SHAFI NA HUƊU
by @ameeraadam
*GAMMON RAMA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA HUƊU
Da wani irin sanyin jiki Rakiya ta matsa kusa da shi, ta zuba masa ido tana karantar mummunan yanayin tashin hankalin da yake ciki ta ce.
"Koda wasa kada ka yi ja-in-ja da mahaifiyarka. Tabbas ana sake mata, amma duk duniya babu mai maye maka gurbin mahaifiya. Ba tun yau Inna take gwada mini ƙiyayya ba, amma a wannan gaɓar ta zarce kowanne lokaci."
Rakiya ta ja gefen hijabinta ta share hawayenta sannan ta cigaba.
"Ban ga laifin Inna ba, domin kowacce uwa tana son ganin zuri'ar 'ya'yanta. Ni kuma kalar ƙaddara ta kenan ta rashin haihuwa, sai dai ba yin kaina ba ne..."
Kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata, Malam Hasan zai yi magana ta katse shi da cewar.
"Baban Fatihu ka bi mahaifiyarka, ni kuma zan tafi duk inda Allah Ya ƙaddara zamana zai ƙare a can."
"Ba za ki tafi ko ina ba Rakiya."
Malam Hasan ya furta cikin hargitsattsiyar murya mai cike da zallar ɓacin rai, sannan ya ɗora da cewar.
"Koda ace ba ki kasance matata ba, haƙƙina ne na kula da ke matuƙar ba kya ƙarƙashin wani."
Za ta sake magana ya riƙe hannunta da ƙarfi suka fita daga gidan, kai tsaye gidan Kawu Sani suka ƙarasa. A lokacin da suka shiga Kawu yana tsaye a bakin ƙofar ɗakinsa yana rufewa, kallo ɗaya za ka yi wa su Malam Hasan ka fahimci kwanciyar hankali ta bijirewa gangar jikinsu.
"A'a, yau Hasanu ne da farar safiya haka?"
Kawu Sani ya furta yana ɗan faɗaɗa fara'arsa. Murmushin yaƙe Malam Hasan ya saki ya ce, "Mune Kawu, barka da safiya."
Kawu Sani ya amsa sannan suka gaisa da Rakiya wacce fuskarta ta yi jajir saboda kuka. Iya matarsa ce ta ƙarasa suka gaisa, tana shirin kai su ɗaki Malam Hasan ya ce.
"Kawu dama ba zama muka zo yi ba, akwai maganar da take tafe da mu."
Kawu Sani ya girgiza kai ya ce, "Hmmm Kulu ce ko?"
Malam Hasan ya gyaɗa kai sannan ya kwashe duk abin da yake faruwa ya sanar da shi. Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cikin faɗa-faɗa ya ce.
"Indo wai yaushe Kulu za ta yi hankali ne? Wanne irin rashin hankali take son aikatawa haka? Yara sun rasa ɗansu ko gawarsa ba a binne ba take ƙoƙarin sake saka su a wani tashin hankalin."
Iya da ke gefe ta furzar da iska mai zafi ta ce.
"Wallahi a kullum lamarin Kulu yana sake ba ni mamaki, wai me ya sa wasu iyayen suka fi ƙuntatawa 'ya'yan da suke fi yi musu biyayya? Saboda Allah ina adalci a cikin hukuncin da ta yanke, rayuwa da mutuwa duk a wurin Allah suke, sai kace ba ta san ƙaddara ba."
Kawu Sani ya girgiza kai ya dubi su Malam Hasan ya ce.
"Ku wuce mu je gidan, wallahi idan Kulu ba ta yi wasa ba sai ranta ya yi mummunan ɓaci."
A ɗan sanyaye Malam Hasan ya ce. "Amma Kawu don Allah kada ta..."
"Kada ka damu na san yadda zan ɓullo mata."
Kawu Sani ya katse shi, sannan suka wuce can wurin Inna.
Lokacin da suka ƙarasa gidan a soro suka ci karo da Zuwaira, tana ganin Kawu Sani ta haɗe fuska murya ciki-ciki ta ce.
