NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)

CHAPTER 26 (A part of him.....)

by @deejasmah


Shiriritar da ta dinga yi a cikin d'akin ya sa har aka idar da Magrib ba ta fito ba,sai da Ummu ta kirawota a waya  kafin ta fito ita fa har mantawa tayi da azumi ake yi ta k'ule tana d'iban kayan da zata wuce da su kd kamar wacce ba ta dasu. Sanda ta fito dukansu suna baje a parlor ana iftar har da Abbu don zuwansu Hajjah ya sanya dole yau a nan za a yi ba can parlornshi da aka saba ba.



Kusa da shi ta zauna tana mai gaisheshi kafin ta masa barka da shan ruwa, kanta ya d'anyi taɓa kad'an yana cewa " lafiya lau sweetheart, ya kike da maigidan naki?". Sai time d'in ta dubi gefen Burhaan dake zaune yana juya cup d'in kunun gyad'an da aka zuba masa alamun an saka madara ne a ciki da sugar, wani kallo yayi mata a kaikaice mai d'auke da harara. Murmushi ta saki tana cewa " mu na lafiya Abulkhairi, Yaa an sha ruwa lafiya?" Ta buk'ata tana mai sake dubanshi, d'an d'ago idanu yayi yana mai cewa " Alhamdulillah, ke ma dai ki samu ki sha ruwan yanzu" toh ta furta kana suma su Hajjah tayi musu duk suka amsa da kulawa. A natse suka yi bud'a bakin inda ita Nadeefah ta dinga passing daga kwanon Abbu zuwa na Ummu, shi dai Burhaan kallonta yake tayi cikeda birgewa ta gefe guda kuma wani kewa ne yake shigarshi duk dako ga ta a gabanshi amma kuma sabawar da yayi wurin iftar da kuma yanda take tarairayarshi a gida. Duk da dad'in dda abincin yayi masa amma bai wani ci da yawa ba ya zame hannunshi ya d'au kunun kawai yana sha, Ummu ce tace " son ka k'oshi ne ko bai maka bane a yi maka wani?".


Murmushi yayi yana cewa " no, i'm okay". YaMara ce tace " ke ma Sameeha da d'aurema k'arya sai kace baki san iyayin Burhaan ba, kina kallon yanda tun d'azu yake wani d'aga hanci kamar ya fi kowa kafar shan iska a nan". Kusan kowa a wurin sai da yayi k'aramar dariya ba kuma na maganar da ta fad'i ba amma na yanda ta wani kyab'e baki tana hura hanci irin yanda yake yi, Nadeefah ko dubanshi tayi yanda shi d'aya ne bai yi dariyar ba sai ma d'aure da yayi murmushin dake kasheta ya d'auke d'if daga fuskar tace " kai YaMara...."



"Toh mara ta ido shigar masa zakiyi ke a dole mai miji ba haka yake yi ba ne ko menene " Ta katse maganar da tayi niyyar yi Hajjah da ta gama goge baki ne tace " ai baki san shiga fad'a ba sai a na gobe Ramadan........" Ta d'auko labarin dramarsu da Lele tana basu me za a yi in ba dariya ba har shi Burhaan don da shi bai d'auka maganar tayi tsayi har haka ba, sai da takai k'arshe ne ta d'aura da cewa " wai kuma daga shigarta d'aki sai ga kiran Burhaan a wayata wai yana titsiyeni da tambayar me akai mata, saboda ya maida ni sa'arshi".



Cikin dariya Ya Madari tace " toh inda dukanta akayi rama mata zai yi ne ko me?". Cewa tayi " k'ila da a station zan kwana an tab'a 'yar Lele" sake kwashewa da dariya akayi Abbu yace " wai to menene abun kuka a maganar nan?".



"Samun wuri mana Abbu, ai don taga ana biye mata ne shiyasa ai na fad'i ba ranar da zatayi hankali". Tayyib ya furta cikeda tsokana cije lips yayi yana mai jin haushin kalmar da yake fad'i, ya san sako akan samu haka kuma duk cikin shak'uwa ce ba wai izgili ko muzanci ba but ba fa d'aya ya fad'i ba kusan sau uku kenan a zuwansu Abujan ya sa shi cewa " hey Tayyib, ka kiyaye harshen ka".



