ranar amma bayan abinda ya saba bai k'ara a kan hakan ba, duk da bai k'are darenshi ta dad'i ban haka dai ya sake jurewa ya k'ara mata kwana biyu akai ranar ko ko k'afa bai d'aga mata ba k'afa ba sai da ya huce takaicin kwanakin da yayi cikin kad'aici.
Shima dai daren nasu na biyu ya ji a jikin ta, amma ba kamar wancan ranar ba daga nan bai sake d'aga mata k'afa ba ya cigaba da abinda ya fara. Tun tana raki har ta saba itama ta fara fiddo da nata salon fiye da yanda yake tsammani daga wurin taq, toh ai haka ake so bayin Allah.
A kullum kwanan duniya sake samun kusanci sukeyi da juna, sabo musamman wurin bacci yana sake shigarsu Amma fa akwai k'arancin sakewa, shak'uwa haka soyayya a tsakaninsu.
Zai iya zama kamar almara tunda akwai sabo me ye ya hana shak'uwa mai k'arfi a tsakaninsu, wannan ba komai ba ne face rashin fira ko in ce har da rashin sanin me d'an uwanshi yake ciki. Rayuwarsu a zahiri ma'aurata ne toh amma maaurata ai akwai yarda da kuma fahimtar juna tsakaninsu da ba da shawara ko, toh a gidan BAY dai babu don kowa kamar zamanshi yake yi magana in ba ta kama ba ne basu cika yi ba.
Duk da ko yanda Nadeefahr take k'ok'ari wajen ganin an samu wannan a tsakaninsu, tana yawan jan shi da hira but yana yawan katseta a tsakiya haka in shawara ne ma yana bata masu fissheta musamman a business amma ba kasafai ya cika ba sai in ya ga dama. A lokacin ita ta k'ara saninshi amma shi bai ba tab'a zurfafawa ga sanin nata ba, ko nuna mata bai yi ya gano ita wacece ba ( Nadee's Arts da yake nema ba). Ran da tayi masa kyautan wani frame da tayi na zanenshi duk da yaji daɗi amma a fili ko nagode bai ce mata ba sai "yayi kyau" kawai yace mata kawai. Ita ko bata damu ko ya gode d'in ko akasin haka ba don ta fahimci cewa yaji daɗi kawai yana k'yashin fad'in hakan ne, kuma ma ta sha kamashi yana k'arewa zanenta kallo a kullum ya shiga parlornta shine ma dalilin da ya sa ta dage ta zana masa duk da ƙuiyar Zane duk yabi ya kamata sai tayi da gaske take iyawa.
A haka har aka fara shirin azumi, a tsukin tayi busy da ayyukan rabon da zata yi. List tayi na wainda zata fara ba ma wa da kuma mutanen Yerwa complex za ta fara, a na saura sati d'aya aka kawo motar kaya guda aka ajiye a tsakiyar wajen tunda ga staffs har security kai har mabaratan da kan zo cikin complex d'in da masu shige da fice sai da suka samu na su kason su kuma nata staffs d'in tayi musu k'ari akan salarynsu.
Ranar har ƴan maƙotan plaza da suke wurin sai da suka shisshigo suka amsa, da yake akwai security ya sanya ba a wani yi rikici ba kowa yazo zai amshi card mai number a jiki. Kana zuwa wajen amsa ka bada card d'in zasu yi signing su saka a cikin wata box sai a baka package d'in mai d'auke da kayan masarufi mai d'an yawa, har wasu daga wani wuri can sun zo sun amshi na su ana ta shi ma mai rabon albarka.
Duk da ko ba wanda ya san waye don tayi gargad'i mai k'arfi akan hakan, ranar ko ma office ba ta je ba tana gidan Hajjah. Haka ko a social media ba su sanar ba, mutane ne ma suke ta aikin yad'a maganar ka san duk yanda aka yi da mutanen zamaninmu sai sun yi posting abu a media balle na rabo irin wannan. Su ma kuma Yerwa Group suke ta sawa a matsayin wainda sukayi aikin, ai ko ranar an yi ruwan godiya da sanya albarka a garesu. Yayinda aka dinga tagging manyan k'asa tun daga kan 'yan siyasa da 'yan kasuwa akan suyi koyi da abinda sukayi, ba a tsaya nan ba har gidajen TV da radio sai da aka dinga shela ta nan nan ne aka wasu ma suka sake sani sai dare kafin motar ta wuce tunda kayan sun k'are hakan ne ma ya sa mutanen suka fara watsewa.
