HADIN KADDARA

Chapter 24

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                     By

         
           AyshaNalado


Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍


BOOK 1


Page  24


Takaici da tashin hankali, ba su bari ta iya gama kallon hadadaden bidiyon da aka haɗa hotuna da short clips ɗinta wanda  aka ɗauketa a gidan Mother a sirrance ba tare da saninta ba , cikin salo na romantic video editing mai bayyana zazzafar soyayyar Suraj a gareta, tare da voice over na kalamai masu zafi da taba zuciya.  Dakatar da shi ta yi tare da kife wayar a cinyarta, ta rintse ido tana fesar da hucin baƙin ciki, zuciyarta banda tafasa babu abinda ta ke yi. Ita Suraj zai yi wa haka? shin da wane lokaci ya samu dama har haka a kanta ya yi mata hotuna harda short clips, yanzu me mutane za su ce, me ya ke so a ɗauketa, tabbas ya ci mata mutunci iyakar cin mutunci. Wayar ta  ɗauka ta fara bibiyar sakonnin mutane ɗaya bayan ɗaya, yawanci tambaya ne, dama tana soyayya da Surajudeen Al-Hikima? Ashe Suraj saurayinta ne, wasu kuma fatan alkhari yayinda wasu ke yabon Suraj da taya ta murna da samun irin wannan soyayya, duk ciki babu wanda ta iya amsawa domin idan ta ce za ta yi hakan to lallai za su ji mara daɗi, don haka ma da ta gama ganin sakon take goge chart ɗin. Tana gamawa da nan ta koma kan groups a nan ta tarar da abinda ya lulluka bacin ranta, muhawara aka tafka sosai a group na yan department ɗinsu akan lamarin, wasu na faɗin dama suna soyayya yayinda tsirarun da suka san tsakaninsu ke ƙaryata haka suna bayyana gaskiyar yadda lamarin yake, a General group kuwa. “ Oh my god see luv. Gaskiya sun dace. Wace ce wannan Salmahn ne wai?. Wow the lovers of the year. Gaskiya yarinyar nan ta dace wannan irin soyayya haka. Ta hadu gaskiya,  Masha Allah, this is pure love. Awwn this is so beautiful. Love like this is rare. Ire-iren comment ɗin da aka dinga yi kenan, amma masu tambayar wace ce ita sun fi yawa, hakan ya janyo  dalilin da aka dinga tagging dinta a group din ana yi wa waɗan da ba su santa ba kwatance da bayaninta, a groups na kawayenta kuwa, zagi da tsokana suka tasa ta da shi a gaba wai dama tana son shi munafuka, jibi yadda take dariya tana nishaɗi tare da shi, waya mutu waya dawo. A last group din da ta shiga a nan ne takaicinta ya ruɓanya, wata yarinya ce yar Meduguri Fannah Bakura,  fitattciyar Socialite ce  a makarantar, da  yan term ɗinta, sune suka ta so ta gaba da zagi da isgili kala kala,  yanayin amon kalamansu ya nuna kamar da wata a ƙasa, “In banda kwaɗayi rashin kamun kai da son abin duniya mai zai kai mace gidan su saurayi.” “Iskanci mana, ai da gani ba yau ta saba binsa ba.”  “Ai kuwa dai ta yi  asara ta bada mata, sam babu class.” “Ku bar jaka yar akuya mana.”  Zagi da cin mutuncin salo salo, tsabar bakin ciki bata san sanda hawaye suka fara bin fuskarta ba,  ba ta iya ci gaba da duba sakwwanin ba ta kashe wayar gaba ɗaya ta kwanta, babu abinda ke amsa kuwwa a kunneta sai JAKA YAR AKUYA, tunda Ammie ta kawo ta duniya ba'a taɓa yi mata zagin cin mutumci irin wannan ba, amma ba komai laifin Suraj ne, don ko kadan bata ji haushin Fannah ba,  wani irin haushi da sabon kiyayyarsa take ji a ranta fiye da na baya, tabbas ba zai ci banza ba yadda ya yi nasarar fassalawa duniya abinda ke lulluɓe a ransa, itama haka za ta fallasa irin kiyayya da  ta ke yi masa a gaban dukkan mutanen da suka gani har ya burge su, a gaban dukkan mutanen da suka zageta a kansa, tabbas wannan kukan bakin cikin  da ya sanya ta, sai ya yi makamancinsa  ko ma fiye da nata ta ci alwashi. Abinda Salmah bata sani ba, ba iya cikin school bidiyon ke trending ba, har  a can kafar Tictok, in da a nan ne ya fara daura bidiyon, bidiyon ya samu karɓuwa fiye da tunanin shi karan kansa Suraj ɗin.
Muryarsa  a voice-over ɗin ta ƙarawa bidiyon  wani armashi na musamman, kalaman da ya yi amfani da su  suna ratsawa cikin zuciya kamar ana faɗa kai tsaye ga mai kallo. Wannan ne ya sa mutane suka kasa daina sharing likes  da comment akan shi, wasu ma suna amfani da muryar a matsayin sound a posts ɗinsu.


