LULLUƁIN BIRI

47

by @halimahz

Yana gama bin azkar ɗin da yake sauraro a tv ya jinginar da kansa da kujera, lokacin tuni gari ya waye har ƙarfe shida da rabi ta kusa. 
Idonsa a lumshe hoton Fullo nata haska masa, lokacin ne Ilham ta fito daga bedroom tana takowa da ƙyar har ta ƙaraso wajensa, abaya ne yello colour jikinta mai bala'in kyau, ta ɗora hular chantly akan kwantacciyar sumar kanta, ta yi kyau sosaida light makeup ɗin da ta yi sai zuba ƙamshi take yi, ta ɗauke hannunsa akan kujerar sannan ta zauna a kusa da shi ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, hannun nasa kuma ta ɗora akan cinyarta.

Muryarta a sanyaye kuma a shagwaɓe ta ce,"Hammah fever na son kama ni, kaina yana ciwo sosai, jikina ma duk ciwo yake yi".

Ta ƙarasa maganar yana jin saukar hawayen nata a kafaɗarsa, yana jin yanda ɗumin hawayen ya tsarga fatar jikinsa, yana kwatanto shi da zafin hawayen Fullo, wacce ya san a duk inda take yanzu kuka take yi.

Bai ce da Gimbiya Ilham komai ba har wucewar daƙiƙa uku, lokacin wayar da ke kusa da shi ta yi ringing, yana kallon new number ne a jiki yaƙi ɗauka.
Har sau biyu kiran na katsewa tunaninsa duk Gimbiya Aisha ce, sai kira na uku ya shigo da lambar Inna Falmata, kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga yana yin sallama.

Daga can ɓangaren Boɗejo ta amsa sallamar tasa tana ɗorawa da faɗin,"Ban kiraka da lambata ba saboda na san ba ɗagawa zaka yi ba, ashe sabuwar lambar ma baka ɗagawa, sai ka ɗaga ta Falmata da yake kasan ta ƙanwar ubanka ce, ko ba komai halin girmama manyanka na burge ni, duk uban miskilancinka ka san darajar manyanka".

Ya ji kamar ya kashe wayar dan mugun haushinta yake ji, amma sai bai yi hakan ba. 
A daƙile ya ce,"Ina kwana". 

Ta ce,"Lafiya lau, kun wayi gari lafiya?". 

Ya ce,"Lafiya lau". Yadda ya amsa ɗin kamar a fusace.

Ta sake cewa,"Yauwa dama zan tambayeka ne ya ka sami Ilham ɗin?". 

Ta faɗa tana yin ƙasa da murya. 

Ya ce,"Lafiya lau, ba ki da lambarta ne?". 

Ta ce,"Ya salam, baka gane nufina ba ne? Ita yarinyar a ya ka sameta na ke nufi?". 

Ya ƙara cewa,"Lafiya lau, ba ki da lambarta ne?". 

Boɗejo ta ji kamar ta kai masa duka ta cikin wayar, kuma da ta iya ashariya sai ta yarfa masa. Dan in kusa gareta yake ma ba abin da zai hana faruwar hakan wajen bige masa baki.

Cike da takaici ta ƙara yin ƙasa da murya tana faɗar,"Ya zanyi tunda kai farin shiga ne, sai na yi ɓaro ɓaro tukunna zaka gane. Dama haka zance maka ya zancen budurcinta? Ya ka same shi? Fatan dai ta kawo shi lafiya?".

Da ƙosawa ya ce,"Gata ki tambayeta". 

Ya faɗa yana direwa Ilham wayar akan cinyarta.
Ta buɗe idonta da ke rufe bacci na so ya ɗauketa, ta kalla wayar da call ke tafiya, da sauri ta ɗau wayar ta saka a kunne tana cewa,"Inna ina yini". 

Boɗejo ta ce,"Ilham ni ce, lafiya na ji muryarki haka, kuka kika yi? Ko ba kya jin daɗi? Mene matsalar faɗa min, Turaki ne ya gaya miki magana babu daɗi?".

Ilham da muryar ban tausayi ta ce,"A'a". 

Ta faɗa tana sakin sabon kukan shagwaɓa. Hankalin Boɗejo a tashe ta ce,"Ni bana son kuka, ki buɗe baki ki min bayani, ko sai na zo?". 

Cikin muryar kuka Ilham ta ce,"Boɗejo jikina duk ciwo yake min, zazzaɓi ne ajikina. Kaina kamar zai cire, ki zo don Allah". 

Rai ɓace Boɗejo ta ce,"Ba wa mara mutuncin wayar". 

Ilham ta kai hannu ta ɗora masa wayar a kunne, da masifa Boɗejo ta ce,"Daga mugu sai kai Turaki, yanzu yarinyar babu lafiya shine dan tsabar zalunci baka iya ɗaga waya ka kira duk likitocin da muke da su a Family an zo an dubata ba? Haka ka ga ubanka na yiwa Madina?. Gaskiya ban yafe ba sai Allah yay mana sakayya tsakanina da kai. Kuma dan uwarka Madina ka amsa min tambayar da na yi maka tun ɗazu, in kuma sai na zo har gidan ka ga tsayina in ji".

