Chapter---13
***Namiji Ƙanin Ajali***
By
Amdy Tejj d'Unique
Bismillahir Rahmanir Raheem.
Page ---- 13.
Na rintse idona da mugun ƙarfi ƙirjina yana bugawa,banyi aune naji saukar hannunsa akan hijabina ya fara ƙoƙarin rabani dashi,lamarin da yasa na buɗe idon da sauri na fara ƙoƙarin ƙwatar kaina dan sai yanzu na fahimci abin dake shirin faruwa, addu'a kawai nakeyi a cikin raina Allah ya kareni daga sharrin waɗannan azzaluman kada ba su ya basu nasara akan mummunar ƙudirinsu,to tayama zanƙi cin biri kuma inci dila? abinda na gujewa kenan na tarar?,Ohh Allah ka taimakeni.
Duk yadda naso ƙwatar kaina abin ya gagara sai da gardawan mazannan uku suka kaini ƙasa,toma ta ina zan iya ƙwatar kaina ko ɗayane ma balle har uku, ƙarfina dana ɗa namiji ai ba ɗaya bane, cikin ikon Allah sukayi nasarar yaga min hijabina biyu suka rirriƙe hannaye na, shi kuma ogan nasu ya fara ƙoƙarin ɓalle belt ɗinshi,na sake rintse idona akaro na biyu batare da na daina ƙoƙarin ƙwatar kaina ba,haka nayita roƙonsu ina kuka ina fisge-fisge amma a banza,ina fisge-fisgen ne cikin ikon Allah ya bani iko na damƙe hannun ɗayan da haƙorina da ƙarfin tsiya,bani da tabbacin yayi jini ko baiyi ba amma nasan ya cizu ba laifi,naushin da yakai min a gefen fuskata ya sa ni sakinsa ba shiri,shima ya sakeni yana yarfar da hanu,ban bi takan zafin da nakeji ba na wawuri wani dutse na rafkawa ɗayan da yake riƙe da ɗayan hannuna a kai ya saki ihu,shiko ogan nasu yayo kaina gadan-gadan nan shima Allah ya bani sa'a na kai mishi hauri a ƙasanshi,aiko ya durƙushe yana malelekuwa cikin azaba hannunsa riƙe da mararsa,ni kuwa wuf na miƙe a kan ƙafafuna ban bi takansu ba na doshi ƙofa ɗayan ya samin ƙafa daga kwancen da yake,nayi taga-taga zan faɗi Allah cikin ikonsa na tsaya daram, aiko banyi wata-wata na kwasa a guje ina jin sanda suka biyoni ni kuwa na ƙara ƙarfin guduna.
Nasha gudu ba na wasa ba a karo na biyu, banma san sanda suka daina bina ba wata ƙila ko dan sunga na fara fasowa garine suka koma oho musu,wani ƙarƙashin bishiya ƙarasa yaraf na zube a dandaryan ƙasa ina maida numfashin wahala,na rufe idona na kai hannuna kan jakar kuɗina da na ɗaure da ɗan kwalina a ƙuguna ɗaurin huhun goro,wanda yanzu haka zafi nakeji a ƙugun,na kai hanu na shafa gefen fuskata da yake min zafi sakamakon naushin da nasha wanda sai yanzu ma na tuna dashi,ya kumbura dan inajin hakan a yanzu ko ban taɓa ba saboda inajin yadda idona ya ɗan shige ciki.
Bansan iya adadin lokacin da na kwashe a wajen ba magana naji akaina hakan yasa na buɗe idona kalli mai maganar, wata tsohuwa dattijuwa ce"baiwar Allah lafiya kike kwance a ƙasa haka kodai ba lafiya ne?"tayi maganar tana taɓani.
Da ƙyar na buɗe idona na kalleta,yunƙurawa nayi na miƙe zaune na kalleta a karo na biyu nace"sannu mama"nayi maganar a kasalance,da gajiya sosai a muryata.
"Sannu ƴannan,daga ina kike? me ya sameki? Kika zo kika kwanta anan"ta jero min tambayoyin lokaci guda.
Na kalli yanayin garin,rana ta doshi faɗuwa da alama ma anyi sallar la'asar"dan Allah ki taimaka min da wuri inyi sallah"na furta kawai ba tare da na amsa mata tambayoyinta ba.
