BAKIN RAFI.....

Chapter 4

by @hauwausani476

  

*bugun Zuciya*

Aisha cikin tsinkewar numfashi. Duk da ta san hannun mijinta ne, zuciyarta ta ƙara bugawa kamar yadda take yi kowane lokaci da ya kusanto ta ba zato ba tsammani.  

Ta juyo a hankali, fuskarta cike da murmushi mai gauraye da kunya.  
“Ka firgita ni wallahi,” ta furta cikin muryar da ke dauke da nishadi.  

Ibrahim ya kalli idonta, ya ɗan saki murmushi. “Ban so ki manta da cewa ke din tawa ce, ko da na fitar minti ɗaya.”  

Ya miƙa mata hanci, ya shaka turaren da ta shafa. “Kin san kin fi wannan turare ƙamshi.”  

Aisha ta sunkuyar da kai, kunya ta ƙara rufa mata fuska. Amma a cikin zuciyarta, kalamansa sun sake sanya natsuwa ta mamaye ta.  

Sai dai, cikin wannan lokaci mai daɗi, tunanin saƙon da ya zo mata ya sake dawo mata.  
Fuskarta ta ɗan canja.  

Ibrahim ya lura.  
“Me ya faru Ashantyyna? Me yasa murmushin ki ya ɓace haka?”  

Aisha ta ɗan girgiza kai. “Ba komai… kawai jiki na ne ya ɗan gaji ne.”  

Ibrahim ya lumshe ido kaɗan, kamar yana tantance karya ce ko gaskiya. Amma bai matsa ba. Ya riƙe hannunta kawai, ya ce:  
“Idan akwai wani abu da ke damun ki, ki sani ni ina nan. Ba za ki yi shi ke kaɗai ba.”  

Aisha ta danƙa masa hannu, amma a zuciyarta ta ce:  
_Idan ka san gaskiyar, basan ya za ta kasance a gare ka ba.  
Cikin wannan hali da muke ciki, bama zanbari ka sani ba. Zan walwale matsalar da kaina insha Allah._

Iskar da ya hura mata ne ya dawo da ita daga zancan zuciyar da take yi.

Ya ce: “Kawai ki sani ina tare da ke, ko da har yanzu kin ƙi bani labarinki.”  

Don taka warda zancen, tace: “Bari na sakama ruwan wanka, zumana.”  
Murmushi ya maida mata, domin ya san tayi hakan ne dan abar zancen.

Bayan kammala wankan, ya shirya cikin wasu kaya na shan iska, ya fito ya zauna inda ta yi musu shimfida. Yana kallon yanayin tsakiyar gidansu da ya sha gyara, yana yaba tsafta irin ta Aisha.

Gidan nasu ba gidan azo a gani ba ne.  

Sai dai yadda matar gidan ke tsara komai yadda ya dace, da kuma ajiye komai a muhallinsa, shine ke bawa gidan natsuwa da walwatacciyar ni’ima, a cikin kowane saƙo na gidan.

> *Anan mulura mu gane:*  
> Ba wai ƙaton gida kaɗai ke sa a sami natsuwa a gidan aure ba.  
> A kowanne yana yi, macce ta tsintsikanta, to ta samarwa da gidanta natsuwa, tsafta da kwanciyar hankali.  
> Sai taga tana farin ciki kamar yadda masu babban gida ke yi.  
>  
> Sannan mu gane da cewa, idan aka ce maka “wannan gida ne na masu hali” ko “na masu ƙaramin ƙarfi”, to gyara da tsafta yakeso. Ki iya ajiye komai a muhallin da ya dace. Wannan kenan.

---

*Back to labari*

Bayan takawo musu abincin, sunci sun sha ruwan randa mai sanyi. Sai ta tattara kayan, ta saka a cikin robar wanke-wankensu, ta kawo ƙyale ta rufesu gudun kar wani ƙwaro ya faɗa musu.  

Ta dawo gurin mijinta, ta fara yi masa tausan gajiyar da ya kwaso a gurin aiki. Yayin da shi kuma yake yi mata fira mai cike da nishadi, ita kuma tana murmushinta mai ƙayatar dashi.

Can kuma sai ya fara rera mata waƙar “Nazifi Asnanic”. Ya rungumota a jikinsa, ya fara da baitin nan kamar haka:

> Ke, ke, kece tasawa a mota,  
> Kece zinariyata,......

Har zuwa ƙarshen baitin, 

kiran sallah ne ya dakatar da su daga wannan soyayya.

Bayan ya fita zuwa masallaci, ita kuma ta shimfida darduma ta fara sallah.  

Bayan ta kammala, tayi wa Annabi salati, tayi istigfari, tare da azkar na magrib. Ta fara addu’o’inta da ta saba, waɗanda a koda yaushe suke tuna mata da tsohon labarinta, wanda ke sa ta kuka da damuwa da baƙin ciki.