SARTSE COMPLETE

25

by @legendspen

“Sardauna ba zai dawo ba ne?” 

Na tambayi kaina ganin har ƙarfe sha ɗaya da kwata, tabbas nasan a yanzu sun sasanta kansu, ƙila ma sun tsayar da ranar aurensu, yanzu burin Hajiyar zai cika. 

Sai sha ɗaya da arba’in Sardauna ya shigo ɗakin da nake, daga yanayin yadda yake magana zaka san fuskarsa fal take da fara’a kamar wanda aka yi wa bishara da gidan al’janna. 

“Nana! Kina ina?” 

Ya faɗa yana kunna hasken ɗakin, da sauri na runtse idona da. 

“Oh My, wai kinyi bacci?” 

Daidai lokacin wayarsa ta fara ƙara alamun kira na shigowa.

“Salamu alaikum.”

Ya faɗa cikin amon muryarsa. 

“Alhamdulillah yanzu nake shiga gidan, ya na barki.” 

Wani irin abu na ji ya doki zuciyata fiye da wanda na ji ɗazu, ita ce ta kirashi kenan? 

“Na gode sosai da kulawarki agareni.”

“Har kulawa ta bashi kenan?.” 

Na tambayi kaina, dariyar da yake ce da ita ce ta katsen tunanin da nake. 

“Ai nagani, shine abinda ya ƙara burgeni da ke, idan zan dawo a ƙara yi min.”

Ji na yi dama na mutu, dama na mutu da wannan baƙar ranar da nake ganin, kamar kunnuwana ba daidai suke ba, yau Sardauna ke waya da wata mace a gabana, akan idona, me ta yi masa da ya sa ta burgesa? Ƙila ma Samosar da na koya mata ne. ‘Na shiga uku ni Nana.’ 

Har ya kamalla wayar ina kwance ban buɗe idona ba, kusan minti ashirin yana wayar, sannan ya sake yi min magana. 

“Nana tashi mana.” 

Hannu yasa a jikina ya fara taɓani, ta dole na buɗe ido, amm sai na ji bana ma son ganinshi, na mayar dasu na rufe. 

“Nana na dawo.” 

“Har ka dawo.” 

Na faɗa ina tashi. 

“Har ne ma?”

“Sannu da zuwa.” 

“Yawwa.” 

“Nana baki tambayi yadda muka yi da ita ba” 

Murmushi na yi masa wanda yafi kuka ciwo, sannan na ce. 

“Tun da naga ka daɗe ai nasan kun fahimci juna.” 

“Eyh hakane kam, Nana na gode miki sosai.” 

“Da na yi me?”

Hannuna ya kama sannan ya ce. 

“Da kika yi komai ma, Nana a yanzu an kai matakin nasara kar ki bari sheɗan ya shiga zuciyarki, ya lalata miki komai, ya ɓarar miki da ladanki.” 

“In sha Allah.” 

“Koma ki kwanta to.” 

Ba musu na kwanta abuna, zuciyata gaba ɗaya babu daɗi, amma nasan ta bakin Sardauna ne sheɗan ne yake son ya shiga zuciyata ya haifar min da wani abu wanda zai ɓarar da lada na duka. 

Abu Kamar wasa Sardauna da Bilkisu, kullum sai Sardauna ya je gidansu Bilkisu sai bayan sha ɗaya yake dawowa, gashi sai su kai ƙarfe ɗaya na dare suna waya, haka da safe kafin ya fita ma sai sun yi waya, duk abin ya dameni yadda sardauna ya fara janye lokacinsa daga kaina. A haka ma tun ba ayi auren ba, ina kuma ga idan anyi auren? Tsakanina da Bilkisu ko ta waya ba ma gaisawa ba ta sake cemin komai ba, ko kiranta na yi a waya ma bata ɗauka, gaba ɗaya na damu kamar na yi gangancin haɗa shi da ita, wani lokacin idan na zauna ina tunani sai na ji kamar ma Sardauna ko Bilkisu wani na son wani kafin yanzu, amma idan na tuna irin yadda na shiga na fita akan Bilkisu da Sardauna sai naga kowa da ta shi matsalal, yadda muka yi da Bilkisu da kuma yadda muka yi da Sardauna, sai na ji kawai Allah ne ya haɗa jininsu a lokaci ɗaya. 

