TALES OF THE WAZEERIS

The struggle

by @surayyahms

30...🦋🦋🦋

SURAYYAHMS

Tales of the wazeeris...

A hankali hira tsakanin ta da ummu hareera ta lafa bayan ushna tagama cin breakfast din data kawo mata.

sosai tsohuwar ta dinga bata dariya da labaran baya kala kala har yanayin ushna yayi sanyi duk da ma har yanzu akwai wani sabon nauyi da kuma tausayi dake tasowa acikin kirjinta na tunanin irin yadda komi na gidansu ya lalace da irin tarin wahalar da addarta arisha tasha wajen taya mahaifinsu rufa ma masarautarsu asiri

acikin ranta take juya abun har tagama goge bakinta da food napkin nan ne ummu hareera tamike tsaye ahankli tanamai gyara mayafinta, suna hade ido tace" ranki shi dade ki tashi muje in rakaki can sashen tun kafin na wuce nawa..

ushna ta sauke ajiyar zuciya batare da ta musa ba ta mike ta dauki hijab dinta fari mai laushi tasaka akan dogon rigar barcinta snan tabi bayan tsohuwar ahankli.

shiru ne ya ratsa atsakanin su ayayinda suke ratsa manyan hallways na cikin masarautar acikin nitsuwa,

few servants her nd der na gaishe su acikin yanayin girmamawa yayin da ushna ke tafiya ahnkli kanta na kallon kasa tana jin wani iri a zuciyarta.

koda suka isa private parlourn mahaifyarta gimbiya amani noorain, tun daga bakin kofa ushna ta hade ido da ummu zaliha dake zaune akan wani royal couch tana sipping herbal tea cikin ynyin kasaita.

daga dayan bangaren kuma gimbiya amanin ce zaune jikinta sanye da simple but expensive morning sleeping dress idanunta sun dan haura kadan da alamun itama bata wani samu bacci mai kyau ba.

ummu hareera ce ta doka musu sallama saidai tun kafin su karaso ciki ummu zaliha ta hade rai tareda kura musu ido tanamai watsa musu wani irin masifaffen kallo tana karkada kafafunta..

hmm sarauniyar duk duniya yau aka sako a gaba..???

ta fada tana aje cup din tea dinta ahankli.

ummu hareera bata ko kulata ba ta dan taba gadon bayan ushna da alamun ta karasa...

cikin sanyin nitsuwa ushna ta karaso da jinin mulkin ayanayinta har gaban gimbiya amani takai snn ta tsugunna kasa kanta adan sunkuye tanadan murza fareren yatsunta ahnkli tace "...ina kwana mummy

...kafin gimbiya amani tace wani abu takuma cewa "i am sorry about yesterday dan Allah kiy hakuri in sha Allah hakan bazai kara faruwa ba...

wani irin murmushi ne ya kufce ma gimbiya amani lokaci guda kuma idanunta suka cika da kwalla dan wani wankuwa ranta yay fess da ushna tazo ta bada hakurin nan agaban ummu zaliha da tun jiya take famr kushe hankali da tarbiyan ushna harma take cewa ushna bata da hankli da tarbiyar da zatazo ta bata hakuri.

shafa kan ushna tayi cikin gamsuwa saidai kafin ta budi baki tayi wani magana caraf sukaji ummu zaliha ta hargitso cikin katseta da tsaki mai wani irin karfi

cikin kyabe baki tace...ikon Allah..lallai ana munafurci agidan nan tabb di jammm

a masife kuma da karfi ta kalli ushna tace kee...kalle ni nan.

ushna ta dago kai suna hade ido tace wato ke yanzu har kin fara zabar manyan da zaki girmama agidan nan ko?

take parlourn ya dau shiru...

tafara masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba..

sai jefa habaici take wa ummu hareera tana nuna cewa ai dake itace ta lalata yarinyar shiyasa sai abunda tace mata takeyi amma su basu isa da ita ba.

kamar zata daga palon da masifa tace"wanda suka isa dake a gidan nan basu baki umarni kizo ki gaisheni ko ki ban hakuri ba ko???....

when i am talking to u you better answer me...

ushna ta dago kai kadan ta kalli ummu zalihan sannan ta sake maida kanta kasa ba tare data furta uffan ba dan sumtimes idan mulkin ya motsa itama haka take da taurin kai da miskilanci

ummu hareera ta daure fuska tace ke dai zaliha walh girma ya fadi ai kya kyale yrinya tay magana da uwarta kafin ta dawo kanki

azafafe tace keeee hareera dan Allah ki kyale ni dan banyi dake ba, haka kawai yarinya zata shigo nan bata gaisheni ba amma kowa sai ya maida hankalinsa akan wani batun tazo bada hakuri na banza ni ba tureni tay jiya akasa dagangan ba

cikin katsetsu gimbiya amani tace mama ya isa haka ba wani abun tashin hankli ba ne

tana fadin hakan tamaida kallonta kan ushna da taushin murya mai cike da lallami tace "little princess ki gaishar da kakanki kibata hakuri kinji?

da ladabi ushna ta juyo zata aikata hakan cikin sauri ummu zaliha ta mike tsaye tana gyara mayafinta"

"o oo ke da Allah rike gaisuwarki bazan amsa ba, munafuka kawai..ni dai na fada abunda zan fada ke amani idan kika cigaba da rainon wannan baqin halin nata toh anan gaba kece zaki gani wallh.

har lokacin ushna bata dago kai ba ji kawai take zuciyarta na kara yimata nauyi dan batasan me ta taɓa yiwa ummu zaliha data tsaneta har haka ba...