"Sannu da zuwa Kawu..."
"Wuce ciki mu je baƙar munafuka."
Sum sum sum Zuwaira ta juya ta shige ciki, tun daga tsakar gida Kawu Sani ya fara ƙwala wa Inna kira.
"Kulu! Ke Kulu ko sai na shigo ɗakin?"
Inna ta fito fuskarta a cunkushe ta ce, "Ga ni Yaya."
Kawu Sani ya janyo hannun Malam Hasan ya ce, "Maza zo ki tsine masa, na ce ki zo ki tsine masa sakarai wacce ba ta da hankali. Wato so kike ki sabauta yaron nan ko ki saka masa hawan jini ki tsugunnar da shi ko Kulu?"
Inna ta sake haɗe fuska ta ce, "Yaya kai ne ba ka san abin da ya faru..."
"Idan ba ki yi mini shiru ba sai na ci mutumcinki, wai Kulu yaushe za ki gane Allahn da ya busa miki numfashi, Shi ya dasa miki ƙwan da kika haihu ba tare da sisin kwabo ko wayo da dabararki ba? An ya Kulu kina son ki wanye lafiya kuwa?"
Gabaɗaya shiru suka yi wurin ya yi tsit, Kawu Sani ya nuna Zuwaira da yatsa sannan ya ce.
"Ke kuma daga yau, idan na sake jin kin faɗa wa Rakiya wata magana ke ko kallon banza kika yi mata wallahi tallahi sai na tattaka ki." Ya waiga wurin Inna ya ce.
"Yanzu zan samu mai gari da Malam Liman a suturta yaron nan, zuwa nan da dare za mu zauna mu tattauna."
Kawu Sani ya juya zai fita, har ya je bakin ƙofa ya waigo ya ce. "Idan kun ga dama bayan na fita ku cigaba da rashin mutumcin da kuka saba. Kai Hasan zo mu je." Ajiyar zuciya a fili Malam Hasan ya saki, jiki a sanyaye ya rufa wa Kawu baya suka fita.
Bayan fitar Kawu daga Inna har Zuwaira babu wacce ta yi mata magana, ganin haka ya sa Rakiya ta ɗan samu ƙwarin gwiwar shiga ɗakin da gawar Fatihu take. Tana tsoma ƙafa cikin tsawa Inna ta ce.
"Kada ki sake ko da wasa ki taɓa mini gawar jikana. Idan kin so kuma kin ga dama kina iya haihuwar naki, tun da ke dai kin zama ƙaddara wacce ba ta da zuciya."
Shiru Rakiya ta yi sannan ta fito bakin bishiyar darbejiyar da ke tsakar gidan ta zauna. Tana nan zaune Zuwaira ta fita ta fara sanarwa da maƙota, cikin ƙanƙanin lokaci maƙota da abokan arzikin Inna da suka cika gidan. Sai dai a yadda Rakiya ta lura kowacce mace ta shigo da irin wulaƙantacan kallon da take jifanta da shi. Wanda hakan ne ya alamta mata ruwa ba ya tsami banza, don ta tabbata akwai maganar da Zuwaira ta sanar da su a kanta.
"Don Allah ki dubi yarinyar nan kamar mutuniyar arziki, yanzu wa zai ce za ta iya aikata rashin imanin nan haka."
Rakiya ta ji wata tsohuwa ta furta ƙasa-ƙasa, tana cikin nazarin kalaman tsohuwar ta sake jin wata ta ce.
"Ke kuma Tatu kamar ba ki san karuwancin matan birni ba? Yoo shi ma Hasan ɗin ai an ce ba banza ta bar shi ba."
Wata tsohuwa da ke kusa da Inna, wacce kana ganin yanayinsu za ka fahimci ita ce babbar aminiyar Inna ta karɓe zancen da cewar.
"To Allah na tuba kya ce ita, ai ki ce ubanta tuni ya gama da Hasan. Abin da tun bai san kansa ba ake ba shi a ruwa da abinci yake ci me ya rage kuma? Ai wallahi matuƙar kika cigaba da zama Kulu za ki zaunau ganin idonki."
