SAWUN KEKE season 1

*🪻SAWUN KEKE...🪻*

by @auntyindo


A take wani irin duhu ya rufe masa idanu ganinsa ya fara ɗaukewa, hakan ne ya basu damar ci gaba da yankarsa; yanka uku su ka yi masa ƙwarara ya zube a wurin jini na   shatata. su na ganin haka su ka ara a ta kare su ka bar wajen cike da farin ciki da murnar sun yi nasara.

a sannu-sannu  duhun da ya mamaye ganinsa ya fara washewa har ya buɗe idanunsa tangaras, cikin ƙarfin hali da tsaurin zuciya irin na shi ya miƙe ya na takawa a hankali a hankali ya nufi makaranta,  kafin ya kai ga zuwa tuni waɗan da su ka ganshi a hanya sun je sun kwanzamawa su Sheikh Auwal nan fa duk hankalinsu ya tashi su ka bar cikin makaranta su ka fito wurinsa.

Cikin tausayawa Sheikh Auwal ya ce "Akhiee maza  mu je a kai ka Asibiti don ka na guƙatar temakon likita."   Kamar ba shi da kunne haka ya yi don kuwa ko alamar ya ji ma bai yi ba,  Yasayyadi Usman ne ya dubi Sheikh Auwal cike da takaicin baƙar gaddama ta Akhiee ya ce "Ka ga irinta ko?  ya na ji fa ba wai ba ya ji ba amma sabida ɗan iska ne ya yi banza,  ka je ka mutu ma mana ina ruwan wani?"  
Yasayyadi Muhsin ya ce "Ai shi dama hadari ɗaya ba ya yi masa ruwa,  Kai Akhiee ka zo tin da girma da arziki a kai ka Asibitin  nan don wallahi jini na zuba a jikinka  sosai."
Cike da zafin rai gami da zafin ciwo ya ce ''Ku ƙyaleni abina, ba ruwanku da ni tinda ba a jikinku ciwon yake ba kuma in na mutu ba ku da asara, duk ku watse ku ba ni wuri."
Yasayyadi Jameel ya tausasa murya cikin sigar rarrashi ya ce "Yanzu ba lokacin wannan ba ne, duk  ƙara ɓata lokacin da ka ke yi ƙara cutuwa ka ke yi, don Allah ka bar labarin yasayyadi Usman ka ƙyale surutansa ka zo mu je."  wani dogon tsaki ya doka ba tare da ya ƙara ce musu ko kanzil ba,  sai lumshe idanu yake ya na cije gefen leɓensa.

Sheikh Auwal da Yasayyadi  da sauran wasu daga cikin malaman har ma da maƙota sun taru akansa sai rarrashi su ke yi su na haɗa shi da Allah da Annabi amma ya yi kafus,  ya ce murje shi fa allambur ba wanda ya isa ya kai shi wani Asibiti.
Haka su ka yi ta fama da shi har Tashin hankali  ma ya sa sun manta  sun baro ɗalibai a ciki gashi har lokacin tashi ma ya wuce ana ta turnuƙu da shi.  shi kuwa har lokacin girarsa ɗaya ba ta karayaba.

Magriba ce ke shirin rufawa amma a yau MADARASATU NOORUL ISLAM   ba alamun za a sallami ɗalibanta.
 Tin su na karatun da aka koyar da su cikin ƙwarin guiwa har su ka gaji wasu su ka fara yin shiru, ƙananu kuwa tuni wasu sun fara kuka sabida tsoro don sun yi tunanin anan za'a bar su su kwana.

Husnee ce ta shafa cikinta da ke kukan yunwa kafin ta ce "Asiya wai lafiya kuwa?  ace har yanzu ba malamin da mu ka gani bare ya sallamemu?"  Zara ce ta leƙo tsakaninsu gami da cewa "Bari na je na duba ni dai wallahi na gaji a zo a sallamemu haba!"  Husnee ta yi dariya ta na cewa "Yauwa ƙanwar masu abin jeki don Allah."
Harara ta maka mata kana ta fice.   Ba ta wani daɗe ba ta dawo hankali a matuƙar tashe, ganin haka ya sa zuciyar Husnee ta fara dukan sittin saba'in tamanin casa'in ɗari da hamsin!
"Ƴan Daba ne su ka sassari Akhiee, jini sai zuba ya ke yi a jikinsa amma ya ƙi yarda a kai shi Asibiti, shine duk su ka taru a kansa, har  babban Yayanmu ma ya zo  amma ya ƙi Amincewa, kuma wallahi ya na shan wahala sosai jininsa zai iya ƙarewa"   
Ta ƙarasa maganar gami fashewa da kuka mai taɓa zuciyar duk wani me imani.
Husnee ta na jin haka ba ta bi ta kan Zara ba ta falla da gudu ta yo waje.
Turmutsawa ta yi tsakankanin mutanen da su ka yi masa da'ira wanda yawanci Yayyensa ne..........