Duka kallo suka bi shi da shi jin yanda yayi maganar  da sauri Tayyib ya dubi fuskar Lele gwalo tayi masa tana murmushin nasara, kai ya gyad'a yana cewa " sorry Yaya" da ido ya amsa masa alamum issokay. Tafa hannaye Ya Mara tayi tana mai cewa " eh ni ko yanzu naga zahiri, au har yayanta ma shiga tsakaninsu zaka yi?". Kumbura baki yayi cikin basarwa yace " Yayantan ai k'anina ne ko?". 



"A wurinta kuma wa ne kar ka sa ta raina shi don matar nan taka ba ta iya samun wuri ba " tale baki tayi zata yi kukan shagwab'a jin maganar YaMaran shi ko sake cewa yayi " duk samun wurinta ai raini baya cikin halayyarta" sai kuma ya cije cikin bakinshi don jin fitar maganar kawai yayi,duka 'yan parlorn gum sukayi Dalhat ya kalli Tayyib da baki yayi masa magana mara sauti " love nwantiti" dariya suka k'umshe dukansu. Abbu da Ummu ko duban juna sukayi suka saki wani murmushi mai d'auke da sak'onni da yawa don ko ba komai hankalinsu ya kwanta da irin kulawar da Burhaan yake ba wa Nadeefah atleast yanzu ba su da damuwa ba kamar da ba haka su Hajjah suma. 



Ita ko sai murmushi take kamar wawa wai yau Yaa Islaam ne ya yabeta har da tare mata fad'a, ahh lallai da alamu hak'arta yana kan ganiyar cimma ruwa. Shi dai ko a jikinshi don tashi yayi ya d'auki excuse ya fita ya koma can d'akin da aka sauke shi, zama yayi a parlorn yana mai jiran kiran sallah yayinda yake sake jin kewar tata na kamashi da yanzu a gida ne da tana kwance a kafad'arshi tana ba shi labari ko da ba zai amsa mata bane ko tana waya ko video call da 'yan gidansu. Yana nan zaune har aka kira sallah ,yau a nan parlorn Ummun sukayi taraweeh dukansu shi ne kuma ya ja sallahr Dalhat ya yi masa ladani.



Ana idar da sallahr Nadeefah ce ta fara hayewa sama don yin baccin k'aidan da ta sabarwa kanta na bayan ishai, da idanu ya bita a ranshi yana cewa " lazy girl zata je baccin sabo ". Su ko basu ma kula da ita ba don sabon hira aka fara cikeda shak'uwa da kuma so da fahimtar juna kasancewar shi ba ma'abocin magana ba ne ya sanya shi fita ya bar musu d'akin, zama yayi ya kunna news yana kallo sai time d'in ya kira su Abba da Umma a waya sun ko dad'e suna hira kafin suka ajiye wayar. Data ya kunna yana chat rabin hankalinshi yana kan TV.



Ba ita ta tashi ba sai kusan 11 yanda ta saba, wanka ta samu tayi ta sanya nighties a cikin na ta na gida. Abaya ta sanya tana sauka k'asan bene babu kowa a wurin alamun duk sun wuce ciki sun kwanta, zama tayi a cikin couch ta ciro wayarta ta fara dialing numbern Burhaan. Sai da yayi ringing kusan uku ya d'aga a kasalance yace "wife....."



"Yaa kana lafiya?" Ta tambaya da kulawa lumshe idanu yayi ya bud'e kana yace " lafiya lau, har kin tashi daga baccin?". Cewa tayi " na tashi ka ci abinci kuwa?".



"Na yi iftar ofcourse".


"And baka buk'atar komai kuma?".


Cije baki yayi tabbas shi ko yakeda buk'ata ba kuma na komai ba sai na kasancewar ta kusa da shi a wannan daren amma abunku da mai hali sai cewa yayi " uhm babu".


Sake shagwab'e murya tayi tana mai cewa " Yaa mana, na san iftar kawai ba zai rik'eka ba shall in dafa maka indomie toh?".


Kallon agogo yayi after 11 yaushe har aka dafa noodles d'in har yaci sai dai kamar yadda ta fad'i d'in yana buk'atar abinci yana kuma buk'atarta so dole ne ya san yanda zai yi ya ganta kuma that's the only hanya. Ya sa shi cikin sanyin murya yace " ba indomie ba dai dare yayi da za kiyi girki just ki nema min wani abu mara nauyi amma kar ki yi girki".