Washe gari kuma suka tafi orphanage da gidajen gajiyayyu aka kai musu na su har da kayan sawa, ba su tsaya nan ba har prison da rehab centres. Sai fatan Allah ya k'ara arzik'i kawai ake yi.
Yau da mugun gajiya ta dawo gida ga yunwa tana ji don ko breakfast ba tayi ba ta fita, wanka ta samu ta watso ta samu wuri akan sofa ta kwanta ko ta kan abincin ba ta bi ba don ba ta shi take ba gajiyar da tayi ma ya isheta. Agogo ta kalla 5:15 ta san ko bacci tace zata yi yanzu ba wani dad'inshi za ta ji ba, amma tana buk'atar hutu ko jikinta zai sake ta gaji fiyeda kowace rana sauk'inta ma daga yau shike nan sai kuma shirin tarban azumi da ake yi nan da kwana biyu.
Hamma ta sake yi a karo na barkatai wayarta ta janyo tana kiran number Hajjah, tana shiga ta d'aga da kulawa tana cewa " Lele yanzu nake zancenki a raina wallah, kin koma gida dai ko?". Ajiyar zuciya ta sauke tana mai cewa "uhmm gani nan ma kwance ga yunwa ga gajiya, amma fa ba zan iya girki ba" ta k'are tana k'wal da idanu kamar za tayi kuka kai ka ce tana gabanta ne, cewa tayi " Sannu diwu, ai aikin lada kike yi Allah ya karb'a yayi miki albarka yanzu ya zaki yi da abincin ko zaku siya ne kawai?".
"Uhm uhm, ni naki nake so bari ma in kirashi yazo ya amsa kawai ".
"Ya zo ya amsa tunda d'anki ne ko? Bari in kira Mele ya kawo miki tunda kin ga wurin ba kusa ba ".
"Toh Hajjah, a saka nama da yawa please ".
"Ba zan saka ba 'yar nema mara naman zan aiko da shi in kinga dama kar kici".
"Ki bar kayanki kawai mijina zai siya mini, don ma kin samu ana son aci abincinki ".
Dariya tayi tana cewa " ai ban kiraki na rok'eki ki ci ba, ba mijinki zaki kira ba ki kira na gabanshi in kin isa kafin ma ki san zaki yi shi mu har mun yi namu balle wai ki cusa mana takaici kuma soyayyar da muka ci ko rabinta ba zaku iya ci ba".
"Wai Hajjah kuma lokacinku ana soyayya ne? Like auren soyayya kuma kuka yi? Na zaci fa irin na ladan noman nan aka muku da shi".
"Ina fa ake soyayya a lokacinmu? Ai soyayya sai gidan su Nadeefah da Burhaan, dalilinsu ma aka haifeta wasu ma tabarraki suke dangwala balle kuma mu da aka yi wa auren biyan bashi ba ma ladan noma ba".
Dariya ta k'yalk'yale da shi tana cewa " ni fa na ga alama ashe ba ma na ladan noma ba ne bashi aka biya, Amarya kuma Uwargidan Aji Garwa".
"Wallahi Nadeefah ki kiyayeni" ta furta tana murmushin halin Nadeefahr ita kowa bai tsira da tsokanarta ba, daga su kakanni har iyaye.
Cewa tayi " Hajjah Nadeefah fa kika ce? Ina Lelen ya tafi?" Ta k'arashe tana fashewa da kukan shagwab'a, " za ma kiyi ki gama ne amma na cire Lelen ban kuma kira " ta furta tana gimtse dariyarta.
"Ki yi hak'uri toh Ka'a, zau yaye(Please)".
"Uhm tohm, sai anjima " ta katse wayar kamar da gasken tayi fushi, amma tana ajiyewa Mele ta dannawa kira akan yazo tana nemanshi. Da yake yau ya fito gida tun safe ya sa da sauri don gudun rikicin Hajjah, ga kuma ba a dad'e da musu rabon azumin ba su ma infact ba su kad'ai ba har danginsu don kowa wakilcin unguwarshi aka ba shi. Kafin ya zo ta sa Yana ta shirya musu abincin a kwanukan acrylic masu kyau, an kuma cika mata naman da ta neman yana zuwa bai ko zauna ba ya kwashi kayan zuwa gidan Lelen.