********

Tun safe Anty Adiza ta kirani a waya akan yau za ta zo, na ji daɗin zuwan ta sosai, haka ma Sardauna da na faɗa masa, sai da ya ce kar na kuskura na yi mata zancem ƙarin aurensa. Wajen ƙarfe ɗaya ta ƙara so, na tarbeta da murna itama haka, bayan mun gaisa ne tasha ruwa ta kalleni sannan ta ce. 

“Nana duk kin rame, kamar mara lafiya ji yanayin jikinki ko kina da hawan jini ne?” 

Na girgiza kai sannan na ce. 

“Na dai yi Low Bp kwanaki, bayan rasuwar Alhaji.” 

Domin yanzu na zama mashahuriyar maƙaryaciya akan al’amuran Sardauna, har uwata ma ƙarya nake mata. 

“Ayyah Allah Sarki, amma da kin mai da hankali akan ganyayyaki da sun ƙara jini sosai Nana.” 

“Tom shikenan Anty Adiza zan maida hankali in sha Allah.” 

“Nana.” 

Ta sake kiran sunana, na ɗago na kalleta. 

“Munyi magana da Yaya Radiya, akan wasu abubuwan dake faruwa, Nana wai menene asalin matsalalki?” 

“Nifa ba ni da wata matsala, bansan me suke magana a kai ba.” 

“Nana duk wanda ya ganki yasan da damuwa a tare dake, ga shi ba inda kike zuwa.” 

“Mijina ba ya son fita, indai ba wani ƙwaƙwaran uziri ba.” 

“Hhm, Me yaja miki Low Bp.” 

“Tun rasuwar Alhaji ne.” 

Anty Adiza wayayyiya ce, tasan ta yadda zata kama mutum ta dole, wasu irin tambayoyi ta dinga watsomin har sai da na yi suɓul da baka na ce da ita Sardauna ne zai ƙara aure, murmushi ta yi sannan ta ce. 

“Nana kenan, bayan nan fa.”

“Babu komai Allah.” 

Matsowa ta yi kusa dani ta kama hannu, ta fara magana cikim tausasawa.

“Nana karki kasance sokuwa, karki kasance shashasha! Daga lokacin da miji ya fuskanci kin shashantar da kanki a kansa, zai mai dake marar amfani, zai mai da ke tsanin da zai taka ya hau kowane mataki, Nana ba a ce babu soyayya ba, ba a ce soyayya ga miji ƙarya ba ce, amma Nana ki mutunta kanki, muma duka Nana ai muna son mazajenmu, so ba ƙarami ba Nana, amma muna mutunta kanmu ta yadda suma zasu mutantamu, Nana babu mijin da ya isa ya zo sama da ‘yan uwa ko iyaye, kowa matsayinsa daban. Ki farka daga wannan baccin da kike Nana, kisan idan kika tunkara karki zauna ki lalace a haka.” 

“Shikenan Anty Adiza, na gode sosai kuma in sha Allah zan gyara.” 

“Shikenan Nana Allah Ya sa gyara mana.” 

“Amin amin .” 

Kalamanta duk sun shige ne ba ƙarya, kuma a iya hasashen da na yi gaskiyya ta faɗa min, amma ni har yanzu banga mafarkin da nake yi akan Sardauna ba, matsala ɗaya ce rashin zuwa gida kuma in sha Allah zan dinga zuwa.

Bata jira Sardauna ya dawo ba ta tafi sabida tabar yaronta a wajen masu aiki, ba ta daɗe ta tafiya ba na sake gwada lambar Bilkisu amma ba ta tafiya. 

“Allah Ka sa wannan baiwar taka tana lafiya.” 

