BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----11

Suhail da kyar ya iya kaiwa ɗakin sa.

Rufe kofar Dakin yayi ya jingina bayansa jikin ƙofar tare da runtse idanunsa.

Wani irin nauyi yake ji a ƙirjin sa tamkar an ɗora masa dutsi 

A hankali ya cire agogon hannunsa ya ajiye saman drawer kafin ya zauna bakin gadon sa yana dafe kansa

Zeenah ke ta mishi yawo a ransa tabbas Amincewar Maganar Abba daidai yake da yaci Amanar zeenah
Tun ranar da suka haɗu a university Zeenah ta nuna masa soyayya ta gaskiya duk da bai taɓa furta mata kalmar soyayya kai tsaye ba, ya saba nuna mata kulawa da kusanci har hakan yasa ta gina duk wani burinta akansa.

duk samarin ta ,ta kore su saboda dashi bata kula kowa ta jure tsangama daga mahaifinta da sauran dangin ta duk Saboda dashi a cewar su yana bata mata lokaci bayan ga manyan yaran masu kuɗi suna son ta da aure ciki harda Cousin brother dinta dan yayan mahaifinta saboda hakan yasa wa Zuciyarsa soyyayar zeenah ta karfi.

wayar dake kan gado ta fara Ringing sunan zeenah da ya gani ya ƙara cefa zuciyar sa cikin tsananin tashin hankali sai da ta kira kusan sau ukku yayi picking.

"hello Baby"

ajiyar zuciya ya sauke ba tare da ya ce komi ba zeenah ta kara magana "Suhail are You okay"

"Eh zeenah ykk"

"i'm fine naga dare yayi ko ka fasa zuwa ne"

suhail ya ce"I'm sorry zeenah bazan iya zuwa ba kaina kemin ciwo"

cike da kulawa ta ce"oh sorry babe kasha magani ka huta it's just stress of work"

"thank You zeenah for you care" 

"it's my plessure"

katse wayar yayi ya jefar da ita chan karshen gado.

A ɓangaren Mami kuwa…

Tana shiga ɗakinta ta ɗauki wayarta cikin fushi ta fara neman lambar Zarah

A can Abuja Zarah ce zaune a dining tare da mijinta Sadiq  da Amatullah suna cin abinci lokacin wayar Mami ta shigo.

"Mami ina wuni"

"Lafiya qlau Zarah ina junaid"

"lafiya qlau gashinan yana cikin abinci but mami lafiyan ki naji Muryar ki so bored ko jikin na kine "

"kina da labarin auren da abban ku zaiyi wa Suhail"

murmushi Zarah ta ce"ai Mami tun Ranar da abba yaje gidan su yarinyar ya kirani a kan na taya shi da addu'a"

Mami ta ce"kuma ya faɗa maki ko yar gidan wacece"

"Eh,ya ce diyar wani malamin addini ce dan har inda suka haɗu ya faɗamin"

dogon tsaki Mami taja ta ce"Allah ya wadaran naka ya lalace da alamu ma Zarah kamar farin ciki kike da Auren nan ko"

"Mami ai abun farin ciki a ce ƙanina ya Auri mace ta gari"

Mami ta ce"kema yanzu kin fara biye wa Fauziya ko"

haɗe rai Zarah tayi ta ce"Mami why ke kullin ana magana sai kin kira aunty Fauziya yanzu ina ruwan ta a ciki"

Mami ta ce"koma minene zanga ta yadda zatayi auren nan"

katse wayar tayi 

sadiq ya kalli Zarah da mood dinta ya chanza ya ce"Mami ce ko?"

"Eh mana she Always looking for trouble har ta saka wani ma"

murmushi Sadeeq yayi ya ce"ku cigaba da haƙuri da ita hadda tsufa"

kallon sa Zarah tayi cikin takaici maganar da yayi wai tsufa  ta ce"wani kalar tsufa baban Amatullah she is just 52 years kawai dai ita bata so taga an zauna lafiya ne"

Kawar da zancen Sadeeq yayi suka cigaba da wata hirar

mami na ajiye wayar ta ja tsaki ta ce"Nayi da na sanin ma kiran wannan sakariyar yarinyar tun farko ma da Naima Na kira dan ita kadai ke supporting di na kuma ita kadai ke fahimta ta"

kira biyu ta wa naima Amman wayar ta a kashe har tayi dailing Number Aisha sai kuma ta fasa dan itama wani takaicin zata kwasa a wajen ta

daren Ranar bacci ya kauracewa Idanun Iman sai juyi take akan gado zuciyar ta cike da tunani sabuwar Rayuwar da take shirin farawa a hankali ta furta "Allah kayi min zabi na Alkairi cikin rayuwar ta"

wayar dake kusa da ita tayi haske alamun shigowar sako

yaya Mubarak ne ya turo mata sako "Autar Ammi nasan bakiyi bacci ba kina ta tunani ki kwanta komaii zaiyi kyau in sha Allah i love You so much my forever sister"

Murmushi ya ƙubuce mata karon farko da taji ranta yayi dad'i tun bayan da aka fara zancen auren ta.

