TALES OF THE WAZEERIS

Home cominng prince

by @surayyahms

27...🦋🦋🦋

SURAYYAHMS

Tales of the wazeeris

tace "...ni sam baki min adalci ba amani..

gimbiya amani noorain ta dago idanunta da sukayi jajur tsabar kuka ta kalle mahaifiyarta dasu cikin rauni sai bai tace mata uffan ba ta kyabe baki

da takaici ummu zaliha tace yanxu ma wannan shaidaniyar yarinyar zaki zauna kina bata hawayenki saboda ta shigo gidan nan ta daga miki murya ta gaya miki ta tsaneki ko dan sbda ture ni na fadi kasa datayi..

cikin runtse ido da budewa gimbiya amani ta girgiza kai ahankli snn tace mama laifin ushna kawai fa kike gani amma bakiganin irin abunda ya jawo har tayi wannan fushi....

cikin datsar nmfashnta tace..a’a bana son wannan sakarcin naki amani, meye ya jawo tay fushi inba akan maganan banza da bai taka kara ya karya ba..shekaru nawa arisha ta deba tana karatu a egypt kin taɓa ji dan zata dawo gida saita ishe mutane da kananan magana ko itace tadaban yar gwal...wato tanason dan kawai zata dawo sai kowa yadena numfashi ataru ayi gagarumin biki ga sarauniyar duk duniya zata dawo gida ko...

cikin yanayin hade fuska tace amma mama kinsani sarai ushna ba haka take nufi ba...

da tsawa tace haka ne mana danni banga wani abu tashin hankali aciki ba, tun tuni nake gaya miki wannan yawan tausayi da kika cusa aranki akan ushna shine yake dada lalata, yarinya duk tabi ta zama munafuka me fuska biyu, soyayyar banza da marigayi sarki saleem da hareera suka nuna mata walh shine ya saka takejin zata iya yima kowa rashin kunya..ke baki lura da yanayinta bane?she want to manipulate everyone dan anayin iya abunda takeso.

hawaye suka kara sauka a fuskar gimbiya amani cikin muryar kuka tace mama ba haka halin ushna yake ba.

ummu zaliha tayi dariyar takaici tace babu shakka shiyasa ma naga ta dawo gidan nan tana miki ihu kmar mahaukaciya ai

gimbiya amani tadan yi shiru sai can snn ta dago kai ahnli snn tace mama, dazu lokacin da ushna ta tsaya tana kuka agabana nikadai nasan irin xafin hakan danakeji araina, dan ya tuna min ne da yadda tafi tabar gidan nan tana kuka banso ace ta dawo tana kuka ba..

gudun irin hakan yasaka na tsaya kadan nace sai na sanar da mahaifinta zuwanta dan nikaina bansan ko intazo cikin gidan nan gatsau ko ace nine kawai nabata izini akn tadawo mahaifinta zai amsheta da tarba ko kalamai maikyau ba..

kisanshi, komi ushna tay a idonsa laifi ne..

...naso na sanar dashi zuwan tan amma kma hakan baiyu ba...nide kuskure danayi shine daban kula na sake tambayarta yadda tafiyar tan ya kaya ba amma kuma gaskiya banason wani abu irin haka yasaka har ushna taji aranta cewa ta tsaneni.

atake Arisha data tsaya bayan kofar dakin tana sauraransu tadan jaaa tsakiii tay rolling eyes inta with disgust...

ummu zaliha ta kalleta cikin takaici tace to in ta tsaneki sai me?aikin banza ai itace zatayi asara tunda kece uwarta ba itace uwarki ba, ke kullum ina gaya miki wannan raunin naki ne yake kara lalata rayuwar ushna amma kinki ji na, ki duba yau har budan baki tay tana gaya miki ta tsaneki amma wai kece kika zauna nan kina zubda hawaye saboda ita toh wallahi amani idan baki gyara wannan yarinyar ba sai ta hau muku kai gaba daya agidan nan. shi munafukin yaro haka yake, zata kai kaine ta baroki, yar banza kawai shashasha wallh badon agaban yarki muke dazu ba da sai na sharara maki mari kema, wa yar iskan yarinyr data miki tsawa tace ta tsaneki zaki zauna kina wani rungumar hotonta kina kuka?

