28
by @legendspen
Tun bayan gama wayarmu da Dr Na’ima na rasa me yake min daɗi, ta shi na yi na shiga ɗaki na ɗauko drugs ɗina na kwanaki na dawo falo, fridge na buɗe na samu ragowar cake na zo na zauna na tura shi da tea kamar ina cin ganyen darbejiya haka na tura shi, ina gamawa na ɗauki drugs ɗin na sha, ciki har da nasa bacci.
Banyi ƙwaƙwaran minti sha biyar da shan maganin ba bacci ya ɗauke ni, sai dai kuma banyi nisa da baccin ba na ji muryar Sardauna akaina, a hankali na buɗe ido.
Dishi dishi na fara ganinsa, sai kuma can naganshi tar.
“Wayyo Allah.”
Na faɗa yayin da nake ƙoƙarin miƙewa zaune.
“Nanaty mene yake damunki?”
Girgiza masa kai na yi kawai, ba tare da na ce mai komai ba.
“Ki yi haƙuri Nana dan Allah.”
Na sake girgiza kai, hawaye suka shiga zarya a a fuskata.
“Ya salam! Nana mene dan Allah.”
“Yanzu shikenan sabida zaka ƙara aure ka manta da ni? Ka watsar da ni ka manta akwai wata mata Nana a duniya?”
Ya kamo hannu ya matse su, sannan ya ce.
“Nana har abada. Babu abinda zan samu na manta da ke, na manta da hallacinki, ki yi haƙuri dan Allah.”
Ya sa hannu ya fara gogen hawayen, na kauda kai gefe na ci gaba da zubar da abuna.
“Nana dan Allah ki yi haƙuri, ki tuna yau fa wannan babin zai ƙare, zamu shiga sabon babi, sabuwar rayuwa, sabon zama Nana, ki bari mu mori wannan lokacin a matsayin na ƙarshe tsakanina da ke.”
Na ɗago na kalleshi, alamun bangane na ƙarshen da ya ce ba.
“Nana! Daga yau mun gama zama matsayin ni dake mu biyu kawai, mun zama uku, mun ƙara yawa Nana. Zanyi kewar hakan sosai da sosai.”
Na ji wani irin tausayin Sardauna, son sa ya sakw mamaye guntun ɓacin ran da nake ji, na kama hannunshi cike da soyayya.
“Sardauna ko mu ɗari ne a gidannan, ni taka ce kai nawa ne har abada.”
Ya yi murmushi, ya sa hannu ya ɗaukeni muka yi cikin ɗaki, muna shiga ya mai da hasken zuwa Dum light.
Ɗakin ya yi duhu, ƙanshin turaren wuta na ɗan kullum ya cika kowane lungu da saƙon ɗakin, yana tashi a hankali. Sardauna yana zaune a gefen gadon, yayin da ni kuma ya kwantar da ni akan gadon, amma na ɗora kaina a kan cinyarsa, yana wasa da gashin kaina cikin wani irin salo mai cire wa mace kowace irin damuwa.
Ya sauko da fuskarsa daidai tawa, idanunsa cike da wani irin kallo mai narka zuciya, ya kawo bakinsa dai dai kunnena ya raɗa mini cikin sanyayya muryarsa.
“Nana... kin san wani abu? Duk duniya babu macen da nake gani na ji numfashina ya tsaya sai ke. Wannan auren da za a yi, kaddara ce kawai ta iyaye, amma babu wata mace da za ta taɓa samun ko da rabin matsayin da kika taka a zuciyata ne. Son da nake miki, ya wuce tunanin kowa.”
Na ɗago idona na kalle shi, ina jin yadda duminsa jikinsa yake ratsa ni. Murmushi ya yi, ya sumbaci goshina sannan ya hawo kan gadon, ya kishingiɗe a jikin manyan matashin gadonmu, yayin da ya jawo ni jikinsa na kwanta luf, na ɗora kaina a kan ƙirjinsa, jikinsa ɗumi, ina jin yadda bugun zuciyarsa yake harbawa a hankali. Hannunsa ɗaya yana yawo a cikin gashin kaina, yana rarraba su a hankali, yayin da ɗayan hannunsa kuma yake shafa lallausan kumatuna da bayan yatsunsa.