Turaki yay guntun tsaki ya ce,"Ni dai karki ƙara zagar min uwa. Amsar tambayarki kuma ta kawo shikenan, kar ki ƙara kirana, ki kira wayarta idan kina son magana da ita, ni ban haɗa komai da damuwa ba, ki barni in ji da abin da ya dame ni".

Bai jira cewarta ba ya kashe wayar yana miƙewa ya bar wajen, Ilham tabi bayansa da kallo tana jin hawaye na sakko mata.
Yanzu shikenan irin wannan zaman za su dinƙa yi da shi? Ana aure dan farin ciki amma tun ba aje ko ina ba ta fara fuskantar ƙalubale, tana ji ana faɗar tun daga daren farko mace ke fara samun kula da tarairaya daga wajen mijinta amma ita nothing like that, ya sameta a virgin ɗinta amma kamar wadda ta zo masa a fafe, sai faman haɗe rai da kumbura yake, duk uban kukan da ta sha daren jiya sannu wannan bata samu ba, balle taimako daga garesa.

And cikin ƙarfin hali ta gyara kanta duk da zafi da raɗaɗin da take ji amma hakan bai sa yaji tausayinta ba a sanda ta tabbatar da yaji uban zafin dake jikinta sanda take kwantar da kanta jikinsa, yanzu shikenan ita wannan soyayyar da take ta kwaɗayi a gidan aure ba zata samu ba kenan? Son sa fa take, ta jima tana dakon sonsa fa, ko ace ba ayi wannan haɗin ba dama zata faɗa masa. Ashe duk wannan so da kulawar tasa da yake nuna mata shi ba haka ya ɗauka ba, ba aurenta yake so ya yi ba, kuma ba zai iya haƙurin zama da ita ɗin ba a matsayinta na ƴar uwarsa wadda ya ke so, ya ke ji da ita.

Sai kawai ta kifa kanta a hannun kujerar ta fashe da kuka mai ban tausayi. Daga can masarauta kuwa tuni ko'ina ya ɗauka da batun Gimbiya Ilham ta kai budurcinta gidan miji, kowa kuma sai ya shiga saka kyautukansa a cikin wata ƙatuwar kwalla da ke dire a ƙofar turakar Fulani Azima, guɗa kawai kake ji na tashi da tafi ana son barka ana yabon Fulani Azima da tarbiyar da ta bayar.

Ƙarfe goma sai ga manyan motoci ƴan ubansu na jiniya a ƙofar gidan Turaki, mota guda biyu ɗauke da hadimai mata, suka fito suka isa inda wata baƙar mota take cike da sassarfa. A cikin motar ne aka shiga fito da manya manya coolers na abinci, wasu coolers ɗin abinci ne cikinsu irin na gidan saurata, sai wasu coolers ɗin kuma uban kayan gara ne kamar hauka. Gimbiya Ilham tsab zata shekara da su indai ba cin yunwa aka dinƙa musu ba.

Haka suka dinƙa shiga da coolers ɗin suna fitowa suna kuma ɗibar wasu, sai da suka gama shigar da su tas sannan kuma sai ga ma'aikatan kamfanin Arewa culture Decoration suna shigowa ɗauke da kayan aiki a hannunsu suna nufar can baya inda ƙaton haraba yake wajen filoti guda, a wajen har da swimming pool irin tafkeken nan. Suka baje kayan aikinsu kuma cikin ƙanƙanen lokaci suka shiga gyara wajen da decoration irin na gidan sarauta bango zuwa bango, haka ƙasan wajen ma duk an malale shi da uban carpet mai taushi an baza uban tumtum.

Wata ƙawar Fulani Azima na zuwa taga irin yadda decoration ɗin ya haɗu, ta yi tsaye ta kasa motsi ta saki laɓɓa tana bin wajen da kallo cike da burgewa.

"Wow, la'ila ha'illahu, dan Allah a ina aka samo waɗan nan masu iya aikin. Kan uba ke kiga wuri kamar dama can a haka aka ƙera shi, na rantse da Allah wanda bai sani ba ya zo wajen nan sai ya ce masarauta ya shiga".

Sai ta yi saurin zaro waya a jaka tana miƙawa ɗaya daga cikin ma'aikatan tana cewa,"Ungo maza lafta min lambarku a wayata, ina zan yi saken wannan azababben decoration ɗin da bikin ƴata, habawaa ai dole jama'a su zo su yi kallo na ke ce raini, ta yadda gobe ba za su ƙara ɗaukan gaji garin masu decoration na musu aikin wofi suna asarar kuɗi ba".

Ma'aikacin na murmushi ya ce,"Hajajju bari na karanto miki kawai". 

Hajja Balkisu ta ce,"Yi da sauri, ai ni duk a tsume nake. Yanda kasan in ɗauke wajen nan in tafi da shi".

Ma'aikacin still da murmushi fuskarsa ya shiga karanto mata lambar yana rubutawa,"***". 

Ta ce,"Me zan saka a sunan?". 

Ya ce,"Kawai rubuta Arewa Culture Decoration".

