26
by @legendspen
“Yaya bana son irin wannan maganar, ai daman na san kwata kwata ba kya son Sardauna.”
Na faɗa a fusace.
“Ke dalla malama rufe min baki kafin na yi ƙasa ƙasa dake anan, rashin kunya zaki yi min akan Sardaunan?”
“Ni ba rashin kunya zan miki ba, amma kema kinsan ai abinda kika faɗa bai kamata ba, miji na ne fa.”
“Au mijinki ko? To mene amfanin aure irin na Sardauna?”
“Yaya wai mene haka?”
“Duka na zaki yi Nana? Duka na zaki yi?”
Ta faɗa tana miƙewa, ganin tashin hankalin na ta ya yi yawa na miƙe da cewa.
“Ni kinga tafiya ta.”
Har n kai gab da ƙofa ta kira sunana.
“Nana!”
Na juyo na kalleta, ta yi min alama da hannu sannan ta ce.
“Zo.”
Dawowa na yi na zauna, itama ta zauna kusan minti biyar Yaya Rumaisa ta gyara zama, ta dubi ni, wadda idanuna suka yi jawur saboda riƙon da ta yi min kaɗai ya karyan zuciya da kuma fargabar abinda zata ce min. Ta nisa, sannan ta ƙara kama hannun na ta matse shi sosai, cikin muryar tausasawa ta fara magana.
"Nana, ki nutsu kar kice zaki yi kuka ki saurare ni da kyau. Rayuwa ba soyayya ce kawai ba, kuma zaman gidan miji ba hauka ba ne. Ina kallon yadda kika lallace akan Sardauna, kina neman mayar da shi tamkar abin bautarki. To ki buɗe kunnenki ki ji; Iyaye daban, Miji daban."
"Kar ki taɓa kuskuren nuna wa miji ya fi iyayenki a gare ki. Iyayenki sune tushenki, sune suka san ki kafin Sardauna ya san ki. Namiji, komai son da yake miki, idan lokaci ya yi zai iya juya miki baya, amma iyaye ba sa taɓa watsar da ɗiyarsu. Idan kika ɗaukaka miji sama da iyaye, to ranar da zai watsar da ke, ba za ki sami wurin komawa ba."
Ta gyara zama ta ci gaba, "Nana, musamman yanzu da za a yi miki kishiya, kada ki kuskura ki shashantar da kanki. Wannan biye-biye da lallaɓawa da kike yi masa, ki rage shi. Namiji idan ya ga kina rawar ƙafa a kansa da yawa, to wulakanta ki zai yi. Ki kame kanki, ki mutunta kanki a mace. Mace mai mutunci ita ce wadda take da sirrin kanta, ba wadda take zama tamkar tsumma a gaban miji ba."
"Kada ki bari kishi ya sa ki zama mahaukaciya, kuma kada ki bari soyayya ta sa ki zama doluwa. Ki zauna a matsayinki na Uwar Gida mai daraja. Ki yi masa hidimarsa na matsayin miji, amma ki bar wa zuciyarki sauran sararin numfashi. Idan kika bayar da komai na rayuwarki ga Sardauna, ranar da waccan matar ta shigo, za ki tarar ba ki da ragowar komai na kanki."
"Ki tashi, ki gyara kanki, ki daina wannan kukan banza. Namiji girmama shi ake yi, ba bauta masa ake yi ba. Idan kika mutunta kanki, shi ma zai mutunta ki. Amma idan kika zama tamkar tabarma a gabansa, to kowa ma takawa zai rinka yi ya hucewa."
*******
Ko da na dawo gidan Hajiya ban faɗa mata yadda muka yi da Yaya Rumaisa ba, na barwa raina da niyar in sha Allah zan ɗau matakin gyara, tsakanina da Sardauna soyayya ce da kulawa babu bautawar da kowa yake tunani, tun ina saka ran zai zo ya ɗauke ni har na kira sa, gaba ɗaya hayaniya ce a inda yake shi ya sa ban wani ji mai yake cewa sosai ba, na katse kiran na yi masa text akan ina jiranshi, amma amsar da ya dawo min da ita ta nemo ta jefani cikin ruɗani.
“Nana ba zan iya zuwa ba, Daddynsu Bilkisu ne ba lafiya tun safe ina asibiti!”
Tunawa na yi lokacin da Alhaji ba shi da lafiya, Sardauna bai ko shigi gidan nan ba sai da ya dawo. ‘Wai anya maganar da ake faɗa min ba gaskiyya ba ce? Bai ci ace na buɗe idona na yi tunani a kai ba?.’ Na tambayi zuciyata, amma da yake tafi ni mutuwa akan Sardauna sai ta ɓoye hakan, ta shiga lissafomin uzurirrika kala kala da zasu kare Sardauna, ina shirin tafiya Ra’is ya shigo yana faɗin.
“Hajiya ga Yaya Turaki nan.”
Mamaki ya kamani wai Yaya Turaki, to me yake yi anan.
“Bari na ɗan gyara wajen kafin ya shigo.”