Murmushi tayi tana mik'ewa tace " sure, bani minti biyar" alright ya furta yana sake kwanciya a cikin couch d'in da yake kai. Ita ko kitchen ta nufa nan ta fara duba abinda za ta kai masa, a cikin wata bowl mai murfi taga peppered soup na kayan ciki. Sa shi tayi a microwave don d'umama masa, bayanshi ba taga komai ba don an tabbatar da an fitar da kayan fridge d'in gidan don gabad'aya za su wuce Umrahn da su Ummu. Sai kawai ta ciro apple da kwakwa da kankana da dabino ta yayyanka shi kuma dabinon a cikin ruwa ta sanya ta d'an zafafa shi a wuta har ya d'an narke, yogort mai sanyi sosai ta ciro ta had'a masa yogofruit ta zuba minced fruit mai d'an yawa a kai. A fridge ta saka sannan ta wuce d'aki veil ta d'auka ta yafa don dama ba d'ankwali a kanta, tana fitowa ta ciro komai ta had'a a tray ta d'auki ruwa da drink ta k'ofar kitchen d'in ta fice zuwa part d'in shi.




Knocking tayi a bakin parlorn a hankali gudun kar su Ɗalhat su jiyota, kana ta tura k'ofar shiga parlorn ba haske sai na tv kawai. Tsayawa tayi ba tayi gaba ba ba kuma ta koma baya ba tana mai tunanin hanyar da zata bi ta isa gareshi, sai kuma ta ciro wayarta da niyyar kiranshi har ta fara kiran number shi sai kawai ya kunna hasken na shi wayar cikin muryarshi mai amo da dad'in saurare da ya k'ank'antar a k'asan mak'oshi yace " gani nan, ki kunna wutan".



Ajiyar zuciya ta sauke ta hasken da ya kunna ta isa inda switch yake guda d'aya kawai ta kunna na jikin ceiling , k'afafuwanta ta cira ta isa gareshi a kan table d'in gabanshi ta ajiye trayn hannunta. Kamar yadda a kwanakin nan take son kwanciya gefenshi haka yau ma tayi, shigewa jikinshi tayi duk da ko kujerar tayi musu kad'an.


Rik'eta yayi da kyau yana cewa " ba abinci kika zo bani ba kenan?". Cikin k'aramar muryar da ta sake saukar masa da kasala tace " shi na kawo mana, oops gashi nan ma kar ya huce ". Lumshe idanu yayi ya bud'e yace " uhmm". Sai dai maimakon ya tashin sai ya fara shinshinar wuyanta yana sakin mata numfashi mai d'umi, itama lumshe idanu tayi tana karb'ar sak'onninshi a jikinta tana tayashi abinda yake mata sai aikin sakin numfashi sukeyi cizonta yayi a kunne kad'an yana janyewa duk jikinshi yayi weak. D'aukar abinshi yayi zuwa ciki inda a can aka baje kolin abinda rai yake da murad'i aka maida miyau inda ya d'auke su lokaci mai tsayi sosai, har wanka ma tare sukayi sai da suka fito ne ta kalli agogo ta zaro idanu tana cewa " innalillah Yaa dare yayi fa sosai ".



"In kina jin bacci ai sai ki kwanta". Ya furta yana sake tsane ruwan kan shi, tura baki tayi tace " Yaa za a ga bana nan, ban gaya ma kowa ina nan ba fa".


"And so? Ai ba laifi kika yi ba babu mai ce miki don me".

"Ai Yaa da kunya da asuba a ganni na fito daga nan ko".



"Saboda zunubi kika aikata ko? Yanzu toh me zakiyi?".



"Ka rakani please ta k'ofar kitchen na fito " ta k'arashe tana shagwab'e fuska, cewa yayi " tunda nan daji ne da baza ki iya kwana ba " ya furta yana fita daga d'akin zuwa parlor da idanu ta rakashi sai ta dafe kanta tana mai cewa "ohh ni Lele, Yaa Islaam so yake ya ja min tijara a cikin gidan nan ". Towel d'in jikinta ta zare ta maida kayanta da ya cire kana ta biyoshi parlorn, a hanya suka had'u zai koma ciki hannunta ya rik'o ya janyota zuwa kan gado bai bata damar magana ba ya kashe haske.




Idanu ta runtse tana mai yin duk adduar da tazo bakinta don ta riga da ta tabbatar da cewa yau sai ta gamu da su Ya Mara amma ya zata yi tunda ba zata iya fita d'aya ba kuma ma mai gidan ya yanke hukuncin da bata isa ta ja da shi ba?. Tana ta sak'e-sak'en yanda zata koma bacci ya sace ta, ba su fi 1hr 30mins da yin baccin ba ya tada ta har lokacin idonta cike da bacci.





