TALES OF THE WAZEERIS

fake apology

by @surayyahms

*28...🦋🦋🦋*
SURAYYAHMS
*Tales of the wazeeris..*


Daga bangaren sarauniya Areesha kuwa har lokacin tana cikin dakinta zaune akan lafiyayyen gadonta mai yalwar girma hannunta dayaji tsadaddn awarwaron gwal dake rawa rawa tsabar zumudi na rikeda hadadden camera din data sa aka je aka dauko mata hotunan Sultan Shamsan wazeeri da bata taɓa ganin ya kamanninsa yake ba.

computerta ta jawo snn ta danna wani button ajikin gado nan da nan dakintan ya sauya gabaki daya yadawo soft golden luxury light dake kara wa dakin natsuwa...

tana bude computer tabi ta jonashi da memory din camera kirjinta na wani irin harbawa ahankali ta fara flipping pictures dinsa daya bayan daya tanaji ajikinta kamar zata zauace dan duk lokacin data zooming fuskarshi gabanta sai yawani irin faduwa dan ko a imagination dinta data jima tanay ibatayi tsammanin haka zata ga siffar yarima data jima tana mafarkinsa a duniyarta ba

his sexy rare cloudy grey eyes ga wani irin sharp jawline, da calm royal expression din dake fuskarsa mai tafe da wani irin masculine beauty daya hade da tsantsar ruwan mulki da kasaita da nitsuwa 

tuni yanayinsa ya kusa zautar da ita tun tana zaune har ta sulale kan gado ta kwanta suuu a mugun ragwabe batare da shirya hakan ba

shamsan ba irin gayun nan bane masu social status beauty musmn me tafe da hayaniya shi yana da wani kalar kyaune irin wanda zai iyasaka mutum jin kmr in ya tsaya kallonsa harna tsawon lokaci ba zai taɓa gajiya ba.

tunda ta zuba mayun idanunta akansa har akayi sallahn magriba da isha bata motsa ba 

sai can snn ta cije lower lips dinta still idanunta nakafe akan wani hotonsa lkcin daya fito yanamai sauka daga hadaden motarsa yayyafin ruwa na zuba a kafadarsa kadan kadan..

ahankli cikin lumshe ido tace...he is a God..

ta kara shafa hoton jin
wani irin sanyi na ratsa kirjinta, for a moment taji ta manta da komai da kowa snn bata jin motsin komi a idonta da zuciyarta face shi...


tana cikin wnn yanayin saikuma kanwarta Ushna ta fado mata arai...

bakomi take tunawa face sai yanayinda taga ushna din taxo acikin ruwa,da hawaye da datti nan take sai kuma fuskar Areeshan yacanza,...slowly ta ajiye camera din agefe snn tamike tsaye taje gaban madubi tafara kallon kanta acikin mirror daga sama har kasa.

duk wani kyaunta da kwalliyar dake jikinta da duk matsayinta na babban sarauniya da take mugun ji dashi har cikin ranta tasan idan Ushna ta tsaya kusa da ita tabbas mutane da yawa zasu zaɓe Ushna sau goma kafin su kulata

wannan tunanin yasaka taji kirjinta ya wani irin matsewa da zafi.

ahankali ta dada gyara doguwar rigarta tana cewa...“i need to calm this girl down dan insan asalin meyene plans dinta tun kafin taxo takara lalata min komai...

harcikin ranta bata son ayi wani hayaniyar da zai jawo har ushna ta  janye hankalin kowa uwa uba bataso ace mahaifiyarsu takara zulmewa cikin rauni da jin tausayin yarinyar gara dai kawai tasan yadda zatayi a korata ta koma inda ta fito akan lokci musmn yanzu da yariman tharim vale ya riga yadawo gida..

ko tsayawa yin salla batay ba a nitse ta dada gyara gashinta da lips dinta kafin nan ta dan fesa turare mai tsananin sanyi sai ta bude wani drawer ta dauki spare key na cikin dakin Ushna ta fito dashi...


anitse ta nufo sashen ushna ayayinda wani kalar siririn murmushin munafunci yake kkarin subuce mata can cikin ranta tace hmmm my poor little...


dagata bangaren ushna kuwa tunda tagama kukanta ta miƙe slowly jikinta babu wani karfi, mud stained jacket dinta tafara cirewa ahankali sai veil dinta daya jike  sai yan sauran kayan jikinta da suka lalace da brown dirty water for some secnds ta tsaya tanata kallonsu tana tuna irin takaici da kunyar dataji da matar can ta tureta dazu acikn ruwan datti.

