SHAFI NA BIYAR
by @ameeraadam
*GAMMON RAMA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ba tare da izinina ba.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
***
SHAFI NA BIYAR
A hargitse ya wurgar da ledar hannunsa jikinsa yana rawa ya ƙarasa ya riƙe hannun matar ya ce.
"Umman Sumayya wace ce ta mutu?"
Sototo ta yi tana kallonsa da mamaki, ganin haka ya sa shi girgiza hannunta yana ƙara tambayarta. Don haka ta ce.
"Fauwaz wai kana nufin ba ka san Abida ta rasu ba? Ina ka je ne?"
Bai jira ta dire kalamanta ba ya faɗa cikin gidan a guje, ita da ragowar matan da ke tsaye suka bi shi da kallon tausayi.
Kai tsaye ɗakinsu ya shiga, sai dai yana shiga ya hango katifarsu da kayan da ya fita ya bar Abida da su a jikinta. Da wani irin sanyin jiki ya shiga, don har lokacin zuciyarsa wasu-wasin abin da kunnuwansa suka ji take yi.
'Abida ba ta mutu ba, ɗazu fa na fita na bar ta a wurin nan.'
Zuciyarsa ta raya masa, amma sai ɗaya tsagin zuciyar tasa ya ankarar da shi.
'Idan ba ta mutu ba tana ina? Shin Umman Sumayya za ta yi maka ƙarya ne?'
Cikin sauri ya fita daga ɗakin, kai tsaye ɗakin Tani ya shiga. Daga can jikin bango ya hango Goggo Jamila ƙanwar mahaifinsu tana kuka, sai Tani da ke lungu tana sharɓar kuka waɗansu kitika-kitikan ƙawayenta suna rarrashinta, waɗanda sune suke sake ɗora Tani a duk turbar da take kai.
"Kaico mutuwa! Yanzu shi kenan Abida ta tafi, yanzu ko kallon Fauwaz na yi dole hankalina ya dinga tashi. Yaran nan kullum suna tare, ta ina zai fara jure rashinta."
Tani ta furta cikin kururuwa, ilahirin mutanen da ke ɗakin suka bi Fauwaz da kallon tausayi. Wani abu ne ya tokare masa maƙoshi, sai kuma ya ji wani irin sanyi tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa. Da ƙyar ya iya jan ƙafarsa ya fita daga ɗakin duk da ya ji Goggo Jamila tana ƙwala masa kira.
Yana fita ƙofar gida ya ga Sumayya ƙawar Abida tana kuka, tana ganinsa kukanta ya ƙaru ta ce.
"Yaya Fauwaz wai shi kenan ba zan sake ganin Abida ba? Shi kenan mun daina wasa da su 'yar gala-gala?"
Motsa bakinsa ya shiga yi sai dai ya gagara furta koda kalma ɗaya, da sauri ya wuce ta ya nufi maƙabartar cikin sauri da yake a cikin unguwarsu take, yana fatan ya ga koda gawar Abida ce. Sai dai yana shiga ciki ya hango mutane suna fitowa, bai fasa tafiya ba har suka haɗu a hanya. Mahaifin Sumayya ne ya ce, "Fauwaz ina ka shiga tun ɗazu ana ta nemanka?"
"Hmmm zai wuce ya tafi yawon banza, tun da shi ya saka a gaba. Me ka zo yi maƙabartar? Ai da ka yi zamanka a can ba sai ka zo ba."
Abba ya furta yana yin gaba, ba tare da ya jira cewar Fauwaz ba. Yawancin mutane wuce shi suka yi, sai tsiraru da suke yi masa ta'aziya.
Zannur abokinsa ne ya dafa shi ya ce, "Ka yi haƙuri Fauwaz, mu ƙarasa ka yi mata addu'a ba."
"Me ya sa ne Zannur? Me ya sa rayuwa ta juya mini? Me ya sa duniyar ta yi mini zafi? Na rasa Umma a daidai gaɓar da ban zata ba, ga shi yanzu mutuwar Abida ta shammace ni. Me ya sa Abba ba zai fahimci halin da nake ciki..." Kuka mai tsuma zuciya ya ƙwace masa.
"Saboda kowanne bawa akwai launin ƙaddarar da ke bibiyarsa, taka a haka ta zo maka. Ina fatan za ka yi addu'ar Allah sa haka ne mafi alheri. Yanzu mu je ka yi mata addu'a."
Zannur ya furta yana jan hannunsa, cikin kuka Fauwaz ya ce.
"Ina jin kamar ba zan iya zuwa na ga kabarin Abida ba."