Ita ko su na gama wayar murmushi tayi ta ajiye wayar, ta san halin Hajjah ba wani fushi da tayi ta dai fad'i ne kawai. Mai da kanta tayi inda yake ta sake kwanciya ba tayi baccin ba, sai ma kallo kawai da ta kunna abinta duk da ba wai tayi focusing completely kan kallon ba ne kawai dai saboda kar zaman ya gundureta ne.
Gab da Magrib Mele ya kawo sak'on, bell ya tab'a ta taso a gajiye tana d'aukar hijabi ta d'aura a kan gown d'in da ta sanya. Armless ce kuma short don iyakacinta guiwa akwai kuma tsagu a gefe da gefen rigar, fita tayi ta ganshi zaune cikin kujerun waiting room d'in.
Gaisawa sukayi a mutunce sannan ta amshi kayan ta koma ciki bayan ta shaida masa ya gaida Hajjah, tana shiga ta dire su a dining cupboard ta bud'e ta d'auko plates da spoons ta d'auraye kana ta shiga kitchen ta d'auko ruwa da drink ta dawo ta zauna.
Serving kan ta biskin da miyar ganyen tayi wanda har da yankakkiyar kub'ewa a ciki ta zuba nama ta yawa, ta ci sosai ko dan tana jin yunwa ne oho sai da ta tattabar da cewa cikinta ya d'auka kafin ta tashi a wurin lokacin ma ana kiran Magrib.
Ba shi ya shigo gidan ba sai bayan ishai da ledarshi, ajiyeta yayi a parlor yayi wanka first kafin ya wuce d'akinta jin shiru. Ai ko a kan gado ya tarda ta ta shige cikin bargo tana son yin bacci, ganinshi ya sa ta kwab'e fuska don ta san me zai biyo bayan shigowar ta shi.
Zama tayi tana cewa " Welcome home, Yaa".
"Uhmm thanks wife, ba dai bacci ba?" Ya tambaya yana zama a gabanta, gumtse bakinta tayi daga murmushin kiranta wife da yayi a shagwab'e tace " Allah ya na gaji ne ".
Cewa yayi " ai kwana biyun nan kullum a gajiye kike, da mutum ya tab'a ki ki fara raki ".
Rufe idanunta tayi a kunyace tace " kai Yaa".
" Ba wani kai Madam, mu je in ci abinci and gwara ma kin shirya tarba ta a daren nan". Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye yana miƙa mata hannunshi wai ta kama, nata hannun ta sanya cikin na shi da kanshi ya d'agata sai sake narkewa takeyi. Sai da suka je dining ya zauna kafin ya saki hannayen nata, serving d'in shi tayi ta na bashi labarin Hajjah ce ta aiko mata da shi kan shi ya gyad'a yana jinjina irin matsayinta a wurin Hajjahr in da wata ce ma fad'a zatayi mata akan k'in yin girki amma da yake ita ce sai ma aka kawo mata.
Bai ce uffan ba ya fara cin abincinshi, yayi dad'i don yana gwana ce wurin girki amma shi dai bai wani ci da yawa ba don in ba abincinta ba bai iya sakin jiki ya ci da yawa ko da na Umma ne kuwa. Turewa yayi gefe ya na goge bakinshi da tissue, tattara wurin tayi ta kai sauran kayan kitchen ta ajiye komai a inda ya dace kafin ta fito. A tsaye ta tarda shi ya kullo k'ofofin gidan ya dawo, ajiyar zuciya ta sauke tana bin shi a baya sai da ya shiga toilet d'in ta yayi brush kafin ya hau gadon yana janyota jikinshi kamar dai yadda ya fad'in bai ko d'aga mata k'afa ba har sai da ya samu natsuwar da yake buk'ata nan wani gajiyar ya sake sark'afarta haka ta koma gefe tana numfashi.
