BAKIN RAFI.....

Chapter 2

by @hauwausani476



Ibrahim ya gama share tsakiyar gida, ya ɗago kai ya kalli Aisha.  
“Aisha, zan fita wurin aiki yanzu. Ki kula da kanki.”  

Aisha ta daina murmushi kaɗan, ta ɗaga kai. “Allah ya kai ka, ya dawo da kai lafiya.”  

Bata yi saurin bayyana damuwa ba, bata kuma nuna sha’awa sosai. Kawai ta miƙa masa sallama kamar yadda mace mai fahimta ke yi wa mijinta da ya fita neman halal.

Ibrahim ya fice, iskar safiya ta ƙara sanyaya fuskarsa. A ciki har yanzu sautin dariyar Aisha na jininsa.

Ibrahim ne tsakiyar motoci, suna sauke buhu hunan dusa, yayin da zafin rana mai radadi ke addabarshi.  
Amma haka masu sana’ar ke jurewa — ga zafi, ga nauyin kayan da suke ɗauka daga motar zuwa cikin shagon masu kaya.

Duk wannan zafin rana da aikin wahala ba su sa Ibrahim cikin damuwa ba.  
Sai ma tunanin Aisha da ke addabar zuciyarsa — irin kalaman da a koda yaushe take nanata masa:  
Na ƙauna, na natsuwa, da kuma nisantarda shi daga haram, komai sauƙinta.  
Tana kuma ƙwadaitar da shi ga halal, komai wahalarta.

Wani abokinshi mai suna Sultan ke mamakin murmushin da ke shimfiɗe a fuskar Ibrahim.  
Har ya kasa haƙura, ya tambaye shi: “Me ka tuna haka, har kake wannan ƙayataccen murmushin, yayin da muke cikin wannan zafin rayuwa?”

Ibrahim ya buɗe baki kawai, sai ya ce:  
“Na tuna kalaman Ashantyyna ne.”  

Sultan ya yi murmushi, domin shi ma ya san abin da za a fada kenan.  
Domin labarin gizo, ba ya wuce na qoqi.

Sultan ya yi murmushi ya ce: “Oh!!  
Mu dai Allah ya aurar da mu. Idan ya taso, ya zabar mana matar da ko mun yi nesa da ita, tunaninta zai mantar da mu wahalar zafin neman da muka fito yi — kamar Aishar ka.”

Nan take Ibrahim ya tanke fuska, kamar ba shi ne ke murmushi ba.  
Sultan ganin haka ya ce: “Yi min afuwa abokina. Addu’a ce kawai na yi. Bansan na furta sunanta ba. Duk da na san yabo na gwani ya zama dole, mai da wuƙar shugaban yan kishin duniya.”

Ibrahim ya nisa kaɗan, tare da fesar da iska mai zafi. Sai ya ce wa Sultan:  
“Oho dai, ai zafin ƙauna ke sa ka yi kishin abin da kake bege.