Gaba

Da tambaya su ka isa ƙofar gidan   jikinta sanyi  salam haka ta fito daga mota ta na ƙarewa tafkeken get ɗin gidan kallo,  yadda gidan yake tamfatsetse idan na shiga  ina zan fara tinkara?  tambayar da zuciyarta ta ke yi mata kenan.

Kamar Amadu ya sani ya ce "Innata shiga za ki yi da Bismillah ki na addu'ar Allah i haɗa ki da wanda ki ka sani kawai."
Jinjina kai ta yi gami da sauke ajiyar Zuciya sannan ta nufi get ɗin gabanta na ƙara faɗuwa.

Sallama ta yi a  haraba  ta na rarraba ido don ganin ta inda za'a ɓullo.
Ji ta yi an amsa sallamar daga can gefenta ta yi saurin kai dubenta wurin, Hamza da Adamu ne zaune kan wata makekiyar tabarma sun tasa kofuna da fulas ɗin shayi gaba da alama karin kumallo su ke yi ko kuma za su yi.
Danne fargabarta ta yi ta ɗan dubesu gami da cewa "Ina kwana!"  duk idanunsu na kanta  Hamza ya yi zaram ya amsa ya na fara'a.
Cikin kame-kame ta ce ''Um!..in..ina ne... zan ga Akhiee?" 
Idanunsu ne su ka ƙara girma  su ka yi kallon kallo cikin madarar mamaki, Adamu ne ya yi saurin shiga zancen da cewa "Waye kuma Akhiee ?  daga ina ki ke meye haɗinki da shi??"  
baki na rawa ta ce "Muhammad Risslan fa ni...ni..a..."  kasa ƙarasa maganar ta yi sabida kuka da ke shirin  kufce mata.

Hamza ya karkaɗe mazaunar rigarsa ya miƙe ya na cewa "Abin ya ƙara girma kenan, bari dai in matso in ji yadda ake ciki."
"Ƴar ajinmu ce  ita, kuma ta zo duba lafiyarsa ne,  Husnee sannu da zuwa mu je in raka ki wurinsa." 
Zara da ta iso yanzu ta basu amsar tambayarsu, kana ta ja hannun Husnee su ka kutsa kai ciki.
Riƙe haɓa Hamza ya yu ya na cewa "Iyye?  neman mata ma ya fara yi kenan?  to Allah i sauwaƙe lallai Abhi ya haifi bala'i."  Adamu ya taɓe baki ya na cewa "Ƙaddararre ni wallahi na so ma sun kashe shi kawai mu huta aikin banza, kullum sai ya yi mana baƙin tambari ya gada mana abin magana sannan ya ke jin daɗi, ya gama gurɓata kima da mutuncin Ahalinmu."  Hamza ya ce "Ni ma da hakan ta faru ai sai na fi kowa murna wallahi, yanzu ga dai wannan yarinya har yarinya amma ya lalatata."
Adamu ya ce "Umm! to ya za mu yi haka za mu suba ido har sai ya mutu sannan mu huta, ɗan wahala kawai."
Masifa su ka ci gaba da zazzagawa kowa na tofa albarkacin bakinsa wanda yawanci ba alkairi su ke faɗe akan Akhiee ba.


Sai da su ka ƙara shiga ciki Husnee ta ƙara tabbatar da girman gidan, sashi kala daban-daban ga ɗakuna rututu haka mutane yara manya maza mata duk gasu nan  a hakan ma wasu sun tafi makaranta, matan gidan da ƙananun yara sun fi yawa sai samari su  na ta shirin  fita kasuwa.
Ita dai kamar ɓarauniya haka ta ke tafiya saɗaf-saɗaf sai fiƙi-fiƙi  ta ke yi da idanu kamar an tarfa munafuka.