"Nagode yayan Auta" ta tura masa da reply

Washe gari kamar yadda Iman bata runtsa ba haka Suhail 

Da sassafe ya shirya cikin wata ash color suit mai matuƙar kyau ya fito daga ɗaki 

part din ya nufa tana zaune a baƙin gado tana shan maganin ta na diebeties da sallama ya shiga bayan ya gaishe ta ta amsa ciki-ciki ta ce"jiya ya kuka kare da Abban ku ina fata baka Amince da auren ba"

"Na amince mami,bazan iya ja da Abba kamar yadda kema bazan ja da ke ba"

cup din hannun ta ra ajiye kan side Bed ta ce"na sani hakan ce zata faru  to ka buɗe kunnuwanka da kyau ka jini Babu hannuna tare da albarka ta a cikin bikin ka kaje chan kai da Uban naka naka da kuma ɗayar uwarta ka sun isheka tun da sun fini"

ɗago idanun sa yayi ya kalli ta Cike da bakin ciki tun kan ayi auren ma kenan ina ga anyi tashi yayi ya fice daga ɗakin.

yana fita ya hadu da aunty Fauziya tayi hanyar dakin sa ta ce"oh da Wajen ka zanje Alhaji na kiraka a waya bata shiga " sai lokacin ya tuna da yabar wayar a ɗaki"

tare suka nufi part din Abba 

Cike da ladabi ya gaishe da Abba 
Kallon ɗan nasa Alhaji Munnir yayi ya lura yadda idanuwan sa sukayi jajir kamar wanda baiyi barci ba.

“Suhail lafiya kuwa?”

Murmushi yayi da ƙyar.
“Lafiya lau Abba.”

Shiru ya ɗan ratsa wajen kafin Alhaji Munnir ya ce
“Yau da yamma zamu je gidan su Yarinyar domin tsaida ranar biki"

bugun zuciyar Suhail ya ƙara sauri amma ya daure ya ce,
“Shikenan Abba"

da kyar Suhail ya kai kasan wajen aiki a mota makullin office dinsa ya amsa wajen nadia duk ma'aikatan wajen sun lura da yadda Suhail ya shigo ba yadda ya saba ba 

kallon nadia yayi ya ce"Bazan sami damar gani kowa yau ba"

jinjina kai tayi ta ce"okay sir"

ganin ya tafi bai ce a kawo coffe ba ta ce"sir coffe din fa"

"no need" kawai ya faɗa ya shige office din sa 

nan fa suka fara gulmace gulmacen su anya Suhail lafiya kuwa nadia ta ce"may be bashi da lafiya ne"

suna ganin Sameer ko wacce tayi shiru da bakin ta Sameer ya kalli nadia "Suhail ya shigo"

"Eh yana office"

a Zaune ya sami Suhail ya kifa kansa da Table bai masan sanda Sameer ya shigo ba sai ya buga table Suhail bya ɗago jajayen idanun sa.

ganin da Sameer yayi wa suhail cikin wani yanayi ya sa ya zauna da sauri ya shiga tambayar sa lafiya miya same shi 

Suhail bai boƴe wa Sameer komai ba  ya faɗa masa dangane da auren da abba zaiyi masa.

Sameer abokin shi ne tun suna secondry school tare suka tafi Oxford University America inda suka ƙaranci law wanda gaba daya Abban Suhail ne yayi sponsoring karatun nasu Sakamakon iyayen sameer basu da karfi hakan yasa Suhail ya dauki Sameer Tamkar wani dan uwa na jini basa boye wa junan su komai 

Ajiyar zuciya Sameer sauke ya ce"Suhail a ganina wannan ba damuwa bace nasan kana tunanin Zeenah ko kar ka manta namiji dan mace hudu akayi sa  ka kira zeenah kayi mata bayanin nasan zata fahimce ka"

jinjina kai suhail yayi cike da gamsuwa da shawarar da sameeer ya bashi.

ko zai fada wa Zeenah ba yanzu ba sai bayan bikin dan baya so tension yayi masa yawa gana mami ga kuma na zeenah 


like 
comment 
share