Wannan dare ya yi Salmah tsayi,  domin yadda taga rana haka bakin ciki da damuwa suna habata rintsawa, masifa ya dinga cin zuciyarta, ta dinga jin kamar ta dauki waya ta kira Suraj tun a daren ta wankesa, sai dai sama ko ƙasa ta rasa lambarsa  a wayarta,  karshe ta yi tsaki ta kashe wayar gaba ɗaya ta kwanta tana tunanin irin abin da za ta yi masa gobe wanda ko hanya ya hado su sai ya canza, wanda zai sa ya ji ya tsaneta ko kyauta Abie  ya ba shi ita sai ya mayar. ba ita ta samu rintsawa ba sai gabanin asuba, ko da ta yi sallah kai tsaye kitchen ta nufa ta haɗa breakfast mai sauƙi, ta shirya na su Ammie a basket, ta koma ɗaki ta yi wanka ta yi shirin makaranta, dressing ta yi ranar na daukar magana,  wata hadaddiyar abaya ce, ruwan ƙasa mai karshen tsada, wanda ko makaho ya laluba zai shida haduwarta,  to balle ya samu jiki mai  structure irin na Salmah kyau kan kyau kenan, kun san dai mutuniyar wajen gayu karshe ce.


tsabar yadda bala'i ke cinta ko ruwa ta kasa sha, kana ganinta kasan tana tattare da ɓacin rai,  Abie ne ya yi mata magana ganin bata  cin abincin. cewa ta yi ta riga ta ci nata a kitchen ci, Salman kuwa da ya riga ya san abinda ke faruwa kai tsaye a kai ya daura zargin yanayin da take ciki, sai dai ya ja bakinsa ya tsuke don baya son ya janyo hankalin Abie  a kan su.


Karfe takwas saura minti uku suka shiga asibitin, sun tarar da Aysha na barci, jikin dai sai a hankali, yanzu haka ma Dr Lukman suke jira ya zo ya sake duba ta, idan da abinda za a kara mata a kara, ba su wani dade ba, su ka yi wa Ammie sallama suka tafi, Ammie ta dauka fushin jiya Salmah ke yi da ita, shi yasa ba ta damu kanta da yanayin da ta ganta a ciki ba.

A bakin get Abie ya sauke su, ya basu kudin transport na dawowa saboda yana sauri, don sai kiransa a waya ma ake yi. Bayan tafiyar Abie duk yadda Salman ya so ya yi magana da Salmah ƙi ta yi, sam bai ga fuska ba, sai ma baƙin glass ɗinta da ta zaro a karamar jakarta da ta yi wa wani irin ratayawa ta yan gayu ta kwama, sai kawai ya shareta, amma a baɗini jininsa a ƙumba yake ya san halinta ciki da bai shirunta akan abu yana nufin abubuwa da yawa, bai ankara ma da shigewarta ciki ba saboda abokinsa Abdul daya karaso inda suke  suka tsaya suna gaisawa.


