BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----13

Tun bayan fitan Suhail daga gidan su Zeenah…

Zuciyarsa ta ƙara shiga wani irin hali.

Driving yake amma gaba ɗaya tunanin sa baya kan titi

Mami ce zaune a palorn kiran Aunty aisha ya shigo ta daga bayan sun gaisa Mami ke fada mata Maganar bikin Suhail.

Aunty aisha ta cika da mamaki ta ce"Ummi Suhail zaiyi aure kuma sai yanzu za'a fadamin "

Mami ta ce"yanzun ma abinda yasa na faɗa maki dan kar kiji daga sama ne nan tayi mata bayanin komai daya faru sannan ta ce kuma babu ruwan ta a Safgar bikin sa"

Aunty aisha cike da takaicin maganar mami ta ce"haba ummi a gani na ai wannan ba abin damuwa bane kawai ki musu fatan Alkairi"

katse wayar mami tayi da ba wannan ta kira taji ba.

Mami su biyu kadai iyayen su suka haifa daga ita sai aunty Aysha iyayen su sun rasu lokaci guda sakamakon hadarin jirgin sama mahaifinsu baban proffesor ne a Abuja mutun ne mai tarin Ilimi tun bayan rasuwar su rikon aunty aisha ya dawo hannun mami ita ta aurad da ita ga mahaifin Meerah wanda ya rasu shekara biyu da suka wuce  bayan fama da ciwon daji hakan yasa aunty Aisha ke kiran mami da Ummi ta riƙe ta tamkar yar ta ta cikin ta duk wani responsibities na uwa shi mami ke yi mata.

bayan ta ajiye wayar meerah dake kan kujera tana ɗan na wayar ta ce"momy wai maganar bikin wa ake"

"Wai Suhail ne zaiyi aure sai yau ummi take faɗamin kawai dan zai auri yar talakkawa"

wayar dake hannun meerah ta fadi ta mike cike da tashin hankali ta ce"wani Suhail din momy"

hararar Aunty aisha tayi ganin ta fita hayyacinta jin maganar auren Suhail ta ce"Wani Suhail kika sani banda nq ummi"

ji tayi kanta ya sara har ta fara jin wata irin juya 

Momy ta ce"ke lafiyar ki kuwa"

kokarin daidaita kanta tayi ta ce"bakomai momy"
wayar ta ɗauka ta nufi Dakin ta key ta saka wa kofar ta jefar da wayar ta kan gado ta saki wani irin kuka har sai da taji nauyin dutsen da ya tsaya mata a kirji ya fara raguwa.

Aunty aisha ta tashi ta bi bayan ta jin kofar ta murda taji alamun an saka key "meerah" ta kira sunan ta shiru tayi bata amsa ba sai sasshekar kuka da take aunty Aisha har ra gaji da bugun kofar ta koma dakin ta dauko spare key.

tashi tayi ta nufi bathroom ta wanko fuskar ta

Meerah na gama wanke fuskarta…

ta ɗago tana kallon kanta cikin mirror

Idanunta sunyi jawur saboda kukan da tayi

kan gado ta koma zauna aunty aisha ta gama duba ko ina bata ga keys din ba hakan yasa ta dawo wannan karin ta samu kofar a buɗe shiga tayi ta zauna kusa da meerah.

meerah ta kasa ɗago fuskar ta ta kallli mahaifiyar ta cike da kulawa aunty aisha ta ce"Meerah tashi magana zanyi dake"

ɗago fuskar tayi da tayi jajir sakamakon kukan da tayi ta kasa haɗa ido da ita sai nuƙar dakai take.

hannun momy ta kama ta ce"Ameerah miyasa kika boyen min tun farko kina son Suhail"

gabanta yayi mummunar faduwar ganin momy na nema tona mata asirin da ta shafe shekaru sama da goma tana boƴe wa"

"momy Suhail kuma waya fada maki san shi nake"

momy tayi murmushi ta ce"Meerah kenan a tunanin ki akwai abinda zaki boye min kar ki manta ni mahaifiyar kice ina lura da duk wani motsin ki a cikin gidan ina lura dake kuma nasan kina son Suhail alamomi da yawa sun suna na hakan yadda baki jituwa dashi da kuma yadda kika taɗa hankalin ki daga kin Maganar auren sa"

hawaye suka fara saukowa daga idanun ta a wannan karon ta kasa cewa komi 

momy ta ce"miyasa tun farko baki faɗamin ba kar ki manta nida mahaifiyarsa ciki ɗaya muka fito kuma matukar na faɗa mata da kina son Suhail zata shige maki gaba har ki mallakesa amman ki ƙi sai ma kaurace masa da kika fara kika cusawa zuciyarki tsanar sa ta babu gyara babu dalili Yanzu kuma bakin alqalami ya riga ya bushe"


meerah ta faɗa jikin momy ta fashe da kuka Aunty aisha ta tausaya mata sosai ganin yadda ciwon so ke wahalar mata da diyar ta gashi a wannan gabar ta kasa taimakon ta dan bata san da wani ido zata kalli ummi ta faɗa mata Meerah nason Suhail Yarinyar da Kowa yasan ta tsanesa ko inuwa guda bata yarda su hada da Suhail.

Bayan sati biyu 

lefe na gani na Faɗa su aunty Fauziya suka hado a kano kudi masu yawa Abba ke kashe wajen gudanar da bikin yau ne za a kai kayan gidan su Iman mota ukku Abba ya tada guda aka saka akwatunan sai ɗaya aunty Fauziya da Zarah gudar kuma naima ce sai aunty Aysha.

a kofar gidan Malan aka yi parking aka fara shigar da akwatunan ciki.

Tsakar gidan ya cika da akwatunan lefe masu uban yawa.

Akwatuna talatin da biyu cif-cif ne jere tamkar ana baje kolin kaya.

wanda ammi ta kira dan karɓar lefen bakin su yaƙi rufuwa tsabar mamaki Aunty zaituna kuwa sai washe baki take.

shimfida akayi masu bayan an gama shigowa da kayan bayan an gama gaisawa aunty zaituna ta fara bude akwatunan kayan ya salam kaya ne masu tsada cike fam da akwatunan masu tsada da daukar ido.

karamin akwatunan kuma sakar gold ce guda biyu manya ko wanne da abin hannun su.

Wata dattijuwa ta ce"
“Ni dai tun haihuwata ban taɓa ganin lefe irin wannan ba iman tayi Goshi Allah yasa gidan zaman tane ya kade fitina"

duka suka amsa da "amin" banda Naima da tunda ta siho take haɗe rai sai tofar da yawu take duk ta nuna alamun ƙyamarta wanda duk motsin ta akan idon Ammi da ta kasa kallon ko abu daya cikin akwatin.

haka aka gama komai aka fito masu da lemuka da biscuit wanda duk kokarin Mubarak ne gudan kar azo a rena su suma.

cikin kudi million biyu da aka ɗora cikin kayan suka raba suka na su a matsayin tukwuici Aunty Fauziya da Zarah duk suka ce a barsu kawai amarya tayi dinkin amman Naima ta sa hannu caraf ta amshe a cewar raba mugu da makami ibada ne.

dan da da ita aka je siyan lefen nan wallahi ko rabi baza ta bari a siyo ba Wannan lefen ai da gidan arziki ya dace ba gidan talakkawa da basu san darajar kayan ba.



Kuyi manage da Wannan banda charge wlh 

yaushe ya kamata muyi hutun sallah mu hade a comment section🥱