murmushin takaici ne yadan kubce mata tace hmm..what a welcome...

daga nan sai kuma ta tattara kayan ta nufi loundary area dasu dake nan daf daf kusa da gefen medium walk in sink area na cikin room dinta.

nan ta bude washing machine, ta jefa kayan gaba daya ciki kafin nan ta kunna yafara aiki duk dama still cikin emotional numbness take yin komai ko kadan jikinta babu kuzari bbu wani natsuwa face ji datakeyi har yanxu zuciyarta na mata wani irin nauyi.

bayan tagama wanke kayan tasss direct cikn bathroom ta wuce dke 
luxurious bathroom ne akwai komi da komi aciki saidai baida wani girma hannu tasa ta kunna warm white lights wajen ta kara haske kafin nan tafara cire last piece na kayan jikinta tana kkrin yaface pant inta knn taji wani irin sabon period cramp ya murde mata ciki wanda atake taji gabanta ya fadi

dasauri tadan leka ƙasarta tanajin wani irin anxiety ganin fresh jinin period ne ya ballo mata ahnkli ta runtse ido dan tasan bazai wuce stress da uban kuka da tashin hanklin data shiga ciki bane ya sake dawo mata da period dintan baya ba..


cikin sauri ta juya ta dawo dayan side din bathroom din ta dauki duk wani abunda take bukata kafin nan ta dawo.

kai tsaye  tasakar ma jikinta warm water yafara zubowa tun daga kan dogon bakin gashinta har zuwa kan gadon bayanta yana sauka kasa ahnkli..

cikin jan ajiyan zuciya ta lumshe idanunta akaro na farko kenan  tun data dawo nigeria
ta dan ji dama dama

ta dade sosai anan tana wanke kanta dan saida ta goge duk wani dattin ruwan datti da laka daya manne mata ajiki har cikin gashinta kanta saida ta wanke shi thoroughly black silky hair dinta ya kara larnewa ajikinta tsabar yaji ruwa....

sai can daga baya ta hada ruwa me zafi tabi ta nutse cikin bathtub tana jin dumin ruwan yana sassauta mata ciwon cikinta tare da tashin hankalin dake mata yawo akanta.


almost one hour tay anan sannan ta fito ta jawo wani orange bath robe me laushi tasaka ajikinta loosely sabida black wet hair dinta ya gma watsewa sharkaf a bayanta har kusa da waist dinta...

fatar jikinta da ta gurzu sosai hartana wani irin glowing dake tana da irin soft clear skin in nan ne me tsananin laushi da sheki kamar anashafeta da ruwan zuma da madara

kana iya kallon long fresh legs inta dayayi complimentn rounded hip da wani irin natural feminine shape ga nan madaidaitan nonowrta dake nan acike cikin bathrobe din da bai sauka mata har kasa ba yadda komai nata yake nuni da soft nd elegant phsyique dinta without even trying too hard.

Ushna had the type of beauty da baya buktar announcement sbd duk inda tashiga kusan dolene kaji kyanta ya dauke maka hankali

bayan ta fito daga bayin zaune tayi gaban vanity mirror ta kunna hair dryer data ganshi anan tafara drying long wet hair dinta ahankali.

pink lips dinta sun dan kara jaaa saboda sanyi idonta kuma har yanzu bai gama sakewa ba...

karar hair dryer ne ya cike dakin tanata Allah  Allah ta gama dan ta sha wani pain reliver ta samu tadan kwanta..

adede wann lokacin ne kuma kofar dakin tan ya dan budu ahankali batare da taji karar shigowar kowa ba...

Areesha ce ta bayyana cikin sanda da spare key din a hannunta..

tana daga idanunta sama kuwa caraf sai ta hango Ushna wani irin tsayawa cak tay takasa yin gaba ta kuma kasa yin baya jin numfshinta ya dauke cak na seconds biyu

ahnkli kwayar idanunta suka fara bibiyar fresh hadadden jikin Ushna ryt from her long wet natural hair to her bare fresh smooth glowing glass skin to her soft rounded boobs nd hips ga wani mayen atrctive long legs datake dashi

wani irin muguwar ruwan kishi atake ya tsaya mata a kirji..