Daga cikin gida kuwa Gimbiya Ilham na zaune tana ta bin Hadiman dake kaiwa da komowa wajen kimtsa kayayyankin da suka shigo da shi. Sai ta ji suna tafiya da zaman kaɗaicin da take ciki. Tuni Turaki ya fice daga gidan ko sallama ɓata haɗa su ba. 
Can kuma sai ta ji parlon ya karaɗe da wata uwar guɗa kamar gidan zai tsage, ta rumtse idonta for the first time da hawayen farin ciki ya sakko mata tun kawota, ko ba komai ta san duk wannan abin da ake yi na murnar ta kai budurcinta gidan miji ne. 

Boɗejo ta fito daga bedroom ɗin da suka kwana riƙe da farin bedsheet ana haskawa mutane ɓacin da yay domin su shaida, ta bawa Jakadiya Hanne tana barin wajen da rawa.

Ta isa wurin Ilham ta rugumeta tana ƙara sakin wata uwar guɗa ta musamman, sai kuma kowa ya yo kanta ana cewa,"Barka Gimbiya, sannu Gimbiya, sannu sannu, Allah ya huce gajiya, ubangiji ya kawo albarkar ɗaki, sannu. Fulani Azima na cewa agaishe ki, a gaishe ki, ayi miki gaisuwa irin gaisuwar da babu mahaluƙin da ya taɓa samunta".

Daga nan Boɗejo da Inna Falmata suka kamata su kai cikin ɗaki da ita. Bayan an yiwa Gimbiya Ilham gashin ruwan ɗumi mai kyau, sannan aka haɗa ruwan lalle da turare Boɗejo ta yi mata wanka da shi, aka fito da ita sai zuba masifaffan ƙamshi take yi. Duk wannan hidima dai da ake yi Boɗejo ƙwafa kawai take jerawa tana tunanin irin rashin mutumcin da zata yiwa Turaki, tun da yasa ƙafa ya bar ɗanyan amarya ita ɗaya kamar wadda bata da gata.

Kwalliya aka yiwa Ilham ta gani ta faɗa, ta yi azaban kyau, aka fito da ita a lulluɓe da alkyabba fara tas mai adon red a jiki, babu ta inda ake ganinta hatta ƙafarta kuwa dake sanye cikin wani half conver na sarauta, akan cushion na babban parlon gidan aka zaunar da ita ta yi zama irin na masu mulki.
Mutum uku daga dangin mahaifiyarta suka zo suka ɗaga hular alkyabbar nata ana fasheta da turare mai bala'in ƙamshin gaske, suna yi ana tafi ana busa shantu ana rera mata waƙa na son barka da kawo budurcinta lafiya lafiya, after sun gama bajakolin fesa turaren sai wasu bayi guda biyu suka zauna kusa da ita gefe da gefe suna mammatsa mata ƙafafunta.

A can ɗaya ɓangaren kuwa Turaki na fita gida ya wuce, kai tsaye part ɗin Baffa ya nufa don zatonsa ko suna can suna breakfast, sai dai ko da ya je duk basa can Baffan ma bai tashi ba, dan haka ya taho side ɗin Maama.
Lokacin duk sun zauna za su yi break fast, kallo ɗaya Maama tayi masa ta san bai ci abinci ba, hakan yasa ta miƙe ta shiga kitchen ta dama masa kunun gyaɗa shap shap ta soya irish, duk da cewan akwai soyayyan irish ɗin amma tasan ba zai ci ba.

Sai after break fast ɗin ne Maama ta zaunar da Turaki a ɗaki ta yi masa nasiha sosai akan yadda zai zauna da matar da ba sonta yake ba, ta nusar da shi in har yay haƙuri ya kyautata mata to tabbas zai ga ribar hakan, tun da har ya yi biyayya Allah ba zai barsa haka ba. 

Ta ce,"Mai Babban suna ko ni zan iya zaɓa maka Ilham matsayin wacce zaka aura, saboda yarinya ce mai hankali da tarbiyya, ita kaɗai ta fita zakka a cikin yaran Mai Martaba, to nasan dan ka aureta ba faɗuwa ka yi ba ka sami uwar ƴaƴa ta gari. But ni ta yanda aka zo da lamarin auren ne ya ɓata min rai, shiyasa duk na ji na tsani auren wallahi, amma ya zamu yi tun da ubangiji ya shirya faruwan hakan tuni. Addu'ata Allah ya baku zaman lafiya ya kauda fitina tsakaninku, ya kuma baku ikon fahimtar junanku ta yadda ɗaya ba zai cuci ɗaya ba".

Sannan ta ƙara cewa,"Ka dai ji me na ce maka ko?". 

Ya ɗaga kansa kawai tabbacin yaji, don bai jin zai iya magana.
Suna zaune da ita suna ta hira kiran Boɗejo ya shigo wayarsa, yana kallo yay banza da kiran, da ya ƙara shigowa ya kashe wayar gaba ɗaya yana jan tsaki tare da kwanciya kan gadon Maama. 
Ita dai tana kallonsa amma ko kusa bata yi magana ba, saboda tasan irin ɗacin da yake ji a zuciyarsa, and beside ta lura kamar yana da wata damuwa a can ƙasan ransa, sai dai bai faɗa mata amma tasan duk runtsi zata sa ni.

