TALES OF THE WAZEERIS

insomnia

by @surayyahms

*29...🦋🦋🦋*
SURAYYAHMS
*Tales of the waxeeris*

ata bangaren sultan shamsan kuwa bbu bata lokaci shida mahaifinsa mai martaba suka nufi babban masallaci mai dauƙe da kayatattacun daddumai masu kyau da tsafta golden nd red in colour na sarauta,

babban masjid ne wanda aka tanadar na cikin fada wanda sarki tareda jama'arsa suke yawan gabatar da ibadansu, yau daya kasance musu tamkar wata rana ta musaman makil aka cike cikin masallacin da jama'ar dake cikin fadan da duk wani hakimin sarki da nakusa dashi duk sun hallara ayau domin su taya sarki farin cikin kasancewarsa tareda dansa bayan shekaru masu yawa da tafiyansa yawon neman ilimi da aiki a kasashen waje.

Yau Bakaramin shiru masallacin ya dauka ba.

Daɗɗadar sautin muryan babban limaminsu shiya karade ilahirin cikin masallacin da zazzkar sautin kira'arsa ayayin da yake karatu cikin nitsuwa shamsan yana tsaye agefe kusa da mahaifinsa a sahun farko suna sallahn tare har aka kammala sallahn magrib akayi na ishai inda kusan kowa ya xauna wajen zamansa a nitse ana faman addu'oi.

Duk son jama'arsa da su gaisa da dansa shamsan yau haka suka hakura harsaida aka kammala duk abunda za'ayi acikin masjid aka samu fitowa zuwa ainihin cikin fadar sarki aka xazzauna snn akayi ta gaishe gaishe daga nan bai wani dade ba mahaifin sa ya bada umarnin a kyaleshi suje sashen mhaiyarsa domin ya ci abincinshi ya kuma huta sabida gajiyar hanya daya debo ajikinsa.


daga cikin hadadden shashen gimbiya hajarat sakeena daga shi sai mahaifinsa sai kuma ita data shirya musu kawatattun abinci na musmmn wanda ita dakanta ta girkasu...

tsabar son kwalliya da iya kasaita already har ta sauya shigarta zuwa wani hadaden kayan marar nauyi amma mai balain daukar hankali

bayan tagama shirya komi traditionally suka zauna akan wani hadadden lallausar turkish dadduma cream colour nd red suka fara cun abincin cikin nitsuwa time to time haka suka discusing business da wasu muhmman abubuwan game da project dinsa da yaa kawosa nigeria.

bayan sun kammala atare duka suka rakashi har sashen kakansa wato nana hafsa,..tsohnuwr mata ga shugaba khaleefa na thrim vale, wacce take kmr queen mother na masarautarsa.

estate mai dauke da chamberta baida wani nisa da asalin cikin masarauta she have many servants around her da suke mata aiki duk dama tadan tsufa amma bai hana tana tsayawa akan dukkn lamari daya shafi  danta mai martaba sarki abdallah ba...

tun bayan rasuwar shugaba khaleefa a tharim vale nana hafsa bata kara yin wani aure ba amma kuma ta bude musu wasu gagarumin gidajen marayu da marasa karfi, tana da both national nd internationl charity nd humanarian organisations datake tallafawa musulunci da kuma marasa karfi a duk duniya iya karfin ta..

after all these years batasake komawa tharim vale ba amma kuma kowa acikin ahalin yana iya zuwa nan kano ya gaisheta,

sai wasu yan uwanta na jini kmrsu dadda Aisha da kuma hjiya sanah sune suke dan zuwa time to time dan su zauna atare da ita msmn idan sun shigo nigeria daga saudi.

sosai taji dadin ganin yadda jikanta shamsan ya girma ya zamo tmkr shugaba khaleefa wajn
jarumta da kyan yanayi

sunfi awa biyu tareda shamsan din a wajenta suna gaisheta kafin nan suka mata saida safe kowa ya koma sashensa dake dare yayi


bayan shamsan ya dawo royal chambersa da kyar ya samu ya runtsa duba da yadda mahaifinshi ya bada dokar kada wani yaje kusa dashi bare a damesa,iya wannan kalmar kadai yasa aka hana kowa wulgawa ta estate dinsa.


