GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

*🪻GAƊAR GIWA...🪻*

by @auntyindo



Daga Alƙalamin... Ayeesha Abdulkareem ( INDO)
 
بسم الله الر حمن الر حيم

Rana tsaka  kimanin ƙarfe 01:00 na rana,  a wannan lokacin ba abin da  Hamdan ke yi face Kaikomo a Office ɗinsa, wanda ya ƙawatu da tsadaddun  kayan alatu na more rayuwa.

  A kowane harbawar Second ji yake tamkar lokacin yana ƙara nesanta shi da farincikinsa ne, wani irin zafi ke ƙara karyo masa tun daga ƙasan zuciyarsa har zuwa gangar jikinsa, duk sanyin AC da ya cika ɗakin fal! ba ya ratsa fatarsa  bare har jikinsa ya amsa.

Dakatawa yayi da zagayen ya nemi guri ya zauna kan luntsumemiyar kujerarsa wadda ke fuskantar table .
Tafukan hannunsa ya ɗora akan fuskarsa tare da furzar da wani zazzafan huci,  wayarsa ya janyo gami da zuba mata ido nan take dukkan  sassan Zuciyarsa masu faɗa a ji suka shiga muhawara.

Sai da ƙyar ya iya tsaida  shawara ɗaya, dan haka ya shiga laluben wata number ya  tura kira.

A ɗayan ɓangaren 
Jiki a sanyaye ta kara wayar a kunnenta gami da yin sallama sai kuma tayi shiru don jin abinda zai biyo baya...  "MAA-MA!" Taji an furta sunan da Ƴaƴan cikinta suka saba kiranta da shi, nan take zuciyarta ta yi wata ƙwaƙƙwarar bugawa, "Na'am! waye ? da wa nake magana?"  ta fada cikin kaɗuwa, "HAMDAN AHMAD (MAI MATASA)!"  Ya bata amsa cikin muryarsa me ɗauke da nutsuwa,  cikin sauri  ta maimaita sunan kafin ta ɗora da cewa "Lafiya Kuwa?" "Lafiya lau, HIBBA nake nema"  "Allah Yasa ba laifi ta yi ba!" jim ya ɗan yi yana sauraren yadda zuciyarsa ke bada wani ƙwaƙƙwaran duka, ga wani nauyi da take kara yi masa, a takaice ya ce "Neman ta nake, ina so in gaishe ta!" sai da ta samu gurin zama sannan ta sauke ajiyar zuciya, cikin fara,a wadda ta fi kama da ta yaƙe ta ce "Yanzu  ba ta nan, idan ta dawo zan ba ta wayar sai ku gaisa!"   "Maa-Mah!  so nake in ganta, don Allah ina zan same ta?"   kasa cewa komai ta yi har sai da ya sake kiran ta da "Maa-ma" sannan ta numfasa ta ce "Hamdan! ka yi haƙuri don Allah, Hibba tana farinciki a halin da take  yanzu, kar ka zamo Barazana ga wannan farin cikin namu!"

   Runtse idanunsa yayi da sauri hakan ya ba wa zazzafar ƙwallar da ta cika idanunsa damar sauka,  sai da ƴan sakanni suka shuɗe kafin ya iya cewa "Hibba Yar Uwata ce!, ba zan taɓa yin abin da zai cutar da ita ba, sai dai kuma ba a tara sani ga Allah kuma Ƙaddarar da Ta Faru ita ce ake sanin Matsayarta, dukkanmu babu wanda yasan Yaya Ƙaddararsa ta Gobe take!"  

  Shiru ya yi, a nata gefen ma ta kasa magana sai maimaita zantukansa take a zuciyarta.
   
Dan janye wayar ya yi daga kan kunnensa  ya ja wani bahagon numfashi ya sauke kafin ya kara wayar ya ce "Ina ne wajen Aikinta?" 
   "Hamdan! Don Allah kar....."    "Don Allah kar ki kafa min Sharaɗi akan ta, ji na nake tamkar dokin da ba shi da Linzami,   Maa-Mah!  ke Uwa ce kuma Uwa ta ƙwarai ga Ƴaƴanta, na tabbata kina fahimtar Saƙon Zuciyar su tun kafin bakinsu ya furta!"   ɗan tsahirtawa yayi sannan  yace "Kuma nima Ɗanki ne Maa-mah!,  ba zan ɓoye miki ba,  na Kamu da son Hibba, kuma duk Duniya  babu wanda ze ƙarfafa min gwiwa sai ke kaɗai!"