Tare da shi suka fita zuwa parlor ta d'auki abayarta da aka cire jiya da gyalenta ta d'aura, lokacin har ya fito da yogofruit d'in da niyyar sha. Kallonshi tayi a shagwab'e tace " Yaa zan koma can kar su ga ba na nan" lumshe idanu yayi ya bud'e har ta fara tunanin ba zai amsa ba sai kuma ta ga ya mik'e yana cewa " mu je in raka ki". Ajiyar zuciya ta sake tana bin shi a baya, a tare suka jera har zuwa part d'in Ummun ba tareda sun ce uffan da juna ba kuma har suka isa ba wanda ya fito ta k'ofar kitchen d'in ta shiga sannan ta waigo tana murmushi. Hannu ya d'aga mata alamun bye itama ta d'aga masa da yake ta k'ware a neman rigima har da blowing masa kiss, murmushi yayi kawai ya juya ya koma.



Ba ta k'arasa ciki ba ta tsaya ta dafa noodles ganin ba a yi komai ba a kitchen d'in don duka-duka yanzu 3:15 ne fa, tana cikin dahuwar indomien Ummu ta shigo ciki gaisawa tayi ita da maids d'in da ta taso suka fara had'a abun sahur ita ma a nan kitchen d'in taci indomien kafin ta shiga ciki sai da ta kwanta ne ta tuna ta bar wayarta a can d'akin.



Kasancewar da bacci a idanunta ya sanya bata iya tsayawa an yi sallahr asuba ba, bacci tayi mai tsayi ba ita ta farka ba sai da Ummu itama ta tasheta akan ta tashi ta shirya don jirgin safiya zasu bi. Cikeda bacci a idanunta tayi wanka ta samu ta gabatar da sallah tana istigfari a k'asan ranta.



7:36 suka fito dukanninsu a harabar gidan family car d'in Abbu suka shiga dukansu inda driver ya jasu zuwa airport sai time d'in ne Burhaan ya bata wayarta da ta baro a wurinshi, tafiya ce mai d'an tsayi daga gidan zuwa airport ko da kuma suka isa an d'an dad'e kafin jirginsu ya tashi don shima transit suka hau dukansu a VIP suka zauna. Duka suna gaba while ita da Burhaan suke kujerar baya jirgin yana d'agawa sai da ya daidaita a sararin samaniya sannan ta samu sukunin cigaba da baccinta, wanda sai da suka yada zango a Cairo kafin ta farka a lokacin ne suka samu suka yi sallahr azuhur kafin aka sake boarding tun daga nan kuma basu sake tsayawa ba sai da suka sauka a Jeddah sun sha doguwar tantancewa kafin aka sallamesu luxurious bus suka hau zuwa Makkah inda sanda suka isa har an fara kiraye-kirayen sallahr magriba direct wani family gidansu dake kusa da harami sosai aka ajiyesu.


Gidan babba ne kuma a gyare yake tsaf don duk da ba kowa a ciki akwai maaikata masu lura da gyaran gidan kamar masu shi suna nan, domin dai ba laifi sukan zo sosai ga kuma masu karatu a nan makkahn suma duk da yanzu duk babu kowa. 



Direct d'akunansu suka nufa sai da akayi wanka aka yi sallah kafin suka had'u a wurin cin abinci, da suka kammala kuwa mazan suka wuce harami amma ita dai sakamakon galabaitar da tayi ya sanya ba ta iya binsu ba sai ma lallab'awa da tayi tai ishai kana ta wuce ciki zuwa d'akin da suka sauka ita da Hajjah ba ta ko jima ba bacci ya kwasheta.



Washegari suka fara gabatar da umrah cikeda karsashi, kowa ya maida kanshi abinda yake gabanshi wato ibada. Haka ta b'angaren Nadeefah ma duk da tana saurin gajiya ga kuma baccin da bata gajiya da shi bai sa ta k'i yin ibada ba, don kashe dare take a masallaci tana mai kaiwa Allah buk'atunta sai bayan subh take komawa ta samu tayi bacci ba ta komawa sai around 3 daga nan kuma sai an yi taraweeh a can take samun restaurant tayi iftar. Bayan taraweeh ma in ta koma bacci take yi sai wurin 11 kafin ta koma, ko da suka je madina shima haka take zaryan zuwa ziyara. A bakinta addua d'aya ce wato soyayyar Burhaan da tunda suka zo ta ajiyeshi gefe don ko had'uwa ba su cika yi ba saboda tsarin da tayiwa kanta k'arin bud'i gareshi, gamawa da duniya lafiya da k'arshe mai kyau , sai adduar samun y'ay'a na gari, arziki da lafiya wa iyayenta da su Hajjah suma da k'arshe mai kyau haka kanta da sauran 'yanuwanta da ma duniyar musulmi baki d'aya.