Washe gari kam k'in fita tayi don ta gaji da yawa, a yanzu kam ta tabbatar tana buk'atar mai taya ta aiki balle kuma ga azumi yana zuwa taa tabbatar cewa aikin zai fi haka amma kuma ta ina zata fara tunkararshi da maganar shi ne ba ta sani ba. Lumshe idanu tayi tana lissafin ko dai Umma za ta kira ne kawai? Amma kuma ai zai iya zama rikici a tsakaninsu don ta tabbatar d'an sakin fuskar da yake musu zai iya dainawa gabaɗaya, in ma bai wulak'anta ta irin na baya ba so yanzu kwanciyar hankalinta da shi ya fiye mata komai amma kuma gajiyar mafita ce a gareta bayan ba ta tashi taga ana wahala a gidansu ba a k'asan ranta ta furta '' zan fara magana da shi in ya yarda toh in kuma yace a'a haka nan zan yi haƙuri'.
Wayanta ta janyo tana sake tuna wa wainda zasu kawo package d'in da tayi order, sun bata tabbacin yau da yamma za a kawo godiya ta musu tana sakin murmushi ta tabbatar zai so abinda take masa shiri. Kamar an tsikareta ta tashi da gudu ta nufi artroom d'in ta, cikeda k'warewa ta fara design d'in calligraphyn da take son had'awa a cikin package d'in shi ne ma ya d'auke mata hankali ta ma nemi gajiyan ta rasa.
Ayar " sharur-ramadhanal-lazhi-unzila-fihil-quran" ta rubuta da larabci ta kuma yi translation d'in sai can k'asan ta rubuta Ramadhan-Mubarak Habibie, tayi mai kyakkyawan wasali da khad'd'i mai d'aukar hankali. Rufe rubutun tayi da plain paper tayi spraying da gold kana ta bud'e, gyara inda bai samu ba tayi sai shi kuma rubutun ta sake tracing da bak'in kala mai k'yalli. D'an 3D finishing tayi da bak'in shi ma ta sake embosssing rubutun da glitters shi ma, ja da baya tayi tana sake kallon design d'in yayi mugun kyau. Wasu k'ananun abubuwa ta sake gyarawa har yayi mata yanda take so kafin ta fara framing a wani gold resin frame mai matuk'ar kyau anyi customizing wata a ciki da taurari, lumshe idanu tayi ta bud'e tana cewa " yayi kyau sosai, kamar dai mijina".
Sai ta saki murmushi sai da tayi hotuna da videos kafin ta d'auka zuwa parlor, a kan dining ta ajiye ta zauna cikin kujera tana jiran masu kawo sak'on duk ta k'agara. Ba su suka kawo ba sai 3:15 ita ta fita ta amso tayi signing kafin security suka shigo mata da shi cikin gida, bud'e package d'in da akayiwa kyakkyawan wrap tayi komai da tayi order an saka tunda ga carbi da customized dadduma mai taushi ga mug, Kur'ani har da trainers da track suit farare na Puma a ciki. Murmushi tayi ta maida ta d'aure da kyau yanda aka kawo ta had'a da frame d'in ta nufi ciki da shi, sallah tayi kana ta fito kitchen.
Yau tuwo tayi musu na shinkafa da miyar egusi, da assorted meat traditional drink tayi masa na pineapple, ginger da kuma coconut. Shirya komai tayi a dining sannan ta shiga d'aki, wanka ta shiga ta dad'e kafin ta fito haka ta sake zama a gaban madubi light makeup tayi da nude lips sai kuma smoky eyes. Roller ta d'auka tayi rolling gashin kanta da kyau yayi kamar spagetti red hair color ta fesa a k'arshen gashin ba tareda ta d'aure shi ba turare ta shafa a gab'ban jikinta kafin ta nufi closet shiryawa tayi cikin wata double slits straight gown na Giorgio Armani. QWanda ya amshi jikinta sosai musamman ma 'yar kib'ar da tayi da ta k'ara k'awata jikinta, tsayawa tayi a gaban madubi tayi juyi 360 har ta d'auki wayarta da niyyar shiga snap sai kuma ta fasa don ganin rashin kyautuwar hakan. Hijabi ta d'auko ta hau kan dadduma tana tada sallahr magriba, kamar yadda ta saba yau ma bata tashi ba sai da ta gabatar da sallahr ishai. Turare ta k'ara a jikinta ta d'auki wasu shegun heels na kamfanin Fendy kamar mai zuwa party kafin ta fita parlor, a daidai k'ofar shigowa part d'in ta taci karo da Burhaan zai shigo.