Miƙewar Maama kenan zata shiga toilet ta ji an banko ƙofar ɗakin, kallon wajen da za ta yi taga Boɗejo a fusace ta shigo, tabi Turaki da ke gadon idonsa a rufe ta ƙarasa wajensa tana ta zazzaga masifa kamar zata bankawa ɗakin wuta. Hajiya Madina kam dama tana ganin ita ce ta shige toilet ta rufe ƙofa, haushin duk wanda ke da sanya hannu akan lamarin auren nan take. 

Bata fito a toilet ɗin ba sai da ta ji Boɗejon ta fita, ta fito a ranta tana jin haushin irin zagin da Boɗejo ta dinƙa mata ita da Turaki, cikin ranta tana jin ina ma ace akwai ƙasar da babu wanda ya sa ni sai ita, da ba abin da zai hanata ɗauke Turaki a gobe ta kaishi can yaje ya huta na kwana biyu ko zuciyarsa tayi sanyi.

A can gidan Turaki dai sabon biki ne ya tashi, yana zuwa ya tarar da danginsu da dangin Fulani Azima an cika gidan sai tashin busar algaita ta ko'ina, ta dole Boɗejo ta shirya shi har da cewa wallahi idan bai yi wasa ba sai ta yi masa wankan da kanta. 
Ya fito cikin dakakkiyar shadda fara da ta saje da alkyabbar Gimbiya Ilham, ya yi azababben kyau har yafi na ranar ɗaurin aurensa. Kamar dai wancan kwanakin haka yau fuskarsa duk babu walwala har aka yi taron aka gama, sai da Boɗejo ta tabbatar sun gama cika al'adarsu sannan hankalinta ya kwanta.

Jama'a sun ci sun sha an bar arziƙin abinci a inda yake, bayan kammalawa Inna Falmata ita ta yi jawabin godiya ga duk waɗanda suka zo da kuma tarin addu'oi wa ma'auratan, daga nan kuma sai aka shiga ɗaukar hotuna kamar hauka, kowa burinsa bai wuci ya yi vedio yana hasko gidan ba ta yadda duniya zata gani ta shaida ya je gidan arziƙi.

Ƙarfe biyar na yamma Turaki ya wuce police station kan sabon report da ya shigar tun a ranar da ya dawo, suka kuma tabbatar masa da cewar suna kan yin bincikensu, bai dawo gida ba sai ƙarfe shida, kuma ba gidansa ya wuce ba wurin Maama ya wuce, inda ya je ya tarar ta wuce wajen Kaka an zo an ce tana can ta suma.

*Kidnappers.*
Ga duk wanda ya san Fullo, to a yanzu zai iya rantsewa ba ita ba ce, saboda yanda ta fita a hayyacinta, abinka da mara ƙiba, kallo ɗaya zaka yi mata ka zubar mata da hawaye saboda yanda ta fige, idanuwan nan sun ƙara ɓurmawa ciki.

Zaune take akan ƙasan simitin wajen an ɗaure ƙafafunta da igiya, haka ma hannayenta an ɗaure su ta baya, yanda fuskarta tayi jawur da yanda jini ke fita daga bakinta kaɗai za su shaida maka irin azababben dukan da ta sha a iyakar yau.
Ƙaton mutumin dake gabanta ya ƙara buga mata bindigar hannunsa a fuskarta, take bakinta ya ƙara fashewa kanta ya lanƙwashe.

Cikin burkitacciyar hausarsa ya ce,"Muddin baka daina yi mana gardama ba, to wuya yanzu ka fara shanta. In baka yi wasa ba sai mun kaseka a yau ɗin nan".

Da ƙyar Fullo ta miƙar da wuyanta ta ɗago tana kallonsa, dan idanonta guda ɗaya ma bata iya gani sosai da shi, kawai saboda irin kuka da wahalar da take sha na yawan duka a wajensu, hakan ya nemi ya kashe mata idanuwa.
Kallonsa take yi tana hango ranar da suka tsareta suka ce ta bayar da lambar wanda za'a kira, lambar Amir kaɗai ta haddace a duniyarta kuma bata tunanin zata iya bayar da shi, saboda tsoronta kar ya cutu da jin halin da take ciki, bata san me za su yi masa ba.

Sai da tayi da gaske tukunna ta iya haɗa lambar Yami ta bayar, ba wani haddaceta ta yi sosai ba, kuma sai da aka gwada lambar kusan sau uku duk ba correct ba, sai ana huɗun Allah ya taimaketa kiran na shiga ta ji muryar Yami da aka ɗaga, da wannan ta samu ta kuɓuta daga wahalar da suka ɗau kwanaki suna bata.

Bayan wancan kai kuɗin farko da Amir ya yi, ya ƙara komawa ya kai musu wasu, komawarsa uku duk shiru, saboda har zuwa lokacin dai ba a samu an haɗa amount ɗin da suka nema ba.

