29 End
by @legendspen
Kamar saukar aradu haka na ji maganganun Sardauna suna dukan gangar jikina. Gaba ɗaya na ji duniyar ta yi mini tsit, kalaman sa suka baibaye mini tunani na, jiri na ji yana neman kwasata.
"Na gode Nana... na gode da kika share mini kukan zuciya ta hanyar aura min mace mafi soyuwa a raina. Na gode da kika cika mini burina na aurar min da matar da nake so a cikin zuciyata."
Waɗannan kalaman na Sardauna su ne suka daki kunnena ta baya. Na ji tamkar an tsire min zuciya da mashi mai zafi. Na ɗago raunanun idanuna da suka riga suka yi jaƙaɓ da hawaye, suna mini wani irin zazzafan zafi, na kalli fuskarsa.
Fuskarsa daban da waccan da na sani a baya, Sardaunan Nana, babu sauran ɗigon tausayi ko ƙauna, sai tsantsar wulaƙanci da ya bayyana a cikinta. Na juya na kalli fuskar Bilkisu, wadda ke tsaye tana kallona tamkar tana kallon dabba.
A daidai lokacin, na fara kokawa da zuciyata ta ina ƙoƙarin ƙaryata abun da kunnena ya ce ya ji. A raina na ce, 'Ba Sardauna na ba ne... mafarki nake yi... Sardaunana ba zai mini haka ba.'
Cikin taƙama da jiji da kai, Bilkisu ta saki wata daddaɗar dariya mai cike da baƙar baƙantawa, ta kalle ni ta ce.
"Kanki ya ɗauke wuta ko, Nana? Ke yarinya ce marar wayo, marar ilimi da tunani!"
"Bilkisu, yi shiru!"
Sardauna ya dakatar da ita. A lokacin, wani ɗigon fatan alheri ya ɗarso a zuciyata. Na rinƙa jiran abinda Sardauna zai ƙara cewa. A cikin raina addu’a nake yi, 'Ya Allah... Allah Ka sa cewa zai yi ƙarya take yi... Allah Ya sa cewa zai yi shi nawa ne.'
Amma sai na ga ya tako a hankali, ya tsaya daidai inda nake, ya zuba mini idanun sa da babu alamar tausayi a cikinsu, ya ce.
"Nana! Ba ke nake so ba. Ƙuciyar jikinki kawai nake so... wadda na riga da na gama mallaka gaba ɗaya. Nana, ban taɓa son na rayu da ke a matsayin macen da zan so ba, sai dai na rayu da ke a matsayin wadda zan killace ta, na hana ta kula kowa a duniya, saboda zazzafan kishin ki na ƙaddara da nake ji a rana, Nana."
Ɗum...!
Haka na ji kaina ya ɗauki wani irin zafi, wani baƙin abu mai nauyi ya daki ƙarƙashin ƙirgina, ya tare mini numfashi. Jikina gaba ɗaya ya daina aiki, ya saki tamkar gawa. Kafin na dawo cikin hayacina, muryar Bilkisu ta sake dukan kunne na.
"Na shigo rayuwarki, na shigo jikinki ne kawai saboda Baby ya nuna yana son hakan. Ya nuna yana son wasu banzayen abincin da kike dafawa na ƙazanta wai su ya fi so a duniya, sannan kuma ya yi amfani da wautarki ya sa ki nema masa aure da kanki! Nana, ke ba ajina ba ce da zan tsaya ina kula ki. Wayewata da ilimina sun fi ƙarfin matsayin yarinyar da ba ta wuce Secondary School ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa na ja miki rai da farko kafin na amince, saboda idan na azabatar da zuciyarki da baƙaƙen maganganu da cin mutunci, na wuce wani ɓari na takaicin kula da ke da na yi a matsayin ƙawa. Domin ni, aji na da matsayina, sun fi ƙarfi da darajar ki har abada! Kuma Sardauna, mun haɗu da shi a ranar da kuka fara zuwa umguwar nan, wanda rabona ne ya kawo ku."