Inna ta sake yin tsumu abin duniya yana sake damunta, cike da sanyin jiki ta ce.
"Abuwa ya zama dole na ɗauki matakin da ya dace."
"Atoh ke da ɗanki amma wata juyar banza ta fi ki iko da shi ina dalili."
Abuwa ta amsa cike da taƙama tana jifan Rakiya da mugun kallo, don yadda take ɗaga murya da gayya take faɗa don Rakiya ta ji. Suna cikin tattaunawa Malam Hasan da wasu maza biyu suka yi sallama domin ɗaukar gawar Fatihu. Kai tsaye ƙaramin ɗakin da aka suturta shi suka shiga, lokacin da Malam Hasan ya rungumo Fatihu suka haɗa ido da Rakiya. Wani sabon kukan ta fashe da shi, duk yadda ta so tausar zuciyarta sai hakan ya gagara.
"Yaya haka kawai nake jin kamar ba zan rayu da Fatihu ba, don Allah ga amanarsa nan, ki yi masa duk abin da mahaifiya za ta yi wa ɗanta. Domin na yarda da ke, kuma Fatihu ɗanki ne. Zan so ki tuna da wasiyar nan tawa a ranar da Fatihu ya zama magidanci, a ranar da za ki aurar da shi domin wannan ranar ita ce mafi mafarinciki ga kowacce mahaifiya."
Kalaman bankwanan da mahaifiyar Fatihu ta yi mata a baya suka faɗo mata a rai, cikin wata irin murya da ba ta yi zaton kalaman za su fito ba ta ce.
"Shi kenan ba zan ga auren Fatihu ba? Shi kenan yadda na rasa Hafsatu mahaifiyarsa shi ma na rasa shi? Na rasa Fatihu mai ɗebe mini kewa kenan Baban Fatihu?"
"Ban yi zaton Ruƙayyar da na sani mai sanin hukunci da dokokin Ubangiji za ta cigaba da furta waɗannan kalaman ba. Na yi tsammanin ke ce mutum ta farko da za ta lallashe ni a kan babban rashin da muka yi." Malam Hasan ya furta mata haka a lokacin da ya ƙarasa gabanta da gawar a hannunsa.
"Ruƙayya!"
Ya kira sunanta da wata irin muryar mai taushi, wacce take bayyanar da zallar soyayya, kulawa da tausasawa. Ba ta iya amsa masa ba sai ido da ta zuba masa waɗanda suka kaɗa jajir tana hawaye, ya sake kwantar da murya ya cigaba.
"Yana da kyau ki tuna, Ubangijin da Ya ba mu Fatihu yana iya ba mu ninkinsa a lokaci guda..."
"Amma ba da wannan juyar ba."
Furucin Inna ya katse shi, waigowa suka yi lokaci ɗaya suna kallon Inna. Matan gidan da suka shigo gaisuwa duk suka yi carko-carko, don tun lokacin da ya ƙarasa wurin Rakiya suka saki baki da hanci suna bin su da kallo. Wasu su ce ta mallake shi, wasu kuma su ce mahaifinta ne ya mallake mata zuciyarsa, shi ya sa yake mutuwar sonta ya gagara rabuwa da ita.
"Hasan kai muke jira fa."
Kawu Sani ya furta, ganin Inna ta yi tsaye a gabansu ya sa shi cewa.
"Lafiya dai Hasan ko da wani abu?"
Cikin sauri Hasan ya ce, "A'a babu komai mu je Kawu." Daga haka ya wuce suka fita da shi, sai dai har ya kai soro yana jin gunjin kukan da Rakiya take yi mai tsuma zuciya. Inna kuma ta koma ta zauna ƙawayenta suka cigaba da ƙus-ƙus suna zuga ta. Cikin lokaci ƙanƙani aka sallaci Fatihu aka kai shi makwancinsa, da yake rasuwar ƙaramin yaro ce daga mutanan ƙofar gida har matan cikin gidan ba su wani daɗe ba kowa ya watse sai tsirarun ƙawayen Inna da suke shirin ganin ƙwal uwar daka.