Don ya shigo gab da Magrib ya ji k'arar ruwa a toilet d'in ta kasancewar yayi alwala kuma fita zai yi zuwa masallaci ya sa bai shiga toilet d'in ba don ya tabbatar sai ya karya alwalarshi in ma bai yi missing sallahr a jam'i ba. Ya sanya ya ja 'yanmatan k'afafunshi zuwa masallaci, yanzu ma da ya dawo ya ji shirun yayi yawa ya sanya ya biyota tunaninshi ko dai ba lafiya ba. Kyakkyawar ganin da yayi da ita ya sanya shi sandarewa yana binta da kallo sala-sala, bai tab'a ganin mace mai kyau da kwalliya yake wa mugun kyau kamar Nadeefah ba. Smoky eyes d'in da tayi ya sake fito mata da idanun ta ta masu girma da kyau ga su kusan kullum a lumshe kamar na mai jin bacci, miyau ya had'iye yana kallon lips ɗin ta da suka ji lip gloss mai k'yalli yana tuna laushin su da zaƙin su.
Cikin muryarta mai sanyi, taushi da kwantar da hankali tace " Yaa ka dawo?".
Lumshe idanu yayi ya bud'e a kanta yana cewa " yeah, ya kike?".
"Lafiya lau, ya aikin?".
Kasa amsawa yayi ya matso gabanta yana sake kafe lips d'in ta da idanu, saitawa yayi yana k'ok'arin had'ewa da na shi. Zillewa tayi cikin salo tana cewa " na san kana jin yunwa, mu je in baka abinci". Da wani kallo ya bita idanun shi, cije baki yayi yana bin bayanta idanunshi k'yar a kan kwankwasonta da take juyawa yana jerawa da tafiyarta na catwalking.
Kafin ya iso ta ja masa kujera zama yayi ita kuma ta fara serving d'in shi, kafin ta saka wa kanta itama spoon ta ba shi ta san yafi ci da shi ita ko hannunta ta wanke ta sanya a ciki. Gutsura tayi d'an dai-dai tana kaiwa bakinta, yanda ta sanya hannun kamar da wani salo sai da ya sake motsa masa da magudanar jinin jikinshi. Balle da ta tsotse yatsun tana lumshe idanu tana gyad'a kai alamun abincin is giving, lashe na shi bakin yayi yana had'iye yawu. Har sai da tayi loma uku kafin ta lura bai cin abincin cewa tayi " Yaa ka k'oshi ne or baka so in sama maka wani abun?".
Girgiza kai yayi ba tareda yace uffan ba ya fara cin abincin bai ko sake dubanta ba, don in ya biyewa kallonta kuma zai iya yin abinda bata tab'a zata ba. Shi fa ma bai san me yake fusgar shi a kanta ba? In dai zai ganta ko da kayan mutunci ne sai yaji shaawarta balle kuma yau da tayi shigar tada hankali kuma ko ta nuna ta san abinda yake faruwa. Allah ya sani wannan na d'aya daga cikin weakness d'in shi yana son mace mai natsuwa da ɗan haɗin festara a jikin ta musamman a bedroom ga shi ya samu Nadeefah fiye da abinda yake so a d'iya mace. Da haka aka k'are cin abincin shi ya fara tashi don yadda take cin abincin kamar yaron goye dake koyan cin abinci kan couch yaje ya zauna ya sake kafa mata idanu kamar tsohon maye irin na Soban nan masu gani har hanci.
An ɗauki lokaci kafin aka samu ta kammala cin abincin, hannunta ta ja tissue ta goge da bakinta kafin ta tashi. Wanko hannun tayi ta kwashe kayan kan dining d'in ta goge, ta dad'e a cikin kitchen d'in hakan ya kawar masa da hankalinshi daga kan ta zuwa TV. Wanke-wanke tayi ta goge koina ta tsane kayan, kafin ta maida su inda ta d'auko kamar ba a yi amfani da su ba.
