Chapter 3
To, bari mu koma wurin Aisha.
Tun da Ibrahim ya fita, Aisha ta rage sautin dariya, amma cikin zuciyarta har yanzu sautin fira da suka yi na jininta.
Ta kammala karin safe, ta duba agogo. Ranakun ba su da yawa, amma aikin gida yana kira.
Iskar safiya ta sake shigowa ta taga, ta tuna kalaman Ibrahim na jiya da dare:
“Ki kula da kanki. Karkiyi aikin mai wahala. Duk wani aiki da kika san zai wahalar da ke, yahanani. Samun kulawa ta musamman daga gare ki ajiye shi, idan na dawo zan yi. Saboda jikin ki bai dace da aikin wahala ba.
Dani ya dace. Ke kawai an halicce ki ne domin ki nishadantar da ni, ki bani natsuwa. Ki yi mini tausa yayin da aiki ya gajiyar da ni, tare da wannan lallausan hannu ki mai santsi.”
ta lumshe ido. Sa’an nan ta buɗe su, tana jin kamar yanzu ne yake furta mata kalaman.
Ta yi murmushi kaɗan, ta fara goge ɗakin.
Aisha ta gama goge ɗakin, ta duba agogo sau biyu. Lokaci na tafiya a hankali, amma zuciyarta na cike da natsuwa saboda kalaman Ibrahim.
Kafin ta gama shiru, tunanin da ba zai taba barin zuciyarta ba ya sake dawowa mata. Duk da tana ƙoƙari ta ɓoye shi daga Ibrahim, sai bayan ya fita ne take samun damar tuna wannan abu mai barazana ga rayuwarta.
Tana tsoron rashin sanin makomar aurensu idan haka ya ci gaba.
Aisha na cikin wannan rudani na rayuwarta. Tana tunanin yadda za ta fuskanci mijinta a irin wannan halin, ita ma da ba ta gama tantance wa kanta ko shi waye ba.
Saqon wayarta ne ya dawo da ita daga tunanin da take yi.
Ta ɗauko wayar da hanzari, hannunta na rawa, domin ta san a irin lokacin ne yake turomata saƙon. Sai dai ta san mai saƙon ba cikakken imani da shi. Zai iya aikata komai, dan ganin ya maidata cikin halin rayuwar da ta bari baya, muddin bata walwale abinda ke tsakaninsu ba.
Cikin rashin kuzari ta miƙe, ta je ta kammala abincin rana da dare gaba ɗaya. Rashin wadatar da suke da ita ce ke sa idan suka tashi girki, take yinshi sau ɗaya don rana da dare, domin sauƙaƙa musu cefane.
Tuwo garin masara ta yi, tare da miyar kubewa busasshiya. Ta ji daɗawa da kayan miya, da wake wanda shi ne madadin nama a gare su.
Shima gidan ya ɗauki gyara. Ta share tsakiyar gidan da ke cike da yashi mai sanyi — alamar da ke nuni da suna kusa da bakin rafi.
Bayan kammala ayyukanta, ta je ta buɗe robobin da suke tara ruwa. Ta ɗauki bokitin roba, ta zuba ruwa, sannan ta ɗauki sabulu da suso ta nufi bandakin da ke tsakiyar gidan.
Ta yi wanka, ta fito ta koma ɗakinta. Ta buɗe ƙaramin akwatin ƙarfe, ta ɗauko kayan da za ta sa. Atamfar “yar roba” ce — riga da siket.
Bayan ta gama shafe-shafen jikinta, ta ɗauko turaren ruwa da Ibrahim ke siyo mata duk lokacin da ya je wurin aiki. Kwalba ce mai ɗauke da ƙamshi iri-iri. Ta shafa shi a kowane lungu da sako na jikinta, sannan ta saka atamfar.
Atamfar ta zauna mata sosai, domin jiya ne Ibrahim ya kai mata dinki, ya umarci su matse mata shi yadda idan ta sa za ta bayyana kyawun jikinta.
Tana tsaye tana gyara kanta, tana tsaka daurin dankwali, sai kawai ta ji an rungumota daga baya ba zato ba tsammani. Nan take ta ji saukar kiss a gefen wuyanta.