GAMMON RAMA

SHAFI NA UKU

by @ameeraadam

*GAMMON RAMA*

       ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

 SHAFI NA UKU

   Fauwaz ya jima yana saka wa Abida ruwa a jikinta, har sai da ya ji zafin ya ragu sannan ya matse rigar ya shanya. Bacci ne ya ɗauke ta, don haka ya fita daga ɗakin yana tunanin yadda za a yi ya saya mata magani. Don har zuciya ta ayyana masa ya je ya samu mahaifinsu ya faɗa masa, amma da ya tuna irin makircin da Tani take ƙulla musu ba su cika kwashewa ta daɗi da shi ba, sai kawai ya haƙura. Ya yanke shawarar fita tsintar gwangwanaye kamar yadda ya ga abokinsa Musa yana yi. Kusan tun gabanin sallar Magriba da ya fita, ba shi ya dawo gida ba sai kusan tara saura na dare. Zuciyarsa a cunkushe take, sakamakon ya sha yawo sosai ya tsinci gwangwanaye da jarkoki, har ya sayar amma bai samu mai chemist ɗin layinsu ba. Sakamakon Peter mai chemist ya je garinsu kirsimeti, kuma shi kaɗai ne mai kemis ɗin da ke zagayen unguwarsu. Tani tana ɗaki ba ta ji shigarsa ba, Fauwaz yana shiga ɗakinsu ya samu Abida a zaune. Sai dai daɗin da ya ji da zazzaɓin jikinta ya sauka, tana ganinsa ta saki murmushi sai shi ma ya mayar mata da martanin murmushin.

  "Ya Fauwaz, idan na girma zan gina mana gida mu tafi mu bar su Abba a nan." 
Abida ta furta a hankali don kada Tani ta ji, zama ya yi a gefenta ya ce.
 "Ai ni ne babba, ni zan fara gina mana gida mu tafi, kuma har sababbin kayan wasa zan saya miki."
Jin haka ya sa Abida ta saki murmushi har fararen haƙoranta suka bayyana.

  "Fauwaz! Don Allah, koda wani yanayi da zai gifta wanda zai sauya maka rayuwarka, ka kula da ƙanwarka. Ku biyu Allah Ya azurta ni da su, ku haɗa kanku, ka ja ƙanwarka ka ji Fauwaz."

Kalaman mahaifiyarsu ne ya dawo cikin kwanyarsa ana gobe za ta rasu, idanunsa suka ciko da ƙwalla. Gudun kada Abida ta fahimci damuwarsa ya sa shi saurin kawar da kansa. Suna nan zaune Tani ta ƙarasa ƙofar ɗakin ta ce.

  "Kai Fauwaz! Fito ka ɗebo mana ruwa."

Shiru ya yi kamar bai ji ba, saboda gabaɗaya ya ɗora rushewar faruncikinsu a kanta. A karo na biyu ta sake yi masa magana, kai tsaye ya ce.
  "Yanzu dare ya yi."
Ai kuwa kamar wacca ya kwara wa ruwan zafi a hassale ta ce.
  "To tun da ba za ka ɗebo ba, sai na bari idan ubanka ya dawo ya ɗebo mana." 
Wani irin ɗaci ya ji a ransa, cike da damuwa ya ce.

 "Ki daina zagin mahaifina."

Za ta yi magana ta ji motsin shigowar Alhaji, yana ƙarasawa ya ce. "Me yake faruwa hayaniyar me nake ji?"
Tani tana jin haka ta yi zaraf ta ce, "Wai don na ce Fauwaz ya ɗebo mana ruwa yake yi mini rashin mutumci. Ni dai ina jin Alhaji zan bari ka dinga yi masa magana da kanka, don ina gudun watarana na yi masa magana ya zage ni." Fauwaz da zuwansa bakin ƙofar kenan,  ya bi Tani da kallon mamakin sharrin da ta yi masa.
 Tass! Alhaji ya ɗauke fuskar Fauwaz da mari har sai da ya bugu da jikin bango, da sauri Abida da ke gefe ta riƙe shi a tsorace da hukuncin da Abba ya zartar masa. Abba ya nuna shi da yatsa ya ce.

