SAWUN KEKE season 1

*🪻SAWUN KEKE...🪻*

by @auntyindo


Kamar daga sama aka jefota haka ta faɗa  ɗan madaidaicin Kangon da su Ɗan Kurada ke zaune su na ƙidaya kuɗin da Dodon Lungu ya basu na aikinsu, sai murna su ke yi kamar an yi musu Albishir da Aljanna.

Ba wanda ya ankara sai ganinta su ka yi akansu, fuskar nan ta-ta ba annuri, cikin tsananin ɓacin tai ta ce "Wai har da kai za'a ci amanata a karɓi kuɗi a kashe wanda na ke so,  to wallahi duk sai kun gane kurenku!"  Ɗan Kurada ya yi saurin miƙewa ya na tausa kuɗinsa cikin wata ƴar lalita, cike da son kare kansa ya ce "Wallahi kin san dai ba yin kaina ba ne, Dodo ne ya samu kuma kinga aikinsa mu ke yi ba zai lamunce mu ƙi yi  don ki na son Sahun Keke ba, wannan kuɗin ma da ki ka gani ba nawa bane na waɗannan ne"  ya faɗa ya na nuna abokan aikin nasa wanda su ke zazzare ido kamar na mazarin tsire a kasuwa,  sun tsorata da ganinta don dukansu ba wanda bai san halinta ba,  ana cewa mace akwai tausayi amma ita ta fi wani namijin rashin imani.

Ƙwafa ta yi kafin ta ce "Ɗan Kurada ka je don kanka  kai ba zan taɓa ka ba amma tabbas sai na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro."  Jin haka ya  sa sauran miƙe su na neman wajen tsira,  a hankali ta taka ta doshi inda suke, baya-baya su ka fara yi su na bata haƙuri gami da bata yadda aka yi amma ko saurarensu ta ƙi yi,  sai da su ka ƙure da bango sannan su ka dakata.
Cikin dakakkiyar muryarta  ta ce "Da ku da suwaye ku ka aikata??' Asabubu ya ce "Wallahi Ɗan Kurada ne babbanmu, sai wannan sai sauran yaran Oga, ni ba abinda na yi masa wallahi."  ya ƙarasa maganar ya na yi mata nuni da na kusa da shi.

Wata lafiyayyar wuƙa ta zare a ƙugunta  ta na zuba musu idanunta masu ban tsoro, sai da ta goge wuƙar sannan ta ce "Ya zama dole ku ɗanɗana!!"  ta yi maganar tare da ketawa Asabubu wuƙar akan cikinsa, ihu ya zunduma sabida azabar da ta ratsa shi har cikin ƙoƙon ransa,  cike da rashin tausayi da imani ta ƙara kafta masa sara a kafaɗarsa hakan ya sa dole ya zube a wajen.
Takawa ta yi da gudu ta bi ɗayan da tuni ya tsela a ta kare ya na neman ceto,  kafin ya kai ga fita ta cimmasa, ta na danƙo shi ta shata masa yanka a hannunsa kan jijiyar gaɓar hannun ai kuwa jini ya ce salama alekum,  riƙe hannun ya yi ya na wulwula shi cike da azaba,  ba ta saurara masa ba  ta burma masa wuƙar a ciki ta zareta gami da sa ƙafa ta harbatsa shi can gefe.

Ɗan Kurada da jikinsa ke ta tsuma ta kalla ta na huci  kamar wadda aka danne za'a yanka,  "Wallahi Tallahi indai ka ƙara taɓa Sahun Keke sai na raba kanka da gangar jikinka,  ka je ka gayawa Dodo na ɗauki mataki akan yaransa, duk hukuncin da zai yi mini ina jira, don Uwar babassa ko me zai yi ya yi, kuma daga yau na bar aiki a ƙarƙashinsa, nima ƴar kaina ce kuma ina da tawa dabar,  ku iya takunku tin kafin na hallaka ku."
Ɗan Kurada ya jinjina kai alamar ya fahimta, da kyar ya harhaɗo magana ya ce "Amma bai kamata ki bar ƙarƙashin Dodon Lungu ba, na san ma don kin yi haka ba zai ce komai ba."   "Idan ma ya faɗa ba ni da asara  ka je ka gaya masa saƙona."  ta na gama faɗen haka ta fice fuuuuu kamar iska.

Husnee
Ko da Amadu ya kai ta makarantar cewa ta yi ba za ta shiga ba gwara ya kaita wani wurin idan  lokacin tashi ya yi sai su koma gida.
Cikin sanyin jiki ya ce "Innata ni yanzu ina zan kai ki don Allah?"  
"Mu je bakin titi kawai ka ajiye motar zan zauna a ciki"  Amadu kamar ya fashe da kuka ya ce "Hakan fa bai da amfani ki yi haƙuri mu koma gidan dai tinda ba kya son makarantar."  
"Ba na son gardama don Allah kawai ka yi mini abinda na ke so."  rausayar da kai ya yi sannan ya kunna motar gami da fara tafiya.