Idan bata manta ba tana jin shi ƙaton na cewa,"Wato iyaye naka suna sonka sosai, tun da har ga shi suna ta wahalar nemo kuɗin su kawo. Wannan ya nuna mana sewan sun tara kuɗi da yawa, don haka ba zamu sake ka ba sai an cika mana kuɗin mu".

Tana jin abin da suka faɗa ta ƙara saddaƙarwa, yanzu inda ace babu Amir wa suke da shi da zai dinga wannan sintirin kawo kuɗin? 
Kuma a ranar ne suka kira waya aka sawa su Kaka muryarta tana cewa azo a ceceta, the first abin da Kaka ta faɗa mata shine,"Ki daina kuka, ki yi ta addu'a kin ji za ki kuɓuta, banda ƙarfin da zan kawo musu amma Amir zai zo ya tafi da ke kin ji".

Ta sani a irin son da Amir yake mata, zai iya sadaukar da ransa da lafiyarsa ma wurin ganin ya kuɓutar da ita daga wajensu, kuma a yanzu hakan ma ta san da dukkan ƙarfinsa da ƙoƙarinsa ake ta faɗi tashin ganin an samu waɗannan uban kuɗin da ba ta san nawa aka bayar ba har yanzu, ita dai kawai ta san kuɗi ba su cika ba, kuma a yanda take ji a ranta ko kuɗi sun cika bai zama lallai su saketa ba, kasheta kawai za su yi, ita dama ta mutu kafin lokacin kawai ta huta da wannan masifar da take ciki. Lallai a duniya in aka cire iyayenta da Kaka, bata da wani wanda ya wuce Amir.

Dukan cikinta da aka yi da ƙafa shi ya dawo da ita daga duniyar tunani. Ta saki kukan da bata jin zata iya riƙe shi, ta shiga ambaton Allah a fili da kuma zuciyarta. 
Ta buɗe bakinta wanda leɓenta suka kumbura, halittar fuskarta duk ta sauya, ta ce,"Ku kashe ni kawai, don Allah ku kashe ni. Na faɗa muku bamu da wani gata sai na Allah, don Allah don Annabi ku kashe ni kawai".

Ƙaton ya jawo jakar kuɗi na ukun da Amir ya kuma kawowa naira miliyan biyu, sun jima suna kidnapping su yanke kuɗaɗe masu uban kauri, kuma ba a yi musu wasa da hankali wajen kawowa, amma ba su san me yasa akan wannan yarinyar ba ake ta raina musu hankali, ana kawo kuɗi da kaɗan kaɗan, kuma sun kasa zartar da hukuncin kasheta har yanzu.

Cike da rashin imaninsa yasa ƙafa ya ta-ke ƙafarta ya ce,"Ka san menene yaro? Ko iyaka motan gidanku da muka ƙwamusoka daga wajen da muka ganka ranar idan siyar da shi za a yi ya haura sama da miliyan ɗari uku, saboda haka ku daina ce mana baku da shi. For the last time zamu kira waya ka faɗa a gida ka ce a ciko mana kuɗi, ana cikawa mu kuma mun yi alƙawarin zamu sake ka".

Cikin tsananin azaba da wahalar da take ji ta ce,"Ni Kakata kawai nake da ita a duniya, bayan ita banda kowa. Wannan motar ba tamu ba ce ta gidan da nake aiki ce, don Allah ku taimaka min, na tabbata Kakata duka gadonmu na wurin mahaifiyarmu ta siyar aka sami wannan kuɗin, a yanzu kuwa na san babu wani abu da zata ƙara ɗagawa ta siyar, ku yi min rai don Allah".

Shirunta yay dai dai da shigowar wani mutum dogo kamar sanda, ya ƙaraso gaban ƙaton mutumin yana miƙa masa waya yana cewa,"Oga ka duba news ka gani".

Ogan ya shiga kallon shafin facebook da yake nuna masa yana karanta bayanan dake jiki na ɓatan Fullo ƴar aiki a gidan Judge Alƙali Dikko, da kuma hotonta a ƙasa sanye da hijab. 
Sai ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yana sa ƙafa ya yi fatali da kujerar dake kusa da shi, ya mayarwa da mutumin wayar yana faɗin,"Ase kamu muka yi mai soka bamu sani ba".

Yay shiru yana ƙara sakin dariya ya ce,"Hardo ka je ka nema mana numban waya na gidan Alƙali, wannan yaro yana da taurin kan jaraba ba zai bamu wani number ba. Ka yi sauri ka kawo min in the next few minutes, muna neman miliyan ɗari bakwai ne a yanzu".

Ya faɗa yana miƙewa daga kan kujerar yana ƙara sakin dariya cike da nishaɗi.
Sannan ya ƙara kallon ɗaya a cikin yaran nasa ya ce,"Jibril, ka siyo kaza ka basi ya ci, domin ina sha'awan wannan yaro, ina so na huta da shi. A siyo masa kayan gina jiki a basi ya ci kafin na zo na biya buƙatana akansa, ina ta haɗiye yunwana akansa kwana da kwanaki, tun a ranar farko na ji ina sa'awan budurci nasa. Kafin na gama cinsa zuwa nan mun samu uban Alƙalai ya kawo mana kuɗaɗen mu, sai muna sakinsa yana tafiya".