"Za ka iya, domin addu'arka tana da muhimmanci a gare ta."
Da tausasawar Zannur Fauwaz ya ƙarasa gaban kabarin Abida, sai da ya ci kuka mai isarsa sannan ya kwarara mata addu'a. Tsakanin kabarin mahaifiyarsu da na Abida babu tazara sosai don haka ya ƙarasa ya yi wa mahaifiyarsu addu'a suka fito daga maƙabartar. Koda suka ƙarasa gida zaune ya yi a ƙofar gida, komai da kowa ya fita daga rayuwarsa. Domin ji ya yi rayuwar ta ishe shi, har fata yake yi ina ma ajalinsa ya riske shi domin ko kaɗan gani yake ba zai iya jure rashin Abida ba. Yana daga nesa yana hango mahaifinsa yana ta karɓar gaisuwar mutane. Yadda yake haba-haba wurin karɓar ta'aziyya ya sa shi tuna mahaifinsu na baya da ke bakin ƙoƙari wurin ganin ya kula da damuwarsu. Don a yanzu gani yake kamar an canza musu shi, haka aka cigaba da zaman makoki dangin mahaifinsa suna lallashinsa da ba shi baki.
A cikin waɗannan kwanakin rayuwar ta yi masa sauƙi a fanin kyara, hantara da ƙalubalen da yake fuskanta a ɓangaren Tani da mahaifinsa. Sai dai ji yake da za a dawo masa da Abida da ya gwammaci ya cigaba da zama a cikin ƙuncin rayuwar da yake ciki. Wani babban abin da ya ɗaure masa kai da Tani yadda take haba-haba da shi, har idan aka gama girki take aikawa a kira shi, ta sa a ba shi nasa daban wai ya ci ya ƙoshi kada ya zauna da yunwa. Sai dai hakan ba ƙaramin sake hura wutar ƙiyayyarta ya yi a zuciyarsa ba, don haka a kodayaushe ta yi masa maganar abinci kalma ɗaya yake furta mata ya ƙoshi. Su kuwa dangin Abba ban da farinciki babu abin da suke yi, don Goggo Jamila cewa ta yi tabbas Fauwaz ba zai yi maraici ba.
Ranar sadakar bakwai da safe, Abba yana zaune bayan da aka gama addu'ar bakwai kira ya shigo wayarsa. Saboda haniyar mutane sai da ya fita daga cikinsu ya koma bakin masallacin da ke kallo su, sannan ya ɗauka cikin sallama. Ba a iya amsa masa ba, sai jawaban tashin hankalin da aka rattabo masa. Tun bai gama wayar ba, ya zame hular kansa yana faɗin.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!"
Shiru ya yi ya cigaba da sauraro har aka gama jawabin aka yanke kiran, daɓar ya zauna a kan dandamalin da ke gaban masallacin cikin firgici da tashin hankali ya ce.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel! Allahumma ajir ni fi musibati, wa aklifni khairan minha."
Yana gama faɗar haka ya yanke jiki ya faɗi.
KAWU SANI
Murmushin takaici Kawu Sani ya saki, Inna ta sake tsuke fuska don a wannan karon ta ci alwashin dole Malam Hasan ya bi umarninta.
"Ina ce wannan tsohuwar magana ce Kulu? Ba tun kafin Zuwaira ta yi auren farko aka yi maganar ba yaron nan ya ce ba ya yi mata son aure sai na 'yan'uwantaka?"
Kawu Sani ya wurga mata tambaya, Inna ta cure baki wuri ɗaya ta ce.
"Haka ne."
Kawu ya ce, "To a yanzu ma babu ita..."
"Don Allah ka yi.haƙuro Kawu, Baban Fatihu zai aure ta a wannan karon."
Rakiya ta yi ƙarfin halin furta haka, wani irin kallo Malam Hasan ya wurga mata cikin wata irin murya ya ce, "Ni na furta miki haka Rakiya?"
Rakiya ta girgiza kai sannan ta ce, "A wannan karon matuƙar ba ka auri Zuwaira ba ni ma na gama zaman aure da kai."
A wannan karon shiru ɗakin ya yi, Kawu Sani ya numfasa ya ce.
"Ka ji abin da matarka ta ce?"
Gyaɗa kai Malam Hasan ya yi sannan ya ce, "Na amince zan aure ta."
Rakiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci tana jin kishin mijinta, domin idan ta ce ba ta ji kishin kalamansa ba ta yaudari kanta. Amma ta san hakan shi ne kwanciyar hankalinsu gabaɗaya, don ba za ta taɓa manta tarzomar da suka sha a shekarun baya ba.