Wuceshi tayi ta kinkimo package d'in ta zo gabanshi ta zauna, a kan cinyarshi ta ajiye tana shafa cinyar k'adan da akaifarta masu d'an tsawo amma an yanke su ba yanda zai ji ma mutum ciwo ba. Kallonta yayi da idanu ya tamabyeta ko na menene, itama da idanun ta nuna masa ya bud'e kawai. Tab'e baki yayi ta bud'e cak ya tsaya ya kalli cikin box d'in ya sake dubanta, murmushi tayi kawai ciro kayan yayi ya bubbud'e originals d'in ne kuma masu tsada ba wai gama gari ba.
Had'asu yayi da trainers d'in kana ya zaro daddumar itama mai mugun taushi an rubuta Habibie a kai, haka mug d'in da customized Qur'an, littafi da biro sai casbaha mai kyau bak'i na maza sai wani k'aramin alarm clock. Duk yanda ya ɗaure sai da yayi murmushi ƙarami ya d'aga box d'in idanunshi ya sauka akan frame d'in da yake da tabbacin ita ta zana shi, yana son zane sosai hakan ya sa yafi jin zanen a ranshi fiyeda komai.
Mazewa yayi yana b'oye farin cikin shi yace " na miye?". Murmushi tayi tana cewa " gift ɗin Ramadhan neYaa, Allah ya amshi ibadunmu na alkhairi".
"Ameen, but wife da baki wahal da kan ki ba saboda.....?"
"Ba ka so na so bai cancanci ka amshi kyauta daga wurina ba ko? Nima fa ba wai ina forcing ɗin ka bane ka karɓa ba amma ba zaka iya amsa ko a matsayin kyautar ƙanwa ga yayanta ba?".
"Wife.....!".
"Issokay in baka so, na gane". Daga haka ta tashi tana danne hawayenta ta shige cikin d'akinta tana buga ƙofar da ƙarfi, da idanu ya rakata yana mai jin ba dad'i a abinda ya faru. Wai shin ma menene tayi masa da zafi haka da har ya sa bai iya bata girman da ya kamata? Tana son shi tana son daidaita komai tsakanin su amma shi ba abinda yake yi sai korar ta da kuma nuna mata cewa ba ta kai matsayin wacce zai iya rayuwa da ita ko son ta ba.
Ba laifin shi ba ne Allah ma ya sani, yana iyaka k'ok'arinshi a kanta he hates been mean and cold towards her amma zuciyarshi ta k'i ba shi had'in kai. Shin hakan na nufin shi mutumin banza ne? A wurare da dama amsar ɗaya ce EH. Shi mugu ne tunda ya kasa tank'wara zuciyarshi ga son wacce ta cancanci a so ta a kuma kula da ita, bai kuma tsaya a nan ba sai ya nuna mata cewa kasancewar ta gare shi bai da wani muhimmanci a gareta sai ta wajen shimfid'a.
Wannan kuma cin zarafi ne saboda Nadeefah daban ce a cikin mata ta tara dukkan abinda yake so " amma kuma ta zubda ajinta wajen fad'a maka tana sonka" zuciyarshi ta furta masa cikin son sake nuna masa cewa ita d'in tayi k'aranta da yawa amma hakan na nufi ita ɗin mara daraja ce kamar yadda ya zata a farko? Amsar shi ne A'a don ita aba ce mai matuƙar daraja da ba kowa ke samu ba sai mai tsananin rabo ya kuma san da haka sai dai hange-hange irin ta zuciyarshi ya hanashi kamuwa a cikin soyayyar tata kuma bai son saka mata rai ta hanyar mata cewa ya karɓi komai har ma ta fara tunanin cewa ya fara sonta ne don duk ran da ta gane bai son ta d'in ya san wannan abun zai iya fasa mata zuciya in ta gane rufe mata yayi abinda kuma bai so ko fata ne har abada musamman a yanzu da ya san muhimmancinta tarkata kayan yayi ya bi bayanta da sauri.
Ba ta bedroom d'in da ya saba shiga ciki, bud'e ɗakin da ke dama yayi ba ta ciki shi ma na hagun ya bud'e nan ya tardata a kujera mai lilo da ke gefen ta zauna ta tura k'afafunta cikinta ta kuma d'aura kanta a kan tank'wasassun guiwoyinta hakan ya ba wa gashinta bajewa a gadon bayanta da ma fuskarta. Gabanta ya k'arasa yana mai k'ok'arin d'agata k'wacewa tayi in da ta kusa fad'uwa saboda kujerar dai lilo take yi ga uban pillows a ciki da kuma shape d'in ta, saurin rik'ota yayi cikin jikinshi yana bubbuga bayanta alamun rarrashi yana cewa "shhhhh......".