“Kishinki nake yi, Nana. Kishinki nake yi ko da da iskar daren nan ne da take taɓa fatarki. Wani lokacin idan na rufe idona na tuna cewa nan gaba kaɗan zan rinka raba kwananki, har hakan yana sanya ni tsoro da fargaba. Na san ranar da ba zan kwana tare dake ba, ba zan iya baccin kirki ba, domin jikina ya riga ya saba da numfashinki da zazzafan duminki, Nana.”
Hannuna na hagu na ɗora a kan fuskarsa, ina shafa sajen sa da ya sha gyara, ina jin yadda dukkan jikina yake ɓari saboda kalamansa. Ya kama hannun nawa, ya zura yatsunsa a cikin nawa ya matse su da ƙarfi, sannan ya ce.
“Har yanzu ba zan taɓa mance ranar farko da na ganki ba. Nana kinsan ba ranar da na zo umguwarku na fara ganinki ba?”
Ya ƙarashe maganar yana kallon cikin idona, wanda zallan mamaki ya bayyana.
“Kin tuna wata rana da kuka je Manpower ke da Alhaji da wannan yayan naki a wajen taron nan? Kina sanye da fararen kaya, a lokacin kallo ɗaya na yi miki na ɗauke kai, amma Nana wata magana da kika yi ta ja hankalina gareki, haka kawai na ji ƙuruciyarki ta burgeni, kin iya tsokana, kin iya dariya, kin iya fari sa ido, sannan kin iya shiru. Fuskarki kamar ta jirirai da basu san komai ba sai rigima Nana, tafiyarki ta kamun kai da yadda kike kallon ƙasa, shi ne abun da ya fara sace mini zuciya. Na so na ƙyaleki amma sai na ji bazan iya ba, tun daga nan na fara bibiyarki, yadda kike rayuwa da komai Nana, a hankali kika fara shiga raina, har ta kai ko ina gida na kan iya tuna wasu ɗabi’unki na yarinta.“
Ya ƙara matso da ni jikinsa, yana shafa fuskata cikin soyayya, “Nana bansan ina son ki ko kishinki ba, sai ranar da kika nuna kin zaɓi ƙawayenki a kaina, Nana ranar duniya ta tsayamin zafi, na ji wani irin zafi a raina, a ranar na ji a raina ina so ki zama mallaki na nine kaɗai Nana.”
Ya rage tsayin muryarsa ta koma kamar raɗa, ya sumbaci gefen wuyana wanda ya sanya wani irin sanyi mai daɗi ya ratsa mini dukkan jikina, sai kuma ya ce.
“Ranar da na ji zai kin zama mallaki na ni kaɗai, ranar da nazo da hotonki family meeting, kowa yana gani ana bawa wancan mitsiyacin yaron Sardauna kallon da ya yi wa hoton, kallo ne mai nuna sha’awa, na ji wani zafi a zuciyata, kuma na ƙudirci cewar sai na kareki daga dukkan sharrinsa, sai na haramta masa ke har Abada Nana,ke tawa ce ni kaɗai, daga yau har abada Nana.”
Na ɗago idona waɗanda suka riga suka yi ja saboda shauƙin ƙauma, na kalli cikin kwayar idanunsa. Ya ƙara matse ni a jikinsa, yana shaƙat ƙanshin jikina tamkar wanda ke tsoron za a ƙwace masa ni. Murmushi ya yi, ya sumbaci lips ɗina a hankali.
“Nana sai bayan na aureki na ji ina da burin mallakarki har abada, sai dai ƙuruciyarki da take burgeni kin dage sai kin kawar da ita Nana.”