gimbiya Amani noorain zatay magana da tsawa tace nide kimun shiru

..kuma wallh naji ance kinje kin lallami yrinyar nan baki barta ta shiga hayyacinta ta gane kuskurenta tazo ta tsuguna agabanki ta baki hakuri saina gaya maki maganan da har ki mutu bazaki manta ba.. inke bazaki iya tarbiyantar da ushna agidan nan ba ni nan zaliha nayi alkawari zan dauki mummunan mataki akanku gabaki daynku. idan naji ance kinje kin lallabata Allah ya isa tsakani na dake inkuma kinaso ki nuna min cewa ban isa dake ba toh shikenan.

gimbiya amani tayi kasa da kanta ahankli batace komi ba..

daga bakin kofar kuwa

wani irin relief Arisha taji aranta me sanyi saboda a karona farko tun dawowar ushna gidan nan komai ya fara turning badly against her exactly the way she wanted.

cikin sauri tabar wajen dan kar ummu zalihan ta fito ta sameta anan, tana kuwa komawa sashenta sai ga nan wanda ta aikesu suje su wajen taro sujiyo mata meke faruwa snn su dauko mata hotonan yarima a kawo mata taganshi dan bata taɓa ganin siffarsa ba

servant din suna mika mata saqon suka hau sanar da ita ai yarima bazai iso nan yankin zamkora ba dan har yagama abunda zaiy ya tafi...

snn rashin tura wani babba ko represntative daga nan zamkora yasaka dawuya ne duk wani abunda aka zantar na ihsani da kawo cigaba ya iso garin zamkora...

bayan tagama jin bayanin batace uffan tasa hannu takarbi hadadden cameranta data basu mai dauke da hotonansan da akaje aka dauko mata snn takoma cikin dakinta ta kulle kofa da zumudi dan ta kalleshi,

for the first time in her life kenan yau zataga kalar kamannin shamsan na asali duk dama ansha gaya mata cewa gayen ya hadu makurar haduwa

******

Daga nan cikin babban masarauta na kano kuwa bakaramin shirye shirye akeyi na tarban dan sarki shamsan wazeeri ba, wanda already har an shirya kosashun dawakai an musu kwalliya ankuma tsaftace wajaje anyi ado na sarauta ma hanyoyin wucewa da benaye.

Yau tun sassafe aka tashi da shirye shirye da zirga zirga acikin fadar wanda already an sakeyi masa canjin tsari daga tsohon ginin sarauta zuwa sabbin gini na zamani aka kuma tsara cikinsasa da wajensa da kayan alatu na gani na fada yau kowani lungu da sako na zagaye ne da royal guards karfafa dasu wanda zaka iya rantsewa ko murmushi basu tabayi aryuwarsu ba kowannensu yasha sabbin kayan sarauta da rawani kalar ja da green da zuka zukan dorinai a hannayen su wanda akewa lakabi da maganin yan wargi.

dagata bangaren shamsan kuwa Akan Wata shimfidadiyar titi suke tafiya ana janshi a nitse,not too slow,not too fast,tafiya kawai suke a dede kusa da normal speed inda babu wani mahalukin dake isowa da abun hawanshi kusa dasu.

After thinking about ushna's pretty face for while ahankli ya dan sauke ajiyan zuciya yanamai dada nitser da kanshi cikin soft cushion din motar cikin langwabar da wuya a hankli snn ya lumshe kyawawan cloudy grey eyes dinsa yana jin kanshi daban cos is been so many years rabonshi da dawowa gida nigeria.

adan dolensa ya aje tunanin yarinyar nan agefe yakuma tara hankalinsa waje guda

bayan wasu lokuta suka iso gaban wata katotuwar royal black gate wanda bazan iya misalta tsawon shi ba..

ana bude musu gate din yanayin ginin cikin masarautar ya bayyna ga yawan mutanen dake haraban gidan da alaman masu murnan tarbanshi ne

tun daga tsarin kofar wannan katoton gate din komi ya sauya domin kuwa tsaban yalwataccen security ne aka watsa suna kare gidan ta kowani bangare.

manyan mansion ne guda uku na farkon dayafi kowane girma shine fadar sarki abdallah Wazeeri wanda ba asauya mai gininshi na sauratar hausa ba saidan gyare gyare na zamani da akayi,.

sauran biyun kuma thy are totally new morden mansion masu girma sosai kuma kowane mansion yana da personal inner gate dinsa wanda suka kere tsayin kowani katanga.

Gate din farko da aka bude musu wata katuwan mega parking space ne zagaye da manya driveways harda round about,a Kusa da shi kuma wajen aje dokuna ne acike fall yake da kosasshun kuma lapiyayyun dawakai.

koriyar ciyawane maiji da rai da lpya akasar wajen masu lura da dawakan ne kawai ke shawagi anan wajen.