Duk wanda ya lura da su sai ya tambayi wacece da uwar safiyar nan ta zo musu gida musamman matan gidan, sai Zara ta yi zaram ta ce Ƴar ajinsu ce sai kuwa su taɓe baki.
Da haka su ka isa  can ƙarshen gidan. inda   ba mutane  wuri ne a ɗan kewaye wanda za a iya kiransa gida   ɗan ƙarami me ɗaki ɗaya sai banɗaki da wani ɗan ƙaramin ɗaki wanda bai kai a kira shi ɗaki ba sai ɗan tsakar gida ba wani babba ba,  wurin shiru sai iskar safiya da ke kaɗawa a hankali a hankali don kuwa wurin ya yi nesa da cikin jama'a sosai kwata- kwata bai alaƙanci wani sashi na  mutan  gidan ba.
Husnee dai da bata iya gani ta yi shiru sai da ta kalli Zara ta ce "Ni ban taɓa ganin ƙi da tsangwama ba sai a gidanku, wato ɗakin nasa ma shine a can bayan gari  inda ba mutane, wajen kwanan ma sai an  nuna bambanci ko?"  Zara ta ce "Ai ba laifina ba ne Husnee nima tinda na yi wayo a nan na ga ya na kwana tin kafin ya girma shima, ban sani ba ko shi ya zaɓi hakan ko su su ka zaɓa masa, amma ba me shigowa ma sai in baya nan ko kuma dai wani babban abu ya kawo mutum."
Daidai lokacin Zara ta kutsa kai cikin ɗakin nasa  tare da sallama, Husnee kuwa dakatawa ta yi domin a bata izini sannan ta shiga.

Turus Zara ta yi ganin Wata kyakkyawar budurwa wadda ba ta wuce shekaru daidai na da na Husnee ba zaune ku sa da shi idanunta sun yi jajir sun yi ɓulu-ɓulu  da zarar me hankali ya kalla ko ba a faɗa ba ya san kuka ta ci har ta godewa  Allah, har yanzu ma akwai sauran hawayen akan  dogayen gargasar idanunta.
Akhiee kuwa ya na zaune bisa ƙaramin gadonsa wanda aka shimfiɗe shi da kyakkyawan bargo duniyar kuliya.
abin ya bala'in bawa Zara mamaki don kuwa kaf shirin ɗakin da su ka yi ita da Sheikh Auwal an canja shi ciki kuwa har da wasu abubuwan irin su bedsheet pillows da sauransu.
Idanu ya zubawa Zara alamar tambaya,  ta yi ƙasa da kai zuciyarta sam ba daɗi ta ce ""Husnee ce ta zo dubaka shine na rakota."

Juyawa ya yi ya zubawa ƴar budurwar ido a na yi mata wani shegen  kallo me cike da alamomi daban-daban.
Zirrrrrr!!!  hawayen su ka ƙara biyo kan kumatunta. 
Tsaki ya yi kafin ya buɗi baki a hankali ya ce "Ta shigo kawai."
Zara ta juya gami da cewa "Ki shigo Husnee"  ba za ta iya komawa ba don haka ta ce "Ni kam  bari in je wajen su Umma"  gami sa yin gaba.
Husnee ta ce "To"  gami da turmutsa kai ɗakin tare da Sallama.
a inda yake zaune a nan yake bai ko motsa ba,  Husnee kam ba ta ga abinda Zara ta gani ba don haka ta ƙarasa gefen  gadon nasa ta zauna  ta na murmushi me tafe da ƙwalla.
Ido ta zuba masa har na lokaci yayin da nasa idanun su ke a ƙasa ko ɗagowa ya kalleta bai yi ba.

Cikin  rawar murya ta ce "Akhiee!  ba ka son ganina ko? ya jikin naka?  ka yi haƙuri don Allah wallahi ba a son raina na ɗaga maka hannu ba jiya, hankalina ne ya tashi na rasa yadda zan yi don gani   nake tamkar za ka rasa ranka."
"Wannan bai ɓata mini rai ba a kan rashin jin maganata Asma'u, me ya kawo ki har gidanmu? shin bance ki fita daga rayuwata ba ne?   kin ga abinda ya faru da ni  jiya  cikin ƴan mintuna ki sani idan ki na bibiyata watarana ke  za'ayiwa abinda aka yi mini don za  a ɗauka ne kamar ke wata ce a wurina."  Hijab ta sa ta na goge ƙwalla cikin shashshekar kuka ta ce "Ina so in yi abinda ka ke so amma na kasa, Akhiee tausayinka da son kasancewa tare da kai ba zai barni na yi abinda ka ke so ba,  ka barni kawai idan an kashe ni  ka ga dole zan dena bibiyarka"  
"Ke mahaukaciya ce wai Asma'u? meye haɗina da ke da har ki ke tunanin a kashe ki a kaina?  me yasa ba za ki yi ƙoƙarin gyara rayuwarki ba  sai ki yi ƙoƙarin lalatata??"   

