SARTSE COMPLETE

27

by @legendspen

Ina shiga ciki na yi cikin ɗakina na kulle ƙofa nasa Sakata, yadda yake wannan saman ai tsaf ya kamani sai ya ɓallani. 

“Nana buɗe min ƙofa.” 

“Ka yi haƙuri dan Allah.” 

“Na ce ki buɗen ƙofa zaki zauna kina cewa na yi haƙuri?”

“Karka dake ni dan Allah.” 

“Bazaki buɗe min ba Nana, na buɗe da kaina sai na ɓaɓɓallaki.” 

Ba shiri na taso na buɗe ƙofar, na maƙale a jikin bango. Da iya ƙarfin shi ya kamo hannuna ya matse shi sosai, idanunsa har wani hayaƙi ne yake fitowa daga cikinsu. 

“Nana! Nana! Nana! Me ya sa kika shiga motar ɗan iskan can? Me ya sa ?” 

“Bakomai ka yi haƙuri dan Allah.”

“Har wani murmushi kika yi masa? Har ƙamshin turaranki ya ji, ya kama miki hannu ko?” 

Da sauri na girgiza kai. 

“A’a wallahi, ko kallona bai yi ba.” 

“Ni zaki yi wa ƙarya, sai na make ki.” 

Da sauri na runtse idona tare da maƙalewa a wajen ɗaya. 

“Ka yi haƙuri dan Allah.” 

“Me ya yi miki?” 

“Bakomai wallahi.” 

“Bazaki faɗan ba sai na sumar dake?” 

“Zan faɗa ma, zan faɗa ma wallahi.” 

“To faɗamin.” 

“Babu abinda ya yi min kawai ce min ya yi wai ni da kai mun fara hankali tun da har ina zuwa gida, sai kuma ya ce yanzu saura na makaranta na ce mai tom.” 

“Uban mene haɗinshi da ke da har zai ce miki saura makaranta, shi uban me ya kaishi unguwar Talakawan nan? Nana daga yau har Abada kar na sake ganin magana guda ɗaya ta haɗaki da Turaki, kin jini?” 

“Eyh! Na ji ka.”

“Shi kuma sai na ɗau mummunan mataki akansa.” 

Yana faɗin haka ya fice zuwa ɗakinsa ya barni anan, sai da na yi kuka na na gode Allah sannan na yi wanka na kwanta, dan yanzu Sardauna ba ko yaushe muke kwana tare ba. 

Washe gari na tashi da ciwon kai sabida kukan da na yi daren jiya, adaddafena haɗa masa shayi da soyayayyen biredi ya ci, har ya fita ya dawo ya kalleni. 

“Nana Har abada bake ba Turaki.” 

“Tom.” 

Ya sa kai ya fice, nasan dai asibitin su Bilkisu zai tafi, wai ashe ma ƙanin babanta ne ba shi da lafiya shine duk ya ruɗe, bai fi awa ɗaya sa fita ba ya kirani a waya wai ‘yan uwan Bilkisu zasu su yi mata jere acan part ɗin, ban ce masa komai ba bayan tom, ni a yanzu kalaman Yaya Rumaisa nake son zama na baje su a faranti na yi musu filla filla. Amma bansami damar hakan ba sabida kiran da Sardauna ya sake yi min akan lallai na yi wa ‘yan uwan Bilkisu abun taɓawa. Ta dole na tashi na shiga kwaɓa musu cup cake, bayan na yi na haɗa musu sa cincin, sabida bana son abun da zai wahalal da ni.

Wajen ƙarfe biyu na ji motoci suna shigowa nasan sune, hakan ya sa na ƙara gyara jikina na fito. Manyan matane masu kyau, gayu da ilimi, kowacce tafiya take cike da izza, sai na ji ma na raina kaina abun da na yi musu. Kowacce ta shigo zata ɗibi iska daga gabas ta watsa yamma, sai na zama kamar wata ‘yar aiki, dan ba wadda tabi ta kaina, hakam yasa na tattare jikina na koma ɗaki, sai da suka kammala na ji wata na cewa. 

“Ba mutane a gidan ne?” 

Fitowa na yi, tare da faɗin. 

“Gani.” 

“Ke kamar ba kya ganin mutane ne?”

Murmushi na yi sannan na ce. 

“Na gaisheku tun zuwanku, ganin kamar ba ku kula dani ba ya sa na shige nawa part ɗin.” 

“Ke ‘yar talakawa ‘yar mitsiyatan Yelwawa, ki iya bakinki nan baki ga mai kama da wacca zaki gayawa magana ba.” 

Wani irin ɓacin rai na ji ya ziyarce ni, wannan da ta yi maganar ba manta ta ba, ita ce ta ce danj ballagaza a lokacin da na je wajen Bilkisu, cike da ɓacin rai na ce. 

“Ko da na ke ‘yar mitsiyatan Yelwawan na sami ilimi da tarbiyar da nasan na girmama baƙo a duk inda ya same ni, kuma a ‘yar mitsiyatan Yelwawan nake da ƙimae da ‘yar masu kuɗin Takur zata nemeni da kanta.” 

