BARRISTER SUHAIL
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
KUYI HAƘURI DA RASHIN SAMUN POSTING JIYA YA FARU SANADIYYAR RASHIN CHARGI
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️----12
Sameer na barin office din nadia ta shigo hannuta riƙe da files
ɗago idanun sa yayi ya kalleta kallo da yayi mata irin na miya kawo ta ne din nane
Nadia ta ce"sir daman Akwai meeting da chef of staff by 12pm"
"cancel it"
Zaro ido tayi tana kallon Suhail,a iya Sanin ta Suhail bai taɓa fashin meeting ba kasa Daurewa tayi ta ce"sir everthing is okay, ko kana bukatar taimako na"
a fusace ya ce"no nadiya Please leave"
juya wa tayi ta fita bata so Ganin Suhail a wannan yanayin ba gashi ya nuna baya bukatar taimakon ta,ta tabbatar da wani ke cikin damuwar nan da tuni Suhail ya nemi hanyar da zai fitar dashi gashi shi a damuwa ta ƙasa fitar dashi tana wannan tunanin har ta ƙara sa reception inda ta tura takarda cewar Suhail bashi da lafiya bazai samu damar hallatar meeting ba.
bai jira lokacin tashi ba ya koma gida da kwanciyar sa bacci mai nauyi ya dauke sa bashi ya farka ba sai karfe hudu da rabi wayar sa ya dauko ya tarad da misscall din Abba sai lokacin ya tuna da Maganar da yayi masa da safe.
bathroom ya shiga yayi wanka ya daura Alwala farar jallabiya ya zura yayi sallah yana gama wa kiran Abba na sake shigowa baya ya daga Abba ya ce"Suhail kai nake jira fa"
"Abba gani nan"
ajiye wayar ya fara shirya kansa cikin wani Haɗaɗɗen men laces White colour an mishi dinki Captain ya fito a Suhail dinsa matashi mai ji da wanka indai kasan Suhail to tabbas kasan yaro ne ɗan kwalisa kaf cikin abokan sa babu wanda yafi shi daukar wanka duk kayan da yasa suna dace wa da jikin sa feshe jikin yayi da wasu tsadaddun perfumes wanda takanas yayi ordern su daga makkah Suhail mutun mai bala'in san Kamshi duk tsadar turare indai Kamshi sa ya kwanta masa baya shayin ya fitar da kudi ko nawa ne ya siya.
Bayan ya gama ya dauki keys din motarsa da wayar sa ya fita a parking space ya tarad da Abba yana jiransa ba bata lokaci ya buɗe masa back seat ya shiga shima ya zagaya kujerar driver ya tada motar suka fita daga compound din gidan.
Cikin natsuwa yake tukin har suka isa gidan da taimakon Abba dake yi mashi kwatance gidan Malan.
a kofar gida suka sami Malan kamar ko yaushe yana bada karatu ganin fitowar Abba daga mota yasa ya tashi da sauri ya taresa sa Suhail baida niyyar fitowa sai da Abba yayi masa magana suka ɗunguma zuwa cikin gidan.
Malan a falon sa ya Sauke su bayan sun gaisa Abba ya gabatar da Suhail a wajen malan,tun daga yadda Suhail ya buɗe wa mahaifinsa kofar mota Malan ya yaba da tarbiyar sa da hankalin gashi duk maganar da ake yaki daga ido ya kalle su.
Abba ya ce"idan ba damuwa yana so ayi bikin nan da karshen wata"
jim malan yana so ya ce "nan da sati ukku yayi kusa"
" Abba yayi murmushi dan yasan harkar biki akwai kashe kudi gashi bai jima da hidimar sauka ba"
ya ce"Malan inaso ka sani duk wata hidima da zaku yi a bikin nan tun daga kan abinci da sha da sauran abubuwan buƙata na dauke maka su"
Malan ya ce"a'a Alhaji bazayi haka ba kaima kaji da naka ɓangaren"
Abba ya ce"ko ba Suhail zai auri yar ka ba ni mai tsaya maka ne a Wannan bangaren dan haka kar kaji komi"
Malam har ya rasa kalaman da zaiyi amfani dasu wajen godewa Alhaji munnir Mahmud bisa wannan karamcin da ya masa malan ya ce"Alhaji mun gode Allah saka da Alkhairi ya jikan magabata"
Tashi yayi ya ce"muna ta zance bari a kawo maku abin sha"
ya shiga dakin Ammi tana zaune kan kujera Imam ta dora kan ta akan cinyar ta tana mata tsifa gashin nan baki wullik duk ya zubo ya rufe mata fuskar ta.
Malan ya ce"Maryama ki Iman ruwa da lemu ta kawo wa baƙi daki na"
"to" Ammi ta ce
Iman dake ƙoƙarin tashi daga cinyar Ammi ta ce"Ammi su wanene"
"ta ina zan sani Iman bayan tun dazu muna nan tare,kin san Malan bai rabo da baƙi"
kinga tashi ki shiga ciki ki dauko sabon tray din nan da zaituna ta kawo kizo ki miƙa yana jira.