Sai da ta kimanta lokacin tashi sannan su ka nufi gida,  Mommy na harabar gidan ta na duba shuke-shuke  su ka shigo,  baki a sake ta tsaya kallon Husnee wadda ta yi jemai-jemai da ka kalla za ka gane a bala'in wahale take.
"Ikon Allah kwanan nan dai duk in ki ka fita ba kya dawowa ƙalau, me yake faruwa ne??"
Numfashi ta ja ta sauke shi tare da nannauyar ajiyar zuciya,  cikin muryar da ke ƙara nuna tsantsar damuwar da take ciki ta ce "Ba zan ƙara zuwa makarantar nan ba har sai bayan wani lokaci."
"Oo ni ƴasu, to dalilin me?"   "Mommy Ba ni da lafiya  kuma shine su ka doke ni, don Allah Mommy kar ki matsa mini akan hakan ki barni duk ranar da na yi niyya zan koma."  Mommy ta rausayar da kai kamar kazar da ke jin yunwa, a sanyaye ta ce "Shi kenan, Allah i ba ki lafiya, dama ke ki ka zaɓi makarantar ai ba ni na zaɓa miki ba, ranar da ki ka ga dama kya je, kuma idan yayyenki su ka tambayeki dalilin rashin zuwanki sai ki san abin gaya musu."
Gyaɗa kai kawai ta yi alamar ta yarda da hakan, ba ta ƙara cewa kanzil ba ta wuce ciki,  tinda ta zauna ta doka tagumi ba abinda take tunani sai irin tsatstsauran matakin da Akhiee ya ɗauka akanta,  a yanzu ba ta da zaɓin da ya wuce ta ƙaurace masa na wani lokaci, kuma ta dinga addu'ar Allah i yaye mata duk abinda ta ke ji akansa, tunane-tunanen da ta ke yi kenan gabaki ɗaya hankalinta ya tafi akai.


Hajiya Laure da Hajiya Saudah ne zaune a gaban Boka Barore  sai tsitstsilla  idanu su ke yi sabida tsoro da fargabar abinda zai fito daga bakinsa.
shi kuwa Dariya kawai ya ke  tilliƙawa kamar an yi masa wahayinta, ya kai aƙalla minti biyar ya na yi sannan ya ci mur kamar ba shi ba, kallonsu ya yi ɗaya bayan ɗaya kafin ya fara magana ya na yi ya na zare musu munanan idanunsa,  "A kwana uku na ce ku dawo, shine ku ka ƙi dawowa sai yanzu da ku ka yi niyya, to aikinku ya tarwatse,  wadda mu ka turawa aikin a lokacin ta na tare da shi kuma ya temaketa   ya hana aikin shiga jikinta,  kuma ba ku dawo lokacin da mu ka ce ba kun tarwatsa komai, Shaiɗanun Aljanu sun Fusataaa!!!!"  ya kai ƙarshen maganar tare da wani ƙaraji da gurnani tamkar mahaukacin zaki.

Kallon Kallo  Hajiya Saudah da Hajiya Laure su ka yi cikin tsoro da shakku kafin Hajiya Laure ta ce "Ranka ya daɗe Boka Barore me zamani, wallahi rashin lafiya ce ta kama ni ba zato ba tsammani kawai sai na tashi da cuta har ba na iya ko tashi zaune sai an temaka mini, amma yanzu na ji sauƙi shine fa na yi maza na garzayo, abin dai ya na raina amma tsautsayi ne ayi haƙuri manyan mutane"  ta ƙare maganar cikin sigar rarrashi.
"Hahahahahahaha!  Ta baya ta wuce,  za ayi aiki me wahala kuma za mu ƙara tura shi ne kan wannan yarinya,  amma muddin ku na so aikinku ya yi kyau sai kun cike sharuɗana"  Hajiya Saudah ta ce "Meye sharaɗin?  ai tinda da akwai mafita komai me sauƙi ne Boka"   ''Ina buƙatar yarinya ƴar shekara ƙasa da ashirin, za ku kawota gobe  bayan ta yi kwana uku za ku zo ku ɗauketa, muna buƙatarta!!!!."  
Hajiya Laure cikinta ya bada wani ƙulululu!!  ita duk irin wannan manyan asirce-asircen ba iya yinsu ta yi ba, abinda ta fi ganewa  ƴar mallakar miji  da ɗan abinda ba a rasa ba shima mallakar ba irin ta muguntar nan ba.
Ganin ta ruɗe ya sa  Hajiya Saudah ta ce "Za mu kawo Boka, indai za mu yi nasara dole ne za mu nemo mu kawo."  
Boka ya yi dariya me isarsa sannan ya ce su zube kuɗi ya sallamesu.

