Chapter 25
🌀 HAƊIN ƘADDARA 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki RUKAYYATU (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 25
Tafiya Suraj ya dinga yi cikin fitar hayyaci, domin ko ganin gabansa da kyau ba ya yi balle ya kula da inda yake jefa ƙafafunsa, kaɗaici shine kaɗai abinda yake buƙata a wannan lokacin. Sai da ya shige can karshen campus sannan ya dakata. Wajen tsit babu mutane, da wuya ma wani yazo wajajen sai da kwakkwarar dalili, don sabbin gine ginen da ba a fara amfani da su ba ne a wajen, wasu ma ba a kammala gina su ba, ga kuma tarin bishiyoyi da suka haɗu suka sanya wajen ya yi duhu. Karkashin wani katon itace ya zauna a ƙasa cikin sharar busasssun ganyaye ya haɗe kansa da gwiwa. Jin zuciyarsa yake kamar ta takure ta cure waje guda, wani irin kunci wanda tunda Mother ta kawosa duniya bai taɓa tsintar kansa a ciki ba sai yau, kalamanta masu zafi suka dinga dawowa a kansa tamkar yanzu ke take gaya masa musamman inda take faɗin “Ni ba tsarar ka ba ce. Kai ba ajina ba ne. Ba na son ka Suraj, bana kaunar ka, na gaya maka sau babu adadi, amma ka ƙi ka fahimta saboda ƙwaƙwalwarka cike take da dauɗar Kuruciya, to ka sani this should be the first and last time da za ka kuma saka ni a cikin haukarka.” Sam baya jin zafin marin kamar yadda yake jin zafin waɗan nan kalaman, wanda ya ke jin da ta faɗe su gara ta yi ta zabga masa mari har sai ta ji sanyi a ranta, ji yake a ransa ko sama da ƙasa za su hade ba zai taɓa iya daina sonta ba, yana jin labarin masoyan da suka rataye kansu wasu suka sha guba wasu suka bar gida suka faɗa harkar shaye-shaye a kan soyayya, a baya yana ganin wauta ce, amma a yau a irin yanayin da yake ji a zuciyarsa wallahi zai iya aikata komai a kan soyayyar Salmah. Danshin da ya ji a fuskarda yasa ya fahimci kuka yake yi, hawaye ne suke kwaranya daga idanunsa, sai kawai ya ɗaga kai ya kalli sama ya lumshe idanu yana mai basu damar zuba da kyau, ko zai samu irin sassaucin da yake buƙata a zuciyarsa. Yafi mintina goma cikin wannan yanayin, tun yana yi a zuciya, har ya fito fili ya dinga sauke wani irin numfashi, yana shessheka kamar karamin yaron da aka yi wa dukan zalunci. Bai kara gaskata zancen mutane na cewa zubar hawaye rahama ba ce sai yau, domin ji ya yi kaso hamsin cikin dari na kuncin da yake ji a zuciyarsa ya kwaranye.
Sai dai duk da haka, zuciyarsa ba ta samu nutsuwa gaba ɗaya ba. Wani ɓangare na cikinta har yanzu tana masa nauyi, tana masa wani irin ciwo da ba zai iya misaltawa ba.
Ya sauke numfashi a hankali, ya buɗe idanunsa kadan yana kallon hasken ranar da ratsowa daga sararin samaniya ta ratsin ganyanyakin, da suka yiwa wajen rumfar.
“Me yasa…?” Ya furta a hankali, kamar yana tambayar wani a kusa da shi. “Me yasa ita…?” ya sake faɗa a hankali tare da runtse idanunsa da ƙarfi, hotonta na sake bayyana a idanun da ƙwaƙwalwarsa kamar wanda yake kallon allon majigi, yadda ta tsaya a gabansa tana jifansa da mummunar kallo na tsantar raini da wukakanci, yadda bude baki tana gaya masa maganganu don ranta, musamman kalmar nan da ta fi komai masa zafi “Ba na son ka Suraj. Na tsane ka…” Tuna wannan yasa ya ji numfashinsa ya soma sarƙewa, ya ɗan girgiza kai kamar yana son kore tunanin… amma ya kasa.
A hankali ya kai hannu kan kirjinsa, yana jin yadda zuciyarsa ke bugu da ƙarfi…
kamar tana son ficewa daga ƙirjinsa.
“Ba zan iya ba…” ya furta da ƙyar.
“Ba zan iya daina sonta ba…”
Muryarsa ta yi rauni, ta karye sosai kamar ba, buɗaɗɗiyar zazzaƙar muryar nan tasa ta musamman ba. Wani irin shiru ya sake lullube wajen, sai motsin iska mai ɗan sanyi da ke kaɗa ganyayen Wannan yanayin yasa
ya ji kamar zuciyarsa na karanta masa wani saƙo, wani abu sabo da bai san shi ba, kalmomi ne a tsare daki daki.
A farko bai kula ba, sai dai ko wannen sakon da yake ɓatawa ji yake yi kamar ana raɗa masa su a kunne. Ya lumshe ido a karo na biyu, ya ja dogon numfashi ya fesar, kafin a hankali, cikin rauni, ba tare da ya shirya ba, ba tare da ya sani ba, ya fara maimaita abinda take zano masa cike da ladabi da bin umarni. A hankali ya fara rera waka da buɗaɗɗiyar zazzaƙar muryarsa mai wani irin amo na musamman.