after few hours da dawowarsu kusan koina acikin Msarautar yay shiru tareda nauyin duhun dare wanda daga nesa ne kawai zaka iya jiyo sassanyar karar saukar ruwa daga fountains dake zagaye da cikin gidan sai kuma sanyin iska mai kadawa ahankli tana girgiza fararen curtains dake manyan hallways din sashen gaba daya.

daga cikin private chambar Shamsan kwance yake akan katafaren king sized bed dinsa idanuwansa a lumshe hadadden duvet din dake kwance aginannen jikinsa ya dan zame kadan yana mai bayyanar da fresh faffadar kirjinsa mai kyau da haske

Duk da tsantsar nutsuwar dake kwance akan kyakykyawan fuskarsa juyi yakei cikin wani yanayi da alaman mafarki ne ke kkrin katse masa bacci

adan firgit ya bude idonsa yanamai sauke numfashi ahnkli saida ya karewa dakin kallo cikin runtse ido da budewa snn ya tashi xaune jin mafarkin na dawo masa akansa
...fuskr yarinyar nan dayay tunanin ya gama binnewa a zuciyarsa..

for seconds bai motsa ba kawai ya zauna akan gadon cikin nitsuwa hannunsa daya ya daura akan goshinsa yayin da idanuwansa da sukay luhu luhu suka tsaya cak cikin duhun dakin

Wani cold breeze ne yake kadawa Shamsan ya sauke hannunsa daga saman goshinsa sannan ya mike tsaye cikin kasaitaccen takunsa mai cike da nutsuwa bai damu da saka slippers din dake gabansa ba ya taka ahnkli har ya isa gaban giant window din dake kallon cikin harabar masarautar ya bude windon ahnkli 

hannayensa cushe cikin aljihun sleeping trousers dinsa ayayin da idanuwansa suka tsaya stilll akan silent darkness na palace din

Masarautar gaba daya 
ta tsaya cak Amma kuma cikin ransa yau baijin wannan shirun.


A hankali ya lumshe idonsa kafin nan ya nemi waje ya zauna yanata kallon duhun dare...

bakomi yake tunawa va face yadda idanun ushna suka kalleshi ayayinda take kokarin boye rauni. da yadda jikinta duk ya baci da ruwan datti amma har lokacin kyanta bai gushe ba.

Wani irin silent exhale ne ya kubce masa

duk dama Deep within him yanata kokarine wajen ganin yahana kansa sakata aranshi dan ya riga da yasan kanshi, baya iya saka mutum aransa musmn ma strange girl din da baisan komi akanta ba tukuna.

curiosity dinsa ne kawai take cizonsa ata ciki bana kadan ba

ji kawai yake yanaso yasan meyasameta meyasa take kuka har take jan zuciya lokacin data dago ta kalleshi

mikewa tsaye yay daga jikin windown ya nufi side table dinsa inda wayarsa take bai damu da karfe nawan dare bane kawai yasaka hannu ya dauka.

har yatsunsa sun tsaya cak akan screen zai fara rubuta sako wa abokinsa itban knn daga bisani kuma sai yasake ajiye wayar ahankli ya koma ya zauna akan dark couch cikin sauke ajiyan zuciya ya dan jingina bayansa kwayr
Idanuwansa a lumshe.


ya jima ahaka bai motsa ba jin bacci ma gabaki dayane ya kaurace masaa idonsa kafin kace wani abu har asubahin farko yayi

Lokaci zuwa lokaci kawai yake bude idanunsa yana kallon sararin samaniya da ya fara canza launi 

karona farko cikin shekaru masu yawa
yarinya da baima san sunantaba tana neman tahanashi sukuni cikin dare saidai yasan Pride dinsa bazai barshi ya kira gurd dinnan ya tambayesa inda ya kaita ba. 