Suna fitowa Hajiya Laure ta ce "Haba Hajiya Saudah, yanzu ina zan bi in samo yarinyar mutane in kawowa boka?  haba a dinga tunawa fa a duniyar muslimci muke ba ta kafirai ba."
Hajiya Saudah ta yi wani Shu'umin murmushi kafin ta ce "Hmm!! kin ɗauki duniya da wasa Ƙawata, ki na son ɗaukar fansar mijinki, amma ki na tsayawa sanya, samun budurwa ba wani abu ba ne ba fa,  kuma ba wai kasheta zai yi ba  kawai ina tunanin zai ɗan ci amarci da ita ne" ta ƙarasa maganar ta na dariya,  ita ko a ƙasan silifas ɗinta.
Hajiya  Laure dai har yanzu abin bai yi mata ba, cikin sanyin jiki ta ce "To yanzu wa zan samu in kawo masa a goben nan?"  
"Ba ki na da Ƴar aiki ba?  ƙila ma ba ɗaya ba to a cikinsu za ki zaɓa ki darje kawai ki ce ta zo ta raka ki, indai boka ne da ya gama abinda zai yi ya rufe bakin shegiya shi kenan."
Hajiya Laure dai ba ta iya cewa komai ba sai tunane-tunane, wannan Damar Hajiya Saudah ta samu ta zizzigata ta kwantar mata da hankali har ta ji ta yi na'am da hakan.

Washegari kamar yadda su ka shirya tin wuri Hajiya Laure ta ci ado ta gaiyaci Ma'u ƴar aikinta rakiya,  su na zuwa su ka direwa boka ita su ka yi nasu wuri.
anan fa Ma'u ta ga tashin hankali, tin ta na kuka da hawaye har su ka gaji su ka dena zubowa.

Bayan kwana uku.

a cikin ƴar bukkar Boka Barore su na zaune gabansa  sai fara'a su ke yi da alamu dai duniyar ta buɗe musu, Ma'u kuwa ta na gefe ta haɗe kai da guiwa tsirit da ita.
Hajiya Laure ta ce "Boka ɗana ya takura mini akan hakan, ban san ya  zan yi masa ba."  Barore ya yi dariya sannan ya ce "Za mu rufe masa baki, ba zai ƙara hanaki yin abinda ki ke so ba"  ta ji daɗin hakan ta yi masa godiya kana su ka miƙe,  yau ma kwana uku ya basu su dawo.
Ma'u dai da kyar da kyar take iya tafiya, duk ta zama kamar sokuwa ba um ba um-um, su Hajiya Laure ma ƙyamarta su ke ji da sun kalleta sai su tsartar da yawu su yatsine fuska, da haka har su ka dawo gida.

Hajiya Laure ta yi Sa'a  da su ka shigo gidan duk ba kowa a kusa don haka ta yi sauri ta balbale Ma'u da masifa akan  ta je ta yi wanka ta dawo daidai,  cikin yanayinta me kama da sokunta ta aiwatar da abinda Hajiya Laure ta ce.
Ba laifi ta ɗan dawo hayyacinta sai dai tana nan sukuti da ita.

Husnee na kwance kan gado ta na malelekuwa kamar yadda ta saba don kwanan nan aikinta kenan, Mommy ce ta ƙwala mata kira, ta amsa cikin muryarta da ta gama dashewa, Mommy ta ce "Zaman ɗaki da kwanciyar nan naki ya isheni ya ishi kakata INDO  ba dole cuta ta ƙi warkewa ba ki na famar kwanciyar kamar ɗan malele? anyi allura ansha maganin amma abu ya ci tira, fito ni ki tayani girki ko kya ji ƙwarin jikinki." 
Da kyar ta iya amsawa da "to"  sannan ta yunƙura ta tashi ta na bibango sabida wani ɗan jiri-jiri da ke ɗibarta.

Ta na fitowa daga ɗakin daidai lokacin ƙullin asirin Boka Barore ya nufota gadan-gadan, ƙiris ya rage ya faɗa mata Razia ta faɗo kanta da ƙarfin gaske hakan ya sa ta ƙwalla ihu gami da faɗuwa gefe ragab, a take ta sassanƙare kamar gawar sababi.  tsafin Boka Barore kuwa ya faɗi ƙasa ya ƙone ƙurmus tuni ya bi iska ya san inda dare ya yi masa.