Bisa tsari Motocin sukayi parking masu tsaro tuni suka rufe wajen anata kidi ana busan sarauta ana zuba tsantsar fadanci irinta babban gidan sarauta seda kowa ya gaji ya fito ya tsaya a tsaye still kafin nan bayan kusan minti 10 saiga shamsan shima ya sauko duk mutanen da suke wajen suka fara gaisheshi yana dan daga musu hannu akasaitance.

private body qurds dinsa ne kawai tafe a gefensa ayayin da shikuma yake tahowa a tsakiyarsu yanamai jefa kafafunsa cikin nitsuwa, haddaden takunsa mei jan rai da masifar daukar hankli, Direct wata hall way suka wuce wanda yamiko su har cikin wata tsaleliyar royal palour wanda ya wuce ace dashi palor saidai royal hall kawai sabida tsabar girmanshi

Acikin mansion guda ukun nan na tsakiyar itace private bangaren shamsan

Koda ya taho tanan Kuyangi da bayin gidan sai zubewa suke suna sunkuyar dakai can kasa suna gaishe sa duk dama ko kallonsu bai iyayiba bare harma ya iya amsa musu da tsadadden muryanshi dan sosai yaji yagaji

kuma bakomi ne ya gajiyar dashi ba face yawan mutane da hayaniya...

Yana nufar kofar sashen sa masu tsaron kofar sukay marmaza suka bude mashi yana shiga ciki private qurds dinsa ne kadai sukayi saurin mara masa baya.

Suna shigowa Fully wani queit hallway suka ratsa mai farin haske dan asaman kowani hallway din Dake gidan akwai crystal chandelliers Masu fidda azabar sheki.

daidai kofar dakinsa wani gurd yay sauri ya bude mai kofarsa ya shige ciki kai tsaye snn Su kuma sukaja suka tsaya daga waje. ..

wani irin relief yaji for some minutes dayaji wajen ya dau shiru babu wani hayaniya wayarsa ya soma ajiyewa akan table yanamai sauke ajiyar zuciya ahnkli..

Duk dama ya saba sosai da yadda ake yawan karramashi tun yana karami amma har yau bai gama karban abun acikin ranshi ba cos deep within him he doesnt want this too much attention da ake bashi asalinsa yafison quiet life.

A nitse Ya kare ma ko ina kallo ganin dakin nasa yafi karfin ma ace dashi daki don yana da girma sosai yana da faloka da kitchen da komi da komi aciki

A tsakiyar dakin aka kafa masa sharbaben king size bed dataji kwalliyan zanin gado me tsada

zaune yay akan lafiyayyen kujerun dake wajen idanuwansa a lumshe yanajin kmr yau baici komiba dan bayan cimen da yay a jirgi da safe haryanzu baisaka komai a cikinshi ba dan Ahalin yanzu ma bai jin sha'awar cin wani abinci inba abincin maman shi ba.

Jiyay zuciyarshi tana harbawa da wata boyayyar feeling na zakuwa da soyayya dan kamar bazai yi ido hudu da iyayenshi ba haka yakeji ba.

ata wani bangaren zuciyarsa kuma ji yake kamar yafara kosawa da yasan wacece ushna inane gidansu meye sunanta snn waye iyayenta saidai harga Allah yasan halinsa na miskilanci ma bazai iya barin shi ya kira gurd dinsa ya tambayesa inda ya kaita dazu ba.

cikin wann tunanin ya jawo wayarsa ya bude da kamar zai tura ma abokinsa itban text mesg akan haka sai kuma ya fasa, cikin lumshe ido aransa yace inde anan garin take bazai rasa samun cikaken information akanta akan lokaci ba

Saida ya dau lokaci ya huta sosai batare da andameshi ba can Kafin nan ya dan tashi ya fita ya bada baya domin ashigo adan hadamai ruwan wanka yanaso ya shirya knsa zuwa cikin fada domin ganawa da iyayenshi duba da lokcin sallahn magrib takusa.

As usual yana dan bada bayar kuwa cikin dan kankanin lokci wani servant ya shigo cikin dakin, direct cikin bayinshi ya nufa wnda girmansa kmr babban daki ne

full sized jaccuzi shine a tsakiya da kuma site din golden glass wall shower dake wani kyalli kamar ba ataba taba shi ba Komi dake bayin white colour ne

Nan danan servant din yay setting masa ruwan wankanshi in warm nd relaxing tempureture snn yabi ya sassaka essential herbs nd oil wanda zasu saukar mai da gajiya da duk wani kasalar daya debo.