Ta jinjina min kai"insha Allahu baza a rasa ba muje, gidana ba nisa daga nan kinganshi can"ta ƙarashe tana min nuni da wani gida dake kusa da inda muke,ta kamani na miƙe tana riƙe dani muka shiga gidan, madaidaicin gidane na masu ƙaramin karfi mai ɗauke da dakuna guda uku falle-falle sai kitchen da ban ɗaki da madaidaicin tsakar gida yasha siminti a share fesa"sannu ƴannan samu wuri ki zauna ga tabarma"ta faɗa bayan ta shiga ɗaki ta ɗakko tabarma ta shimfiɗa.
Zaman nayi kamar yadda tace duk da ni sallah naso na fara yi,sai sannu take kai kace ita turoni garin yin barar,matar akwai kirki,bayan ta kawo min ruwa nayi sallah har abinci ta kawo min amma nasan sam bazai shiga wannan cikin nawa ba dan haka ko sake kallon inda yake banyi ba,muka gaisa tace''sai dai
har yanzu bansan sunan malamar ba,nidai sunana Hansatu amma ana kirana goggo Hansai,yara na biyu Maryam da Abubakar duk sunyi aure Abubakar ne babba yana aiki a Abuja, Maryam kuma tana Kaduna yanzu haka dagani sai jikokina muke zaune a gidannan, ƴaƴan wannan yaron ne,sunje makaranta anjima kaɗan zaki gansu Nabila da Kamal, hmmmmm ja'iran yara kenan"
Duk da damuwar da nake ciki sai da taso ban dariya jin ta gama faɗar sunan mutum amma wai yanzu kuma tana cewa wai wannan yaron,hmmmm na fahimci matar akwai surutu kuma bata da baƙunta,ta zauna tana bani labarinta sai kace na tambayeta, koda yake wannan ya nuna tana son na faɗa nawa labarin ne,ina cikin wannan tunanin ne na jiyota tana faɗin
''Babansu wai sai dai na bar gidan nan na koma Abuja ji wani zance fa, gidan da aka kawoni tun ina shekaru goma sha, sai kurum yanzu yazo yace wai na barshi,niko nace bazani ba in yaga na bar gidan nan to mutuwa ce,yoni inama zan yarda inje wannan matar tasa mai halin turawa ta karni tunda sauran kwana, duk da inason ganin Malam amma ba yanzu ba sai naga ƴaƴan wannan ja'irar tukun,
Ta ƙarashe maganar tana matsar hawaye da haɓar zani, duk yadda naso hana kaina dariya ya gagara na sunkuyar da kaina ƙasa inayi a hankali,
Kamar wacce a tsunkula ta goge fuskanta da haɓar zaninta ta kalleni tace"amma ke meya sameki dan bisa ga dukkan ba lafiya ba"
Shiru kawai nayi na sunkuyar da kaina ƙasa.
''Ki saki jikinki yarinya kinji daukeni kamar mahaifiyarki,ko bakiga na haifi Kamarki bane halan"tayi maganar da sigar zolaya
Na ɗan murmusa kaɗan sannan na faɗa mata abinda kawoni garin da abinda ya sameni har ta ganni a wajen da ta sameni a taƙaice.
Fuskarta cike da tausayina murya kamar zatayi kuka tace"Allah sarki sannu ƴannan, amma nidai ban taɓa jin wai in zakayi sai kayi wani register an san da zamanka ba, amma halin mutane sai su,ana zagin shuwagabanni ne kawai, amma kowa ya samu dama koda na gadin ban ɗaki ne sai kinga tsiyar da zai tsula"
Nayi shiru batare da na amsa ba sai sake sadda kaina ƙasa da nayi ina wasa da yatsuna.