Ushna looked too beautiful, taga alama tamafi yin azaban kyau data kara girma, the dangerous kind of effortless feminine beauty wanda baya bukatar kwalliya kwata kwata...

Areesha ta hadiye yawu ahankali tana cigaba da kallonta har wani romanticising perfect body dinta takeyi aranta with intense envy nd jealousy.


“how can someone's skin look this clear..."

tafada aranta ayayinda ruwan idanunta suka kara sauka akan long fresh healthy legs da chest din ushna dake motsawa softly along with her breathing.

then her hips again...

atake wani irin disgust mixed with jealousy ya murde ma arisha zuciya.

deep inside her heart she wish everything was hers, that soft body....the natural beauty..that delicate look. musmn ma inta tuna daxu yadda ko acikin kuka da datti ko kadan kyaun ushna bai gushe ba

wannan tunanin kadai ya kara bata mata rai ta kasa yin wani motsi har saida ta gama kakalo wakanta nitsuwa

A hankali tayi calming yanayin fuskarta snn tayi karamin gyaran murya emm emmm.

Ushna data razana ta dago kai da mugun sauri saida dryer din dake hannunta ya fadi kasa gabanta yanadan bugawa ta mike tsaye 

lokci guda suka hada ido da Areesha dake tsaye daga bakin kofar tadora ma saman fuskarta wani irin fake melancholic exprssion kamar irin itace tafi kowa jin ciwo abunda ya faru.

very softly tace
“little sis.....


da sauri ushna ta dauke kanta batare da amsata ba kawai ta sunkuya ta dauki hair dryer dinta daya fadi a kasa...Areesha tay shiru ta xuba mata ido tanata kallonta kwayar idonta cike da wani irin taushin karya mai boye da wani kalar mugun quduri a karkashinsa.

Slowly ta takaraso har tsakiyar dakin batare da tadauke idonta akan ushna ba, yanayinta kamar zata fashe da kuka tace ushna can we talk please?

Ushna ta mugun hade ranta batace komi ba tamike tsaye tana fmr kokarin juya mata baya dan tamaida hnkalinta wajen busar da dogon gashinta.

kafin ta hankara sai taji Arishan harta karaso kusa da sauri tarike hannunta bibbiyu cikin wani irin yanayin damuwa muryarta na rawa rawa kamarna wacce take kokarin danne kuka

da sanyin jiki tace Ushna please don’t do this to me...ki min magana mana koda zanji sanyi araina. 

nan hawaye masu sanyi suka fara sauka a idonun ushna murya kasa kasa bada sakin fuska ba tace ni me zance..??

cikin lumshe ido da budewa arisha tace  ni fa yar uwarki ne ushna, when you looked at me like i was one of those people hurting nd abandoning you ...wallahi it hurt me so much. dan Allah kiyi hakuri..Yes, i made sm mistakes okay? i shuld have answered your calls amma karkisa hakan yazama wani matsala atsakaninu dan wallahi bansan zaki dawo nigeria yau ba i was just travelling almost the whole day
..nayita tunanin kina dubai ne dinne har yanzu..

dede nan kwayar Idanun ushna ya kara kadawa da ruwan hawaye ahnkli tace "okay..ainaji..

da wani irin yanayin damuwa Arisha ta matso hannunta with soft guilty voice tace
"haba ushna karkice haka mana bawai nace miki banga missed calls dinki bane, i saw it amma very late by then kuma komai ya rikice min i tried calling back kawaide inaga bai shiga bane

Ushna na tsaye itade batace komi tanata kallonta ita bata cire hannunta daga cikin nata ba bata kuma ce mata komiba

Arisha data lura da kmr maganganuntan basu wani saisaita zuciyar ushna sosai ba sai takara matsowa kurkusa da ita da wani kalan muryan lallashi Numfashinta har yana tsinkewa kamr tana kokarin danne kuka.

..“You have no idea how much i love you...i can swear on anything holy cewa i would nver intentionally hurt you. Never....Tana fadin hakan ta saka hannu ta tallafo fuskar ushna suka hade ido lkcin sosai idanunta sukai jajur cikin sanyi jiki tace...i hate seeing you cry like this little liss you have no idea how much i love you..


ushna dake kan jin muryar Arishan na shigewa xuciyarta da kunnuwanta saidai gaba daya ynxu kanta a rikice yake, zuciyarta yagaji da bambamce kalaman gaskiya da karya.