Tun daga bakin gate ɗin, mutane suka fara kallonta. Wasu suna whispering, wasu ma kai tsaye  su ke  nunata. Amma Salmah ba ta ko waiga ba ta ci gaba da tafiya, sanin all eyes are on her ya sa ta dinga yin wani irin taku mai cike da natsuwa da ƙasaita, sai dai sam fuskarta babu rahama, a haka ta dinga ratsa groups na student kuma duk yawansu magana daya ake idan ma ba shi ake yi ba to ana ganinta ake farawa. Kai tsaye in da take da tabbacin samun Suraj ta dosa, yana zaune tsakiyar abokansa, suna ta hayaniya irinta abokai, da alamar tattaunawar da suke tana tsananin ba su citta, Sadam ne ya fara hangota, da sauri ya taɓa Suraj dake kusa  da shi ya sanar masa, hakan ne ya ankarar da su duka zuwan nata, sai suka yi tsit suka zuba mata ido, ba su kadai ba harda group din su Fannah da wasu ma da ma duk sauran mutanen da ke kusa da wajen, har yan nisa da ke iya hangen abinda ke faruwa  sai da suka natsu suka zuba mata ido don ganin abinda zai wakana.  

Yanayin fuskarta kawai Suraj ya kalla gabansa ya faɗi, da sauri ya miƙe tsaye yana jiran karsawowarta,  ai kuwa tana isowa gabansa bata yi wata wata ba ta daga hannu ta sharara masa lafiyayyen  marin da sai da siririn farin glass ɗin da ke manne a fuskarta ya faɗi ƙasa. Tsit wajen ya ɗauki shiru tamkar mutuwa ta gifta, domin ko a mafarki babu wanda ya yi tunanin abinda za ta aikata kenan, har shi kansa Suraj ɗin, da sauri ya dafe kuncinsa yana zato ido,  hannu ta mika ta cire glass ɗinta,  ta yi poiting ɗinsa da shi, kafin ta fara magana a kausashe cike da aji,  “Wannan farin na abinda ka aikata min ne, Suraj ka wulaƙanta ni a idon duniya, ka gama burge mutane da labarin soyayyarka ta karya. To ka sani cewa ni ba abin wasar ka ba ce. Ni ba tsarar ka ba ce, kai ba ajina ba ne.
Ba na son ka Suraj, bana kaunar ka, na gaya maka sai babu adadi, amma ka ƙi ka fahimta saboda ƙwaƙwalwarka cike take da dauɗar Kuruciya, to ka sani this should be the first  and last time da za ka kuma saka ni a cikin haukarka, ka kalle bi da kyau Salmah ba matar yara ba ce ko ka ga ne.” Yadda take maganar shi yafi kowa komai tafiya da imanin mutanen da ke kallon abinda ke faruwa, tana gama fadin haka ta mayar da glass ɗin ta ta juyo ta yi wucewarta  ba tare da ta kalli kowa da ke wajen ba.

Tsit wajen ya sake daukar shiru kamar babu halittu da ke motsi a kusa,  har sai da Salmah ta yi nisa, sannan hayaniya ta barke kusan lokaci guda kamar wadanda aka bawa umarni, kowa na faɗin albarkacin bakinsa.

Ko motsi Suraj ya kasa yi, saboda mamaki da tsoro, kalamanta sun daki zuciyarsa da karfin gaske, maimaita kan su kawai suke yi a kwakwalwarsa kamar a lokacin take faɗa masa, bai san cewa ya yi suman wucin gadi ba, sai da ya ji Sadam yana taɓasa yana ambaton sunansa, wani irin ajiyar zuciya ya sauke, mai karfi, sai kuma ya zame hannunsa daga cikin na Sadam, ya soma tafiya a hankali yana hade hanya, da sauri Sadam ya yi zabura zai sake binsa, Abbas ya yi saurin rike da tare da girgiza masa kai.............





Wacce ta shirya payment yanzu kafin mu gama Book 1,  800₦ ne saura page 1 mu kammala, a saka a wannan account ɗin 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, a turo shedar biya ta ***.


Ina shaida muku ko shafin farko ba mu bude na littafin hadin kaddara ba, ku hanyarta biya  kada ku bari nishaɗin nan  ta wuce ku, ga wadanda suka san rubutu sun sani, ba za ku yi kaico ba, labari na gaba tafiya ce cikakkiya wacce za ta gamsar da ku in Sha Allah.