GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 2

by @nusybee143

Page 2



Matan Alhaji Yusuf maliya uku, Hajiya Zainab ita ce uwar gida,wadda yara suke kira da Ummeey, haihuwarta ɗaya a gidan,ita ce babbar yar Alhaji Yusuf maliya, wato FATIMA SHAHEEDA,sai Hajiya Atika, ƴaƴanta biyar,Safwan shine babba,sai Malika,sai Amina,mukhtar sai auta Fauziyya 

Hajiya Ruƙayya ita ce matar Alhaji Yusuf Maliya ta ƙarshe, tana da yara uku, Zainab,mai sunan Ummeey, wadda ake kira da Iman,sai Nafisa, sai autanta Usman 

Hajiya Sa'adatu, wadda ake kira da Mummy yaranta huɗu a duniya,Muyassar ne babba,ya kammala karatunsa na masters a ƙasar Britain,inda ya karanci civil engineering a jami'ar Harvard,ya fita da kyakkyawan sakamako,sai ƙannensa Hassan da Hussaini, wadanda suke jami'ar cologne suna karantar fannoni dabam dabam na lafiya,sai autarsu Na'ima, wadda take nata karatun a NUN da ke Abuja 

Alhaji Rufa'i yaransa bakwai,uwar gidansa na da uku amaryarshi tana da huɗu,sai Alhaji Aliyu,shi kuma yaranshi tara, duka daga matarshi ɗaya da suke zaune tare,sai auta Salma,mai yara biyu tal a duniya yan maza sakwanni, wadanda zuwa wannan lokaci dukkansu suna matakin farko a jami'ar Massachusetts da ke US 

A bisa al'adar MALIYA family,a duk lokacin da za'a ƙaddamar da wani abu mai muhimmanci,ko wanda zai shafi al'ummar ahalin,ana haɗuwa a katafaren gidan Alhaji Yusuf Maliya, kasancewar shine shugaban ahalin,a matsayinsa na babba,kuma wanda yake gina ahalin a duk lokacin da aka samu wata ɓaraka, musamman da ya kasance mahaifiyarsu gaba ɗaya, Hajiya Zulayhat Maliya, wadda kafatanin ilahirin ahalin suke kiranta da hajiyya innayyo,ta kasance a gidansa,a sashe na dabam da aka ware mata

Kamar yadda aka saba yau ma sun taru a katafaren parlourn gidan,gaba ɗaya iyaye da yaran,da alamu wani gagarumin abu mai muhimmanci za'a tattauna a kai

Parlourn ya ɗauki shiru, Alhaji Yusuf Maliya ya ja numfashi a hankali, sannan ya cigaba da magana 

"Sanin kowa ne a gidan nan,kun san abin da ya faru shekaru huɗu da suka wuce,wani tabo ya samu ahalin nan,girma da mutuncinmu ya zuba a idanun duniya,maƙiya sun yi farin ciki, masoya sun yi baƙin ciki

A wancan karon na ɗauki hakan a matsayin tsautsayi,amma wannan karon ina ganin duk abin da ya faru dole ne mu bar shi a matsayin ganganci,duba da cewa ba shine karo na farko ba,amma menene shawararku akan hakan?"

Hajiya Sa'adatu, wadda ta kasance babba a cikin ƙannen Alhaji Yusuf Maliya ta gyara zama tana jan numfashi, sannan ta ce"Alhaji Ni ina ganin ba wata matsala ba ce hakan, musamman duba da nutsuwa da tarbiyyar yaran,abu ne mai wahala su manta da hakan idan suka samu kansu a baƙon waje

Kuma bugu da ƙari ya dace a ce an saka musu idanu, saboda su mata ne,kuma ita mace sai da sanya idanu,amma ni dai daga gare ni ina yi musu kyakkyawan zato,amma me kika ce Ruƙayya?"ta mayar da tambayar ga matar Alhaji Yusuf Maliya da suka fi shiri,wato Hajiya Ruƙayya, wadda yara suke yiwa lakabi da Mommy 

Mommy gyara zama ta yi, sannan ta ce"to ni dai ba zan ce komai ba,amma kuma ga yaran nan za'a samu kyakkyawar amsa daga gare su "