Wata iriyar azabbariyar hajijiya ce ta kwashe ni. Ƙafafuna suka gaza ɗaukar gangar jikina, na fara ganin komai na dakin ɗai-ɗai yana juyawa, dishi-dishi gaba ɗaya. Idanuna suka kawo ruwa amma na kasa kuka, saboda tsananin ɗacin da ya busar mini da maƙwagwaro.
Muryar Sardauna ta sake dukan kunnenna cikin halin ko-in-kula.
"Nana! A yanzu haka zan sauwaƙe miki, zan raba aurenmu. Amma kuma zan miki alfarma guda ɗaya, wadda ita ce zaki zauna a gidana a ƙarƙashin kula ta da ikona tun daga yau har ranar da zaki mutu, Nana. Tun da dai ke da kanki kika nuna idan babu ni ba zaki iya rayuwa ba. Kuma ko da na sake ki kika tafi, ai ba ki da kowa a duniyar nan, ba ki da inda zaki tafi... ‘yan uwa ne babu, ƙawaye babu, Nana! Ba ki da wata mamora ko amfani a rayuwa. Shi ya sa zan barki ki ci gaba da zama a nan tamkar baiwa, ba tare da kin faɗawa kowa cewar na sake ki ba. Gimbiya Bilki... ɗauko takarda ki rubuta mata takardar sakinta."
Wani irin masifaffen jiri ne ya ɗebeni, na ji ɗakin yana neman kayar da ni. Cikin tsananin razana da gigicewa,na lallaɓa na dafa gefen kujerar da ke kusa da ni, jikina gaba ɗaya yana wani irin karkarwa kamar wacca za a zarewa rai, bakina yana ɓari na fara faɗin.
"Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un...! Don Allah... don girman Allah Sardauna karka sake ni! Don girman Allah karka yi mini haka!"
Cikin rashin tabbas da ƙasƙanci na zube a ƙasa, na rarrafa ina jan gwiwoyina na matsa daidai wajen ƙafafunsa, na sa hannuna duka biyu waɗanda ke rawa tamkar ana jijigasu, na ƙanƙame ƙafarsa da ƙarfi, hawaye masu zafi suka wanke mini fuska.
"Sardauna...! Sardauna ka yi wa Allah, ka yi wa Ma'aiki karka sake ni! Ina sonka... ina sonka da dukan rayuwata! Ban san yadda zan yi ba, ban san yadda zan rayu ba idan babu kai a rayuwata... Don Allah Sardauna, karka watsar da ni...!"
Cike da ƙyama, ya janye ƙafarsa da ƙarfi daga kankamewar da na yi masa, wanda hakan ya sanya na kusan kifa fuskata da ƙasa. Ya ja wani uban tsaki mai tsayi, ya dube ni da waɗancan idanun nasa da suka riga suka zama tamkar na dabba mai cutarwa, sannan ya ce.
"Ke dallah malama, sake ni! Ubanki ma ai kin rasa shi kuma kin rayu, balle kuma ni da kika ganni da haƙoranki talatin da uku! Nana, na gaji da zama da ke... zama marar amfani da riba. Ke ba haihuwa za ki iya yi ba, ba za ki iya samar mini da ‘ya’ya ba, kuma ke ba karatu gare ki ba balle a ce za ki zama wata abar alfahari a nan gaba!"
Na daskare a wurin. Idanuna suka ƙafe a kan kafaɗarsa, wani irin masifaffen sanyi mai daskarar da jini ya ratsa daukacin gangar jikina. Nan take, wani irin sauti mai amo Ƙuuuuuuu...! ya shiga ruri a cikin kunnuwana, yana toshe mini kowane sashi na jiyya.