A tsukin hatta Tayyib ya fara yarda ta natsu ta kuma yi hankali don bata da lokacin biye masa da shiriritarshi, ko tsokanarta yayi bata maida kai ga amsawa ba kuma wai ba ta da bakin amsawa ba ne Aa lafiyar ce bata da ita cikakka sosai duk da dai bai kwantar da ita ba gajiya ce kawai da bacci ba komai ba.



A haka har suka gama yin abinda ya kawosu, sai lokacin ne suka samu damar yin hotuna sun ko yi masu yawa sosai su da iyayen sai wanda sukayi ita da Burhaan wanda da ta zaci ba zai tsaya ba sai ga shi har janyota yake yi a jiki in suna hoton. Duka hutun kwana biyu suka yi inda ta samu ta yi bacci sosai duk da haka dai sallah bai tab'a wuceta ba a harami, sallah saura kwana hud'u suka dawo gida. Ba dirar dare sukayi ba don da hantsi suka sauka a Abuja, screening kawai suka jira sukayi boarding sabon flight mai zuwa kd har da su Ummu don da ma a Kadunar suke sallah. Jirgin kdn ne ma ya sanya suka samu delay kun san k'asar da delay har a airport hakan ya sa basu iso kd ba sai after 5, kusan d'aukacin mutanen familyn ne suka tarbo su kasancewar har da iyayensu aka yi tafiyar motar Safwaan suka bi shi da Burhaan suke ita kad'ai a baya.

 

Motar ElSadeeq kuma Ummu ce da Abbu while su twins suka bi Zaheer, Hajjah da su Ya Madari Baba Tijjani suka bi su duka a haka a jere aka tafi har Yerwa. Ba su had'a tafiyar ba kowa gidanshi aka wuce da shi, suna shiga cikin gidan sai da ta ji wani sabon nishad'i a ranta yanzu kam ta yarda ba wani gidan da yafi gidan miji saboda duk da ibada taje a k'asar da ba a son bari amma tana shigowa gidan taji murna da farin cikin ta ya ƙaru.



A k'ofar shiga ya ajiyesu handbag d'inta ta bud'e ta ciro keyn da ta amsa a hannun Umma a airport don ita suka ba wa saboda gyaran da aka musu kar su dawo su tarda k'ura, tana tura k'ofar k'amshin turare ne ya musu sallama murmushi ta saki tana shiga gabaki d'aya ko ina tsaf a gyare kamar suna ciki.




Tana shiga parlor ta zauna akan kujera tana ajiyar zuciya tana mai bin d'akin da kallo cikeda kewa ta ga har abinci an shirya musu a dining murmushi tayi tana sake godewa Umma duk da dai ko bud'ewa ba tayi ba, zaman ta bai fi da 5 minutes ba security suka fara shigowa da kayansu dake shak'e bayan motar Safwaan duk wanda ya shigo sai ya sake mata barka da dawowa ita ko tana amsawa a sake yanda ta saba kafin ya fita a haka har suka gama shigo da kayan.



Suna gamawa Burhaan ya shigo da sallama zama yayi a gefenta yana sakin ajiyar zuciyar gajiya, dubanshi tayi tace " sannu" da kai kawai ya amsa mata yana sake jingina da kujera bayan kamar minti goma ya mik'e kamar an tsikare shi ya shiga d'akinshi da ba a gyara ba don bai bayar da daman hakan ba.




 Itama mik'ewa tayi ganin an kusa kiran sallah ta shiga ciki ta samu an gyara koina tsaf shima sai k'amshi yake tashi, main bedroom ne kawai ba a gyara ba shima don ta rufe shi ne ruf don haka nan take ji da d'akin da kuma kaffa-kaffa da abinda ya shafeta don shine sirrinta da Burhaan na k'arshen k'oli a kaf gidan.