Alhaji Yusuf ya dubi yaran,da alamu sun zaƙu a tambaye su ɗin,amma maimakon ya tambaye su sai ya mayar da akalar tambayar ga Hajiya Zainab (Ummeey)

A tausashe Ummeey ta dubi Alhaji Yusuf bayan ta gyara zama ta ce

"Alhaji a dai duba sosai,ka ga yara mata ne,kuma inda za su tafi babu wani babba a can

Idan da hali a nema musu makarantar a nan,babu laifi su koma gabanka a Abuja,ko su zauna a anan a gaban iyayensu,a ko'ina aka yi karatun ba wani abu ake nema ba sai albarkarshi 

Idan muka yi duba a baya an yi irin haka,an samu sakamako mara daɗi,to mu bar wancan a matsayin ƙaddara,a wannan karon sai mu kiyaye,idan muka yi hakan sai Allah ya taimake mu"

Da sauri yaran suka kalle ta cikin wani irin baƙin ciki,don gani suke yi Ummeey hassada take yi musu tana son ta shiga tsakaninsu da burinsu,amma babu halin magana, musamman da ya kasance suna gaban Alhaji Yusuf Maliya, wanda ko manyan ba sa yin magana sai an nemi jin ta bakinsu 

Sai dai kafin wani yunƙuri cikin ɓacin rai Hajiya Atika ta dubi Ummeey ta ce

"A'a Hajiya Zainab,wannan ba girmanki bane!wanne dalilin zai saka ki yiwa yara baki bayan ba sune suka yi miki laifi ba?

Ya kamata a rinƙa yi ana saran bakin gatari,don wannan abu bai dace ba gaskiya "

Tana rufe baki Hajiya Sa'adatu ta ɗora"kuma ban da haka ma Allah na tuba ai yaran sun samu tarbiyya sosai,ina su ina wannan abu saboda Allah?

Kawai dai kin san wasu mutanen, musamman waɗanda ba sune suka haifi yaro ba"

Ummeey ta girgiza kai ta ce"kayya!

Allah ya kiyashe mu da aikin danasani da ruɗin shaiɗan 

Kun yiwa magana ta gurguwar fahimta, babu komai, Allah ya tsare su,ya kawo abin da aka je nema 

Hajiya Sa'adatu ɗa ai na kowa ne,da ɗa da dukiya ba'a yi musu mugunta, saboda Allah ne kaɗai ya san wanda zai more su"

Ganin abin zai zama na magana ya sa Alhaji Yusuf cikin ɗaurewar fuska ya ce"ya isa haka!

Bana son na sake jin maganar nan ta cewa babu tarbiyya a gidan nan,hakan yana nuna na gaza ne, Ni kuma na san iya ƙoƙarin da na yi,a cikin matana babu mara tarbiyya,don haka haifar mara tarbiyya ba dai a gidana ba,sai dai idan abin ya zo da tsautsayi 

Sannan ke kuma Hajiya Zainab,maganarki ta cewa a kula babu kowa da yake kallonsu ni na san me nake yi,ku dai ku yi musu addu'a kawai, Allah ya bada sa'a,ya kare su daga ruɗin zamani,ya sa a samo abin da aka je nema"kusan gaba ɗaya aka amsa da Ameen 

Iman da Amina,sai ƴar Alhaji Rufa'i Surayya,sune wadanda ake ta wannan tattaunawar akan tafiyarsu abroad karatu,amma iyalan sun kasance cikin shakku saboda tabon da suka samu a cikinsu wanda ba su san ranar da zai warke ba

Farin ciki sosai ya bayyana a fuskokin yaran,amma babu wanda ya samu zarafin magana tunda har zuwa yanzu Abba(Alhaji Yusuf Maliya)bai ba su damar yin magana ba,kamar yadda tsarin family ɗin yake,wato yaro baya taɓa yin magana sai ya sami umarni daga wajen babba 

Alhaji Yusuf maliya ya mayar da hankalinsa ga yaran da za su tafi karatun,su huɗu ne,bayan Amina da Iman da Surayya akwai Salim da Mufeed yaran Alhaji Rufa'i,amma da yake su maza ne,kuma matsalar da aka samu a baya ba daga mazan aka samu ba shi yasa ba'a damu sosai da nasu ɓangaren ba