BAYAN SALLAR ISHA'I
Kawu Sani, Inna, Malam Hasan da Rakiya ne zaune a ɗakin Inna. Kusan kowannansu fuskarsa a haɗe take babu walwala, Kawu Sani ya dubi Malam Hasan ya ce.
"Idan na fahimce ka Hasan, tun da har zaman can ya gagara za ka dawo nan gidanka wanda ka gada daga wurin mahaifinka?"
Malam Hasan ya gyaɗa kai ya ce, "Kawu a can ɗin ne ba a samun cinikin faskaren sosai, dakon da nake haɗawa da shi yanzu sai a hankali, shi ya sa ma na yanke wannan shawarar ta mu dawo nan gida."
Kawu Sani ya dubi Inna da ta cika fam ya ce, "Kulu kin ji abin da Hasan ya ce ko? Da ma kuma wannan gidan kin san gidansa ne da ya gada a wurin mahaifinsa. Don haka zai dawo tare da iyalinsa, idan na sake na ji wata magana marar daɗi daga gare ki wallahi ranki sai ya yi mummunan ɓaci."
Sai da Inna ta furzar da iska mai zafi sannan ta ɗago ta ce, "Na ji duk abin da ka faɗa Yaya, amma kuma ni ma ina da sharaɗi."
Dam! Ƙirjin Rakiya da na Malam Hasan ya buga kusan lokaci ɗaya, Kawu Sani ya dube ta yana karantar yanayinta ya ce.
"Muna jin ki."
"Ka yi haƙuri Yaya ba rashin kunya zan yi maka ba, amma dai Hasan ɗana ne. Kuma ni da kai ba ma samun kowacce irin matsala sai a sanadiyyar matarsa. Amma ƙiri-ƙiri an shanye..."
"Kulu ba na san ƙananan maganganunki marasa lissafi."
Kawu Sani ya katse ta a ɗan tsawace, wani abu ne ya sake tokare Inna. Ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce.
"Sharaɗina mai sauƙi ne Yaya, don gaskiya ba zan zuba ido rayuwar Hasan ta ƙare babu 'ya'ya ba. Duk cikin 'yan'uwansa shi kaɗai ne bai samu wani cigaban ku zo mu gani ba, ga Gali nan tare suka yi aure 'yarsa Suwaiba mai shekara goma har samari sun fara tsayar da ita. Don haka na yanke shawarar a wannan karon sai ya auri Zuwaira." Da wani irin firgici Rakiya da Malam Hasan suka ɗago suna kallonta cike da zallar tashin hankali.
GIDANSU FAUWAZ
Jim Abba ya yi yana nazari, cike da gamsuwa da shawararta ya ɗago ya ce.
"Maganarki a kan hanya take Tani, domin a makarantar allo ne kaɗai zai samu tarbiyyar da muke buƙata tun da ya riga da ya raina mu. Amma ban da lalacewa ta yaya yaro kamar Fauwaz da bai wuce shekara goma zuwa sha biyu ba har ya fara bin dare yana yi mana ɗauke-ɗauke."
Tani ta saki ajiyar zuciyar farinciki, amma sai ta ɓoye jin daɗinta ta aro fuskar damuwa ta lulluɓawa fuskarta ta ce.
"Shi ne tashin hankalin, amma idan aka kai shi makarantar allo zai koyi neman na kansa har ya iya tsayawa da ƙafarsa. Ka ga a can bai ɗauki na wani ba ballantana ya janyo mana magana, amma matuƙar muka cigaba da zama da shi a haka har 'yar uwarsa sai ya koyawa."
Abba ya yi zaraf ya ce, "Wannan gaskiya ne Tani, wallahi shi ya sa nake ƙaunarki. Saboda kina da hangen nesa da sanin ya kamata." Tani ta saki murmushin jin daɗi, sannan ta cigaba da ɗora shi a kan shawarwarin da zuciyarta take saƙa mata wacce take gani ita ce hanya mai ɓille mata.