  "Daga yau idan aka sake yi maka magana ka musa sai ranka ya yi mummunan ɓaci. Ka yi maza ka wuce ka ɗauki bokiti ko na tattakaka, sakarai marar mutumci."
 Goge hawayensa Fauwaz ya yi, Abida ta ja hannunsa ta yi tsuru-tsuru saboda tsoro. Wani irin kallo suke yi wa mahaifinsu tamkar sun ga sabuwar hallita, domin gabaɗaya ya sauya kamar ba mahaifinsu mai sonsu da nuna musu kulawa ba. Fauwaz yana fita Tani da Alhaji suka rufa masa baya har lokacin bai daina faɗa ba. Fauwaz ba shi ya gama ɗiban ruwan ba sai kusan sha ɗaya saura don Tani har ta kwanta, a lokacin ne ya shiga kicin zai ɗebi abinci ya ci. Sai dai yanq zuwa ya ga sai burbuɗin shinkafa da ƙanzonta. Yadda cikinsa yake ƙugi ne ya kawar da ɓacin ransa, hawayen idonsa ya share sannan ya saka hannu ya kankaro ƙanzon ya zuba da mai ya zauna ya ci. Sai da ya ci ya wanke hannu sannan ya shiga ɗakinsu, a takure a can ƙarshen bango ya hango Abida a duƙunƙune tana rawar ɗari. Da sauri ya ƙarasa wurinta ya ɗago ta yana faɗin.

  "Abida! Sannu zazzaɓin ne?"

Jikinta yana rawa ta gyaɗa masa kai, da sauri ya ƙarasa ya ɗauki rigar da ya shanya ya sake jiƙa ta ya shiga saka mata. 
  "Sannu kin ji Abida, ɗazu na samo kuɗi don na sayo miki magani amma Peter ba ya nan."
Fauwaz ya furta muryarsa tana rawa, ba ta iya amsa masa ba saboda yadda take jin jiki. Ya jima a haka har ya samu jikin nata ya rage zafi, yana nan zaune rungume da Abida ya ji bacci ya ɗauke ta. Ido ya zuba mata yana kuka, yana tuna rayuwarsu a lokacin da mahaifiyarsu tana raye. Yana cikin wannan yanayin har bacci ya yi awon gaba da shi. Wani irin kakari yake ji sama-sama a cikin baccinsa, jijjigar da jikinta yake yi ne ya farkar da shi daga wahalallan baccin da yake yi. Ɗakin baƙiƙƙirin yake, sakamakon fitilar da ke ɗakin kalanzir ɗin cikinta ya ƙare. Kiran sunanta ya shiga yi a hargitse yana jijjiga ta, sai ya ji jikinta zafi zau kamar wuta. A hargitse ya fita daga ɗakin kai tsaye ya nufi ƙofar ɗakin Tani, daga bakin ƙofa ya tsaya zai fara kiran mahaifinsu. Domin tarbiyyar da mahaifiyarsu ta yi musu kenan, babu wanda yake shiga ɗakinsu ita da mahaifinsu kai tsaye ba tare da an ba su izini ba.
  
  "Abba! Abba ka zo Abida wani abu take yi ba ta da lafiya." 
Fauwaz ya furta a ɗan ruɗe, daga can ɗakin mahaifinsu ya ce.

  "Kai waye nan?" 

Cikin sauri Fauwaz ya ce, "Ni ne Abba, Abida ba ta da lafiya wani abu take yi."
Kamar wanda ya watsa wa ruwan zafi a hassale Abba ya ce, "To ni zan ba ta lafiyar ko yaya? Ko kuwa kawai don ka tashe mu ka katse mana bacci?"