"AlhamduLillah! Ma Shaa Allah, Allah Ya yi maka albarka Hasan. Ubangiji Ya haɗa kan iyalinka."
Kawu Sani ya furta sannan ya mayar fa kallonsa wurin Inna ya ce. "Kada na ji ko na ga wata fitina ta ɓullo daga wurin Zuwaira, domin ke da ita duka bakinku ɗaya." Inna ta amsa masa zuciyarta fes don ta san ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli ya ci riba.
Zuwaira tun da ta ji maganar aurenta da Malam Hasan ta shiga firirta da feleƙe, sai dai duk abin da take yi ko kaɗan Rakiya ba ta nuna mata alamar ta fahimce ta na. A cikin kwana biyun da suka yi tsangwamar da Inna take yi mata ta yi sauƙi, sai dai duk wanda ya zo gaisuwa sai ta ji wata mummunar magana daga gare shi wacce za ta sosa mata rai. Ana cikin haka har Malam Hasan ya koma ya kwaso musu kayansu, wanda ya tabbatar mata da Kawu Sani ne ya ba shi kuɗin ɗawainiyarsu.
Ɗakunan da ke cikin gidan ciki da falo-falo ne guda biyu, sai falle-falle guda biyu. Ciki da falon ɗaya su Rakiya suka ɗauka, sai Inna ta haɗe kayanta a ciki da falo ɗaya ta ce idan an ɗaura aure Zuwaira ta ɗauki falle-falle guda biyu. Satinsu ɗaya da komawa Malam Hasan ya kama awakinsa da Inna take yi masa kiwo guda biyu ya sayar, sai suka rage saura tinkiya ɗaya da rago ɗaya. Da wani kaso daga cikin kuɗin ya biya sadakin Zuwaira, ragowar kuɗin kuma ya kafa jarin turare irin wanda ake yawo da shi a kwando ana sayarwa da kayan yari na cikin glass.
Yadda Zuwaira take rawar kai abin ba ƙaramin ba wa Rakiya mamaki ya yi ba, saboda wasu kalaman da abin da take yi sam ba su dace a gaban Inna ba. Amma sai ta ga ita Inna ko a jikinta, a daren ranar Malam Hasan bai shiga gidan ba sai bayan sallar isha'i. Hannunsa ɗauke da kwandon turarensa, ɗakin Rakiya ya shiga ya same ta zukuɗum tana tunani.
"Rakiya ba za ki daina tunanin nan ba? Ko kina son ki dinga ɗaga mini hankali idan na fita."
Malam Hasan ya furta cikin damuwa, ganin haka ya sa ta saki murmushin yaƙe ta ce.
"Tunaninka nake yi fa ba na Fatihu ba."
Ya ɗan haɗe fuska cikin wasa ya ce, "Kina tunanin ɗanki dai."
Ta saki murmushin yaƙe ta ce, "Har abada ba zan daina tunanin Fatihu ba."
"Yanzu dai ba wannan ba, ga kayan da zan fara saidawa. Ki saka mini albarka da bakinki mai albarka."
Ya furta yana miƙa mata kwandon turaren da glass ɗin yari, fara'arta ce ta faɗaɗa. Cikin jin daɗi ta shiga kwarara masa addu'a, sai da ya gama amsawa sannan ya ce.
"Zuba mini abinci."
Hararar wasa ta yi masa ta ce, "Kai da amarya take jiranka, ko ka manta ne?"
Guntun tsaki ya saki, yana jin wani tsantsanin Zuwaira.
"Ni fa na gaji da kara tun da ba ku san zuru ba, na ga alamar idan na yi shiru sai ta gama da kai tukunna."
Suka ji an furta a tsakiyar kansu, a tare suka waiga suka ga Zuwaira riƙe da labule fuska a murtuke.
"Mene ne haka Zuwaira?"
Malam Hasan ya furta, kamar jira take yi ya dire ta ce. "Kwanana na biyo, tun da na ga ana ƙoƙarin cin amana ta. Don ma dai a banza abin yake wai an tsikari kakkausa, tun da ba iya ƙyanƙyashe ƙwan take ba..."
Tass! Malam Hasan ya ɗauke fuskarta da mari, sannan ya nuna ta da yatsa rai a ɓace ya ce.
"Idan ganganci ya sake biyo dake ta cikin ɗakin nan sai na tattaka ki." Da sauri Rakiya ta sha gabansa ta ce.
"Haba Abban Fatihu, me kake yi haka?"
