BAKIN RAFI.....

Chapter 5

by @hauwausani476

*Saƙon Da Bai Dace Ba*

Tana na cikin wannan yanayine wayar ta fara ƙara, alamar saƙo ya shigo. Ta ɗauko ta duba, tasan na wanene zancen.

Har wayau dai shine wannan hatsabibin, ga abinda saƙon ya ce:  

> *“Yanzu wasar zai fara. Idan bakishiga hankalinkiba zan fallasa sirrinki zuwa ga wannan shashan mijinnaki. Da wahala ta mamaye shi ya aureki, ba tare da sanin koke wace ba!!!!”*

Lokacin da ta kammala karanta saƙon nashi, wasu zafan hawaye suka dinga zuba ba ƙaƙautawa. Ta fara kuka sosai kamar ba gobe.

Motsin shigowarsa ne ya dakatar da ita. Ta yi saurin goge hawayenta. Da sassarfa ya zo gareta, yana bincikar ta lafiya, domin yanayin da ta ƙara masa sallama ya san an yi kuka cikin ta.

Ya fara da rungumota, yana ƙara tambayarta. Bata ce komai ba sai numfashin da ke saukewa, alamar ta jima tana kuka.

Can ya nisa ya ce: “Shantyna, kar ki cutarda zuciyata. Ina son sanin abinda ke damunki. Ki sani ina da kishi da kuma tsafi, mussamman idan abinda ya shafeki ne. Zan iya hukunta ko waye har ni, idan aka zo wurin damuwarkine.  

Allah ne ya haɗamu, bansan dalilin hakan ba.  
Sai dai na san ina tausanki, ina kuma zunzurutun ƙaunarki.  
Ki sani idan har na gane wani rashin gaskiya a gareki, wannan son bazai hana ni hukuntaki ba.”

Ita dai bata ce komai ba. Ta fahimci ransa ya fara baci, sai ta yi saurin kawarda zancen gudun karya fara fushin nan nashi mai wuyar sauka.

Sumar kanshi ne ta fara cukulkulawa, tare da yi masa cakulkuli da waƙoƙin soyayya masu tsima zuciya.  

Can ya fara saukowa lokacin da ta fara rera baitin nan:

> Na baka saurata---  
> Dan ka cancanta!--  
> Zauna ka huta!--  
> Ga makullin mota!--  
> Mijina! Ya masoyi!!  
> Kai zanwa bita!!  
> Da kalam so! So!  
> Da kalaman soyayya!!!!!

Tana kan haka baisan lokacin da ya ɗauketa ba sai uwar dakinsu. Be ajeta ko ina ba sai bisa gadonsu, nan labari ya canja salo na ma’aurata.

---

Ibrahim da Aisha na tsaye cikin ɗakin, hannayensu na haɗe. Da murmushin da ke fuskarsa, wayar shi ce da ke kan gado ta yi ƙara.

“Ɗan jira,” ya ce, ya je ya ɗauki wayar.

Aisha ta tsaya a wurinta, zuciyarta na bugawa. Tana tuna kalaman mutumen nan, kawai saƙon daga gareshi ne. Haka take ji a duk lokacin da saƙon sirrin nata ke shigowa.

Ibrahim ya duba allon wayar. Saƙo ne daga lamba da ba a adana ba:  
_“Ka tabbata ka san matar da ka aura? Wasu abubuwa ba sa ɓoyewa har abada.”_

Fuskarsa ta canja. Murmushin da ya daɗe a fuskarsa ya ɓace nan take.  
Ya karanta saƙon sau biyu, kamar bai gane ba. Sa’an nan ya ɗaga kai ya kalli Aisha.

Aisha ta lura da canjin fuskarsa. Ƙirjinta ne ya fara faɗuwa.  
“Ibrahim… me ya faru?” ta tambaya cikin rawar murya.

Ya ɗade yana kallonta kafin ya ce:  
“Ba komai. Kuskure ne kawai.”  

Amma muryarsa ba ta da irin natsuwa da ya saba da ita.

Ya sanya wayar a aljihu, amma tunaninsa ya tashi.  
_Wa ya san abin da ke tsakanina da Aisha? Me ya sani wanda ban san shi ba?_

Aisha ta juya ta nufi taga, tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta.  

A zuciyarta tana :  
_Addu’ar Allah ya kawo mata mafita._