Kalmar Virginity yay wani duka a ƙwaƙalwar Fullo da yasa ta ji ta girgiza gaba ɗayanta, her virgin?
Kamar dai bata fahimci maganar tasa ba da kyau, sai kuma ta ji wanda aka barta da shi na faɗin,"Kash Oga ban ji daɗi ba kana riga ni shiga daɗin wannan kyakykyawan yarinyar, nima ina ta kwaɗayinta tuntuni, amma da zarar ka sha naka rabon daɗin nima zan sha nawa kafin a sallameta". 

Ya ja igiyar ƙafarta ya ƙara ɗaurewa da kyau yana cewa,"Kai Budurci yana da daɗi, gaki da ganinki za ki daɗi ƴan mata".

Ƙwayar idon Fullo tun ɗazu ƙafe take a wuri ɗaya, tun bayan fitar wancan mutumin take so ta fahimci abin da ya faɗa kafin ya fita, kuma bata gane komai ba sai a yanzu, sai yanzu ta fahimci abin da yake nufi daga shi har wannan, suna maganar za su amshi budurcinta ne kafin ta fita daga hannunsu. 
Da sauri ta shiga jujjuya kanta da ke barazanar tarwatsewa, hawaye masu zafin gaske na daɗa biyo kuncinta, ta jinginar da kanta jikin bango tana jin ƙirjinta yay mata wani irin nauyi tamkar an ɗora dala da goron dutse akai, a hankali ta shiga ambaton sunan Allah tana fashewa da wani kuka mai ƙarfin sauti cikin fitar hayyaci. 

Ta jima tana kukan tana kiran sunan Allah, bata ma san time ɗin da mutumin da aka barta da shi ba ya fita ba. zuwa yanzu ta san ruwan hawayenta sun ƙare, ƙazaman maganganun da mutanen ke ta yi na mata yawo a cikin kanta. 
Ta sani shikenan tata kuma ta ƙare, dan haka ta sallama da rayuwar gaba ɗaya, waɗannan mutanen su yi mata fyaɗe ai ba zata ƙara shurawa ba.

Kanta ta buga a jikin bango tana addu'ar,"Allah ka ɗauki raina kafin waɗannan azzaluman su cimma ƙazamin burinsu akaina, Allah ka ɗau raina a yanzu".

Tsananin tausayin kanta ya lulluɓeta, babu ta yanda take tsammanin zata iya guduwa daga wajen nan, ta yi attempting sau ɗaya suka kamata, shine tun daga ranar suka ɗaureta basu ƙara ƙunceta ba har zuwa yau, jini har ya gaji da daskarewa waje ɗaya a jikinta.
Idanuwanta a rufe ta ji kamar mutum na taɓata, a mutuƙar firgice ta buɗe ido tana sakin ihu cikin ƙaraji da bala'in tsoro, da sauri farin mutumin da ke gabanta yasa hannunsa ya toshe bakinta.

Ta ƙwalolo ido waje tana kallonsa, ta san shi sosai kullum shine yake kawo mata abinci. 
A hankali ta ji ya ce,"Ki shiru zan taimaka miki ne ki fita daga wajen nan, ki yarda da ni wallahi ba zan cuceki ba saboda haka karki yi ihu"

Ya sauke hannunsa a bakinta, cike da tsoro don bata tunanin za ta yarda da shi. Ya miƙa mata plate na abinci gabanta ya ce,"Ki fara cin abincin tukunna".

Ta ce,"Don Allah kar ka yi min komai".

Ya ce,"Wallahi tallahi banda niyyar cutar face taimakonki, amma ki ci abincin ko kaɗan ne kin ji. Kwanaki da yawa ba ki sa komai a cikinki".

Tana ta kallonsa ta ce,"Ba zan iya ci ba. don Allah ka taimaka min".

Ya ce,"Zan taimaka miki amma in har ba ki yi wani yunƙuri na tona min asiri ba".

Da sauri ta jijjaga kanta tana cewa,"Zan bi duk ubarninka in har ba wanda zaka cuce ni ba".

Yasa hannu ya kun ce ɗaurin igiyar ƙafarta, sannan ya kun ce ɗaurin na hannu, amma sai dai bai warware ba. 

Ya ce,"Kowa ya fita daga gidan nan, ni kaɗai ne amma zuwa nan da minti goma zuwa sha biyar Babban Oga zai iya zuwa saboda haka ba zan ce miki ki fita nan da wuri ba. Kawai dai ki yi hankalin da ba za su gane cewar wannan igiyar a kwance take ba, idan kika ta shi akwai ƙofa ta nan baya kusa da parlo da aka cire ki jiya, ki bi ta nan ki fita. Kina fita za ki hango wata ƙofa a wurin sai ki yi saurin buɗewa ki fita, za ki ganki cikin daji, kar ki tsaya a kusa-kusa sai kin tabbatar kin yi nisa sosai da babu mai iya riskar ki".

Yasa hannu a aljihu ya ɗauko ƙaramar waya ya ce,"Ga wannan kina iya kira gida ki faɗi inda kike ko da za ki kasa gane hanya".