Yana shirin ba ta amsa Zuwaira ta fita da sauri tana sakin kuka tamkar wacca aka ba wa saƙon mutuwa.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Ka ga za ka janyo mini ko? Rakiya ta furta, Malam Hasan ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Kada ki damu don Allah, na sanki sarkin tsoro ce."
"Hasan! Hasan! Za ka fito ne ko kuwa sai an ba ka izinin fitowar?"
Inna ta furta cikin ɗaga murya, kusan lokaci ɗaya Rakiya da Malam Hasan suka dubi juna. Suna nan zaune suka ji an ɗaga labulen ɗakinsu.
"To sake shi baƙar munafika, tun da ba kwananki ba ne sai ki ba shi dama ya yi gaba." Inna ta faɗa tana wurga wa Rakiya harara.
"Ga ni zan fito yanzu."
Malam Hasan ya furta, tun bai gama rufe baki ba Inna ta nuna masa hanya ta ce.
"Fita mu je na ce maka, shashasha bawan mace."
Babu yadda ya iya, haka ya bi bayan Inna jiki a saluɓe, don ba ya son ya sake wata maganar ya ja wa Rakiya wani sabon zagin ko baƙar magana.
Tamkar raƙumi da akala haka ya bi bayan Inna har suka fita tsakar gida, ɗakin Rakiya ta nuna masa ta ce, "Maza ka shiga wurin amaryarka, idan ka ga dama kada ka taɓuka abin arziki. Sakarai kullum kana can wurin da babu ƙaruwa ballantana mamora."
Jiki a sanyaye ya nufi ɗakin Rakiya bakinsa ɗauke da sallama ciki-ciki, yana shiga Rakiya ta yi farat ya tare shi cike da kissa da kisisina. Tsaye Malam Hasan ya yi yana kallon ikon Allah, don rashin kunyarta ba ƙaramin mamaki take ba shi ba. Ya san dama ba za a taɓa haɗa kunyar budurwa da ta bazawara ba, amma kuma ko kaɗan bai fuskanci haka daga wurin mahaifiyar Fatihu ba, domin ita ma a bazawara ya aure ta.
"Barka da zuwa angona."
Zuwaira ta furta tana dafa ƙirjinsa, mamaki ne ya sake mamaye shi da ya ga ta ware kamar ba ita ce ta fita tana zabga ihu daga ɗakin Rakiya ba. Bai amsa mata ba, sai gefen gado da ya zauna yana haɗe fuska. Ganinsa hannuwa suna dukan cinya ya sa ta wurga masa tambaya, kwata-kwata ya manta da sayen wani naman kazar amarci. Don wannan auren ya yi ne kawai da zummar ko Rakiya za ta samu salama a wurin Inna. Abincin da Inna ta girka Zuwaira ta miƙa masa, kamar ba zai karɓa ba sai kuma ya ci loma biyu ya ce ya ƙoshi. Zuwaira da kanta ta dinga jan Malam Hasan cikin kissa da kisisina har mai afkuwa ta afku a tsakaninsu. Don haka koda gari ya waye ko ƙofar ɗaki Zuwaira ƙin fitowa ta yi, wai ba ta jin daɗin jikinta don a dole ta nuna wa Rakiya wani abu ya gifta a tsakaninsu. Da safe koda Malam Hasan ya fito zai shiga ɗakin Rakiya fir Inna ta hana shi, a cewarta ba kwananta ba ne don haka ba ta da haƙƙi a kansa ranar. Yana ji yana gani ya tafi tallan turaren, don kwandon turarensa ma sai Inna ce ta ɗauko masa.