Ta sake cewa"ki kwantar da hankalinki inshallah zaki samu mafita,bari yaran nan su dawo bansan inda yarinyar nan ta samin wayata ba amma sun kusa dawowa bari tazo ta kira min wannan yaron,karki damu zai taimaka miki zai ɗau nauyin komai"
Wani farin ciki ya kama zuciyata, dama abinda nake faɗawa Habibu kenan, inshallah Allah zai mana mafita to gashi kuma ya kawo,a duk da a ɓangare ɗaya kuma ina tunanin yadda za ace zata taimakamin da waɗannan manyan kuɗi haka,duba da yanayin gidansu bai nuna na masu wannan ƙarfin bane,kau da tunanin nayi gudun kar ya sage min gwiwa duk da banga alamar hakan ba,kamar zan kwanta haka na riƙe hannunta na durƙusa inayi mata godiya ina hawaye ina jero mata addu'o'i ita da zuri'arta,tun tana amsani da amin har sai da ta nuna min godiyar ta isa haka,
"In banda abinki ay wanda yayi alheri shi ya kamata ya gode dan shi aka rubutawa lada,mai kuɗi bai gane bane, da idan yayi alkhairi shi kamata ya gode saboda ajiya yayi a inda wannan kuɗin nasa bazaiyi amfani ba,shi alkhairi da taimakawa mabuƙaci kamar zubin adashine akwai ranar ɗauka duk daren daɗewa,za a riɓanya masa ninkin ba ninkin abinda ka bayar a inda kuɗi ko mulki cin hanci da rashawa bazasuyi mai amfani ba, sai wannan alkhairin daya gina shi abaya a sanda yake hali,shi zai zama gatansa,Allah Ubangiji yana son bayinsa da rahama ya bamu hanyoyi da dama da zamu samu rahamarsa cikin sauƙi amma mukanyi wasa da damarmu,wani idan yasa wannan damar gani yake kamar Allah ya bashi wata dama ne na cin zarafin wani,yana ganin kamar Allah yafi sonshi ne aka wannan ɗin, da wannan damar sai ya zama mai girman kai ya dingayiwa mutane izgilanci,yana ƙyashin yin taimako dan kada ya taimake ka yana ganin zaka fishi arziki inya taimakeka, maimakon yayi amfani da dukiyarsa a inda ya dace a'a,sai yayi amfani dashi wajen saɓawa Allah bazai iya bada taimakon dubu goma a masallaci ko makarantu ba,amma zai kashewa mace dubu ɗari dan yayi zina da ita"
Hawaye ya sulmiyo akan kunci sanda tazo nan a maganarta,na tuno abinda ya baroni da gida,nazo nan.
Ta cigaba da faɗin"su sangarta ƴaƴansu, su saka musu makudan kudi a asusun banki suyi sharholiya da abokansu da ƴammata,wasu ma har shaye-shaye suke yi,su aje matan banza kuma iyayen sunsan a banza a kashe kuɗaɗen amma bai dame su ba,su saya musu suturu masu tsada, wanda wani takalmi kawai da za'a siya asa a ƙafa zai ciyar da gidan wani talaka na wata guda a wadace ba maleji,su saka ƴaƴan su a makaranta mai tsada, Alhalin ɗan maƙocin su na nan baije daidai ko makarantar gwamnati ba,ay rayuwarmu a yau sai dai Allah ya gyara amma taimako yayi ƙaranci a musamman a ƙasar nan tamu”
Shiru nayi bance komai ba ina nazarin maganarta,tabbas maganarta gaskiya ne,ba a taimako a wannan zamanin kowa kawai kansa da iyalansa ya sani, daga masu kuɗi har masu mulkin, tabbas masu kuɗi basu gane cewa talakawa mabuƙata hanyace da Allah ya kawo musu da zasu riƙe a matsayin tsani dan taka wani matsayi da kowa yake fata a ranan gobe ba,kowa kawai burinsa idan ya samu ya gina kansa ƴan siyasa a matsayinsu na shuwagabanni basu damu da waɗanda suke jagoranta ba,burinsu kawai ya za suyi su gina kansu da zarar buƙatarsu ta biya a wajen talakawa shikenan sun gama musu amfani,wani ma bai sake waiwayanku sai ranar da wani buƙatar ta sake tasowa zai tuna daku"
"Allah kasa mu dace''na faɗa a fili
"Amin"ta amsani......
Mu hadu daku a next page zakuce na dage inata kawo sharhi akan masu kuɗi ko? Rashin taimakon da muke fama dashi a wannan lokacin yana damuna shiyasa da aka taɓo fannin yasa na dage wannan kaɗan daga cikin kenan nasan kuma kunsan da wannan,masu kuɗi kuma kuyi haƙuri kuyi duba da maganata gaskiya na faɗa muku, Allah yasa mu dace ya bamu ikon gyarawa Ameen....
Ku cigaba da kasancewa da Ni
Amdy Tejj d'Unique...
Sai kun jini,ngd da bani aron lokutanku.
Bye Bye, see you next time.....