Tabi ƙaramar wayar hannun nasa da kallo kafin ta ɗago ido ta kallesa tana nazarinsa.
Yay mata murmushi ya ce,"Ni dai har ga Allah iyakar abin zan miki kenan, ya rage naki kuma ki kuɓutar da kanki ko kuma ki zauna su cuceki. Dan wallahi ina mai tabbatar miki sai sun mayar da ke yarinyarsu after sun gama talauta danginki, ƙarƙari ki kasa juriyar ɗaukarsu ki mutu su jefar da ke, dan Babban Oga bai da imani wallahi. Wannan Ogan da kike gani ba shi ne babba, akwai na samansa".

Yana gama faɗar hakan ya miƙe ya fita ya barta, tabi bayansa da kallo kafin ta dawo da idonta kan wayar da ya bar mata. Jin kamar motsi ta yi saurin ɗaukar wayar ta tura a cikin rigarta, Allah ya taimaketa kuwa tana sawa ana turo ƙofa a shigo.

Jere ta gansu duk kusan kansu ɗaya, zata iya cewa bata taɓa ganinsu ba duk da cewar fuskokinsu a rufe yake da mask irin wanda take gani a film, suka wuceta suka shiga ciki, in ta lura da kyau kamar har da mace, na ƙarshen ya duƙa gabanta ya mammari fuskarta yana wani makirin murmushi ya ce,"Zamu huta sosai da kai". 

Da faɗin hakan ya miƙe yabi bayan sauran. 
Ta ji sabon hawaye ya taho mata, ta rumtse ido sosai tana rasa ma me take ji a ranta. 

Dai-dai nan ta ji mutumin ɗazu ya dawo can ƙasa da muryarsa yana cewa,"You got the chance, za su yi zaman meeting yanzu and atleast they will take up to 30minutes kamin su gama, babu wanda zai ji motsinki har ki fice, kar ki yi wasa da wannan chance ina daɗa jadadda maki, if not wallahi a yau ko ba'a ɗau gawarki ba sai kin mugun raina kanki, kaf wannan mutane da kike gani sai sun yi amfani da ke".

Yay saurin ficewa gudun kar wani ya fito ya gansa tare da ita.

*A dai-dai wannan lokacin.*
Wayar Hajiya Madina da ke riƙe a hannun Nihal ta yi ringing, ta yi saurin miƙa mata, Hajiya Madina na tambayarta,"Waye?". 

Ta ce,"Ba suna a jiki".

Hajiya Madina da jikinta yake a sanyaye ta karɓi wayar, dai-dai kuma da katsewar kiran, ta sauke numfashi jikinta duk a mace saboda halin da Kaka ke ciki, tun ɗazu suka zo asibiti amma har yanzu bata dawo hayyacinta ba, a sannan likita ya shigo ɗakin yana cewa,"Hajiya meet me in my office".

Da hanzari Hajiya Madina tabi bayansa, nan kiran lambar ɗazu ya ƙara shigowa, ta ɗaga tana yin sallama tana ci gaba da bin bayan likitan. Daga can ɓangaren ta ji wata gwandareriyar murya na faɗin,"Hajiya mune kidnapper na ƴarku".

Tsabagen rikicewa sai wayar ta suɓuce daga hannunta tana tsayawa daga bakin ƙofar tana haki, kamar wadda tayi tsare, saura ƙiris wayar ta kai ƙasa Allah ya shigo da Turaki yay saurin riƙo wayar yana dubanta.

"Lafiya Maama?". 

Da shi da kowa na ɗakin suka tambayeta a tare suna yowa kanta. Tsabar gigita tama kasa cewa komai sai nunawa Turaki wayar take da hannu. Ya kalla screen ɗin wayar yana kallon yadda call ke tafiya, ya kara wayar a kunnensa yana cewa,"Salamu Alaikum".

Cikin ɗaga murya aka ce masa,"Kar ku ƙara yi mana sallama ba ita muke buƙata ba".

Mamaki ya bayyana akan fuskar Turaki ya ce,"Wa ke magana?".

Aka ce,"Wanda suka yi garkuwa da yaro naku ne, kuna san yaron naku a raye ko kuma mu kase si mu aiko muku da namansa?".

Turaki bai san lokacin da yay wa hannu Maama wata muguwar damƙa ba da yasa ta yin ƴar ƙara tana faɗin,"Mai Babban suna zaka karya min hannu".

Bai ma san tana yi ba becouse he is totally getting out of control, ƙwaƙwalwarsa ta shiga faɗa masa anger ɗin ka ba zai yi amfani yanzu ba, just relax and control your self.
Ya buɗe idonsa da ya rufe in just 2seconds, ya ja leɓensa ciki ya cije da ƙarfi sannan a hankali ya sauke dogon numfashi, ƙwayar idonsa da ta sauya kala ta dawo yanda take. 

Ya ɗauko wayarsa a aljihu ya ɗauki lambar ta su, sannan ya bi bayan kiran na su da suka katse. Bugun farko suka ɗaga, cikin kwantar da murya Turaki ya ce,"Muna jinku, me ku ke da buƙata?".