Alhaji Yusuf ya dubi yaran,a nutse ya kira sunayensu ɗaya bayan ɗaya,suka amsa cikin girmamawa, cikin nutsuwa ya fara bayani 

"Ku ba ni hankalinku nan

Kun san tsarin, musamman ku yan mata,a Maliya family ba'a barin mata su fita don zuwa wata ƙasar karatu, saboda kowa ya san abin da hakan ya janyo mana 

Sai dai wannan karon za mu dage mu bar ku ku fita waje don karatu,ba don komai ba,sai don muna kyautata muku zato 


Zainab da Surayya za su tashi zuwa ƙasar US nan da kwanaki takwas in sha Allah,inda Zainab za ta karanci medicine ita kuma Surayya zata karanci business administration, Saleem da Amina za su tafi Turkey inda Saleem zai karanci medicine, Amina zata karanci engineering, Mufeed kuma zai tafi Spain inda zai karanci SOFTWARE ENGINEERING!"

Ambatar software engineering kawai da Abba (Alhaji Yusuf Maliya)ya yi ya sa ɗakin ya yi wani irin shiru,tuni wasu zuƙata suka tsinke,wasu kuma suka shiga kokwanto da fargabar kar a sake afkawa GADAR TSAUTSAYI makamanciyar ta baya,ta rufta da su a karo na biyu,a wannan karon kuwa sun san kafin su dawo daidai za'a ɗauki lokaci mai tsawo

Alhaji Yusuf Maliya shi kanshi ya ji wani canji,amma ko a fuska bai nuna ba,ya cigaba da jawabinsa cikin nutsuwa 

"Don haka ina yi wa kowanne yaro fatan alkhairi,ina fatan Allah ya kai ku lafiya ya ba ku abin da kuka je nema

Nasiha ta kuwa bata wuce ku ji tsoron Allah ba, ku kama mutunci da ƙimar kanku musamman ma ku mata,ku yi abin da ya dace,kar ku ga cewa ba ma kallonku,kar ku manta cewa mahaliccinku yana kallonku,kuma a kowanne lokaci za ku iya ganinmu mun kawo muku ziyara,da wasa muka ga wani abu wanda bai yi min ba zan ɗauki matakin dakatar da karatun ne kawai, wannan gargaɗin ba iya mata kawai nake yi wa ba, har da ku mazan!"

Cikin girmamawa suke jinjina kai,s hankali kowa a cikinsu yake daukar alwashin kiyaye dokokin da aka kafa musu, Alhaji Yusuf Maliya ya cigaba da bayani

"Duk wani abu da kuke buƙata an kawo,ku duba,idan akwai abin da ba ku gani ba to sai ku yi min magana a kawo"Mufeed ne ya fara rissinawa yana faɗin"to Abba mun gode, Allah ya saka da alkhairi "sauran ma suka rissina suka yi godiya, Alhaji Yusuf ya ce"Masha Allah!

Kuna iya tafiya,na sallame ku"babu musu suka miƙe ɗaya bayan ɗaya suka fice daga katafaren parlourn 

Bayani Alhaji Yusuf ya cigaba da yi,da yadda za'a saka musu idanu,ya dubi Muyassar wanda ya kasance shine babba a cikin jikokin gidan ya ce "Muyassar ga ƙannenka nan,ka saka musu idanu,ka tabbatar da cewa ba su aikata wani abin ashsha ba,na san za ka iya in sha Allah"Muyassar ya rissina yana faɗin "in sha Allah Abba! Allah ya ƙara girma"

Alhaji Yusuf ya ce"to alhamdulillahi, Allah ya yi muku albarka baki ɗaya,wani ya rufe mana taro da addu'a "Muyassar ya yi musu addu'a Kamar yadda aka saba,suka yi sallama,taron ya watse kowa ya kama gabansa 






*ROCKY ESTATE,KANO STATE, NIGERIA*

A hankali motar ƙirar Audi A4 take shiga cikin estate ɗin bayan masu sojojin da suke gadin ƙaton gate ɗin estate ɗin sun ɗage shi,kuma kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba motar ta cigaba da tafiya a hankali don isa inda take nufa 