Koda ya shigo kuwa sosai ya dade yana nutse acikin ruwan wankan yanajin balain dadinshi ajikinshi

Bayan ya kammala ya fito Bai dauke wani lokci ba yay yen shafe shafensa ya dada gyara lallausar suman kanshi da sajen sa da gabaki daya suka dau sheki snn ya shafa kamshin bargamot musk a dukka fatar jikinshi kafin nan yabi da tsadadden turare mai tsantsar kama jiki da wani irin sanyin kamshi mai dadi mai kuma ratsa zuciya da kwakwalwa.

asalin kayan sarauta marasa nauyi yasaka ajikinshi farare amma ba irin kall din nan ba provocking his deep sense of royalty nd calmness ya kafa hula data dace dakansa sosai.

Bayan nan ya dora doguwar classy Alkyabba na zamani baki kirin akan suturar tashi wanda ya ksance mai fadi sann kalar alkabban tasa iri daya ne da half cover shoes din dayasaka a kafafunsa

shamsan yay kyau bana kadan ba dan shigar bakaramin kyau yayi masa ba.

Cikakkiyar nitsuwa da dedetuwar hankli duk na tare dashi ayayin da ya sa harman fitowa ahankli ya bude kofar dakinshi, har Lokcin qurds dinsa ne kawai a tsaye,wani azabbaben sanyin qamshin turare mai rikitarwa dake bibiyarshi a duk inda ya ratsa ya fara sanar da kowa fitowarshi.

Ratsa dogon hallway din yay Cikin sanyin taku mai tafe da sassanyar jinin shi ta mulki,kasaita da kuma iko,batare daya kalle kowa ba ya nufo kofar da zatakai shi ainihin falonsa ta kasa daga nan kuma direct suka nufi cikin bangaren mahaifinshi mai martaba wanda ke gefe na dama da nashi bangaren.

palace servant da maids sune a kowani kusurwa ta sashen kowa da irin hidimar dayakeyi, a hnkli cikin barin jiki kowannensu yafara aje abunda ya keyi din yana raɓewa gefe tareda sunkuyar dakai ƙasa sbd qamshin turarensa daya sauyawa iskan wajen da wani irin dadaddan qamshi ta hanyar sanarda kowa isowarsa tun daga nesa.

Lokaci guda kattan maza yan rakiyar fada suka mara musu baya Suna qarasowa hanyar Dazai shigarda shi cikn ɓangaren mai martaba

qurds din suka ja baya ahankali suka tsaya suna kallonsa har ya shiga ƙofarda aka jima da wangale masa shi aka rufo kofar kirif

Parlour ne mai wani irin girma da tsari dayaji adon royal chairs purple and golden komi anan sai kyalli yake an kawata palon da kalar royal purple and gold raɓa daga A Cs yakama ilahirin palon takoina sbd wata irin dukiyace ta musamman aka narkar wajen tsarashi.

Babu kowa a wnnan falon sbd shine falona farko dazai sadaka da fadar sarauta harzuwa turakar sarki.

Ratsa dogon falon yay harya nufi kofarda zai kaisa ainihin babban falon mahaifinsa na musamman yana zuwa wanda ke tsaron kofar yawangale masa qofar a hankali kansa a dan rusune cikin ladabi snn yakoma gefe ya tsaya yana jiran fitowarsa

wani kalar falon sarauta ne na alfarma babu motsin komai aciki saina karar ac dake tashi a hankali

Zaune sarki abdullah waxeeri yake cikin shiga ta Alfarma da kasaita kyakkwan Dattijone sosai da Hutu da tsantsar mulki na jinin sarauta ya gaji da ratsasa rawanin kanshi shi deep emirald green colour wacce ta zauna daram akansa, sai babban rigarsa ta sarauta datasha aikin zaren hannu da wata iriyar doguwar olive colour alkyabba mai adon kananan stones ajiki.

Kallo daya yayi ma dan nasa da idanuwansa masu tsananin kwarjini kafin nan ya iya tattaro nutsuwarsa da qarfin hali cikin salo ta mulki da kamiya yanade farin cikin dayakeji aransa acikin takaitacciyar murmushi mai balain sanyi da ratsa zuciya.

Qarasowa shamsan yayi cikin nitsuwa ya kallesa cikin lunshe idanuwansa dasuka fara canxa kala da sanyi muryan snn ya durkusa gabansa yay masa sallama bayan nan cikin girmawa kansa na kasa yace Allah yataimakeka mai martaba.

