BAKIN RAFI.....

Chapter 6

by @hauwausani476

*Tsakanin Shakku da Tsoro*

Lokacin da Ibrahim ya je gurin aiki, tunani ya hana shi sukuni. Yana son ya dawo gida, amma gidan ya fara zamewa wurin damuwa, sabanin lokutan baya da nan ne wurin samun natsuwa.

Dare ya yi. Ibrahim yana zaune a gefen gado, wayarsa a hannunsa. Saƙon nan bai fita daga zuciyarsa ba.  
_“Ka tabbata ka san matar da ka aura?”_  

Waye shi? Me yake so? Ko dai abinda zuciyarsa ke gaya masa gaskiya ne — cewa Aisha tana da wani sirrin da bai sani ba, wanda batasan ya sa nine, shi ne dalilin boye mai labarinta.

Sai kuma ya yi saurin kauda zancen, gudun kar shaidan ya ci nasar sanya masa zarginta cikin zuciyarsa.

Ya kalli Aisha da ke kwance gefensa, tana yin kamar tana barci. Amma numfashinta ba ya nuna haka.  

“Idan akwai wani abu da ki ke ɓoye mini, Ashanty… me zai sa ki ɓoye mini?” ya fada cikin zuciyarsa.  
Ba ya so ya tambaye ta kai tsaye — yana tsoron jin amsar da zai canja komai.

*Aisha*  

A gefe guda, tunani ya hana Aisha tayi barci. Kowane kalma daga saƙon tana zagaya mata a kai.  
Ta san wannan rana za ta zo. Ta san wannan sirrin zai fito fili.

Amma tana jin tsoro. Tsoron rasa amincewar Ibrahim. Tsoron ganin idanunsa sun canja idan ya san gaskiyar da ta ɓoye tun kafin aurensu.  

Ta lumshe ido, tana addu’a cikin zuciyarta:  
_Allah ka bani ƙarfin zuciya. Idan gaskiya ta fito, ka sa Ibrahim ya ci gaba da sona. Karya yenke alaqar da ke tsakaninmu._

Gidan da ya cika da soyayya da kwanciyar hankali, yanzu shine gidan da ya cika da shiru, ya kuma zama mai nauyi. 

Dukansu suna tare, amma zuciyoyinsu na tafiya wurare daban-daban.  
Ibrahim yana tunanin amana.  
Aisha tana tunanin lokaci.  

Kuma saƙon nan, kamar zai zama abin da zai yanke ko ya haɗa su har abada.