A daidai wani katafaren gate motar ta yi parking,kuma cikin nutsuwa mamallakin motar ya matsa horn sau ɗaya,jim kaɗan kuma aka ɗaga gate ɗin, motar ta shiga cikin harabar katafaren gidan a hankali 

A parking space ya yi parking motar,tsawon mintina kusan biyar babu alamun zai fito,kafin a hankali ya buɗe motar yana mayar da wayarsa aljihu,da alamu kira ya gama amsawa

CSO Haisam Abdulmalik Madaka kenan,zaƙaƙuri,ƙwararre kuma nagartaccen jami'in tsaro na farin kaya (DSS) wanda Allah ya hore masa sanin makamar iko da zuciya,gami da dagiya a bakin aikinsa,mutum ne mai matuƙar ƙoƙari da ƙwazo 

Shi kaɗai iyayensa suka haifa Mahaifiyarsa Hajiya Rasheeda ta rasu,daga baya mahaifinsa ya auro Hajiya Malika, wadda ta haifi yara mata biyu, Hafsa da Haleema, Hafsa ta yi aure shekaru biyu baya,tana zaune da mijinta a Abuja,ita kuma Haleema tana Egypt inda take karantar pharmacy 

Shekaru bakwai baya Haisam ya yi aure,amma saboda wasu matsaloli da suka Kunno kai a rayuwar auren nasu sun rabu da matar, yanzu haka ƴarshi ɗaya tilo mai sunan mahaifiyarshi, wadda ake kira da Amna tana tare da shi,sai dai ya ɗaukar mata nanny,yar dattijuwa da take kula da ita

Kai tsaye ya nufi entrance ɗin gidan yana tafiya a hankali,da sallama ya shiga katafaren parlourn wanda ya gaji da haduwa, Hajiya Malika, wadda suke kira da Mamie ta amsa tana ɗago kanta tana kallonsa, kafin ya yi wani yunkurin ko ya furta wata kalma Amna da take zaune a study table ɗinta tana zane zanenta ta taho da gudu ta ɗafe shi,yana murmushi ya rungume ta,a kunne ta raɗa masa

"I miss you Papa!"

"I miss you papa's baby!"ya faɗa yana murmushi 

Itama murmushin take yi,ya sauke ta ya kama hannunta suka nufi cikin parlourn 

Sai da ya fara shiga ɗakin Mamie ya gaishe ta,ta amsa fuska a sake sannan ya ja hannun ƴar tashi suka nufi part dinsa 

Tare suka ci abinci kamar yadda suka saba duk dare muddin yana gari,suna ci suna hira sosai,tana ta zuba masa shirme shi kuma yana biye mata, cikin dabaru kuma yana tambayarta game da darussanta na makaranta tana ba shi amsa 

Rasheeda Haisam makawa (Amna) yarinya ce mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira,a kamanni na fuska ta ɗebo mahaifiyarta,amma a halaye da ɗabi'u babu inda ta baro Haisam,akwai soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin uban da ƴarshi, shiyasa ko tafiya ya yi in dai ba aiki bane ya sha masa kai baya rabuwa da kiranta a waya 

Bayan sun gama cin abincin babu jumawa bacci ya ɗauke ta,a hankali ya saɓa ta a kafaɗa,ya ɗauke ta ya fice zuwa part ɗin su

Sai da ya fara yin sallama a bakin ɗakin nata, Nanny ɗinta,da take kira da Mama tana zaune tana lazimi tun bayan ta idar da Sallar isha'i,tana ganinsa ta rissina tana gaishe shi,ya amsa yana gaishe ta sannan ya kwantar da Amna, ya yi musu bankwana ya wuce sashenshi 

Kai tsaye bayan ya canja kaya zuwa na bacci ya wuce ɗakinsa da babu wanda yake shiga, ɗakin bincike ne,ko kuma ɗakin sirri,a wannan ɗakin shi da kanshi bai yarda da kanshi ba ballantana ya yarda da wani,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya mayar da dakin ya rufe 

Kai tsaye computer ɗin shi ya buɗe, ba tare da bata lokaci ba ya kunna,kuma kai tsaye ya shiga zuwa inda hotunanta suke,a nutse yake nazartar komai






#Nusy_bee