"To Akhiee kai me yasa ko na rana ɗaya ba za ka kwatanta zamowa mutumin ƙwarai ba?  ba ni da wata alaƙa da kai amma  akwai ƴan'uwantaka ta muslimci Akhiee ko dai kai ba muslmi ba ne?  me yasa za a dinga haɗa ka da Allah akan abu amma ka rufe idonka?  Akhiee!!  indai ba ka zamo mutumin kirki ba to fa  ba na jin akwai ranar da hankalinka zai kwanta,  da ba ka shiga harkar banzar nan ba da babu wani ɗan ta'adda da zai cutar da kai, amma ka  shiga harkarsu, ƴan gidanku duk malamai ne kai ɗaya ne ka zamo daban,  ba ka jin nauyin  yin kisa, ka ɗauki jini tamkar ruwa kwata-kwata zubarsa ba ta tsorata ka, ka yanki wancan ka kashe wancan Akhiee meye  ribar wannan rayuwar?  ka tarawa kanka maƙiya da masu son ganin bayanka,  ƙarshenta fa  haka za su yi maka kisan wulaƙanci  mu da mu ka damu da kai kuma ka bar mu da shan wahalar rashinka; Akhiee!!!   Ka yi min haƙuri amma ba zan iya fita daga rayuwarka ba ina son zamowa Abokiyarka, don Allah ka yarda da ni"  ta kai ƙarshen maganar ta na wani irin kuka me tsuma zucuyar me saurarensa.

Rintse idanunsa ya yi da ƙarfi gami da haɗe kansa da guiwa, zuwa yanzu ji yake kamar ya kasheta ya huta don kuwa ya tabbatar indai ba za ta fita daga rayuwarsa ba za ta sha baƙar wahala ta ko'ina.
Sai bayan wani lokaci zuciyarsa ta  ɗan lafa sannan ya ɗago idanunsa ya zuba mata  "Asma'u Babana kawai na yarda da yiwa ƙarya, Babana kaɗai na ke iya saurara kuma na ke iya amfani da kalaminsa,  sai dai ko shi bai taɓa sa ni dariya na yi ta ba sai ke Asma'u, ban sanki ba bansan wacece ke ba  nan san daga ina ki ke ba, lokaci ɗaya kin shigo rayuwata  kuma ki na son haifar min da matsaltsalu a cikinta,  iya abinda ki ka samu a baya ki yi haƙuri da shi amma daga yanzu ki daure ki ɗauke kanki daga gareni,  rayuwata rayuwata ce ba na jin za ta taɓa canjawa, ki tashi ki tafi."
"Amma Akhiee ai....."  dakatar da ita ya yi da cewa "Ba na son jin komai daga bakinki, na riga na gama maganata ki tashi ki fice mini da gani, ba na son ƙara ganin fuskarki haka ba na son ko da ƙara jin sunanki, da so samu ne  ki yi mini tazarar da har abada ko labarinki ba zan ƙara ji ba, ki fita tin kafin raina ya ɓaci na yi miki abinda hankali ba zai ɗauka ba."

miƙewa ta yi ta na tafiya da baya da baya idanunta da ke famar zubda ruwa su na kansa,  wani irin abu ne ke turnuƙo mata tin daga ƙahon zuciyarta har maƙogoro hakan ya sa ba za ta iya cewa komai ba, yadda take shashshekar kuka kuwa ka ce duk ƴan gidan su ne su ka yi haɗari su ka mutu.
Sai da ta fice daga ɗakin kana ta juya ta ci gaba da tafiya a hankali a hankali.

a haka ta dinga ratsa shafukan gidan daban-daban   ba tare da damuwa akan kallon da su ke binta da shi ba har ta fito waje inda Amadu ke  ta safa da marwa cike da zullumin abinda zai faru da ita a ciki, ganin ta na wannan mugun kuka ya ƙara ɗaga hankalinsa ya shiga yi mata tambayoyi sai dai ko uffan ta ƙi ce masa.