Na faɗa a raina tare da ƙudiri niyar idan Sardauna ya dawo zan tambayeshi, sannan na ce idan ya je ya haɗani da ita.  Ba Sardauna ya shigo ba sai bayan magariba, shima a gurguje ya shigo ya shirya ya fita ko abinci bai ci ba, sai bayan goma ya sake dawowa, hannayen shi riƙe da leda da alama shopping ya yi. 

“Nana ga wannan, Bilkisu ce ta ce akawo miki.” 

Karɓa na yi sannan na ce. 

“An gode.” 

“Munje shopping ne, kinsan an sanya ranar aurenmu wata ɗaya, shine muka je siyayya.” 

Kamar ansoka mini mashi haka na ji shigar maganarsa, amma sai na kauda kai tare da cewa. 

“Allah Ya nuna mana.” 

“Amin Nana.” 

Miƙewa na yi da niyar shiga ɗaki na kwanta, Sardauna yasa hannu ya jawo ni kusa da shi, ya riƙe hannayena duka biyun da ƙarfi, riƙon da ya yi min ya haifar min da nutsuwar dole, shi kuma ya zuba min idanuwansa waɗanda suka riga canza launi zuwa yanayin tausayi da damuwa, sannan ya fara magana cikin muryar sa mai amo ta daɗi. 

"Nana... kin san irin son da nake miki, kuma kin san cewa wannan lamarin ba zaɓina ba ne, kaddara ce ta iyaye. Amma abin da ya fi komai burgeni ya haifar min da nutsuwar da ta bani damar sauke haƙƙin da nake shirin ɗauka shi ne yadda kika nuna min tsantsar girma da biyayya kika amince da wannan auren. Nana, wannan babban Aikin Lada ne kika ɗauko wa kanki."

Ya gyara zama, ya ƙara matse hannuna.

"Nana, yanzu an riga da an sa rana, komai ya fara ɗaukan harama, kuma hausawa sunce aski idan yazo ƙarshe yafi ƙaiƙayi. Ina so ki sani, Shaiɗan ba zai bar ki ba. Zai rinƙa hura miki wutar kishi a zuciya don ya rusa miki ladan da kika fara nema. Kar ki bari Shaiɗan ya yi nasara a kanki. Ki duba yadda kika jure har zuwa yanzu, don Allah Nana ki daure ki ƙarasa wannan jihadin da kika fara."

Ya ɗanyi shiru kamar mai tunani, sannan ya ci gaba.

"Idan aka kawo matar nan, ina so ki nuna mata cewa ke mace ce ta gari, uwar gida mai daraja. Ina so ki sanya ta ta yi miki biyayya kamar yadda kike mini, amma ta hanyar nuna mata ke ce babba. Ki zama uwa a gare ta, ki koya mata yadda ake girmama ni. Idan kika yi hakan, Nana, kin gama mallakar zuciyata har abada, kuma kin tabbatar wa duniya cewa ke ba mace ba ce irin ta sauran mata masu kishin hauka."

"Ina so ki nuna mata girmana da darajata a gidan nan, ta yadda ita ma za ta bi sawun ki wajen yi mini hidima. Ta hakan ne kishi ba zai taɓa samun gurbin zama a tsakaninku ba. Nana, shin za ki iya yi mini wannan alfarma ta ƙarshe? Ki zama jagora a gare ta, ki kuma kare ladanki daga sharrin Shaiɗan?"

Wani irin sanyi na ji ya ratsa zuciyata, soyayya da tausayin Sardauna suka sake lulluɓe ɓargo da fatar jikina, cike da tausasawa nima na fara magana.

“In sha Allah Sardauna, ni zan kasance mai biyayya da tausayawa a gareka har ƙarshen numfashina, Sardauna na yi niyar yaƙi da kowanne irin sheɗani da zai zo ya shiga rayuwata, zan yi haƙuri zan zauna da amaryar ko da ba ta son zama da ni, zan nuna mata girmanka da soyayyarka.”