Me yasa zuciyata ke kiran sunanki,
Ko da kina nesa kina ƙin ganina?
Na rasa kaina a cikin soyayyarki,
Ko ba ki sani ba… ke ce raina…
Na ce zan daina… amma na kasa,
Na ce zan manta… amma na kasa,
Duk inda na dosa, ke nake gani,
Ke ce hasken da ya hana ni duhu ya cinye ni…
Ko kina cewa ba kya sona,
Zuciyata ta ƙi yarda…
Ko kina cewa na bar ki,
Raina ya makale a gare ki…
Idan son ki laifi ne,
To ni zan rayu da wannan laifin…
Saboda ke kaɗai ce…
Da zuciyata ta zaɓa…
Na ji kalamanki kamar wuta,
Sun kona raina sun bar ni babu kowa,
Amma duk da zafin da na ji a yau,
Ba zan iya kin son ki ba… ko da zan so…
Idan kuka ne zai wanke raina,
To bari hawayena ya zuba har ya ƙare…
Amma soyayyarki…
Ba za ta taɓa gushewa ba a cikina…
Ko kina cewa ba kya sona,
Ni zan ci gaba da ƙaunarki…
Ko kina korata daga ranki,
Ni zan zauna da ke a raina…
Saboda ke kaɗai ce…
Da zuciyata ta sani…
Rintse idanu ya yi sosai yana tsara baitocin soyayya cike da hikima da baiwa kai tsaye daga zuciyarsa ba tare da ya tsara, ya rubuta ko ya yi nazarinsu ba. Tun yana yi a hankali har bai san san da ya zage ya ware dukkanin karar muryarsa ba.
Tsananin daɗin sautin da tsarin kalaman suka haɗu suka daskarwar da, Salman da Sadam da suka biyo bayansa suna neman shi, da kyar suka hango bayansa da ya juya musu, suka kwaso a guje domin karasawa inda yake, sai dai tun daga nesa sautin ya yi musu maraba, kallon kallo suka shiga yi a tsakanin juna zuciyoyinsu na tainkewa da tsananin tausayinsa, yayinda a daya bangaren, mamakinsa ya cika musu ciki. Sai dai shi bai ma san da wanzuwarsu ba. Salman ne ya fara takawa a hankali ya isa bayansa ya duka tare da dafa kafadarsa, a raunace ya ce “Surajudeen!” Cak ya dakata, kafin ya ware idanunsa da suka rine a hankali har lokacin da danshin hawaye don bai goge ba, sai kuma ya karya kai ya juyo kaɗan ya kalli Salman da gefen ido ba tare da ya amsa ba. Sadam ne zagaya ta gabansa ya duka, ya ce, “ Wow!!! Ma sha Allahu laƙuwata illah billah, Suraj dama kana waka ? Are you a artist? Ko da wasa ba ku taba sani ba, Gaskiya kai dan baiwa ne, You are so amazing wallahi, ga murya, gaskiya an tashi kaina.” zuba masa ido Suraj ya yi cike da nazarin kalamansa, at the same time, abinda ya faru yanzu na dawo masa a kai, shi dai yasan ba ya yin waka, kuma bai taba sha'awar yi ba, balle har ya rubuta ya yi nazarinta.
Salman ne ya dakatar da maganar da faɗin, “Suraj let's go, ita almost time, za mu shiga, hall yanzu, ka yi hakuri idan mun fito za mu tattauna akan abinda ya faru, ba zan kyaleta haka ba, zan nuna mata ɓacin raina zai hadaya da su Ammie kai harma da Ya Anas da Hajiya Saude.” yadda yake maganar bil haƙƙi a kausashe kai tsaye mutum zai fahimci ransa ya yi matukar ɓaci da abinda yar uwar tasa ta yi. Ɗan duka a kafaɗa Suraj ya kai masa ya ce“ Wa ya aike ka? Ko da wasa kada ka kuskura ka ɓata mata rai, domin akan hakan za a ji mu da kai, ni ta yi wa laifi ka barni da ita zan hukuntata da kaina, ka rubuta ka ajiye wata rana sai ta duka ta bani hakuri akan wannan lamarin a gaban mutane kamar yadda ta aikata a gabansu, in dai har na cika namiji kuma jinin Sulaiman Saless Al-Hikima.” Yunkura ya yi ya miƙe, suma duk suka mike, ya ce, “ Ku je ku yi test ɗin ku, bana jin yau zan iya shiga aji, mu hade gobe.” Yana gama fadin haka ya soma tafiya ya doshi get ɗin da ke ta wajajen wanda masu aikin gini suka buɗe suna amfani da shi. “Surajudeen!.” Salman ya kwala masa kira bayan ya ɗan yi musu nisa, ba tare da ya juyo ba ya daga masa yatsu biyu, sai kuma ya ci gaba da tafiyarsa, a haka har ya sha kwana ya ba cewa ganinsu.
Da alama za mu samu upcoming Hamisu breaker.😅
Kar a manta da payment, yau ne muka kammala book one, 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, a tura shiadar biya ta nan ***.