Ammi ta jera drinks da ruwa akan plate din tun sauran irin na saukar Iman ne da mutane suka tara masu , taba Iman bayan ta saka doguwar hijabin ta har ƙasa ta dauka ta nufi hanyar Dakin.
riskar kanta tayi dajin wata mummunan faduwar gaba ta daɗe a bakin kofar dakin kan ta shiga.
wani sanyayyen Kamshi taji ya daki hancin lumshe idanun ta tayi cike da san ganin mai kamashin a haka ta karasa cikin Dakin Malan Abba na Zaune kan kujera Suhail kuma na duƙe a gaban sa ajiye tray tayi gaida Abba sai lokacin Suhail ya ɗago fuskar sa sukayi ido hudu da iman a tare Zuciyarsa ta buga iman ta fara saukar da idanun jin wani irin kwarjini da Suhail yayi mata.
Tashi tayi zata fita Suhail ya bita da kallo ganin yadda take tafiya a nutse kamar mai kirgar takun ta har ta fita daga ɗakin bai sauke idanun sa.
duk abinda yake akan idanun Abba sai da ya taɓa sa da Kafa ya dawo kunya yaji duk ta kamasa.
bawai bai taɓa ganin mai kyaun Iman ba but komai nata special ne the way she talk so cooly and the way she walk Tamkar mai koyon tafiya.
Malan ya kalli Abba ya ce"wannan ita ce iman duk da ma kai a gare ka ba baƙuwa bace"
Suhail sai lokacin da gane dalilin da yasa Abba ya zaba masa ita bawai saboda ilimi,da tarbiya ko nutsuwa bane komai na yarinyar is special.
Ba irin zeenah ba da gaba daya rayuwar ta babu kamun kai a ciki
Kai jama'a ku jimin Suhail wai shi da kansa yake cewa Zeenah bata da kamun kai🤔😉
Tun bayan fitowar Iman daga falon…
Zuciyarta ta kasa nutsuwa
Kai tsaye ɗakinta ta shiga ta zauna bakin gado a ranta tana tunanin ko su waye?
Har yanzu kamshin turaren Suhail na yawo a hancinta.
Wani irin nutsuwa da kwarjini ta gani tattare dashi wanda kesa zuciyarta bugawa babu ƙaƙƙautawa.
a falon Abba kuwa an tsaida ranar biki sati ukku masu zuwa har aka kare zancen Suhail bai yi magana ba ,haka kawai malan Abdallah yaji Suhail ya kwanta masa a rai tambayar kansa yake dama yaran masu kuɗi akwai nutsatsu haka irin Suhail ga tarin nutsuwa a tattare dashi.
Bayan sun gama tsara duk abinda ya dace Alhaji ya tashi akan zasu wuce malan ya rakasu har Kofar gida a daidai lokacin Mubarak na shigowa hannu ya ba Abba da Suhail suka gaisa.
Suhail ya kalli Mubarak Fuskar iman ya gani amman shi ya dan fita hasken fata ƙadan
Malan ya kalli Abba ya ce"wannan shine Mubarak wato yayan ita Khadija su biyu kadai yaran da Allah ya azurtani dasu"
murmushi Abba yayi ya ce"Masha Allah ya batun karatu kuma"
Malan ya ce"ya kammala degree din sa a fanin computer yanzu haka yayi jarabawar daukar ma'aikata muna jiran sakamakon ne"
Abba ya ce"hakan yayi Allah ya bada sa'a"
duka suka amsa sa Amin
Suhail ya bude wa mahaifinsa motor ya shiga ya ja suka bar Layin.
shiru ya mamaye motar yayin da Suhail gaba ɗaya hankalin naga tuƙin da yake.
Abba ya ce"ina fatan yanzu ka fahimci dalilin da yasa na zabar maka ita"
ƙasa magana Suhail yayi kunya ta kamasa yadda yabi Iman kallo har saida mahaifin ya taɓo sa.
Abba ganin Suhail baida niyyar magana ya kyalesa a haka har suka isa gida Kofar gida yayi parking motar dan zai sake fita da ita.
suna shiga ciki Abba ya nufi part din aunty Fauziya da ita keda girki suhail ma ya koma nashi part din.