A hankali na ɗan zame jikina, sannan na ce.
“Ƙuruciyata kake so ba ni ba?”
“Nana ko bake nake so ba, ke tawa ce har Abada Nana, mallakar da na yi miki ta har abada ce, me yake kawo kishi Nana?”
“Sone.”
“To ina yi miki kishin da babu wata hallita da nake yi wa irin shi, abu mafi girma a zuciyata shine tsanar Turaki, to Nana kishin da nake yi miki ya zarci tsanar Turaki sau ba adadi a zuciyata.”
Na ji wani sabon shauƙi ya lilluɓe ni, kalaman sa kamar zuma suke malala a cikin jyjiyoyin jikina. Duk wata fargabar kishiya da nake ji ta gushe a wannan daren, na ji tamkar ni kaɗai ce mace a duniya.
“Don haka nake so ki kwantar da hankalinki, uwar gidana. Kewarki da zan rinka yi, ita ce zata riƙa addabar rayuwata a kowane minti. Babu wata mace da ta isa ta maye gurbinki.”
A cikin tsantsar daɗin baki da zafafan kalaman Sardauna, na mika masa dukkan ragamar rayuwata, har ina jin cewa ko da duniya zata tashi, wannan mutumin Sardauna nawa ne ni kaɗai.
***********
06:30pm
Zaune yake gefen gadon, ni kuma ina tsaye na gama sanya masa babbar rigarsa, haka hulal ma da kaina na yi masa karinta, ya fito fes kamar ango a daren aurenshi na farko. Duk wani jiri da ciwon kai da nake ji ɗazu, yanzu babu shi.
Muna nan zaune masu kawo amarya suka shigo, kallon kaina na yi a mudubi, na yi kyau na gaji da haɗuwa, lace ɗina dark blue ne da touch ɗin golden, ya yi matuƙar amsar jikina. Ɗikin doguwar rigar ya kwanta a jikina ɗas, na yi ɗaurina mai kyau na ɗora ƙaramin blue mayafi akaina ma zagayoshi ta ka faɗa, kunnena da hannu ɗankun zinare da Sardauna ya siya min ne. Sallama da na ji ana yi a ɓangarena, ya sa na fita zuwa falon, iyayen amarya ne da ita amaryar. Cike da ladabi na tare su tare da basu mazauni.
“To Uwar gida ga amarya mun kawo miki, muna fatan zaku zauna lafiya da juna.”
Na yi murmushina na ko yaushe, sannan na ce.
“Ni da Bilkisu kamar ‘yan uwa muke, in sha Allahu babu abinda zai biyo baya sai ɗimbin alheri, ‘yar uwa barka da shigowa.”
“Ma sha Allah, gaskiyya Nana munji daɗi sosai na yadda kika karramamu, Allah Ya yi albarka.@
“Amin na gode sosai.”
Daga haka suka miƙe nima na miƙe suka fice zuwa part ɗinta, na dawo na sameshi zaune gefen gadon.
“Amarya ta zo.”
“Ina sonki Nana.”
Kallonshi na yi, a raina ina jin daɗi. ‘Me yafi wannan daɗi? Mijinki yana ƙara aure amma babu abinda yake ce miki sai yana sonki. Shin a matan duniya akwai wacca tafi ni sa’a kuwa? Ni Nanan Sardauna.’
“Ina sonka Sardauna, ina tare da kai komai runtsi komai wuya Sardauna, Allah Ya baka ikon yin adalci mijina.”
“Nana!”
“Na’am.”
“Bilkisu ta ce min ba za ta iya girki a gawayi ba, amma na amince mata tunda daman kece kika zaɓi yin amfani da shi, sannan ta ce ba zata rayu ba Ac, ba Iron, ba fridge ba, shima na amince mata, duba da adalaci ke baki saba da su ba, ita kuma ta saba, tun da a addini ma ance idan ka auri mace ka ba ta abinda take ciki a gida, ko wanda ya fishi, idan ba zaka iya ba kar ka aureta, shi ya sa Nana, ke kuma ko da na hanaki wannan Nana nasan na baki fin abinda yafi na gidanku ko?.”