Na tsakiyan ta shiga ta wuce toilet babu kayan wankanta a ciki hakan ya sa ta fito, bud'e main d'in tayi shima tsaf yake don ta gyara sai k'ura da yayi don ma ta lullub'e furnitures d'in da ledoji. Dama ba ta d'auko jaka ba sai Abayar da ta d'aura saman bodycon d'in jikinta ta cire kawai ta fara gyaran d'akin kasancewar da sweeper da vacuum cleaner ne ya sa bai d'auki time ba ta gama tayi mopping ta kunna burner da humidifier sannan ta wuce toilet shima gyara shi tayi tsaf sannan ta tara ruwa a bath tub bata dad'e tana wankar ba don tana ciki aka fara kiran sallah.



A gaggauce ta fito ta shirya cikin wata half gown maroon color wacce take free ba matsattsiya ba, ba ta ko tsaya wani abu ba ta shafa turare sallah tayi kafin ta fita. Jakarta ta bud'e ta ciro dabinon ajwaa mai kyau ta ci sai lokacin ta samu ta sha ruwa, shiga kitchen tayi duk da ba su da fruits don basu bar ko guda ba gudun kar ya lalace amma sai ta tarda an kawo wasu sabbi da Burhaan yayi placing order daga dankama_fruits Safwaan ya kawo su  wanke wainda zata yi amfani da su tayi ta sako su a bowl ta fito lokacin Burhaan ya dawo daga masallaci.



Biyota yayi dining ya ja kujera ya zauna, barka da shan ruwa tayi masa ya amsa a sake serving d'in shi masan da Umma ta kawo musu da kunun gyad'a tayi ta ajiye masa a gabanshi kana itama tayi serving kan ta. A natse suka yi iftar d'in babu mai magana har suka kammala, shi ya fara tashi ya bar dining d'in ita ko tana gamawa kitchen ta koma ta samu tayi sorting d'in fruits d'in da aka bari a kitchen kana ta fito.




Wayoyinta ta d'auko nan taga sim d'in babban 'in ya hau dama bata cire layin ba da iphone11pro d'inta tayi ta amfani a Saudi inda ta sanya masa etisalat, cire sim d'in tayi ta maida airtel d'in dake ciki tuntuni. Zama tayi gefen Burhaan da shima yake ta k'ok'arin saita na shi wayoyin tana lumshe idanu, dubanta yayi kad'an yana kauda idanu ya cigaba da abinda yake yi. Kamar yanda suka saba zaman shiru haka suka yi yanzu ita tana game shi yana kallon news, sai da aka kira ishai kafin suka mik'e shi ya ja su sallahr a cikin d'akinta don bai iya gyara nashi ba saboda gajiya ledojin kawai ya cire sai yayi shara amma bai wani masa yanda yake so ba.



Suna idar da sallahr ta nufi gado da niyyar ta kwanta kamar yadda ta saba, sai dai Burhaan ya hanata hakan da salonshi mai tsayawa a rai duk da bai da rawan jiki amma a yau ta lura da yanda ya dinga rawar jiki da ita cikin fitar hayyaci yake tabbatar mata da ya yi kewar ta a duk wata gab'a ta jikinta. Yau dai ya d'aukesu time mai tsayi don tabbas yayi kewartan sosai, don kuwa rabonsu da juna tun a Abj yau kam sai da ya b'arje guminshi kafin ya barta da gajiya. Lallab'awa tayi tai wanka ta koma ta kwanta, ai ko baccin yayi tsayi don ko bata tashi ba daga wannan kwanciya sai asuba da ya tasheta shi ma a daddafe ta iya yin sahur d'in da so tayi ta sake kwanciyan Burhaan ya jata jikinshi a kunne ya rad'a mata " ko dai in miki massage ne?".


Da mugun sauri ta fara k'ok'arin barin jikinshi tana cewa " massage..? Na yafe wallah" sake janyota yayi yana cewa " yes massage,,,,meye a cikinshi da ba kya so?". Cewa tayi " nothing ni dai na yafe ne kawai"  kallonta yayi yana nazarin fuskarta kafin yace " raguwa kawai, just massage duk kin bi kin rikice wait me ma kike tunani ne....'' Ya k'arashe da wata miskilar dariya, tura baki tayi sama a ranta tana cewa '' ka yi dariya mana, haka nan a b'ige da massage a kashe mutum '' dungure mata kai yayi yana mai cewa " yarinyar nan Allah ya shiryaki dai, daga maganar massage kin d'auki tunanin da nisa bayan ni ban kai nan ba".