a ɗakin Akhiee kuwa Husnee na fita  Razia ta bayyana a gabansa ita ma ta kafa aradun nata kukan,  cikin shashsheka ta ce "Risslan  ina raye  kuma ina tare da kai  amma  ba ka taɓa yi mini abinda ka yiwa wannan yarinyar ba, ka faɗa cikin wannan halin ne fa dominta ka yi abubuwan da ba wanda ya taɓa saka ka yi su  sai ita,  ta ya-ya hankalina zai iya ɗauka?   billahillazi huwar rahmanu Sai na kasheta indai ba ta gaggauta  fita daga rayuwarka ba!!!, in ban kasheta ba kuma zan yi mata illar da duk duniya sai ta Zame mata tamkar wuta, da ita da danginta sai sun gwammace mutuwa ta yi akan irin izayar da zan yi mata."

Jikinsa kawai karkarwa ya ke yi  jijiyoyinsa jikinsa sun wani irin mimmiƙe sun firfito, kansa na wani irin juyi da gwamutsi tamkar karon Babbar mota da ƴar uwarta, Zuciyarsa  wani irin tuƙuƙi ta ke yi wanda ya ke jin tamkar  ba za ta ƙara minti ɗaya ba  za ta yi bindiga ta tarwatse.
Leɓensa na ƙasa ya kame ya cije gami da dafe kansa da dukkan hannayensa.
ganin irin  wahalar da ya faɗa bai  sa Razia ta saurata masa ba,  ta ci gaba da surutai cikin fitar hayyaci da tsananin ɓacin rai,  baƙin kishi ya sa duk ta zamo tamkar mahaukaciya,  ta daɗe ta na faɗar duk maganar da ta zo bakinta sannan ta gaji ta yi shiru ta ci gaba da zabga kuka.
sai a lokacin Akhiee ya samu damar tofa tashi  "Asma'u ba ta da laifi kuma muddin wani abu ya sameta sai na jefa ki a  masifar da har ƙiyama ta tsaya ba za ki fita daga cikinta ba wallahi!!!!  tashi ki bar min wuri kuma za ki je ki haɗu da Father."
rikiɗaɗɗun idanunta ta zuba masa cike da tsananin mamakin furucinsa.
Cikin tsawa ya ce "Ki tashi na ce!!!  ko kuma ni in baki wuri!!!" 
Ya na rufe baki ta ɓace ɓat!!  kamar ba ta taɓa wanzu a wurin ba.
Zafi, ƙuna, raɗaɗi, ciwo, azaba, uƙuba,  ba abinda zuciyarsa da kansa ba sa yi  ya rasa ma abinda zai yi ya samu sassauci.

Zabira da Laita Da sauran iyalin Akhiee su na zaune sun yi jungum-jungum kowa na tunanin halin da yake ciki, Rabi'u kuwa kuka yake ta ɓarzawa  tin jiya da ya ga halin da Uban gidan nasa ke ciki tsoro da tashin hankali su ka hana shi sakatt,  a kyauta Laita ta ba shi abinci amma ya ƙi ci sabida ya gama firgicewa, da kuka ya yi bacci da shi ya tashi, har kawo  yanzu ma ya kasa denawa, su kuwa sai ƙara tsorata shi su ke yi, a take ya ji harkar daba ma gabaki ɗaya ta fice masa daga rai, nan take ya sa a ransa zai yi karatu tuƙuru kamar yadda mahaifiyarsa ta ke so  zai watsar da dukkan wata shiririta.

Zabira ce ta ɗan yi gyaran murya sannan ta ce "Wai yanzu zuba ido za mu yi kenan ba za mu ɗau fansa ba??"   Gwaja ya ce "To in ba da umarnin Sarƙa ba wa zai yi hakan?  sai mun je mun tambayeshi mun ji me zai ce"  Laita ta ce "Ya kamata a gaggauta tambayarsa; anjima kaɗan ku shirya mu shiga gidan nasu."  Salansa ya ce "Hakan ma za ayi, amma ya zama dole mu ɗaukar masa fansa  ko ba ya so  sai mun yi bai sani ba."  
Ɗan Bakwai ya ce "Asalin gaskiya kenan nima haka zan ce"   tattaunawa su ka fara yi kowa na faɗen abinda ya kamata su yi.



by Aunty INDO