Ya sa hannu ya rungumo ni jikinsa, sannan ya ce. 

“Na gode Nanata, Allah Ya yi miki albarka.” 

Na amsa da amin, ina rugume da shi. Ban sami damar yi masa maganar rashin ɗaukan wayata da Bilkisu take ba, tun da gashi har abu ta bada akawo min. Tun daga wannan rana bansake bari sheɗan ya samin wani tunani na kishi ba ko wani abu mai kama da hakan, shirye shiryen biki suna ta ƙaratowa, Sardauna ya yi matuƙar busy abubuwa kawai yake shiryawa na auren, lefe akwati set uku ya yi mata, ni kuma ya yi min set ɗaya. Ranar da aka kai kayan gidansu Bilkisu ya kama ɗaurin auren saura sati biyu cif, amma shagulgulan bikin sauran kwama takwas afara a yadda Sardauna yake faɗan. Har da wasu Events da za ayi a Abuja ma, ɗaurin auren ma acan zaayi sabida Bilkisu na da ‘yan uwa acan, ni dai nawa na yi fatan alheri ne kawai. 

Lokacin da bikin ya rage saura kwanaki biyu a fara Sardauna ya umarce ni da na je gida na faɗawa su Hajiya, idan zan iya ma na kwana ɗaya acan. Na ji daɗi sosai sabida ina son na zaga ‘yan uwa da na daɗe bangani ba, duk da ya ja kunnena sosai akan kar na faɗi wasu abubuwan. 

Da kanshi ya kaini har gida, bayan ya shiga sun gaisa da Hajiya sannan ya tafi, gidan bakowa sai Hajiya Yaya Radiya tana makaranta, Ra’is da Yaya Ridwan ma haka, yaran Yaya Radiya ma sun tafi makaranta. Hakan ya bamu damar zantawa da Hajiya sosai da sosai, har na faɗa mata auren da zaiyi, sai dai na ɓoye mata cewar Bilkisu ƙawata ce, na ce a familyn ɗinsu take, ta yi aure ne ya mutu. 

Yaya Ridwan ne ya fara dawowa, amma bai nuna ko ya ganni ba, ya shige ɗaki sai kuma Yaya Radiya, ita ce ma muka tattauna muka yi hira sosai, sai Ra’is da ya dawo. Da daddare Sardauna ya kirani na ce da shi zan kwana anan ɗin, ya kashe wayarsa na tare da ya ce min komai ba. 

Washe gari na je gidan Yaya Rumaisa, ta yi mamakin ganina a gidan nata dan tun da na yi aure bai fi sau biyu na je ba, shima duk kafin rasuwar Alhaji ne, amma tun da Alhaji ya rasu banje ba. Muna cikin hira ta ce dani. 

“Shashasha, wannan yarinyar ce zaki ce mijinki ba sonta yake ba tuntuni?” 

Ta faɗa tana nuna min hoton Sardauna da Bilkisu a cikin mota wanda Bilkisun ta ɗauka da kanta, na yi murmushi sannan na ce. 

“Yaya ai sun amshi ƙaddara ne, sabida dukkansu ƙaddararsu iri ɗaya ce, amma aina kika sami hotonan?” 

“Nana baki da hankali, a yanzu babu wasu couples da suke trending a social media kamarsu. ko wane shafi kika duba hoton su nr, mutane suna ta posting suna cewa Sardauna Ta ambo, ya sami matar da yake so, wasu a comment sai ƙare miki zagi suke, har da masu cewa ‘yar mitsiyata.”

“Hhm Yaya Wannan tunanin su ne, tun da dai muna zaune da mijina lafiya ai shikenan, duk abinda mutane zasu ce su yi ta faɗa,ni dai ina son mijina shima yana sona, ba shikenan ba.” 

“Ke Nana kalle ni, wallahi Allah Sardauna baya sonki, ke ni yanzu na fahimci Sardauna auren manufa ya yi dake.” 

Legendspen
***