Hajiya ta faɗa tana ɗan kwashe kayan dake wajen, sannan ta sa Yaya Radiya fa ɗauko mata dadduma ta shmfiɗa mai.
“Ke daskarewar uban me kika yi anan? Ba yanzu zai zo ba ne?.”
Yaya Radiya da zata shiga ɗaki ta tambayeni.
“Tafiya zanyi, yana wajen aiki ne.”
Daidai lokacin kuma Turaki ya shigo, shi da Ra’is kamar wasu abokai haka suka shigo suna dariya, ni abun ma mamaki ya ban, ashe akwai sauran mamaki ganin yadda Turaki ya saba da ‘yan gidanmu har da tsokanar Yaya Radiya.
“Ina yini?”
Na faɗa ganin kamar ma bai kula da ni ba.
“Amaryarmu kina nan kenan?.”
“Eyh! Ta nan tafiya ma za ta yi kuma bai zo ba.”
Hajiya ta bashi amsa, tana miƙewa zuwa kicin. Ƙila ma shi ya gyara musu gidan, dan naga Hajiya wani plast da cokali ta ɗauko masu kyau ta kawo ta ajiye a gabansa, ba tare da wata magana ba ya buɗe ya fara cin tuwon, yana ci Hajiyar tana taɓashi da hira, duk da bai da yawan magana amma su kam yana magana da su, kamar yadda yake yi da ‘yan uwansa.
“Hajiya ni zan tafi kawai.”
“Wai ba zai zo ba, to shikenan ina zuwa.”
“A’a ta jira mana mu tafi tare, ai gida ɗaya zamu.”
Ban tanka masa ba na kom ɗaki na zauna, na tarar da Yaya Radiya tana dannawa waya.
“Wai Yaya yaushe wannan mutumin ya saba zuwa gidan nan haka?”
“Tun rasuwar Alhaji, mene?”
“A’a bakomai.”
“Ai yafi mijinki hankali da nutsuwa.”
“Ku ana fara magana sai ku hau sukar mijina.”
Na faɗa ina cuna baki gaba.
“To ai mijin naki ne ba halin arziƙi.”
“Bawani nan, ni kuwa ina Hajja ne?”
“Tana nan tana tijara wai sai an siyar da gidan nan.”
“Anyi mata uban me?”
“Oho mata, sai da Ridwan ya tsinkawa yaron da ya rakota mari sannan suka bar gidan, kuma kinsan yaron da akasa a shagon Alhaji Ridwan ne ya ɗauke shi to yaja masa kunne akan bata komai, shine fa duk take rashin arziƙi.”
“Uhm, aniyar ta can ta bita, yanzu Yaya yaushe zaku gama makaranta?”
“Nan da sati biyu zamu fara jarrabawa, ke ‘yan ajinku yanzu ƙila sun shiga shekarar ƙarshe ko?”
“A’a, za dai su shiga, zango uku ya rage musu gaba ɗaya.”
“Ai gashinan kin cuci kanki, ke ba karatun anan ba ke ba tafiya turan ba, kinbiyewa jirgin ƙarya.”
“Nana fio ku tafi.”
Hajiya ta faɗa tana yayen labulen ɗakin.
“Tom Hajiya.” Na faɗa tare da miƙewa, lokacin da na fito ma baya gidan, na kalli Hajiya na ce.
“Hajiya ya zanyi da Sardauna?”
“Mene da Sardaunan?”
“Idan ya ji labarin Turaki ne ya dawo da ni, bazai ji daɗi ba.”
“To Nana a daren nan tafi a ƙafa.”
Tana faɗin haka ta shige ɗaki tabarni, ba shiri na yi waje na bishi har ya shiga mota abunsa. A hankali na buɗe motar na shiga, wayarsa yake dannawa sai kuma waƙa tana tashi ƙasa ƙasa, yadda baza ta taɓa damunka ba, kashe wayar ya yi ya ajiye ta akan cinyarsa ya ta da motar ya tana tafiya a hankali cikin nutsuwa.
“Ina zaki irga masoya na ki sanyo da ni, ki duba kanki ana kallona majunoni, ni kuma na ce indai kai naki ne ban faɗi ba, saƙo ya bayyana ne tun da ga zuciya..”
Yana tuƙi yana bin waƙarsa kamar shi ya raira abarsa, ni dai bance ko ƙala ba, sai ma tuna tuƙin Sardauna da na yi kamar za a tashi sama, ga uban waƙoƙin turanci wai na wata Ariana grande, kullum su zaka yi ta ji yana ƙurewa.
“Kin shiga raina, kin zauna dan kin sami guri, na ji kiranki na amsa kuma na zo da wuri, ke ce farko kuma kece ƙarshe, bishiyar nan tai girma wadda kikai mini dashi. Matar ƙani.”
Ya faɗa yana kallona, na juyo na kalleshi sannan na ce.
“Na’am.”
“Na ga kun fara hankali ke da mijinki, tun da ta fara barin ki ki zo gida.”
Na yi murmushi sannan na ce.
“Uhm.”
Ban san me yasa ba, amma ni wani irin nauyin shi nake ji sosai, ku sunansa bana iya faɗa.
