BAKIN RAFI.....

Chapter 1

by @hauwausani476

                       
              
*Farkon Tafiya*

_Bismillah Ar-Rahman Ar-Raheem_

Rana ta fadi a bakin rafi, ruwa natsuwa kamar yana sauraron wani abu da zai faru.

A can na hangi wani gida na masu ƙaramin ƙarfi. Wanda idan ka ganshi, ba sai an zayyana maka bayanin mamallakansa ba. Kasan basu da shi, saboda yanayin fentin gidan. Farar ƙasa aka yi shi, sai akwai yalwantar iska mai kadawa acikin sanyi, wanda ke tattare da ƙamshi mai sanya zuciya da ruhi su yi shiru.

Wannan shine ke nuna maka da cewa wannan gidan na gab da bakin rafi. Saboda sanyi da ni’imomin da Allah ya halitta a wurin.  

Tafiyar ce nake, ina ƙara kusanto. Kai na cikin gidan, can na hango wata yar matashiyar mace. Mai ɗan matsakaicin tsawo — watau ita ba doguwa ba, ita ba gajeriya ba. Gata fara, ga diri daidai gwargwado. Ga idon nan manta dasu. Gata yar duma-duma da ita. Ga gashinta da ya bayyana kanshi dai-dai, gashin mu na Hausawa, irin mai sheƙin nan daukar hankalin mai kallo.

Aisha kenan, yayin da take zaune tsakiyar gida, bisa kujerar da ake cewa yar tsakar gida.  

Tana kallon santalelen mijinta, kyakyawa da shi. Dogone shi, sai dai black beauty ne. Fuska dauke da yalwatar saje, wanda yake ƙara bayyana asalin kyawonsa.  

Wanda a koda yaushe ke ƙara shagaltar da Aisha cikin narkakiyar soyayyar mijinta, Ibrahim.  

A cikin wannan yanayi ne Ibrahim ya hura mata iska cikin kunnenta. Nan ta lumshe idonta. Shikuma ya ƙara matsowa daf da ita, numfashinsu na cakuduwa da juna. Ya yi sanyayyan numfashi mai ɗauke da ma’anar ƙauna.  

Cikin sanyayyar muryarsa, mai karya jiki da zuciya tare da raunata ruhin masoya, ya furta: “Ashantyyna!”  

A cikin shauki da kulawa tamusamman, ta ƙarasu shiga jikinsa. Itama cikin kasallaliyar murya mai tada jijiya da tsokar kowane lafiyayen namiji yayin sauraronta, da narkewa a fafaden ƙirjinsa, tare da shagwaba ta samu da wuya ta furta: “Zumantyyynah!”  

Kamar ya dauke numfashinsa yake ji, domin kuwa wani abu ne ya taso masa tun daga cikin kwakwalwarsa har zuwa babban ɗan yatsarsa.  

Yayin da yake shafa sumarsa, mai santsi da laushi, ita kuma ta sa hannunta cikin fafaden ƙirjinsa, tana wasa da yatsunta a saman ƙirjinsa.  

Shi kuma yayin da ya tallafota, idanunsu suka sarƙafe da juna. Ya sunkuya da kansa, ya dora labbansa a kan nata, ya fara yi musu kiss mai rikitar da numfashi da ruhin masoya.  

Sun ɗauki wani lokaci suna kissing juna har suka kasa sarrafa kansu.  

Cikin wannan yanayi ya ɗauketa suka shige cikin ɗan matsakaicin ɗakinsu, domin gudun kada su wuce gona da iri a tsakiyar gida.  

Shigewar da wuya, labarin ma’auratan ya canja salo. A saman gadonsu da ya sha, bedsheet mai kyau na masu ƙaramin ƙarfi. Yayin da ƙamshi ke tashi na turaren ƙara mai sanyaya ɗakin ma’auratan, wanda ke luƙanya cikin tsafaffen ƙaunar juna. Wannan al’amari fa su kaɗai ne za su iya fassara shi.

Iska ne ke ƙara kadawa tare da sanyayyar sanyin rafi, mai haɗe da sanyin safiyar wannan rana.  
Yayin da Aisha ke gudanar da aikin karin safe, sai Ibrahim yana share tsakiyar gida, yana yi mata fira cikin nishadi da walwala.  

Aisha tana murmushi wanin zubi, kuma tana haɗa dariya. Domin Ibrahim, wurin labaran barkwanci da nishadantar da iyalansa, to fa gwanine.