Yana daga waje ya ji muryar Tani tana cewa, "Ni ban san mene ne matsalar yaron nan ba. Wallahi da uwarsa tana raye cewa zan yi ita take kitsa masa duk wani abu da yake aikatawa. To ban da rashin lissafi yanzu idan ya faɗa maka me za ka yi mata? "

 "Shi ne abin da na gani, kai Fauwaz ka wuce ka tafi zuwa safiya sai a san abin yi."
Abba ya furta daga cikin ɗakin, hawaye ne suka shiga sintiri a fuskar Fauwaz kamar an yi masa gorinsu. Har ya juya zai tafi ya ce, "Abba amma da Mama tana raye ba ka mana haka. Na san da tana nan haka ba za ta faru ba..."

 "To ka tafi maƙabarta ka dawo ita mana." Tani ta furta da wata irin murya, shi kuma Abba ya ce.
   "Lallai wuyanka ya isa yanka Fauwaz."

 "Ba irin abin da nake faɗa ba kenan, kai ma ka ga rashin kunyarsa ko?"
Tani ta furta cike da zuga da son ƙara tunzura Abba, sai dai har Fauwaz ya fita daga ɗakin bai sake tanka musu ba. Duk da cikin dare ne hakan bai hana Abba ya cigaba da surfa faɗa ba, zuciyar Tani fes ta cigaba da ingiza shi yana hawa. Sai da ta tabbatar da ya gama cika fal da haushin Fauwaz sannan ta sake kwantar da murya ta ce.

  "Ni fa Alhaji ina son faɗar wata magana, amma sai ruwan tsoro ya mamaye ni."

Tani ta sauya fuska cikin alamun damuwa, hasken ƙaramar fitilar touchlight ɗin da ke hannunsa ta sake bayyanar masa da zallar damuwar da fuskarta take ciki.
  "Faɗi mana Tani, ni a kan yaran nan tamkar mahaifiyarsu haka nake kallonki."
Abba ya furta cikin damuwa, Tani ta gyara zama ta cigaba.
  "Ni fa sai nake ganin kamar ba iya abin da ya kawo Fauwaz ɗakin nan ba kenan."
Cikin rashin fahimta Abba ya ce, "Ban fahimce ki ba Tani."
 Tani ta sake muskutawa kusa da shi sannan ta ce, "Ni fa ina zargin sata ce ta shigo da shi."

 "Sata!" 

Abba ya furta da wata irin murya mai cike da zallar tashin hankali, gaban Tani sai da ya faɗi da ganin mummunan yanayin da ya shiga. Har sai da ta fara tsammanin ko haƙonta a zai cim ma ruwa ba, sai kuma ta dake zuciyarta ta ce.

  "Ƙwarai kuwa, saboda ba rana ɗaya ba, ba kuma biyu ba da na taɓa ganin ya shigo mana ɗaki idan muna kwance. Don ko jiya sai da na nemi ɗari biyuna sama da ƙasa na rasa." Ganin zancan kamar yana shigarsa ya sa ta wara hannuwa tana taɓe baki ta ce.
   "Ka san an ce idan ba ka iya kama ɓarawo ba, sai shi ya kama ka. Ba na son na dinga yawan faɗa maka laifin yaron nan ka ga kamar ba na ƙaunarsa, ni kuma na ga ɗa ai na kowa ne..."
 
  "Haba Tani, amma me ya sa kika rufe mini magana mai girma kamar wannan?"
 Abba ya katse ta a ɗan hassale, cike da kissa ta ce.
  "Ka yi haƙuri Alhaji In Shaa Allahu ba za a sake ba."
Furzar da iska mai zafi Abba ya yi, zuciyarsa tana zafi ya furta.

  "Yaushe Fauwaz ya zama haka? Sata? A cikin gidana? Ina ba zai yiwu ba."