Zuciyata ta fara wani irin juyi na takaici da nadama. Sardauna... Sardaunan da ya zama silar ajiye karatuna tun bayan gama Aji na Farko a jami'a, domin kawai ya ce kishina yake yi ba ya son maza su kalle ni, yau shi ne yake tsaye a gabana yana yi mini gorin rashin karatu? A daidai lokacin da abokan karatuna suke gab da shiga shekarar ƙarshe ta kammalawa, yau ga ni nan daskare a ƙasa, ina karɓar kaskanci a matsayin jahila marar amfani.
"Hahahaha...! Ana bikin duniya, akan yi na ƙiyama! Ga ki nan don Allah, shashasha da ba ta san darajar kanta ba. Miji zai sake ki, amma kina wani durƙusawa a ƙasa kina masa magiya da kuka! Gaskiya Nana, ke jahila ce ta ƙarshe, tabbas!"
Muryar Bilkisu, mai cike da dafin da ya fi na kowane maciji ɓarna, ita ta dawo da ni daga wancan zancen zucin da nake yi.
Ina nan a durƙushe, amma ɗakin gaba ɗaya jiri yake mini, ganina yana neman gaba ɗaya ya canza launi ya koma baƙi. Hawaye masu zafi suka wanke mini fuska, amma saboda tsananin son Sardauna da ya riga ya zama jinin jikina, ban ji kunya ko tsoron sake kaskantar da kaina ba. Da ƙyar, cikin rawar jiki da karkarwa, na sake rarrafawa a kan gwiwoyina zuwa daidai inda yake tsaye, na sake sa hannuna duka biyu na ƙanƙame ƙafarsa, muryata tana fita kaɗan kaɗan.
"Don Allah... don Allah Sardauna karka sake ni! Zan zauna da kai a kowane yanayi... ko da a haka ne. Ba zan nemi abinci ba, ba zan nemi abin sha ba, ba zan sake neman suttura ba! Ko magana ba zan rinka yi maka ba, ba zan sake takura maka ka kalle ni a matsayin mace ba... don Allah muddin dai ina cikin gidan nan da sunanka, zan jure kowane irin wulaƙanci...!"
Ya kalle ni na tsawon daƙiƙa guda, fuskar nan tasa babu alamar imani ko ɗigon tausayi, ya ce.
"Nana, ba zan iya ci gaba da zama da ke a haka ba. Daman ƙuruciyarki na aura, kuma a yanzu gashi ta riga ta tafi, kin rage daɗi. Nana, ba ke nake so ba... ƙuruciyarki nake so, kuma da ita nake son na rayu, ba da ke ba, Nana! Zan dai bar ki ki ci gaba da zama a ɓangaren can na gidan, ba tare da rashin abinci, abin sha, ko suttura ba. Amma kuma babu wanda zai san na sake ki a duniyar nan... har abada!"
Na yi shiru, tabbas ina son Sardauna, so mai girma da zafi, son da ya riga ya zama jinin jikina. Idan har zan zauna a gidan nan ƙarƙashin ikonsa, to wallahi zan zauna, matuƙar dai ina numfashi a inuwar gidansa.
“Saki nawa za a rubuta?”
Muryar Bilkisu ta katse mini tunani, tana tambayarsa cikin isa.
“Ɗaya.”
“Ɗaya kuma?”
Ta tambaya a gatsine, cike da rashin gamsuwa. Shi kuma ya dube ta, ya ba ta amsa a tsawace tamkar zai rufeta da duka.
“Eyh ɗaya! Ki rubuta: Ni Fahad Ta’ambo (Sardauna) na saki Nana saki ɗaya.”
Ba musu ta ɗauki biron ta rubuta. Ni kam wani irin baƙin abu mai ɗaci na ji ya tsaya mini a wuya, ya toshe mini ƙofofin numfashi. Saki mafi ƙasƙanci da walakanci a rayuwar mace, shi ne kishiyarki ta rubuta miki saki da hannunta! Ni Nana na shiga uku! Rayuwata ta gama lalacewa!
“Nuna mata ta gani!”