Hawaye bibbiyu ne suka shiga sintiri a saman fuskar Fauwaz, a hankali ya ja ƙafa ya shiga wurin Abida da har lokacin take cikin mawuyacin hali. Ba shi da wata mafita, domin bai san kuma abin da zai yi mata ba. Don haka ya rungume ta ya fashe da kuka yana jin kewar mahaifiyarsa. Jikinta zafi ya ji shi zau kamar wuta, bakinta yana rawa cikin sanyin murya ya ce.
"Yaya... mutuwa... zan yi."
Girgiza kansa ya yi cikin kuka ya ce, "Ba za ki mutu ba Abida, da safe zan sai miki magani da kudun da na samo."
Idanunta a lumshe suke don ko iya buɗe su ba ta yi, ta ɗago hannu tana laluben fuskarsa. Da sauri ya riƙo hannun ya ce, "Me kike so Abida?"
"Ya... ya... ba na son na mutu na bar ka a wurin Aunty, yanzu Abba ya daina sonmu."
Fauwaz ya kwantar da kansa a fuskarta ya ce, "Ba za ki mutu ba kin ji Abida, Abba kuma ba daina son mu ya yi ba Aunty ce take faɗa masa laifinmu. Shi kuma duk abin da ta faɗa sai ya yarda da shi.
"Zan sha ruwa."
Ta furta masa a galabaice, sai da ya kwantar da ita sannan ya miƙe da sauri ya ɗebo mata ruwa. Ta sha ruwan sosai, ragowar kuma ta ce ya shafa mata a jikinta don ta ji daɗi. Cikin hukuncin Ubangiji ya ji zafin jikin ya ragu da ya zuba mata ruwan, don haka yana zaune yana gyangyaɗi shi da ita bacci ya ɗauke su, ba shi ya farka ba sai da aka fara kiran sallar asuba.
Lokacin da ya tashi idon Abida biyu, a wannan karon jikinta babu zafi sosai. Sai dai numfashinta da take fitarwa sama-sama, sai da ya yi mata sannu ta amsa a hankali sannan ya miƙe domin ya ɗauro alwala don ya tafi masallaci. Har ya je bakin ƙofa ta ɗaga masa hannu, don yadda numfashinta yake fita ya sa ta gagara furta sunansa da ƙarfi.
"Yayy... yaya."
Ta furta a sarƙe ganin har zai fita bai ganta ba, da sauri ya koma ya ce.
"Ga ni Abida me kike so?"
"Na yi mafarki... da Umma, ta ce... ka kusa daina wahala... da ni."
Ta furta a wahalce, sai ta cigaba da cewa.
"Ta... kuma ce na gaishe ka."
Murmushi mai sauti Fauwaz ya saki cikin jin daɗi ya ce, "Allah da gaske Abida? Na ji daɗi sosai, ni kuma tun da Umma ta rasu sau biyu na taɓa mafarki da ita."
Murmushi ta sakar masa, sai ya sake miƙewa zai tafi masallaci ta sake riƙo hannunsa.
"Yaya ina son... na yi kuɗi... don mu koma wani gidan... Aunty ta daina ganinmu."
"In Shaa Allahu idan na girma na samu kuɗi zan gina mana gida mu koma can."
Ya furta mata kalaman har cikin zuciyarsa, sai a lokacin ya fita daga ɗakin ya je ya ɗaura alwala. Yana gama alwala ya ga mahaifinsa ya fito shi ma, babu wanda ya yi wa wani magana har suka fita. Suna hanyar masallaci Abba ya ce.
"Ya jikin Abidan?"
Kamar Fauwaz ba zai amsa ba, sai ya danne zuciyarsa ya ce.
"Da sauƙi."