he really want to hear her story but he cant just bring himself down to ask abt her shikansa yasan bazai taɓa iyawa ba.

as usual kafin a shiga sallah yamiƙe yashiga
bayi yay alwala ya fito yazo ya saka simple royal jallabiyarsa fara kal ya fetsa turare mai sanyi bamai tashi ba snn ya fito.

tun daga bakin kofar dakinsa har yakai kofar masallaci ambaton Allah yakeyi

yana shiga yasamu masu gadi ne kawai mutane basu karaso ba.

batare da ya tsaya amsa fadanci daga wajen servant din ba yawuce can gaba ya tada raka'atanil fajr yana idarwa ya zauna yanay makansa da iyayensa addua after few mins masallci ya fara cika mahaifinsa na karasowa aka hada sahu aka fara sallahn asubahi.

bayan an idar akayi karantarwa me tsayi basu bar masjid din ba sai wajajen 7:00am


 _***zamkora palace_ 

Har alarm ya buga 7.30am ushna na kwance cikin duvet dinta tana bacci mai nauyi saboda gajiyar da stress din tafiyar jiya data sha....

Sanyin AC ne kadai ke yawo acikin dakin tare da dan hasken safiya daya fara ratsowa ta windon room din.


Karar kwankwasawar kofa taji tun anayi ahnkli har aka faray da karfi, dan shiru tayi bata motsa ba da tunanin ko Areesha ce.

Sai kuma taji an sake buga kofar da dan karfi daga bisani taji muryar kaknta ummu hareera 

Ushna...harira ce kibude min kofa.

A hankali ta wara  idanuwanta cikin kasala kafin nan ta mike zaune tana gyara dogon gashinta daya barbaje wajen bacci

Babu laifi baccin jiyan yadan cire mata nauyin dake takeji a saman kirjinta.

cikin sauke ajiyar zuciya ta mike daga kan gadon ta karasa har bakin kofar tasa hannu ta bude ahnkli

Ummu hareeran ce tsaye rike da breakfast tray suna hade ido ta jefowa ushna kallo da idanuwan tausayi..

at same time tanajin wani irin relief data ganta haka..

tana murmushi me sanyi tace..Ah ahh ranki ya dade ashe har kin tashi.

Kai kawai ushna ta gyada mata tanamai matsawa gefe.

ummu hareera ta shiga ciki tana kokarin dora tray din saman table bayan ta ajeshi Sai kuma ta juyo ta karaso kusa da ushna tadan kamo hannunta cikin nata ahankli da jimami tace fatan kin tashi lfya?..

A hankali ushna tace. lafiya grandma...kefa?

Kallon ta na few scnds ummu hareeran tayi kafin nan tajata suka zauna ata gefen gadon

Nan take tsohuwar ta shafa kanta ahankli kamar yar karamar yarinya tafara cewa
jiya kin bani tsoro sosai nisam ban samu bacci ba.

ahnkli Ushna ta sauke idonta kasa bata ce komi ba sbd tausayin matar dataji..

sai can ta dan saki fuska tace "kiy hakuri grandma. ai komi ya wuce..

ummu hareera ta sauke ajiyar zuciya tana gyara zamanta
tace hakane, saidai duk abunda yafaru sam bai kamata har ki furta cewa kin tsane iyayenki ba. banji dadin wann kalamn naki ba sam

atke idanun ushna suka ciko da hawaye cikin rauni tace amma
Grandma su ya dace kenan su dinga cemin sun tsaneni???

dada riko hannunta tay cikin nustuwa tace "A'a baidace ba dan nasan kinajin ciwon hakan sosai...kuma wallahi nasan anyi kuskure akanki jiya Amma iyaye fa daban suke ushna,Ko me sukayi miki kada ki bari fushi yakaiki ga furta musu irin kalaman nan da zasukaiki ga dana sani.

ahnkli ushna ta lumshe idonta tay shiru tana jin zuciyarta na mata nauyi tana bude idon da wata kalar raunanniyar murya tace "i just felt soo unwanted..ya kike so nayi???