“Ya isa.” 

Wata mata ta daka tsawa, sannan ta nuna yarinyar da ta yi maganar. 

“Subisha baku kyauta ba, Nana ki yi haƙuri.” 

Na yi mata murmushi, sannan na ce. 

“Bakomai Anty, har zaku wuce ne?” 

“Eyh, zamu wuce sai kuma mun dawo kawo amarya.” 

“Allah Ubangiji ya kawo ku lafiya, ga Snacks da ya ce ayi muku.” 

Na faɗa ina shigewa kicin, box uku na yi na snacks ɗin na ɗauko na kawo musu, tare da faɗin. 

“Gashi an gode, Allah Ya sanya alheri.” 

“Amin amin, ku ɗauka mu tafi.” 

Suna fita na koma ɗaki na kwanta, dan ni yanzu gidan ma gaba ɗaya ya daina min daɗi, na ƙagu ayi auren nan a gama hankalin Sardauna ya dawo jikinsa. 

Washe gari ta kama rana littinin, ranar suka yi football match, tsakanin familyn Ta Ambo da na su Bilkisu, ba Sardauna ya shigo gida ba sai wajen ɗaya saura na dare, lokacin har na yi bacci na farka. 

“Honey! Duk na yi busy al’amuran aure da wahala.” 

Iaa daga kwancen na yi mishi murmushi, sannan na ce. 

“Sannu ko na yi ma tausa?”

“Mene tausa Nan?”

“Massage.”

“Uhm, ai kema kin gaji Nana.” 

“Idan kana so ai sai na yi ma.”

“Ki huta kawai Sarauniyar mata Nana, uwar gidan Sardauna Ta ambo.” 

Wani daɗi na ji kamar na jawo shi ma haɗiyeshi, washe gari Talata suka yi wani party, tsakanin ‘yan gidan Ta ambo da ‘yan gidasu Bilkisu, ina daga gida amma nasan su kansu ‘yan uwa Sardauna sun fi farin da auren Bilkisu akan nawa, ranar kam sai bacci na yi na ƙyale Sardauna, dan ban san lokacin da ya dawo ba. 

Ranar Laraba suka tafi Abuja, zasu dawo ranar juma’a bayan anyi ɗaurin aure, duk irin hidimar da Sardauna ke ciki ba cikakken awa sai ya kirani. 

“Nana karki kula Turaki, karki kula wani namijn, ko su Ra’is.”

Shine kaɗai abinda yake faɗa da zarar ya kirani, na kira Hajiya awaya na ce mata dan Allah Yaya Radiya ta zo ta yani zama, a yanayin ina buƙatar wani a kusa da ni, Hajiya ta ce sai dai ta dinga zuwa tana yini idan dare ya yi sai ta tafi, ta dole na amince da hakan. 

A zuwan da Yaya Radiya take yi, ta kan ɗan bani ‘yan shawarwari akan yadda zan rayu da kishiyata, ba kowanne al’amuranta zan shiga ba har Sardaunan ma, na dinga kama kaina akansa a gabanta, na ja mutuncina. Haka dai ta dinga ba ni shawarwari. 

Ranar juma’a ƙarfe ɗaya aka ɗaura auren SARDAUNA DA BILKISU, a babban masallacin birnin tarayya na Abuja. Duk da Yaya Radiya da Yaya Rumaisa suna nan hakan bai hanani zubar da hawaye ba, Sardauna dai ya zama ba nawa ba ni kaɗai, ya zama namu mu biyu da wata, ɗakin Sardauna ya zama ba sirrina ni kaɗai ba, ya zama sirrinmu mu biyu, na yi kuka kamar raina zai fita daga baya kuma na haƙura na fawawwala komai. 

A daren juma’ar su ka dawo, amma Sardauna bai shigo, arzƙina ɗaya ina jin motsin Turaki dan baije Abuja ba kwata kwata, sai washe gari asabar Sarduana ya shigo, shima a gurguje ya zo yana shirye shiyen tafiya dinner ta yau. Bai ko tsaya ya ji yana ke ba, ya na rayu bayan tafiyarshi, ta dole na haƙura na sallama Sardauna, Allah Ya kaimu a gama bikin. 

Anyi gagarumar dinner ta gani ta faɗa, wacca gaba ɗaya jihar jigawa ta ɗauka, ko ina kaduba sune suke yawo, Malaika daga kano ta kira layina, ina ɗagaqa ta fara magana kamar zata hau ni da faɗa. 

“Nana ashe tun can da Sardauna ba sonki yake ba kika aureshi? Yanzu gashi duniya ta shaida a yanzu yake auren matar so.” 