Arisha tafi minti goma daga tsaye tana famar saukewa ushna hwaye dakin yabi ya dauka da wani irin shiruuu sbd ushna batace uffan ba

sai can daga baya cikin muryar rauni da gajiya kafin tace...i just want to be alone for now..


for some seconds Arisha ta dago kai tana kallonta cikin sanyi can tace toh shikenan but atleast tell me something abt ur trip
..kinma ci abinci kuwa?

Kai ushna ta girgiza mata ahankali tace ...
"No. 

Da sauri Arishan tace toh bari naje na kawo miki wani abu mana kici saiki gaya min abunda kike ciki ko...

da wani irin tsantsar fake vulnerability ta jawo hannun ushna ta zaunar da ita akan gado tana cewa u have to tell me everything, if there’s one person in this family i can never bring myself to hurt
...it’s you. kema kinsani

Tana gama rufe baki ushna tace but i am not hungry.. kuma bacci nakeji ni gaji.

fuskar Arisha atake ya dan sauya da haushi sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tanajin ranta na baci ta ciki amma babu yadda ta iya,cikin danne komi aranta da wani irin fake affection tafara shafa gashin ushna tana cewa"toh shiknan its okay, u can rest
...duk abunda kikeso ai shi za'ayi..kawaide ina so kisani ne you are my little sister, i can never intentionally hurt you...never.

Ushna bata dago kai ta kalleta ba tadan gyada mata kai

lura datayi cewa ba wani sa'a zataci akan ushna ba yasaka ta juya ahankli da niyyar fita daga dakin tana abu sum sum gwanin ban tausayi kamar irin zuciyarta ya karye innan .

Har ta isa bakin kofa ushna batace uffan ba face saida arishan ta  sake juyowa cikin raunanniyar murya tace..Goodnight little sis...please try to sleep okay?..

Still ushna batace mata uffan ba kawai tagyada mata kai ta tsaya tanata kallon kofar har sai dataji an rufeshi kirif snn wani
Doguwar ajiyar zuciya ya kwace mata

A hankali ta karasa bakin kofar zata kulle shi da security code taciki ta yadda spare key bazai sake budeshi ta waje ba.

tafara dannawa kenan taji ana Kwankwasawa tawaje after few scnds ta bude kofar ahankli

Wata maid tagani a tsaye rike da golden food tray mai kyau ga wani uban kamshi da ke tashi daga ciki

Cikin girmamawa maid din ta gaisheta snn ta sanar da ita cewa kakarta ummu hareera ce tace a kawo mata  abinci...

Ushna ta dan tsaya tana kallon tray din na wasu lkci kafin daga bisani ta karba ahankli.

Kamshin abincin kadai shi yakara tunasar da ita irin yunwar datakeji dan tun safe rabonta da abinci banda few snacks dataci ajirgi.


tana sallamar maid in ta kama kofar ta rufe
Direct kan darduma dinta ta karasa ta aje tray din akai sannan ta daga murfin silver din ahankli danta menene aciki.

Wani irin hadadden kamshi mai mugun dadine ya bugi ramin hancinta, Spaghetti jollof ne me yaji da kayan lambu ga wata mayyar crispy yam balls datayi golden colour tay kyau sai manyan samosas da aka soyasu dai dai yadda takeso, gefe kuma akwai chilled grape drink cikin glass bottle mai sanyi.

tunda Idonta ya sauka akan abincin zuciyarta yake bata kamar wn ba abincin ummu hareera bane

from the look, the aroma nd everything look like her mother’s recipe saidai tasan mamanta ta jima da denayin girki agidan kusan komi servants ne suke musu akowani lokaci ba lallaine taje  tamata girki bayan duk abun tashin hankli da yafaru tsakaninsu dazu ba

saidai tun daga yadda aka yanka vegetables har qamshin din dake tashi cikin abincin
Ushna tariga tasan wnn hannun mamanta 

duk dama bataso taci ba amma yunwa takeji kamr zai kasheta dan haka sai takawar da tunanin komi aranta

A hankali ta dau plate ta debi abincin ta fara ci acikin nutsuwa duk dama sosai take turawa acikinta kamar wacce tay kwana uku masu kyau bata saka komi acikinta ba

Lokaci zuwa lokaci take kurban grape drink din dayake kara tabbatar mata cewa wnn abincin ba na kakarta ba ne

Saida taci ta koshi sai can snn ta lumshe ido jin komi daya farun na dawo mata kanta...