Banza tayi masa tana mai jin d'aci a ranta da kuma takaicin kanta da kanta, Allah ya sani ba ta tab'a nadamar son Burhaan ba haka har yau ba ta dana sanin furta masa abinda ke cikin zuciyarta amma kuma a yau taji haushin abinda ya faru fiyeda komai. Wanda ba komai ya assasahi ba face ganin darajarta yayi fad'uwar bak'ar tasa a idanun Yaa Islaam da yake ganin duk wani da zata yi masa don karkato da hankalinshi ne kanta, wanda in da dan hakan ne ai ba abun kunya tayi ba kuma ita ta na yi ne saboda kyautatawar miji da mata ba don komai ba. Kuma ko bai aurenta ai d'anuwanta ne so ba shi kyautar da duka ba ta fi 200k ai ba wani abu ba ne da har zai iya k'in amsa saboda ba ta kai matsayin ba shi kyauta ba.
Janta yayi zuwa kan carpet yana mai cewa "ki daina kuka, kanki zai yi ciwo".
Cikin rad'a-rad'a da muryar kukan tace " ka yi haƙuri ina ta cusa maka kai na, in shaa Allah ba zan kuma ba".
"Ni ya kamata in baki haƙuri ba ke ba wife, kuma waye yace kina cusa kan ki wurina ehnn kar fa ki manta ni mijinki ne fa".
"But kamar ina wuce makaɗi da rawa, ka yi hak'uri ba zan sake ba ".
"Shhhhhhh ki daina faɗin haka kin ji? Nima ba ƙin karɓa nayi ba, kin shammace ni ne ban taɓa expecting hakan ba ne kuma sai nayi kunyar kaina da ban tab'a baki kyauta ba amma ke kinyi tunanin ba ni ".
'' Ni ban baka ko dan tunanin komai ba,Yayana na bawa in dai ina da wannan matsayin a wurinka ba zaka taɓa yin jinkirin karɓar kyauta daga wurina ba".
''Kin fi gaban nan ma Wife, ki daina kuka kin ji " ajiyar zuciya kawai ta sauke tana janye jikinta daga gareshi, toilet ta wuce wanka tayi tana shilla kayan a laundry ta fito yana inda ta bar shi ko mai bata shafa ba nightie ta zura kawai ta haye gadon har yanzu k'irjinta na suya. Da idanu ya rakata ganin tana ta sauke ajiyar zuciya kuma hawayen bai daina zuba ba, ta lallashi kanta a toilet a kan kukan amma tana ganinshi suka sake zubowa "wato ita gata sakarya wacce bata san me take yi ba ko" yanda tayi ba ƙaramin kyau ya mata ba tayi kamar ƴar tsana, tasowa yayi ya hawo gadon a bayanta ya kwanta yana janyota jikinshi cije baki tayi yau kam ko yafi k'uda kwad'ayi ba ta ba shi sai dai ya karb'a ta k'arfi wato ba ta da matsayi a idanunshi da ya wuce kawar masa da sha'awa toh yau zai ga tsiya don zata nuna masa itama mace ce kuma mai zuciya. Shi ma ko kamar ya san me ke zuciyarta bai ko nema ba tunda ya rungumeta cikin k'irjinshi ya tafi tunanin rayuwa sun dad'e kafin bacci ya kwashe su.
Da asuba yana tashi sallah ya kwashe kayan ya closet d'in shi ya adana, ita ma sallahr ta yi ta kwanta sai lokacin take wa kan ta faɗa akan kukan da tayi. Taune lips tayi tana cewa "ai yanzu sai ya sake raina mu ke da kan ki kikayi alk'awarin daina masa kuka akan soyayya ga shi nan kuma ba ko ayi nisa ba" ta k'are tana tsaki, jan duvet tayi cikeda nauyin zuciya har kanta ta lumshe idanu tana tunanin mafita................
Toh Allah ya wanye mana🌚.
Deejasmah ✍🏼