Wani ƙululun abu ne ua tsayamin a raina, na fashe da wani irin kuka sannan na kashe wayar gaba ɗaya, mutane daman har jira suke wani abu ya faru su hau turama salan su ɗaga ma hankali, haka na yini ina kuka babu me rarrashina, ni dai har na yi bacci banga Sardauna ba, banji ɗuriyarsa ba. Haka na tashi da wani irin ciwon kai mai azaba, ko breakfast ban iya ba na watsa ruwa da ƙyar na kira Sardauna a waya akan banda lafiya, amma bai ɗauka ba sai na kira Yaya Rumaisa na sanar da ita, ba ta ce min komai ba rta kashe wayarta, can sai na ga ta turumin text da wata lamba DR NA’IMA DAƘAYYAWA. Tabbas a yanzu nake ƙoƙarin gano gaskiyyar cewa ‘yan uwa ‘yan uwa ne, duk daɗin da namiji yake baki bai ko rabi ‘yan uwa ba, duk da irin fushin da suke da ni, bai hana su zuwa gidana ba lokacin da nake cikin matsala, haka bai hana su ba ni taimako ba a lokacin da na buƙata. Lambar na kira bugu ɗaya aka ɗauka. 

“Salamu alaikum, ina kwana?” 

“Lafiya ƙalau Alhamdulillah.” 

Ta amsa muryarta a sake, sai da na gyara murya sannan na ce. 

“Ni ce wata da na taɓa zuwa wajenki, har kika yi min faɗa akan Low Bp, sannan na fara yi miki maganar haihuwa.” 

“Oh! Mr’s Ta Ambo Right?” 

“Eyh ni ce.” 

“Okay, me ya sake faruwa?” 

“Daman yau ne na tashi da ciwon kai da jiri sosai. Ko zama na yi jiri nake ji, shine na kira sister ɗina  kuma sai taban numberki.” 

“Ayyah! To mene matsalal Kina cikin damuwa ne ko?.” 

Sai kuma ta fara magana  cikin sanyin murya. 

“Tun a wancan lokacin na faɗa miki sakamakon gwajin jinin da muka yi miki ya nuna cewa hawan jinin ki ya yi ƙasa sosai, wato Low BP. Kuma shi ne yake kawo miki wannan yawan jiri da matsanancin ciwon kai da kike ji.”

Ji na yi idanuna sun sake yin nauyi,  na sauke wayar daga kunnena na kalle ta, ban ce uffan ba na sake mayar da wayar kunnena a cikin raina nake jin kamkar wani sabon nauyi ya sake danna mini ƙirji.

“Nana, ke fa yarinya ce ƙarama, mai ƙarancin shekaru.” Likitar ta ci gaba da magana, muryarta cike da gargaɗi.

 “A wannan ƙanƙanun shekarun naki, bai kamata kina yawo da Low BP irin wannan ba. Illar da zai yi miki yana da yawa; zai iya sanya ki yawan suma, ya raunana miki jiki, kuma yana iya shafar yadda jini yake kwarara zuwa ga ƙwakwalwarki da zuciyarki. Me yake damunki ne?”

Tambayarta ta na ji kamar ta soka mini mashi a zuciya. Me yake damuna? Sardauna ne... auren da zai ƙara ne... kishin da yake shirin cinye mini rayuwa ne.  Watsar da ni da ya yi. Amma sai na tsinci kaina da girgiza kai kamar ta na gani na, hawaye guda ɗaya ya subuce mini a kumatu.

“Dole ne ki rage saka damuwa a ranki, Nana,” ta faɗa cikin muryar lallashi. “Mata da yawa ba su sani ba, amma damuwa ita ce babbar makashiyar mace. Ki janye kanki daga duk abin da zai ɗaga miki hankali, ki huta, kuma ki rinka cin abinci mai gina jiki. Idan ba ki kula da kanki ba, babu wanda zai kula da ke ba, kin ji ni?”

“Eyh na ji.” 

“Yawwa.”

Sai kuma ta sauya salon maganar zuwa wani batu da ya fi komai fasa mini zuciya.

“Sannan akwai zancen rashin haihuwar da ku
Ika zo da shi a wancan zuwan. Ina so idan za ta yiwu, yau ko kuma gobe da safe ki daure ki zo asibiti mu ƙarasa dukkan gwaje-gwajen da suka kamata. Dole ne mu gano tushen matsalar da wurin da take, domin mu san matakin da za mu ɗauka, nasan yana ɗaya daga abunuwan da suke saki damuwa.”

Kalmar 'Rashin haihuw_ar' ta daki kunnena tamkar tsawa. Na ji wani irin jiri ya sake kwasata a kan kujerar. Rashin haihuwa shi ne dalilin da Sardauna ya dogara da shi zai kawo mini kishiya. Shi ne silar da iyayensa suka matsa masa. A take na ji dukkan gidan yana juya mini, maganganun Yaya Rumaisa na cewa na ajiye soyayyar Sardauna gefe na kula da kaina suka dawo mini daki-daki.

“Zan zo Likita... zan zo gobe Insha Allah,” na faɗa cikin dasasshiyar murya, ina ƙoƙarin haɗiye kukan da yake shirin kufce mini.

Legendspen
***