Mutumin yay dariya sosai ya ce,"Kun tabbata za ku bayar da komai muka ce? Idan kun san baku shirya karɓan ƴarku ba karku sa mu ɓata bakinmu wajen yi muku bayani".

Turaki ya ƙara rumtse ido ya ce,"Duk abin da kuke so na tabbatar da zaku sa me shi".

Mutumin ya kuma dariya ya ce,"Good. Ga yaronku nan yana ta kuka kullum yana so ya zo ya ganku, amma mun ce ba zamu sake si ba sai an bayar da miliyan ɗari bakwai tukunna mu barsa ya dawo gida da ƙafafunsa".

Zuciyar Turaki na bugawa fat-fat ya ce,"You got additional of 700million thousand, zan baku biliyan ɗaya da miliyan ɗari huɗu, amma muddin baku taɓa lafiyarta ba wannan alƙawarina ne, ta ya zaku karɓi kuɗin? Through bank za a tura ma ku? In doller or in Naira?".

Mutumin yay dariya sosai ya ce,"Zaka kawo mana kuɗi da hannunka. Ko doller ko Naira, Idan mu ka ji hukuma a wannan maganar za su kase si". 

Nan ya shiga korawa Turaki bayanin inda zai je ya kai kuɗin ya ajiye. Turaki ya tabbatar masa da cewar zai zo nan ba da jimawa ba, komin dare zai riski inda su ke, amma su tabbatar ba su yiwa Fullo komai ba.

Mutumin na bushewa da wani dariyar rashin imani ya ce,"Ga yaronku ku yi magana dan ka tabbatar yana lafiya, idan kun ji jisi yana kuka ba komai bane aka yi masa, soro ne kawai da yake ciki".

Daga can inda mutumin ke zaune kan kujera ya ɗorawa Fullo wayar a kunnenta a tsawa ce yace,"Yi magana da father na ka".

Cikin matsanancin kuka ta ce,"Kaka". Muryar ta fita da wani irin sauti da zaka rantse da Allah ba tata ba ce.

Turaki ya ƙara matse hannun Maama da har yanzu ke hannunsa, Maama babu shiri ta ƙwace hannun nata a nasa, domin tsab zai iya tsinke jijiyar wurin ko yay mata raunin targaɗe. 

Muryarsa a hankali, da sautin da ba kowa zai ji shi ba ya ce,"Fulaniii". 

Sai kuma ya fesar da iskar bakinsa me zafi ya ce,"Kina jina?". Yay maganar jikinsa na ɗaukar kyarma, kamar iskar guguwa da girgiza shi.

A wahalce ta ce,"Turakii, don Allah ka zo ka cece ni, kashe ni za su yi sun ce, wai za su yi amfani da ni, ka faɗa musu Kaka bata da kuɗin da suke nema". 

Ta faɗa cikin wani irin kuka mai karya zuciya, kukan da duk wanda ya ji shi sai tausayinta ya kama shi. kukan da yasa allon ƙirjin Turaki mugun girgiza.

Tana girgiza kanta cikin razani na irin yadda suke tsaye akanta. a hankali da sautin da ba lallai su iya ji ba, ta ƙara ce masa,"Sun ce... Sun ce..."

Numfashinta na yankewa saboda tsananin tashin hankali ta ƙarasa da cewa,"Turaki they said they would rape me..."

Ba zuciyar Turaki kaɗai ba, hatta gadon da yake zaune akai sai da ya girgiza, kuma ba kunnensa kaɗai da ya ji yadda zuciyarsa ta yi wani mugun bugu ba, kowa da yake wajen tsaye ya zuba masa ido, sai da suka ji bugun zuciyarsa da yake harbawa ba a daidai ba.

Kamar ma dai idanuwansa a rufe suke, lokacin da ya miƙe yana tafiya zai fita a ɗakin, tabbas a matsayin makaho ya fita a ɗakin, don ba ya ganin hanya.
Ya kai bakin ƙofa yana jin kamar yawun bakinsa ya ƙafe, neman abin da zai riƙe ya damƙe yake, sai dafa ƙofa kawai ya yi, ya tattaro jarumtarsa da yake jin tana neman barinsa ya ce,"Ki yi shiru ki daina kukan kin ji, zan zo in ɗauke ki yanzun nan. Babu abin da suka isa su yi miki in har bakinki bai gushe da ambaton Allah ba, kin manta kin ce na riƙe zikiri da alƙur'ani, to kema ki riƙe shi har zuwa na ƙaraso. But na faɗa miki ki daina kukan kin ji Fulani". 

Wannan jarumtar tasa ta maza yaji ta ƙwace, bai san sanda ya duƙe a wurin da yake tsaye ba, idonsa na cika da tarin hawaye, ya buɗe baki yana jin kamar ba zai sake iya magana ba, a cikin zubar hawayen da babu wanda zai iya lura da shi a fuskarsa ya ce,"Don Allah kar ki bari su yi miki komai kin ji Fulani, na san wace ke, kina da ƙarfin iya kula da kanki, don girman Allah kar ki bari su yi miki komai, kar ki yarda su yi raping ɗin ki, na roƙe ki don Allah Fulaniiii....".