Sannu a hankali zaman Rakiya da Zuwaira ya fara sauya salo duk da dama ba zaman daɗi suke yi ba. Sai Zuwaira ta ɓullo da duk ranar girkin Rakiya tun rana za ta fara kwanciya ta ce ba ta da lafiya, idan yamma ta yi sai ta haye gado ta rufa da bargo. A kan dole idan Malam Hasan ya dawo Inna take tilasta masa kwana a wurin Zuwaira. Saboda wani lokacin cewa take ana tsorata ta, ko ta ce motsi da giftawar mutum take gani. Tun yana ɗaukar abin kamar gaske har ya fara fahimtar makirci ne, damuwarsa ta ninku musamman da yake buƙace da matarsa Rakiya. Don a ƙalla ya kai sati uku ƙwarara bai kwana a ɗakin Rakiya ba, ko da rana bai isa ya shiga ɗakinta ba sai Inna ta fara yi musu masifa. Watarana Inna ta fita unguwa, yana zaune a bakin kasuwa ya ga wucewarta. Farinciki ne ya lulluɓe shi, don haka cikin sauri ya ɗauki kwandon turarensa ya wuce gida. Ya ci sa'a Zuwaira ba ta tsakar gida, don haka ya faɗa ɗakin Rakiya. A kwance ya same ta idanunta suna kan silin, da yake ta yi zurfi a duniyar tunani ko motsinsa ba ta ji ba. Sai da ya kira sunanta sannan ta kalle shi, da sauri ta miƙe tsaye kamar ta ga sabuwar hallita. Malam Hasan ya zuba mata idanu ganin lokaci ɗaya ta zabge duk ta rame, a hankali ya fara takawa wurinta Rakiya ta matsa da sauri ta faɗa jikinsa sai ta ji kuka ya ƙwace mata. Kukan da ta ɗauki kwanaki tana son zubar da hawayensa ba ta samu sukuni ba, tausayinta ya ji har cikin ransa. Ya saka hannu yana bubbuga bayanta, cikin so, ƙauna da tausaya ya ce.
"Ki yi haƙuri farincikina."
Sai da ta share hawayenta ta ce, "Ka fita kada Inna ta dawo."
Bai iya amsa mata ba, sai janyo ta da ya yi ya sake riƙe ta tsam. Tana son ƙwace kanta amma ta kasa, ya sunkuya saitin fuskarta ya furta.
"Na yi kewarki, kullum da tunaninki nake kwana nake tashi. Ban san ya zan ɓullo wa Inna ba."
"Mu cigaba da haƙuri, watarana sai labari."
Rakiya ta furta a sanyaye, don shi kansa ba ƙaramin tausayinsa take ba. Girgiza mata kai ya yi ya ɗago da fuskarta ya ce.
"Ba zan iya ba Rakiya, saboda ina shiga haƙƙinki. Ya zama dole na nemar mana mafita."Ba ta amsa masa ba, ya cigaba da aika mata kalaman soyayya masu kassara jiki, a hankali yake aika mata da saƙon soyayya mai cike da kewarta. Rakiya mace ce da ta san kanta, don haka ta shiga mayar masa da martani. Kowannensu sai da ya nuna wa ɗan'uwansa ya yi matuƙar kewarsa, don yadda ta ga Malam Hasan ya birkice mata sai ka yi tsammanin babu mace a kusa da shi duk tsawon kwanakin da suka ɗauka.
"Ka tashi ka gyara jikinka ka fita lokaci yana tafiya."
Rakiya ta furta masa, ga mamakinta sai ji ta yi hawaye ya gangaro daga idonsa.
"Me ya faru kuma?"
Ta tambaye shi muryarta tana rawa, don ta fahimci dalilin hawayensa.
"Ina sonki matata, ina ƙaunarki farincikina. Idan na fita yanzu ban san lokacin da zan sake jin ɗuminki ba, a cike nake da kewarki zuciyata ina jin kamar kada na matsa daga kusa da ke."
Yadda yake magana ne ya kashe mata jiki, amma gudun kada a samu matsala ya sa ta shiga tausarsa. Suna nan maƙale da juna suka ji sallamar Inna, tamkar waɗanda suka ga mala'ikan ɗaukan rai haka suka firgice lokaci ɗaya kowannensu gabansa ya shiga faɗuwa.
Tun shigowar Inna gidan ta hango takalmin Malam Hasan a ƙofar ɗakin Rakiya, don haka rai a ɓace ta ƙarasa ɗakin cikin masifa ta bankaɗa labulen ɗakin. Ta windon uwar ɗakin ta hango su da yake a gadon Rakiya a saitin windon yake. A kunyace su Rakiya suka ja zanen gado suka rufe jikinsu. Inna ta ja dogon tsaki cikin masifa ta ce.
."Ke dai wannan an yi jarabaiyar yarinya, yanzu don masifa da rana tsaka ma sai da kika yaudaro mini ɗa? Ki bar shi ya tafi nema amma kin kanainaye shi a ɗaki, wato kin samu dama na fita ko? To ka tashi ka fito ka je ka yi wanka ka fita nema, shashasha sai kace ba shi da wata matar don jarabar tsiya."
Inna ta yi furucin da ƙarfi, jin Hasan ya amsa ciki-ciki ya sa ta ce.
"Za ka fito ko sai na fito da kai da kaina?"
A kunyace Malam Hasan ya zura wata doguwar rigarsa ya fito, ya nufi banɗaki yana jin ɗacin ɓacin rai a zuciyatsa.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
***