Ata dayan bangaren kuwa maid din ce a tsaye agaban gimbiya Amani noorain cikin yanayin girmamawa
tanakan mata bayani.

murya kasa kasa tace ta karba abincin ranki ya dade kuma tana ci yanzu..

Wani irin sight relief ne ya kubcewa gimbiya Amani har saida ta dan sauke ajiyar zuciya me nauyi snn tafarajin duk wani tension din dake kirjinta na sauka

kin tabbata?..ta tambaye maid din da muryar kasa kasa

da sauri maid ta gyada kai tace “Eh ranki ya dade.

A hankali gimbiya Amani noorain ta juya kanta gefe tana kkrin boye hawayenta daya ciko mata a ido cikin ranta tana cewa Allah nagode maka Atleast dai ushna bazata kwanta da yunwa ba.

Hakan sosai ya dan sanyaya mata zuciya cikin nitsuwa tabar kitchen din ta koma cikin chamberta tana shigewa dakinta kuwa tafada wajen wanka dan rabonta datayi girki agidan zaikai shekara 15 inma be fi ba.


daga ta wajen ushna kuwa Bayan ushna ta gama cin abincin gaba daya sai taji jikinta ya fara yin mata nauyi musm ma saboda gajiya

sai can fa mike ahankli ta tattara komi ta zuba akan tray snn tamaida tray din gefe sannan ta shiga bayi ta wanke baki ta dawo ta bude akwatinta dataxo gidan dashi..

wani medium pajamas blue me laushi tasa sannan ta daure duka gashinta daya kusa gama bushewa...


A hankali ta kashe manyan fitilun dakin ta bar bedside lamp daya kadai sannan ta haye kan gadonta bata wani jima ba bacci mai nauyi ya kwasheta saboda tsananin gajiya
..


A fannin areesha kuwa
Tun fitowarta daga nan dakin ushna zuciyarta yke wani irin tafarfasa da bakin ciki da kishi.

dakyar ta nitsu ta biya sallolin dake kanta amma tun bayan nan
she was just Pacing up and down tana safa da marwa a dakin da tunanin yadda ushna bata ma tsaya sunyi magana meyawa bare harma ta fayyace mata asalin meya kawota nigeria ba.

muddin bata aure yarima ba bazai fa yu tabar yarinyar nan ta zauna agidan nan ba...

Wani irin tsaki tayi tana mai dafe goshinta ciki ranta naci da tsananin kishin yadda Komai da komi dake jikin ushna looked annoyingly perfect..

bayan ita koda ta tsaya agaban mirror tana kallon kanta bataga wnn perfecttion din ba, duk dama tasan Eh itadin ma kyakkyawa ce,she is Very beautiful actually... Amma not like breathtakin beauty irin na ushna wanda ke sa mutane su tsaya su sake kallonka.

Areesha farace itama tana da tsayi da kuma gashi yalolo amma bamai tsayi sosai da cika ba, her curves nd breast are normal size hakama yanayin idonta da bakinta, kai komi na jikinta dede wa deda ne baiyi yawa ba kuma beiy kadan ba,she look regular tana kuma  kama da babanta da mamanta ne all 2geda.


itade ushna batama kama da kowa acikin iyayensu da kakansu na kurkusa, da kakan, kakansu imamu waxeri daya asalin haɗe jini da xuriar waxeeris na tharim vale take kma

Wani irin kishi me zafi ne yasake cika zuciyar arisha, tanaji inama ace itace take da asalin kamanni na jinin ahalin wazeeris da kuwa sosai rayuwarta zai bada kala.

A hankali ta matso kusa da mirrorn tana shafa gefen fuskarta.

Maybe i should just do the cosmetic surgery in india...

sabida sune take jin zata iya yin procedures awajensu da zasu dan kara refining mata face dinta da body shape dinta itama ta ciko tazama very attractive
kmr ushna, Lip fillers kadan, da dan skin treatment da Body contouring tasan iya wnn kawai sun isheta shikenan ba wani abu meyawa ba.

Tana cikin wannan tunanin ne caraf sai ta tuno da saurayinta Farees salman, cikin rolling eyes tace thank god my Farees would literally do anything for me.

Ahankali wani kalar manipulative smile yay excaping saman lips dinta...ta jawo wayarta ta kashe wuta ta haura kan gado nan da nan tafara binciken abinda ya kamata tayi....
SURAYYAHMS
***