Fuskar sarki Abdallah wazeeri shimfide yake da wata kalar kykkwan murmushi ya dan taso daga zaune cikin tsare sautin numfashinsa da taushin murya yace

Ran sultan ya dade in fatan ka Dawo lpya?..

Kansa ya kara sunkuyarwa kasa cikin ladabi kafin atakaice Yace lapya kalau Ya dada sassauta muryan sa kasa yafara gaishe sa cikin nitsuwa...

bayan sun gama gaisawa kusan saurin gyara murya acikin nutsuwa mai martaba yay kafin nan ya iya dauke kyakwayaan idanuwansa daga kallonsa....

murya a tausashe yanamai wanzarda takaitaccen murmushi yace "nagode da irin biyayyan dake min sultan, Albarka ta tana nan tana tare dakai kamar iskan da kake shaka a kullum.

Ahankli shamsan din ya amsa da godiya snn ya miƙe tsaye ayayin da haddn alkyabbensa dayake dogo har kasa yabi kan cikakken dirin halittarsa mai nuna tsantsar kasaita da kwarjini dayake yawo ayanayinsa.

kafin ya nemi waje ya zauna dede lokacin ne kuma mahaifyarsa ta karaso cikin wani irin kasaitaccen shiga mai masifar dauke hankali dan sosai ta iya zuba royal dressing mai aji da kwalliya mai daukar hankali duk dama shekaru ya jaa ynxu amma tsabar kyanta ko kadan bai sauya ba.

suna hade ido hawayen datake dannewa ya zuba ahankli wani irin Kallon kamanninshi tay daga tsayen saitaga kamar ma a fili wani sabuwar kyau da kwarjini ya karayi mata naban mamaki.

da mamaki taga shamsan yay mata faffadar murmushi akaro na farko kafin nan ya tsuguna yafara gaisheta ahnkli

Cikin sauke boyayyar ajiyar zuciya ta taho da sauri tadan shafa kansa tana cewa you are welcome back home my son nayi matukar farinciki da dawowarka gareni Allah yay maka albarka har karshen rayuwarka

mahaifinsa dake murmushi yace ameen

dagowa kai shamsan yay cikin kamiya snn ya matso kusa daf da ita baice komi ba..

kallo daya ta masa idanuwanta masu tsananin kwarjini suka cikeda wutar kewa da soyayyarshi a hankli ta karaso tafada ajikinshi ta rungumeshi sosai tanaji har yana saukar da ajiyan xuciya kamr dan karamin yaron da yayi shekaru aru aru baiga mahaifyarsa ba.

hawayenta na zuba

Cikin sauri ta kawar ta tattaro nutsuwarta da karfin hali ayayinda yazare jikinshi ahankli daga jikinta dan baison kwata kwata yana bayyana musu rauni

Hannunsu sakale da juna ta juyo Batare da ta kalleshi ba cikin taushin murya mai tafe da murmushi tace

..ynzu Lokaci ne na ibada inkunje kadawo min da babanka da wuri sabida kuci abincin dana shirya muku na musmman

Kai kawai ya gyada mata Nan da nan mai martaba yay gaba snn ya rufa masa baya suka nufi hanyar masallaci.

daga bangaren ushna kuwa har lokacin tana nan zaune a kasa jikin kofarta rungume da gwiwoyinta gaba daya idonta ya haura ya kumbura saboda kuka.

zuciyarta na mata wani irin nauyi da hatta numfashi ma sai da kyar take janshi

sai can ta dago kanta ahankli tana kallon cikin dakin nata data taso aciki kusan komai na wajen is intact tun daga gadonta,mirror dinta da dukan fararen curtains din dakin ba asauya mata komi ba everything looked familiar yet nothing felt like home anymore

sai can hankali ya koma kan wayarta dake gefenta slowly ta jawo ta bude kan screen din bayan ta karanta text din ziyada tay mata reply sai kuma idonta ya tsaya tana kallon tarin missed calls din da tayi wa mamanta da addarta arisha almost thirty calls ga uban texts masu yawa

wani irin murmushin takaici ne ya kubce mata kafin nan ta share hawayenta da bayan hannunta ahnkl

cikin muryar kuka tace

Dole ne kawai nabar gidan nan da wuri...i have to start looking for a placement tmrw..kuma in sha Allah ba agarin nan zan zauna ba..just cant stand all this..

SURAYYAHMS

2026

COMENT. ..

SHARE...

TALES OF THE WAZEERIS

***