Nan take idon ummu hareera suka cika da hawaye tace Na sani... baki da yadda zakiy amma wani lokacin iyaye basa gane irin ciwon da suke sakawa yaransa aransau sai abun ya rabasu kwata kwata...i dont want u to live witout ur parent blessings. ko kadan baki cancanci kiy rayuwar da babu albarkan iyayenki aciki ba. gara ace sune suka miki laifi akan ace kece kike musu laifi..kinji ko?

hawayen ushna suka sauka ahankli ta gyada kai tana share hawayn

Mamanki ta jima tana kuka jiya a dakinta saboda ke..

Ushna ta dago kanta da dan sauri.

Cikin sanyin murya ummu hareera tace tun bayan abunda ya faru hankalinta bai kwanta ba dan hatta abincin da kikaci jiya
ita dakanta ta shiga kitchen ta girka miki duk dama wancan ballagazar uwarta tayi ta masifa agidan nan wai zata tsine mata..


kedai Ushna...kiyi hakuri Ki bar fushin nan Anjima idan kin samu lokaci ki shiga wajen mamanki ki bata hakuri itama.

Da sauri ushna tace grand ma zan iya hakuri da komi amma gaskiya bana jin zan iya zuwa wajenta bana son taje tasake min wani fada kinga ai wacce take zugartar tana nan bata bar gidan nan ba..

cikin katseta ummu hareera tace umarni nake baki..,ke babu ruwanki da zaliha... tunda nina nace kije kibata hakuri kawai kije

cikin sauke ajiyar zciya tace toh shikn zan je.

Nan take fuskar ummu hareera ya washe tace
Allah yayi miki albarka

daga nan ta jawo mata breakfast tray din tace
Yanzu kuma ki daure ki karya kar yay sanyi

Karamin murmushi ushna tayi kafin nan ta matso kusa da tray din tahau budewa..

hadaden Pancakes ne da fruits salads sai wani fresh orange juice mai sanyi.

Ummu hareera na zaune kusa da ita tana kallonta cikin kulawa har tafara ci Cikin gamsuwa yayin da suke hira sama sama

cikin hirar ne ummu hareera ta fara bata labarin abubuwan dake faruwa acikin gidan lokcin da bata nan...

labarin tun wasu manyan business deals din da mhaifinta ya rasa har komai ya fara rikicewa musu da irin dan uban Basukan gwamnati da pressure din da sukay musu yawa har yanzu

Ushna tayi shiru tana sauraronta duk dama tasan tana gaya mata hakane dan taji zucyrta yay sanyi hartay ma iyayen nata uzuri

wahalar da sukasha kawai ta bata labari bata gaya mata cewa sauyin mulkin da aka samu daga dala da kuma tsauraran dokoki da uwarjini ta kakaba musu daga tharim vale
shiya jefasu cikin wnn mayuwacin halin da suke ciki har yanxu ba

snn bata gaya mata batun auren hadi da akace za'ayi ba...

har labarin abubuwan da arisha tayi acikin shekarun nan saida ta bata,tanamai jaddada mata cewa kartaga yadda areeshan take yawo cikin kwalliya da rayuwa mai kyau a ko yaushe cikin pressure yarinyar take sosai.

tace Mahaifinki ya riga ta dorawa yar uwanki manyan nauyi shiysa bazaki fahimceta ynxu sosai ba..

ushna dake kan cin abincinta da tausayi tace Allah sarki..I didn’t know it was this bad

Kai ummu hareera ta gyada mata tace hmm
shide Mahaifinki baya son fiye nuna rauninshi ne Amma wallahi akwai abubuwa da yawa dasuke damunsa aransa Shiyasa wani lokacin zuciyarsa take zafi yake tsananta muku horo.

Sai kuma takara da kallon idon ushna da tausayi Ba wai hakan yana nufin yanayi miki adalci bane...amma ina so ne ke ki fahimci cewa kowa acikin gidan nan yana dauke ne da irin tasa damuwar.....
SURAYYAHMS
***


TALES OF THE WAZEERIS....