    Goge hawaye ta yi kafin ta ce "Idan Allah ya nufa babu yadda zan yi, amma kai ma ba zan ɓoye maka ba  ba na son alaƙarka da ita, domin Wutsiyar Raƙumi ta yi nesa da ƙasa, Hamdan akwai tazara mara iyaka tsakanin kai da ita,  kuma ina so  Hibba ta kasance a inda ake Ƙaunarta a inda za a Mutunta ta "
  
   "Tabbas KUSKUREN WASU... Shi ke Shafar Wasu, amma a nawa ganin ba Kowane Kuskure ba ne ya kamata ya zamo Baƙin Tabo ga wanda ba shi ne ya aikata ba, ki temaka min Maa-maa!  idan ba kya so na Hibba   ba za ta  taɓa so na ba, kuma ban san ina zan sa kaina ba in kuka guje ni a daidai  lokacin da nake buƙatarku"
         "Ban isa in hana faruwar abin da Allah ya Ƙaddara  ba, ka je ka same ta,  amma ka dinga tunawa ita ɗin Marainiya ce, zan ajiye  maka address ɗin sai ka duba, amma kar ka je inda take a yanzu na san ba za ta saurareka ba!"
    "Na gode " "Ba komai, ka gaisar da Su Abban naka"
   kai kawai ya gyaɗa bai iya bada amsa ba saboda ganin idanun Ammy akansa.

    "Wai me kake ba ka fita ba, ko ka manta abinda Daddynka ya ce ne?"   "Bana cikin yanayin fitar ne Ammy!"  ya bata amsa tare da kawar da kansa gefe.

Ido ta zuba masa tana takowa zuwa ciki, sai da ta zo daf das
 shi sannan  tace "Meye damuwarka ne? da waye kake waya?" lumshe ido ya yi kafin ya ce "Sashina ne!" a ɗan faɗace ta ce "Ban gane Sashinka ne  ba, kana nufin har kana da wani Abokin Sirri da ba zan san tsakaninku ba?"

"Ba haka nake nufi  ba, ni fa ba yaro ba ne  Ammy,  na san duk inda zan jefa rayuwata!"
jinjina kai ta yi kafin ta ce "Hmm! ai naga alama yanzu kam ka girma Hamdan,  ban san me ya tsaya maka a rai ba kwanan nan duk ba ka zaman lafiya da kowa, kai kuma babu dama a tambayi ba'asin damuwarka sai Zuciyata ta fusata"  
  Murmusawa ya yi gami da cewa "Har wani fushi gare ni kuke gani Ammy?, amma sai nake ganin kamar na fi kowa haƙuri da kawaici a Gidan nan"  "Za a iya cewa hakan, amma dai kasan ka fi kowa tsauri akan abinda ya shafe ka,  ka ga ni ba surutu ne ya kawo ni ba, gaya maka zan yi kar ka sake ka yi mana wasa  akan abin da Alhaji ya ɗora ka, don so nake  ku gama mamaye komai kafin wasu su ƙara hankali"
 
Shiru ne amsar  da ta samu, sanin ba lallai ya magantu ba yasa ta fice .
Shi kuwa takaici ya hana shi motsawa, ya rasa gane inda Iyayensa za su kai son abin Duniya.
Ga Dukiya da duk wata Taƙama da Iko Allah ya tara musu amma duk da haka burinsu  su fi wani,  su murƙushe wani, su wulaƙanta wani.
 Bai taɓa sanin Rayuwar da aka ɗora su  akanta babbar illa ce ba sai yanzu da ya kamu da son wadda take wulaƙantacciya a wajen Danginsa, wadda ko a mafarki ba lallai wani  nashi ya ƙaunace ta ba.

   Yana nan zaune yana tufka da warwara  har wani salihin bacci ya sure shi,  bai fi minti biyar ba ya farka a firgice!...  
kamar an tsikare shi ya miƙe ya nufi toilet ya watsa ruwa  cikin gaggawa , yana fitowa ya zura tufafinsa ya suri mukullin Mota ya fice ko inda Dressing mirror yake ma bai  kalla  ba. 

   Yana tafe yana tunanin  yadda Mafarkinsa ya raya masa ana shirin yi masa sakiyar da ba ruwa.   Har ya tsinci kansa Bakin gate na  AL'UMMATY BUSINESS DEVELOPMEMT FOUNDATION....

 tsayar da Motar yayi a cikin jerin Motocin da ya gani a bakin gurin, ya ɗan numfasa kafin ya fara muzurai cike da tunanin ta inda zai fara.

   Yana nan zaune ya ga Ƴan  Mata  da Matan Aure sun fara Fitowa suna ta hira cikin farin ciki da raha.
Da sauri ya fito yana rarraba ido ko zai samu wadda zai tambaya inda Hibba take.

   Cikin yanayinta na zafin nama ta fito da sauri  tana ba wa wadda ke biye da ita amsa da cewa "Yau kwata-kwata ba a daidai nake ba, ba na farinciki sam, gwara in koma Gida ko zan fi samun nutsuwa".
 
"Hibbah!"   ta ji an kira sunanta.... tsayawa ta yi cak! ta kasa juyowa saboda jin muryar  kamar saukar aradu, ba ta gane waye ba amma tabbas kiran ya yi bala'in tafiya har cikin ƙoƙon ranta.