“Sardauna! Ni ba duk wani ƙyale ƙyalen duniya nake buƙata ba a zama na da kai, Sardauna kai kawai nake so, kai nake buƙata, kai ne zan rayu da shi Sardauna.”
Rungumo ni ya yi jikinsa, sannan ya ce.
“Nana girmanki da kimarki a idona abune da bazasu taɓa taɓuwa ba, Nana zan iya yaƙi da kowa akanki, Nana ina so a yadda kike yi min uziri a yanzu ki ci gaba da yimin har ƙarshe Nana, ina sonki ina sonki ina sonki.”
“Ina sonka nima sosai da sosai, yawwa gobe zanje asibiti akan ciwon kaina.”
“Tom Nana, Allah Ya kaimu.”
“Amin amin.”
“Ƙarfe tara ta yi Nana bara na je wajen amarya, ki shiryawa zuwana, da akwai magana Nana.”
“Tom Allah Ya tsare, amma ina kazar?”
“Nana tana mota, yanzu zan shigo da ita, akwai taki akwai ta ta Nana.”
“Tom Ango.”
Ya sa kai ya fice, ni kuma na zauna a gefen gado. ‘Idan ace haka Sardauna zai nuna min soyayya, ya auri mata dubu mana, ni dai Allah Ya sallameni wallahi, na yi da ce da Sardauna, na yi da ce da miji na arziƙi, Allah Ya barmin Sardauna na. Dan na yi imani Sardauna ya cika jarumin maza, ya cika miji, wai ni shin idan ban bautawa mijina na me zan masa, ni na daina zuwa wajen su Yaya Rumaisa, tun da na fuskanci kamar basu san me suke faɗa ba, ina dalili ace wai biyayy zan masa ba bauta ba, Mitcheww.”
Na ja tsaki tare da tashi na fito falo, ina nan zaune har wajen goma Sardauna bai dawo ba, a raina na ce ko Sardauna ya je siyo kaza ya yi dare ne bai dawo ba? Ganin goma da kwata ya sa na ɗaga labule sai dai ga motarsa Nana.
“A’a ina ya yi ne? Ko yana can wajen Bilkisun?”
Na faɗa cike da mamaki, daidai lokacin kuma na ji sautin takunsa, komawa na yi na zauna akam kujera daidai lokacin kuma ya shigo.
“Nana!”
“Na’am.”
“Ta so muje ko?”
“Zuwa ina?”
“Ɗakin Bilkisu mana? Ko kin manta.”
“Na yi tunanin nan za ta zo.”
Na faɗa ina miƙewa.
“Ki kijiki ta zo ta yi miki me?”
“Bakomai.”
Yana gaba ina binsa a baya muka shiga ɓangaren nata, ya ji kaya na alfarma, kina gani kinsan ‘yar masu hali ce a gidan. Da sallama a bakina na shiga, tana zaune kamar ba amarya ba, ta mimmiƙe tana danna waya, ɗaki ga Ac ga fanka abunta.
“Hajiya Bilkisu amarya.”
Na faɗa ina washe baki da niyar zama akan kujera.
“Ke dakata! Kar ki kuskura ki zauna min akan kujera.”
Kallon ta na yi baki a sake, na kalli Sardauna da ya zauna yana danna waya.
“A tsaye zan zauna?”
“Nana zauna a ƙasa.”
Sardauna ya faɗa, mamaki kamar ya kashe ni.
“Ki zauna Nana.”
Ba musu kamar umarnin ubangiji na zauna.
“Nana!”
Sardauna ya kira sunana, na ɗaga kai na kalleshi.
“Nana! Na gode da aura min mace mafi soyuwa a raina, na gode da aura min mace da nake son ta a zuciyata.”