Tani ta dafa kafaɗarsa ta ce, "Ni kuwa idan har da gaske ka ba ni matsayin mahaifiyar Fauwaz, zan ba ka wata shawara wacce nake ganin ita ce mafita a gare mu gabaɗaya." Tana dire kalamanta Abba ya ce, "Faɗi kowacce iri ce Tani, domin mai sonka ai shi zai faɗa maka gaskiya. Wa ya sani ma ko yana yi a waje mutane suna nan suna ta kallona da abin."
 Abba ya ƙarasa maganar yana sakin ƙwafa, zuciyar Tani fari ƙal saboda farin ciki. Amma a fili sai ta marairaice murya ta ce, "Ni ina ganin abin da ya fi, tun da yaron nan nema yake ya janyo mana magana. Kuma muna iya bakin ƙoƙarinmu wurin kula da tarbiyyarsu, kawai  ka kai shi almajiranci."
 Tani ta ƙarasa furucin tana satar kallon fuskar Abba.

ƊANBATTA

  A yatsine Inna ta dubi Rakiya da ke gursheƙen kuka, Malam Hassan  ya matsa kusa da ita cike da tausayi ya dafa kafaɗarta.
  "Yau kuma wani sabon kitifin kika ƙullo ba ki warware shi a ko ina ba sai nan a gabana? To ko laƙanin da bokanki ya ba ki kenan?" 
Inna ta furta cikin masifa, Malam Hassan ne ya yi ƙarfin halin cewa.

 "Inna Fatihu ne Allah ya yi masa rasuwa."

Maganar Malam Hassan ta yi daidai da faɗuwar bokitin ƙullin kunun da ke hannun Inna.
  "Shi Fatihun ne ya rasu?"
Inna ta furta a ruɗe, Malam Hassan ya gyaɗa kai idanunsa suka yi jajir kamar zai zubar da ƙwalla. Hakan ya sa Rakiya ta sake rushewa da kuka, tana sake jin soyayyar Fatihu a ranta. Hannu ya saka ta bayanta ya tallafo shi, Rakiya ta kunto Fatihu da ke bayanta. Malam Hasan yana sauke gawar Fatihu Inna ta zuba salati tana tafa hannu. Zuwaira da fitowarta daga banɗaki kenan ta ƙarasa tana tana faɗin.
  "Lafiya Inna?"
Ganin su Malam Hasan ya sa ta datse kalamanta, ta zuba masa idanu tana kallonsa.

  "Ina fa lafiya Zuwaira, wai Fatihu ne ya mutu. Shi kenan hankalinta ya kwanta ai."
Inna ta ƙarasa furucin muryarta tana rawa, da sauri Zuwaira ta dafe ƙirji tana ja da baya ta ce.

  "Fatihu ya rasu Inna? Yaya me ya faru da shi? In ce dai ba wata gubar Rakiya ta ɗura masa ba..."

 "Sai ma kin tambaya Zuwaira? Kamar ba ki san wace ce Rakiya ba."
Inna ta yi saurin katse Zuwaira hawaye yana zuba sannan ta ɗora da cewar.
  "Shi kenan ɗan ɗaya-ɗayan da Allah Ya ba wa Hasan an halaka shi."

  "Inna don Allah ku tsaya ku saurari abin da ya faru, kada ku yanke hukunci kai tsaye." Malam Hasan ya furta cikin damuwa, a sheƙe Inna ta dube shi ta ce.
  "Hasan wai yaushe rawanin asirin da yarinyar nan ta yi maka zai warware?"

  "Don Allah Inna ki daina faɗar haka, Fatihu tsautsayi ne ya faɗa masa. Kuma tun fil azal Allah Ya ƙaddari shi ba mai tsawon kwana ba me..."
Gabaɗaya duk abin da ya faru Malam Hasan ya kwashe ya sanar da su Inna. Yana rife baki Zuwaira ta wurga wa Rakiya kallon banza, sannan ta buga uban tsaki ta ce.