Sardauna ya ba ta umarni cikin ko-in-kula.
Ta sa takardar daidai saitin fuskata, ta nuna mini rubutun da ya wargaza mini dukkan sauran darajata. Sannan ya kalli takardar, ya ce.
“To yaga, saboda ba na so kowa ya gani.”
Ba musu Bilkisu ta cire takardar, ta yaga ta guntu-guntu ta watso min a fuskata tamkar almajira.
“A tashi a tafi!”
Ba shiri na yunƙura zan miƙe, sai dai kafin gwiwoyina su ɗauki nauyin jikina, na ji ɗakin gaba ɗaya ya kife da ni. Wani duhu mai nauyi ya lullube idanuna, na zube a kasa sumamma...
********
Ɗum... ɗum... ɗum...!
Haka nake jin kaina yana mini wani irin duka kamar an buga guduma. A hankali na fara
Ƙoƙarin buɗe idona, amma wani zazzafan raɗaɗi ya sara mini a tsakiyar kaina ya sanya na sake rufe idon da sauri, ina dafe gashin kaina. Muryoyin mutane na jiyo a kaina sama sama.
“Dr. Na’ima, zan bar wannan case ɗin a hannunki don Allah. Referral ne daga wajen wani abokina, to ba ya ƙasar a yanzu, ki kula da ita sosai.”
“Ni fuskar patient ɗin tamkar na sani, amma bari ta tashi tukunna.”
Sai da na kwashe kusan mintuna talatin ina nishi, sannan na iya buɗe idona gaba ɗaya. A hankali na sauke su a kan kyakkyawar fuskar Dr. Na’ima Daƙayyawa, wadda ke sanye da farar rigar likitoci tana duba wani file.
“Mrs. Ta’ambo, is that you?”
Na gyaɗa mata kai a hankali, hawaye guda ɗaya mai zafi ya fito daga gefen idona. Ta taso kusa da ni, ta zauna a gefen gadon asibitin.
“Duk abin da nake fada miki a baya, ba kya ji ko? Ki godewa Allah da yasa yanzu BP ɗin ya dawo daidai, amma kina da babbar damuwa a ranki.”
Na girgiza kaina na kasa cewa uffan, bakina ya yi mini nauyi tamkar an daure shi. Ta zuba mini idanu na tsawon dakika, sai can kuma ta ce.
“Kin kyauta abin da kika yi wa mahaifarki? Na shan abubuwan da za su hana ki daukar ciki?”
"Ban gane abin da kika fada ba fa..."
Na fada cikin kiɗima, kaina ya sake ɗaukar wani irin sabon jiri. Ji nake yi kamar akan garwashin wuta nake kwance ba a kan gadon asibiti ba.
"Abin da kika shuka da hannunki ne ya dawo miki yanzu.”
Ta faɗa tana yi mini wani irin kallo na zargi da takaici.
"Wallahi ban gane abin da kike nufi ba! Abin da na sani, rayuwata ban taɓa shan wani abu da zai hana ni ɗaukar ciki ba! Hasali ma akwai wani likita da nake zuwa wajensa tun can baya, kullum yana duba ni yana ce mini mahaifata ta fara ƙwari, kuma bai taɓa yi mini irin wannan zancen ba!"
"Uhm... shi wane ne wannan likitan?"
"Sunansa Dakta Ɗan Adala... kuma abokin miji na ne."
Fuskar Dr. Na’ima ta canza gaba daya, ta matso da fuskarta tana kalleni, "Kina nufin da kanki ba ki taɓa shan wani abu ba da zai hana ki ɗaukar ciki ba, wanda gashi yanzu ya haifar miki da mummunar lalacewar mahaifa? Kuma wannan lalacewar tuntuni ta faru, ba yanzu ba."
"Wallahi-Allah ban taɓa sha ba! Ban taɓa sani ba!"
Na fada ina kuka, kaina yana wani irin juya mini, jiri yana ɗibana duk da cewa a zaune nake.