Daga haka suka ƙarasa masallaci, sai da aka idar da sallah Fauwaz ya jima yana yi wa Abida addu'ar Allah Ya ba ta lafiya sannan ya fita. Kai tsaye wani ƙaramin asibiti ya nufa da ke Unguwa Uku da ƙafarsa, har lokacin da ragowar duhu a gari don haka yawancin babban titin Na'ibawa babu ƙananan motoci sosai sai manya. Kasancewar da ƙafa yake tafiya lokacin da ya ƙarasa Unguwa uku gari ya yi tangaran har rana ta fito, ƙaramin asibitin na kuɗi mai suna Farha Clinic ya shiga. A reception ya samu wata mata wacce da alama ba bahaushiya ba ce, sai da ya gaishe ta sannan ya miƙa mata kuɗin hannunsa gabaɗaya sannan ya ce.
"Don Allah magani za ki ba wa ƙanwata, tana zazzaɓi sosai. Sannan mamana kafin ta mutu ta taɓa kai ta asibiti aka ce ƙodarta na ciwo ban sani ba ko ciwon ne ya tashi."
Yadda yake maganar za ka fahimci kalaman daga zuciyarsa suke fitowa, sai dai da yake ba ta jin hausa sosai ya sa ta kira wani abokin aikinta wanda ya kasance bahaushe. Matashi ne siriri, fuskarsa a zagaye da baƙin gashi. Fari ne fat sai dai yana da ɗan ƙaton kai, sai da ya gama sauraronsa ya ce.
"Ina mamanku ko babanku?"
Muryarsa tana rawa ya ce, "Mamanmu ta rasu."
"Babanku fa?"
Ya sake jefa masa tambaya, ya lura da sauyin fuskarsa, sai ya kawar da tambayar da ya yi masa ya ce.
"Likita don Allah ku ba ta magani tana jin jiki sosai, ko kuɗin ba su kai ba wallahi zan yi gwangwan na cika sauran." Tausayin Fauwaz ya kama shi, sai ya dafa kafaɗarsa ya ce.
"Abokina nan asibiti ne, asibiti kuma ba sa bayar da magani kai tsaye har sai sun binciki marar lafiya, an yi masa gwaje-gwajen da ya dace sannan likita ya rubuta masa magani. Ka je gida ka samu wani babba ku kawo ta asibiti, idan likita ya duba ta sai ya ba ta maganin da ya dace ka ji."
Tun bai dire kalamansa ba idanun Fauwaz suka ciko da ƙwalla, cikin damuwa ya gyaɗa kai don idan ya ce zai amsa masa kuka zai iya ƙwace masa. Ya karɓi kuɗin da ya ba su sannan ya juya ya tafi zuciyarsa cike da ƙuna, yana kuma fargabar halin da zai sake samun ta a ciki.
A ƙasa ya ƙara komawa har Na'ibawa, har zai wuya 'yan lemo ya hango kemis ɗin Maman Junior tana ƙoƙarin rufewa don ya lura da alama abu ta ɗauka domin ba ta buɗewa da safe.
"Maman Junior a ba ni magani."
Ya furta yana miƙa mata kuɗin hannunsa, cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce.
"Wone yiri magani?"
"Ƙanwata ce take zazzaɓi, kuma kwanaki an ce ƙodarta tana ciwo."
Zazzaɓin da ya ambata ta fi riƙewa, saboda yau da gobe da ake yawan sayen maganin zazzaɓi da sauran gama-garin cutuka a wurinta. Kemis ɗin ta buɗ ta shiga, sai ta haɗo masa maganin zazzaɓin maleria ta miƙa masa ragowar canjinsa. Gudu-gudu sauri-sauri a haka ya ƙarasa layinsu, tun daga farkon layin ya hango tsirarin yara a ƙofar gidansu.
"Ikon Allah Ya wuce gaban komai, shekaran jiya fa Abida suna tare da Sumayya da ta gaishe ni ta ce min aikenta aka yi. Wai ita ce yau ta amsa kiran mahalicci, koico rayuwa tsakaninta da mahaifiyarta shekara guda kenan."
Kalam maƙociyarsu da take shirin shiga gidansu suka daki kunnuwansa, waɗanda suka yi daidai da bugun zuciyarsa wacce take barazanar tarwatsewa.
Share Pls
Ummou Aslam Bint Adam 🌚
***