  "Inna don Allah ta yaya wacce ba ta san zafin haihuwa ba za ta riƙe ɗa dama? Wai ki ji Fatihu ya zame a ruwa kamar wani ɗan tayin kifi."
 A hassale Malam Hasan ya ce, "Kada na sake jin bakinki Zuwaira! Idan kika sake faɗar magana marar daɗi ranki zai yi mummunan ɓaci."
  Inna da zuciyarta ta gama zuwa wuya ta ce, "Ƙarya aka yi mata? Yanzu idan ɗan da ta ɗauki cikinsa ta sha wahalar laulayi ta yi naƙudarsa ne za ta sake shi a ruwa? Na ce za ta sake shi a ruwa?"
Inna ta ƙarasa furucin tana zuba wa Malam Hasan idanu, sunkuyar da kai ƙasa ya yi zuciyarsa a dagule musamman da yake jin shasshekar kukan Rakiya har cikin ransa. Domin shi shaida ne a kan zallar soyayyar gaskiya da take yi masa. A yadda ya san halin Rakiya da kyawawan halayenta, ba zai yi tantama a kan mutuwar Fatihu ba koda ba ya wurin al'amarin ya faru.

  "Ai ta kashe uwarsa, tun da ta gama da uwar kin ga shi ma dole ta gama da shi yadda za ta kanainaye mini ɗa ba tare da wani ya raɓe shi ba." Inna ta furta cike da masifa, Zuwaira ta taɓe baki ta ce.
  "Inna ka yi magana cibi ya zama ƙari, ƙari ya zama ƙababa."

 "To ni na faɗa, idan ya ga dama ya yi mini duk abin da ya ga dama a kanta, dama ai ba yau ya saba nuna mini iyaka ta a kanta ba. Wanna baƙar annoba ni kam Allah Ya jarabce ni da ita, ga ki dai juya gaba da baya ba haihuwa kike ba amma kin kashe mai haihuwar shi ma ɗan da aka haifa ɗin kin hallaka shi."

Wani irin sabon kuka mai cin zuciya Rakiya ta saki, sai kawai ta fice daga gidan tana jin tamkar zuciyarta za ta tarwatse saboda ɓacin rai. Da wanne za ta ji? Da rashin Fatihu da take jin sa tamkar ɗan da ya ratso ta jikinta ko kuwa da baƙaƙen maganganun ƙazafin da Inna take jifanta da shi? Duk da maganganun Inna ba baƙi ba ne a wurinta, amma na ranar sun fi dukan zuciyarta domin a lokacin ji take yi ko mahaifin Fatihu Malam Hasan ba zai kai ta jin raɗaɗin da take ji na mutuwarsa ba.
  Malam Hasan yana ganin Rakiya ta fita ya bi ta sauri yana kiran sunanta, hakan ya sa Inna ta yi saurin ɗagowa ta shiga ƙwala masa kira.

  "Hasan! Hasan! Ba za ka rabu da ita ba ka zo ina yi maka magana."
 Cike da zuga Zuwaira ta ce, "Ina zai zo zuciyarsa ta tafi Inna, ai wallahi sai kin yi da gaske a kan Yaya don ni wallahi ban taɓa tsammanin abin ya yi tsamari haka ba."
  Inna ta zuba hannuwa biyu a kumatu cike da jimami ta ce, "Zuwaira kin ga ya fifita waccan juyar a kan gawar ɗansa ko?"
  Zuwaira ta saka hannu ta ɗauki gawar Fatihu ta saka a wani ƙaramin ɗaki da suke ajiya shirge-shirgensu. Inna ta zauna a kan turmi zuciyarta tana ci gaba da tafasa, don a wannan karon ji take yi sai dai Hasan ya zaɓa ko Rakiya ko ita.