Hannuna ta kama ta damƙe shi da ƙarfi, sannan ta ce.
“Mrs. Ta’ambo, ki nutsu... ki saurare ni da kyau."
Kallonta na yi, babbar mace wadda na san tabbas ta haife ni, ta haife har Yayatama.
"To..."
Na fada ina saurarenta da dukkan guntuwar nutsuwar da ke tare da ni.
"Mijinki... ya kuke da shi? Ina nufin yanayin zamantakewar aurenku na cikin gida?"
Sai da na goge hawayen idona da gefen rigata sannan na ce.
“Komai daidai yake... yana nuna mini soyayya ta daban."
"Bai taɓa nuna miki bacin rai ko damuwa a kan rashin haihuwa ba?"
"Eyh... bai taɓa ba. Shi da abokinsa Dakta Ɗan Adala ma sune kusan kullum suke kwantar mini da hankali, suke ce mini lokaci ne bai yi ba. Sai dai daga baya-bayan nan ne ya fara nuna damuwa a fili, har abin ya kai shi ga ƙara aure."
"Hhmm... auren soyayya kuka yi ko na haɗin gida?"
Ta tambaya tana girgiza kai. Sai da na kalleta da kyau sannan na ce.
“Na soyayya ne."
"To akwai babbar matsala gaskiya! Tabbas, ko da saninki ko akasin haka, amma an daɗe ana baki kwayar da ke hana ɗaukar ciki, kuma da alamu kin daɗe kina amfani da ita a asirce har aka kai ga wannan matakin na cewa mahaifarki ta mutu!"
Wani muguwan shock ne ya daki zuciyata...! Dakta Ɗan Adala? Magungunan da yake ba ni yana cewa na "Kwarin Mahaifa" ne? Sardauna ne ke karbo mini?
Kafin na gama hada wannan mummunan lissafin a kwakwalwata, aka buɗe ƙofar ɗakin asibitin Sardauna ya shigo, fuskarsa ɗauke da wani irin murmushi. A hankali ya tako cikin ɗakin tamkar babu abin da ya faru. Dr. Na’ima na ganinsa ta miƙe tsaye, ta dube shi cikin ɓacin rai ta ce.
“Idan ka gama da ita, meet me in my office.”
“Okay,” ya amsa mata cikin ko-in-kula, ita kuma ta fice ta ja musu kofar.
Ɗakin ya rage daga ni sai shi. Ya tsaya daidai saitin gadon, ya zuba mini idanunsa da na daɗe ina bai wa amana.
“Nana... kallon me kike mini?”
Wata irin azabbariyar tsana, mai ɗaci da zafi, ita na ji ta dirga ta mamaye kowane sashi na zuciyata a lokaci guda. Tsanarsa ta daki jinin jikina.
Ya duka daidai fuskata, ya rage murya yadda ni kaɗai zan ji, ya ce.
“Nana, kin sami labarin abin da na yi wa mahaifarki ko? To ba iya wannan ba... ki sa rai da shirin ganin abubuwa da yawa nan gaba Nana, waɗanda ma ba lallai kanki da rayuwarki su iya daukansu ba!”
KARSHE EN LITTTAFI NA FARKO
END OF BOOK ONE.
Jama’a wannan bakomai ba ne illa shimfiɗa, littafi na ɗaya ya shimfiɗa mana hanyar da zamu kwarara doguwar tafiya. Ga dai Sardauna ya saki Nana, shin zata zauna a gidan ko tafiya zatayi? Ga kuma Turaki a gefe. Ku hanzarta ku biya kuɗinku ku karanta, na tabbatar muku babu nadama a cikin wannan tafiyar.
*Littafin Sartse na kuɗi ne 700 a whatsapp ake posting, ku tura kuɗin karatu ta wannan acc ɗin 8104743474 opay Hafsat muhammad lawan, shaidar biya ko tuntuɓa ta wannan lambar.*
***