"Ba wani nan Malam tunaninka yafi gaban nan" ta furta a k'asan ranta a zahiri kuma cewa tayi " ni fa ba wani abu nace ba Yaa". Cewa yayi '' ni ma ban kai can ba, kuma ma minutes ne fa ya rage a kira sallah in dai ba so nake muyi 60 ba ai ba zan je can ba, ba abinda zan miki daga taimako?". Gyad'a kai tayi tana cewa " thanks for the help Yaa, Allah ya saka da khairan" a zuciya ta k'arashe " amma massage dai ba dani ba". Tab'e baki yayi ya maida kanshi ga kur'ani, itama shigewa tayi jikinshi tana sauraron karatun ba tareda sun sake magana ba har aka kira sallah shi ya fita masallaci ita kuma a d'aki tayi.



Tana idarwa ko azkar ba ta iya yi ba sake komawa tayi ta kwanta a kwancen ne ma tayi ma tayassara kafin baccin ya d'auketa ba ta dad'e da yin baccin ba ya dawo shima kaya ya rage ya shige gefenta. Ita ce ta fara tashi around 10:16 da addua a bakinta mik'a tayi kafin a kasalce ta zuro k'afarta k'asa, direct toilet ta fara wucewa wanka tayi da kyau kafin ta fito ba ta yi wani shafe-shafe ba shiryawa tayi cikin sassauk'ar doguwar riga ta sanya da hula bak'a kafin ta mik'e. Kasancewar ta wanko toilet ya sanya ta fita kawai gudun kar ta tadashi daga bacci, gyaran gidan tayi tundaga parlornta har izuwa living room ta sanya turare kafin ta shige d'akinshi a can ne gyaran ya d'auketa time mai tsayi don ko tana mopping ya shigo d'aure da towel d'inta da alamu daga wankan direct nan yayo don sai k'amshin turaren wanka yake yi.



Gaisheshi tayi ya amsa da kulawa har da mata sannu da aiki, cigaba da aikinta tayi shi kuma ya shige ciki ya shirya cikin kaya marasa nauyi. Lokacin ta riga da ta gama gyaran kowani lungu na gidan samun wuri tayi cikin kujera ta shige tana waya da su Ummu da Hajjah, zama yayi a gefenta sai da ya jira ta gama kafin ya dube ta yace " zan fita zuwa gidan Umma ". Lumshe idanu tayi tana cewa " ok Allah ya tsare hanya, ka gaishesu " har ya mik'e sai kuma ya dawo ya zauna yana cewa " kafin in manta, ya maganar kayan sallahrki miye tsarin ki?".



Kallonshi tayi da kyau cikin nazari wani irin kayan sallah yau saura kwana uku sallah? Sai kuma ta daure tace " ban da wani plan sai wanda kayi Yaya" Cewa yayi " ai banda wani plans ne a k'asa kin ga bamu yi maganar da wuri ba, da muna saudi ne na tuna sai kuma time d'in bamu samu zama ba ko kawai in tura miki kuɗin? Sai kuma ki min list na abincin sallah kafin in dawo mu ga yanda zaa yi". Lumshe idanu tayi ta bud'e tana cewa " duk yanda kace Yaa, Allah ya musu albarka".



Wayarshi ya zaro yana shiga bank app d'in shi, account details d'inta ya tambaya don bai da shi ta sanar masa 'yan danne-danne yayi sai ya mik'e yana cewa " na tura, ba yawa". Murmushi tayi tana cewa " mai yawan kenan, thanks Allah ya k'ara bud'i ya saka da alkhairi " murmushi yayi shima kana ya duk'a yayi pecking d'in ta a goshi kafin ya wuce ya barta a nan tana mai binshi da idanu, tashin motarshi yayi dai-dai da shigowar alert wayarta zare idanu tayi ganin abinda ya tura sai kuma tayi murmushi tana cewa " Yaa Islaam nawa ni kad'ai, mai abun mamaki wannan kud'in ne yake cewa ba yawa? Allah ya kare min kai ya k'ara bud'i ".




Ganin kud'in tayi kamar kyauta aka ba ta don ta riga ta tanadi komai kafin tafiyarsu, ko a can ma sai da ta k'ara Abaya duk na hidimar sallah da zata yi. Wani tunani ne ya fad'o mata a rai sai ta sake fad'ad'a murmushinta, notes d'in wayarta ta shiga ta fara typing list d'in da ya sata tana yi tana amsa wayar 'yan barka da dawowa. Bayan zuhr ta samu ta kwance kaya tana cikin aikin sai ga su Suliem nan ta saki aikin ta biye musu suka dinga shiririta sai bayan asr suka wuce tsarabarsu ta basu su da mazajensu kafin ta shige kitchen ta fara aikinta wanda har gama bai dawo ba sai kusan magrib kafin ya shigo bai ma ko zauna ba aka kira sallah sai kawai ya sha ruwa da dabino kana ya wuce masallaci.