Aunty Fauziya na dinning area tana jera Flask din abincin dare shigowar Alhaji ya sa ta nufi bakin kofa ta tare sa tare suka ƙaro sa cikin palorn zama yayi kan kujera yana sauke ajiyar zuciya aunty Fauziya ta mishi sannu da zuwa ruwa ta dauko masa ya sha,bayan ya gama ya sheda kan sun ajiye maganar auren Suhail nan da karshen wata.
wani farin ciki taji ya lulluɓe ta ce"Alhamdullilah Allah ya tabbatar mana da Alkairi ya nuna mana ranar lafiya"
Abba ya ce"zan tura maki kudi ba account dinki wanda za'a fara hado lefe"
Gaban ta ya fadi lokacin daya fara'ar dake kan fuskar ta gushe jin Alhaji na son saka ta cikin hurumin da ba nata ba.
da kyar ta buɗe baki ta ce"Alhaji ina ganin kayi wa laila magana kamar tafini sanin abinda ya kamata tayi tunda Suhail ɗa ta ne"
cikin fushi Abba ya ce"ai nasan da ita kinga kema idan kin hauko hanyar musu dani a gidan nan ki faɗa min sai na kira bahijja a kano na tura mata kudin tunda ita na isa da ita"
"a'a Alhaji nima ka isa dani kafi kowa sanin halin laila bana so in zaƙe mata cikin al'amurran ta gudun gori da wulakanci"
Alhaji ya fahimce ta dan Fauziya macece mai taka tsan-tsan tunda ta lura da halin Laila ta kama kanta waje guda ko bikin Naima da za'ayi kin binsu tayi siyo kayan daki yanzu ma Abinda yasa yayi mata maganar yasan ko yayi wa laila zata ce ba Ruwanta q harkar bikin shiyasa ma ya saka Fauziya a ciki
Alhaji ya ce"Yanzu abinda. za'ayi zan kira Zarah idan tana da dama sai tazo lu tafi kanon tare daga chan sai ku wuce tare da bahijjar hakan ai yayi ko"
"Eh,yayi Alhaji"
tashi yayi yana gyara zaman babban rigarsa jin an fara kiran sallah Magariba
Suhail na gama sallar magariba ya hau motar sa ya nufi gidan su Zeenah
Yau ma kamar kullum parking motar yayi ya nufi cikin gidan inda suka saba haduwa ya tsaya bayan ya kira ya faɗa mata Yazo.
bata wani jima ba ta fito sanye da riga da wando na jeans sun fito mata da duk wata hallita ta jikin ta rigar iya ciki ramin cibiyar ta duk a waje.
Suhail da ido ya kafe ta har ta karaso wajen kare mata kallo yayi ganin irin shigar da ta fito dashi kan ta ko dann kwalli babu sai zaren attachment dake binta tamkar wacce babu kalmar shahada a bakin ta.
ganin Suhail ya hade rai yasa ta dubi shigar kanta daga sama har ƙasa tasan fishin da yayi baya da nasa da shigar da tayi tun kan yayi magana. ta koma sako doguwar rigar Abaya tare da mayafinta ta fito .
Abinda ke birgesa da Zeenah idan tayi abinda. ba daidai ba iya kallo ɗaya yayi mata ta sani kuma tana ƙokarin gyara hakan yasa kullin yake ɗora ta akan hanya domin ita duk abinda take yi tana ganin daidai ne.
Zeenah ta tashi a sangarce ita kadai iyayen ta suka haifa bayan shafe shekaru sama da Goma Allah bai basu haihuwa ba hakan yasa ta taso a sangarce duk da mahaifan ta na iya kar ƙoƙarin su wajen nuna mata abinda ya kamata haka Suhail da tun a University shi kadai ya isa ya tanƙwara.
Iyayenta har mamakin ta suke yadda take tsoron fushin Suhail bata tsoron fushin su.
Ganin baida niyyar magana zeenah ta ce"Haba suhail ka saki ran mana"
"Ashe kin san abinda ya dace so how many time nake fada maki ki daina wannan shigar baki gani gidan ku cike yake da mazan da ba muharraman ki ba"
gira taja kadan ta ce"kuma tunda na chanza ba shikenan ba"
zama tayi kusa da inda yake Suhail so yake ya fada mata abinda ke faruwa amman yana tsoron yanayin da zeenah zata shiga.
hirar suka cigaba inda Zeenah take rokansa akan ya turo neman auren ta tana fuskantar matsin lamba sosai a wajen mahaifin ta inda ya bata nan da wata biyu idan har Suhail bai gabatar da iyayen sa zai bada auren ta ga ɗan yayan shi.
ajiyar zuciya Suhail ya sauke ya kalleta ya ce"Zeenah You know i love You kuma nayi maki Alƙawarin zan aurenki"
ki bani nan da wata ukku zan gabatar da iyayena akwai wani project da nake son gamawa idan komi ya lafa zan turo magabata ayi maganar aure trust me"
shiru Zeenah tayi dan ba tun yau yake fada mata haka amman tayi wa kanta Alƙawarin wannan shine last chance da zata ba Suhail matuƙar baiyi abinda ya kamata zatayi haƙuri ta auri Abbas Cousin brother din ta koda kuwa zata mutu da son Suhail din ne
jama'ah ko zeenah zata iya haƙura da Suhail kuwa?
idan har kuna comment yadda ya kamata zaku riƙa samun page biyu a rana ko na kara yawan typing