 Duk yadda Malam Hasan yake sauri sai da ya haɗa da sassarfa sannan ya cim ma Rakiya yana ƙwala mata kira.
 "Rakiya! Rakiya don Allah ki tsaya mana."
Cike da ƙunan zuciya da ɓacin rai ta waigo tana faɗin.
  "Me zan tsaya na yi Baban Fatihu? Me zan zauna yi a wurin da ba a  ƙauna..."
Kukan da take dannewa ya ƙwace mata, wani abu ne ya soke shi a maƙoshi cike da lallashi ya ce.
  "Don girman Allah ki yi haƙuri Rakiya, ni da ke duka mun san halin Inna ba baƙo ba ne a wurinmu. Me zai sa ranki ya ɓaci tun da kin san halinta?"

 "Me ya sa raina ba zai ɓaci ba ko ni ba ɗan'adam ba ce ba ni da zuciya a ƙirjina? Me ya sa har yanzu Inna ta gagara fahimtar ni ba irin yadda take tsammani ba ce? Me ya sa ba ta iya ɗaga mini ƙafa a wannan gaɓar da zuciyata take cike da ɗacin rashin Fatihu ba. Kasan komai fa Baban Fatihu, ka san dai ba zan iya salwantar da rayuwar ɗanmu Fatihu ba..."
 Sai ta sake fashewa da kuka, a sanyaye ya matsa kusa da ita murya a tausashe ya ce.
  "Na san komai Rakiya, na san ba a kyauta miki ba. Kuma duk wanda kika ji an ba wa haƙuri an cuce shi ne, na tabbata watarana Inna za ta fahimce ki yadda ya kamata."

 "Zuwa yaushe kake tunanin Inna za ta ƙaunace ni? A shekara goma da aurenmu ba ta so ni ba sai daga baya?"
Rakiya ta jefa masa tambayar cike da tausayin sabuwar rayuwar da za ta fara tare da Inna. Malam Hasan ya riƙo hannunta ya ce, "Don Allah ki zo mu je ciki, waɗannan maganganun za mu tattauna daga baya."

Sai da Malam Hasan ya sake rarrasarta da kalamai masu taushi sannan suka koma cikin gidan. Lokacin da suka shiga Inna ta cika fam, suna zuwa gabanta cike da zafin rai ta ce.
  "Hasan! Hasan!! Hasan!!!"
Gabansa yana faɗuwa ya ce, "Na'am Inna."

"Sau  nawa na kira ka?"

 Ya shafa kai a hankali ya ce, "Sau uku Inna."

 "To idan ni Kulu, ni na ɗauki cikinka na yi naƙuda na haife ka a yau sai ka saki wannan tsinanniyar yarinyar." Inna ta furta tana kafe shi da ido. Duk da a wannan lokacin ɓacin rai ya sa Rakiya tana son rabuwa da Malam Hasan, kalaman Inna ba ƙaramin tarwatsa nutsuwarta suka yi ba.

  "Hasan a yanzu daga Allah sai kai, ku kaɗai kuka zama gatan Rakiya. Don Allah duk rintsi kada ka salwantar da amanarta da na damƙa maka."
Malam Hasan ya tuna kalaman mahaifin Rakiya waɗanda ya yi su yana gab da barin duniya. Nan take ƙwaƙwalwarsa ta sake tarayo masa da kalaman Inna, cikin girmamawa ya ce.
  "Don Allah Inna ki yi haƙuri, abin bai kai da haka..."

 Tass! Inna ɗauke fuskarsa da mari, ba Rakiya ba hatta Zuwaira sai da abin ya matuƙar ba ta mamaki. Inna ta nuna shi rai a ɓace ta ce.
  "Na riga da na gama magana, idan kuma ba za ka sake ta ba. Ka je ka ban yafe haƙƙina da ke kanka na mahaifiya ba."
Cikin firgici Malam Hasan ya ɗago yana kallon Inna, ba ta tanka masa ba ta shige cikin ɗakin rai a ɓace.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
***