Washe gari da wuri ta fita don 9 tana office nan ta iske har wurin ya fara d'inkewa da masu gyaran sallah da lalle, itama dama abinda ya kawota kenan so tayi a mata amma yanayin mutanen da ta gani sai kawai ta fara tayasu gyaran jikin. Nan ko suka fara cin k'arfin aikin dama masu spa daban masu saloon ma daban haka masu lalle kuma sukan d'auki wasu extra saboda aikin sallah shiyasa bai cud'e musu ba, gyaran jikin ne kawai aka yi mata don yamma tayi su kuma ba da wuri zasu tashi ba sai 10pm abincin bud'e baki tayi musu order kafin ta wuce gida. Tana zuwa itama ta fara aikinta ba ta yi wani abu mai wahala ba saboda dai yamma tayi da yawa kar a kira sallah ba ta gama ba.



Bayan ishai ne Burhaan ya k'ara janta suka fita Sahad stores suka je siyayyan sallah, sun yi siyayya mai yawa duk wani abun da ta rubuta sai da suka siyo kafin suka dawo wurin 10pm. Ko da suka dawo ba ta wani jima ba tayi bacci shima haka don 1:am ya hau kan dadduma ya fara jera tahajjud, bai tashe ta ba sai 3 itama wanda ya sawwak'a tayi ta had'o musu abun sahoor ta dawo d'akin.



Ranar dai 7 ta fita sosai Burhaan yayi mamakin wannan fitar tata sai dai bai tambaya ba, ita ko tana zuwa lip therapy ta samu aka mata sai lalle da yake zane take yi na ja da bak'i a cikin tafin hannun da baya sai k'afa. Kafin lallen ya bushe kuma aka mata gyaran gashi da kitson 2 step k'anana mai kyau irin Liberrian style d'in nan da ya samu waje ya kwanto har bayanta, 11 dai-dai aka cire lallen ko minti d'aya bata k'ara ba ta wuce gida don akwai aiki sosai a gabanta.



Nan ta tarar ya kawo sauran kayan amfanin wanda ba ta siya ba, tsayawa tayi gaban kayan tana tunanin ta inda zata fara sai ga kiran Umma. D'agawa tayi cikeda girmamawa suka gaisa da tambayar juna aiki, Cewa tayi " Umma ga shi nan yanzu zamu fara ma".



"Yawwa Lele na san baki saba aikin sallah ba, shiyasa na sa aka kawo min wata yarinya tazo ta tayaki aikin na sallah kawai kar abun yayi miki yawa".



Ajiyar zuciya ta sauke tana mai jin kamar an mata gafara sai dai kuma tana tsoron Burhaan tunda dai ya nuna bai so hakan ya sa tace " laaa Umma, amma na gode dama fa aikin bai da wani yawa ko da ba zo ba ma zan iya".



Shiru Umman tayi haka nan jikinta ya bata tabbas Burhaan ne bai so kuma Nadeefahr tana tsoronshi ne sosai, don haka tace " na san zaki iya taya ki ai zata yi yanzu zan sa driver ya kawota zuwa anjima zai zo ya d'auketa sai gobe ma zata dawo so sai anjima ban son jin wata magana".


Lumshe idanu tayi tana cewa " ok Umma nagode sosai Allah ya k'ara girma" ameen tace tana katse kiran, tsayawa tayi da wayar a hannu sai kuma tayi dialing numbern Burhaan don kar ya dawo gidan a samu matsala. D'agawa yayi yana cewa " Wife how far" d'an kwantar da murya tayi tana cewa " lafiya lau, ya aikin ".


"Ai ban je aiki ba ina nan wajen aikin jinsami ( kakkawa), kin manta ni ne incharge ne?". 


"Oops na manta shima aiki ne, hope babu wahala dai?".



"Yeah normal, ya naji ki wani iri kin dawo gida ne?".


"Uhmm, dama Umma ne ta kira waya wai yanzu zaa kawo min mai tayani aiki, shine nace bari in sanar maka kar ka ganta kwatsam". Ta furta cikin kwantar da murya.


Shiru yayi yana sauraronta kamar ba zai tanka ba hakan ya sa a tsorace ta kuma cewa " Allah Yaya bani na kirata nace ta zo ba kuma ban son mata musu ne".



Cikin dakewar murya yace.................

Deejasmah ✍🏼