   Cikin matuƙar fargaba ya ƙaraso gabanta gami da ƙwaƙulo murmushi tamkar wanda aka  yiwa dole....
Idanunta na sauka akan fuskarsa  ta gane shi amma sai ta haɗe rai, a taƙaice ta ce "Yallaɓai lafiya kuwa!?" 
Ƙara ware idanunsa ya yi akanta kafin ya ce "Lafiya;   na zo ne in ganki, kuma in sanar miki abun....."   

"Dakata!"  ta faɗa tare da ɗaga masa hannu,  cigaba tayi da cewa "Waye kai? kuma me na ci maka  da kake son gani na?"
  ƙasa ya yi da kai kamar sabon munafuki, da ƙyar ya ƙara ɗagowa ya zuba mata na mujiya gami da cewa "Ki yi haƙuri na yi miki shigar bazata, nasan dama ba za ki kasa gane ni ba,   indai har  kina kallon fuskarki koda baki taɓa ganina ba sai yau na tabbata zaki gane daga ina na fito" 
   "Oh yanzu kam na fahimta!, daga Ahalin masu Kuɗi kake ko?, ashe a nan ɗin ma ban tsira ba?, biyo ni ka yi don ka tozarta ni kenan!"
  "No! babu wannan a tunanina,  kawai na ga ba amfanin ɓoye miki ne" 
Tana shirin mayar da raddi cikin fushin da zuciyarta ta hau,,  ya dakatar da ita da cewa "Ina sonki Hibba!  don Allah ki kasance Matata!"   "What!,,, ka sha maganinka kuwa?!"  ta faɗa  tana zare masa  idanu....
   "Ko da na fi haka tuburewa ba zan iya karɓar maganin da ba ke kika ba ni ba,  da gaske nake miki Hibb....."   katse shi ta yi ta hanyar sakin wata dariya wadda ta sanya ya ƙara kame  kansa.

   "Ya sunanka ne ma?, kawai saboda  rana Ɗaya na shiga Taro Familynku shikenan na zama Abar Wulaƙantawa??, ya kamata fa ka sani akwai bambanci tsakanin Gajiyayyu da irinku, sannan ina gaya maka da babbar murya  don Na kasance Marainiya kuma Iyayena Talakawa ba shi yake nufin na zama Saura ba, kowa ya ɗebo Shararsa ya juyeta a kaina!,  don haka in ma Giya ka sha ka je ka nemo makarinta,  in kuma Kace ka Hau sai ka je ka ga likitan Mahaukata, idan kuma Tozarta ni ka zo yi to ka sani a nan ba ka da Tasirin komai, ka san Kowa a Fadarsa Sarki ne!" 
  "Ya Allah!  don Allah kar ki hukunta ni akan laifin da ba ni na aikata ba Hibba!,  lafiyata ƙalau a hayyacina nake, kawai ban san  ya akai ba ni....."  kasa furta kalamin da yake son furtawa  yayi saboda rauni da zuciyarsa ta yi.

   "Malam ranar nan ka same ni cikin sanyi, yau kuma a fusace na tashi don haka ka gaggauta janye tsumman jikinka ka bar wajen nan, ba na son rainin hankali,  ka duba ka ga yadda ka Tozartani a idon wanda suke ganin Mutuncina, kalli yadda  jama,a suke kallona, Abun kunya ne gare ni a ga  ka tare ni kana yi min wannan rashin kunyar!" 
   Rasa abin cewa ya yi sai salati da ya runtuma,   'Kenan ma ita a gurinta tozarci ne a ganni tare da ita?,  Tabbas me hankali ya kamata ya gane tun a nan Duniya akwai Abinda Kuɗi ko wata Dukiya da Taƙama ba ya iya samarwa Mutum, ina ma Dangina zasu fahimci hakan, da an samu  babban Sauyi a cikin Ahalinmu'
Ya yi nisa cikin tunani ya ji Muryar wani ta bayansa yana faɗin "Me yake faruwa ne Hibba?"  durum!!!!  Zuciyarsa ta buga, ya ƙurawa Hibba ido cike da son ganin motsinta,  tsaki ta doka gami da zagaye shi ta nufi wajen Ɗayan,,,,  a zafafe ya cafko hannunta  yana shirin jefata cikin jikinsa, cogewa ta yi tare da ɗago zaratan yatsunta ta sharta masa wani lafiyayyen Mari,,,,  fizge hannunta ta yi tare da nuna shi da yatsa ta ce "Kar gigi ya ƙara sa Hannunka ya taɓa jikina, in ka yi hakan kuma zaka sha Mamaki!,  talaka ba Bawa bane kuma ba mara mutunci ba ne, Allah ya riga ya mutunta kowa sai dai wanda  ya wulaƙanta kansa!......"
   Juyawa ta yi kan Kyakkyawan Saurayin dake bayanta gami da cewa "Mu je Ismail!"..................

*Aunty INDO*