Hankali a matuƙar tashe Mommy ta yo kanta ta na kiran sunanta, ta na taɓata ta ji ta sandare komai na jikinta ya dena aiki sai zuciyarta ce kawai ke bugawa, Addu'o'i ta fara jerowa ta na tofa mata nan fa hankalinta ya ƙara ƙololuwa wajen tashi ganin Husnee ta fara kanannaɗewa  ta na wani irin lanƙwashewa kamar jikin tsutsa gareta, ma'ana dai tamkar ba ƙashi a jikinta.

Mommy ta fashe da kuka  ta na ƙara karanto addu'o'i gami da janyota jikinta ta rungume ta na ƙoƙarin  hanata lanƙwashewar sai dai kash abin ya ci tira.
Ta ɗebi kusan minti shidda cikin wannan halin sannan kuma jikin nata ya dawo daidai ya wani saki lakaf kamar gawar da ta samu ziyarta lahira yanzu.

wani azababben kuka ta saki ta na cewa "Mommy zan mutu kaina zai fashe  wayyo Allah na"  jin haka ya sa Mommy ta ƙara rungumota ta na cewa "Ki yi haƙuri Husna ai cuta ba mutuwa ba ce, ki yi ta addu'a za ki samu lafiya in sha Allahu."    inaa kukanta kawai ta ke yi ba ji ba gani don ko fahimtar inda Mommyn ta dosa ba ta yi ba bare ma ta yi addu'ar, su na  nan zaune Mommy na Kuka Husnee na yi har wani lokacin kafin ta saki kai ta kama ciki  ta na kukan cikinta na ciwo,  ita dai Mommy ta ga tashin hankali, Ayatul Kursiyyu gami da Suratul Baƙarah da sauransu take  karantowa in ta saki wancan sai ta kama waccan gabaki ɗaya ta burkice.
Ta na cikin haka ta ji wani hucin zafi ya bugeta itama ta zame ta kwanta a wajen a sume.

Russlan ne ya yi dirar mikiya a wajen ko ƙasa bai sauka ba ya fizge Razia daga jikin Husnee su ka yi sama, nan take Husnee ta ji kamar cirar ƙaya sai dai ko yatsanta ta kasa motsawa ji take kamar an daddatsa ta da adda, idanunta ma kansu sun yi mata nauyin da ko buɗe su ta kasa yi, Mommy kuwa itama ta na kwance a sumenta  ba me tashin wani tsakaninsu.

Su na cikin wannan halin Muneeb ya shigo fakam-fakam tare da sallama bai bari an amsa ba ya ci gaba da cewa "Mommy  kin ganni  da wuri yau fita zan yi."   da yake hanyar banɗakin tsakar gida ya nufa sam bai lura da su ba sai da  ya leƙa banɗakin ya fito da nufin ajiye wayoyi da tarkacen jikinsa kafin ya shiga wankan, nan fa idanunsa su ka yi alaragab da su a sheme.
cikin hanzari ya yi kansu ya na tambayar lafiya.
  
Ya na taɓa Mommy ya ji ta a sume zuciyarsa  ta bada rimm!! idanunsa ya kai kan Husnee da take zubda ƙwallar wahala ita ma ƴar siriri take bin gefen idanunta, hankali tashe ya ce "Ke Husnee lafiya??"  ba za ta iya magana ba  don haka bai samu amsa ba.
Ruwa ya lalubo ya  yayyafawa Mommy ai kuwa ta ja wani gwauron numfashi ta sauke ajiyar Zuciya sai kuma ta ci gaba da kuka ta na cewa "Ina Husna, kar dai sun ɗauke mini ita"  cike da mamaki da tsoro Muneeb ya ce "Me ya faru Mommy?? su waye za su  ɗauketa??"  ba tare da ta dena kukan ba ta ce "Yauwa gwara da ka dawo, ashe da gaske Aljanu sun hau Husnee kar ka ga irin wahalar da su ka bata"  ta yi maganar ta na ƙoƙarin tashi zaune, temaka mata ya yi ta Zauna, ganin Husnee kwance a kusa da ita ya sa farin ciki ya kamata,  goge hawayen ta fara yi ta na cewa "Kalleta nan kar ka ga yadda su ka dinga cukurkuɗa ta kamar ba mutum ba."  
sunanta ya kira ya na shafa gefen fuskarta cikin tausayawa, a hankali ta buɗe ido ta na kallonsa sai kuma ta ɓare baki ta kama kuka ta na cewa "Jikina ciwo ya ke yi   ji nake kamar zan mutu!"  ya ce ''Sannu kin ji, Allah i sauwaƙe ki dena cewa za ki mutu ai  mutuwa sai lokacinta ya yi."  Mommy ta ce "Ɗauketa ka mayar da ita ɗaki, laifina ne ni nace ta fito."  ta faɗa ta na goge hawaye.
Rungumarta  ya yi ya kaita ɗaki ya kwantar ya na  ƙara jaddada mata sannu.




by Aunty INDO