“Yanzu saura makaranta ko?”
“Eyh in sha Allah.”
“Tom Allah Ya taimaka ya bada sa’a.”
“Amin amin.”
Daga haka bai ƙara cemin komai ba, ya mai da hankalinshi kan tuƙi ya ci gaba da bin waƙarsa.
“Ke kika ce zaki rayu da ni, so wanda bai gamuwa.”
A raina na ji dama sardauna ne yake da wannan yanayin, ina son waƙoƙin soyayya, mussaman ace ni da mijina ina yi masa yanayin min.
*********
Sai ƙarfe tara da arba’in muka shigo gidan, kusan minti talatin muna tafiya a hanya, tafiya kamar ta barin gari sabida yadda yake tuƙi, amma kwata kwata ban ji na takura ba, ko dan waƙoƙin da yake sawa suna haifar min da shauƙin da yake sani hasasomu ni da Sardauna.
Yana tsaye a bakin ƙofarmu, waya a kare a kunnensa da alama ma waya yake, gabana na ji ya tsanamta faɗuwa, na shiga maimaita Hasbunallahu wani’imal wakil, shi kam Turaki ko a kansa ya ƙarasa wajensa ya yi parking mota.
Ganin kamar bazan fita ba ya sa shi buɗewa zai fita, ba shiri na sa ƙafa na fito, gabana yana wani irin bugawa dum dum dum, kamar ana buga ganga. A hankali nake takawa kamar wacca ke tsoron taka ƙasa, idona yana a ƙasa bana son ma ɗagasu na kalli Sardauna.
“Ɗaga kai ki kalleni.”
Ya faɗa a tsawace, sannan ya juya ga Turaki dake shirin buɗe bangarensa.
“Kai uban me ya haɗaka da matata?”
“Tambayeta.”
Turaki ya faɗa yana ƙoƙarin shiga, wani irin tsalle Sardauna ya yi ya cakumo Turaki ya yi baya da shi.
“Uban me ya haɗaka da ita, na ce uban me ya haɗaka da ita?”
“Cika min riga kafin na yi ƙasa ƙasa da kai anan.”
“Ni zaka yi ƙasa ƙasa da shi, kar ka fasa Turaki uban me ya haɗaka da matata?”
“Na ce ka tambayeta mana, ko ita bata da baki ne? Idan bakasan darajarta ba ka barta ta na tafiya a titi da tsohon dare, ni nasan darajarta a matsayinta na mace, ko ba ita ba naga mace na tafiya a hanya cikin dare ni mai iya taimaka mata na kai ta gidane, bare kuma ita da nasan gida ɗaya zamu je.”
A fakaice dai Turaki ya rufa asirin cewa daga gida ga ɗaukoni, ya sauƙaƙa min sosai.
“Daga yau… ba kai… ba wani abu nawa… Turaki ba kai ba matata, ko a jeji kaganta ba kai ba ita.. na faɗa ma.”
Idanun Sardauna nake kalla yadda suka rini suka koma jawur, ga wasu jijiyon kansa da suka fito raɗau.
“To cikani, kuma matarka ce na ɗauko a mota ta, tana gaba ina gab…”
Kuɓus! Haka Sardauna ya make bakin Turaki, sannan ya saki wata ƙara kamar sabon Mahaukaci.
“Turaki akan iyalina wallahi zan iya kashe ka, ka fita sabgarta.”
Riƙe bakinshi Turaki ya yi da yake jini, a hankali ya taka ya buɗe ƙofarsa, sai da ya gama shiga sannan ya leƙo da kai.
“Kuma har ƙanshin Turarenra na ji.”
Yana faɗin haka ya tura ƙofarshi ta shige, da gudu Sardauna ya bi shi yana knocking.
“Turaki ka buɗe ƙofar nan na kakkarya ka.”
Da wani ƙarfi yake buga ƙofar yana kiran sunan Turaki.
“Wallahi Abubukar yau sai na raba hannunka da gangar jikinka, ka buɗe na faɗa maka.”
Can ta wajen window Turaki ya ƙara leƙowa.
“Ga fuskarta mai kyau, ta iya murmushi.”
Da gudu Sardauna ya dawo wajen tagar, yana faɗin.
“Abubakar zakaci kutumar ubanka wallahi, karuwa ɗan iska, me bin matan mutane.”
“Matarka dai akwai kyau ma sha Allah.”
Turaki ya faɗa daga wajen ƙofa, ni dai ina daga tsaye, na fuskanci Turaki dai haukata Sardauna yake son yi, kamar daga sama na ji yana cewa.
“Uban me kike yi anan? Sai na zo na ɓaɓɓallaki, shashasha.”
Ba shiri na shige ciki, ya yo kaina yana faɗin.
“Wato Nana ke baki da hankali ko? Da zaki shiga motar wani namiji da ba mijinki ba, Nana ko yayanki uwa ɗaya uba ɗaya ai bazaki shiga mota tare da shi ba, shine zaki shiga da wancan ƙasurgumin ɗan iskan ko? Wallahi Nana yau sai kinji a jikinki.”
Legendspen
***