dan tun suna yara take yawan nuna musu bambamci tsakaninta da addarta Arisha sai tanacewa ai sanadiyar haihuwar ushna ne aka cire ma gimbiya amani mahaifa

anasu al'adar she consider ushna to be a badluck child wanda taxo duniya da kafar haqu tareda hana uwarta samun chances na haifo musu ɗa namiji magajin sarautar zamkora.

duk dama tasan da labarin cewa abu ne dayake yawo acikin zuriar zamkora zamani zuwa zamani kusan kowa yasani cewa tun bayan haihuwar sarki murad ba'a sake haifar ɗa namiji a zuriar zamkora ba har ynxu..

amma ita wnn dalili ta rike aranta ta dorawa ushna laifin komi...

cikin sauke ajiyan zuciya gimbiya amani tace shikenan ushna tashi akasa ki zauna kinma ci abinci kuwa

bari akira servant ki gaya mata abinda kike so sai akawo miki

a hankali ushna ta mike harzata zauna kusa da mamantan kenan ummu hareera tariko hannunta tana dan murmushi tace "aa amani, dama hakuri kawai taxo ta baki kinga ai bazata zauna atsakiyar ku tana hada fada tsakaninki da mahaifiyarki ba indan dan abinci ne karki damu ni zan jagorance komi.

gyada kai gimbiya amani tayi cikin nuna fahimtar hakan duba da irin mugun kallo da ummu zalihar take musu tasani sarai bazafa ta yi shiru ta kyale ushna ba.

ahnkli tace..toh shikenan u can go.

ushna ta mike da nitsuwa tafara bin bayan kakanta suna kaiwa bakin kofa tun basuyi nisa ba ummu zaliha ta saki wata ihu cikin bori tanacewa

"..amani kin bani mamaki..ashe haka kike sakarai marar hankali???

gimbiya amani ta juyo da sauri

cikin tsananin bacin rai muryan ummu zaliha harna rawa rawa tace ai bansan shashankin yakai haka ba, yau kin nuna min ke tababbiya ce son yarki ya riga ya rufe miki ido, keda zaki yi fushi ki shareta kiki mata magana har sai

ta galabaita wajen baki hakuri ta koyi hankli shine har kike wani lallaminta agaba kina tambayarta ko taci abinci??

gimbiya amani ta sauke numfashi tana kokarin controlling kanta kafin nan tace "mama please..ushna fa ƴata ce nine nan na haifeta kuma ina son yata..bazaiyu inbari har tanaji aranta cewa na tsaneta ba after all these years that you made me abandon her

Da karfi ummu zaliha tafashe da kuka tana mai dafe kirji tace ohhhhhh Allah, wato laifin ma nawa ne amani...ai da tuntuni sai ki gayamin cewa ke baki son laifin yarki da ban sha wahala wajen gaya maki gaskiya ba toh wallh daga yau na cire hannu na aknta kenan har abada ke kije kiyi duk abunda kikaga dama inta gama lalacewar ina dai yarki ce??? dadin abun nima na haihu bazaki zauna kina walakntani akan yarki ba... i am leaving this house ryt now

tana gama fadin hakan cikin fushi ta fita daga parlourn gaba daya

shiru ne ya ratsa wajen sai can gimbiya amani tamike ahankli tabi bayan mahaifiyartan

daga bangaren ushna kuwa direct sashenta ta koma bayan ummu hareera ta tafi

tana kaiwa dakin ta cire hijab dinta tana jin wani irin kasala ajikin ta bayan yan wasu mintuna sai kawai ta shiga wanka dan ta wanke duk wasu yan kananan tension dake mata yawo akanta da jikinta gabaki daya

ruwan shower mai dumi ta sakar akan soft skin dinta yayin da dan lumshe ido tana kokarin samar makanta cikakken nutsuwa.

bayan mintuna kadan tagama wankan tana fitowa daga bayin daure da towel a kirjinta kenan taji wayarta na ringing.

da saurii ta karaso ta dauka ganin sunan mahaifyar deeja ne akan screen yasa gabanta faduwa

tana daukawa tasaka wayar ahandsfree dan ta samu daman saka pad ajikinta kar jini ya bata mata jiki..da sanyin murya tace helo aunty ina kwana...

cikin yanayin tashin hankli matar ta amsa suka gaisa ba yabo ba fallasa..

after some akward silence tace ushna dama nakiraki ne dan ki taimake ni, naji duk abunda khadija ta miki abakin ziyada but please tell me the real truth...waye wannan mr abdul din? deeja is now very scared, she is no longer eating her meals makaranta sunce wai za’a iya expeling dinta saboda wasu hotona da videos data turawa malami

jin hakan yasaka atake fuskar ushna ya sauya gaba daya tay sauri ta saka pad a hankali ta zauna bakin gadonta tafara bawa matan labarin yadda komai ya faru tun daga yadda mr abdul ya dauke su da kirki da mutunci a farko har zuwa gidan sa daya kai ta da yadda yaso yay drugging dinta dan ya kwana da ita.

cikin jin tausayin matan tace anty mr abdl is a fraud, he lie to us on everything...just tell him u will sue him base on u know abt his true personality zaki gani zai rabu daku

matar ta dinga yima ushna godiya ushna kuma tana dan bata karfin gwiwa

bata sani ba daga bakin kofarta Areesha ce tsaye tajima cikin shiru tanamai sauraren komai da komi da suke fada tun daga farkon zancen har karshe babu abunda bataji ba ayayinda kwakwlwarta yariga ya hasko mata wani muguwar tunani

koda ushna ta katse wayar tana kkrin sauke ajiyan zuciya Areesha ta saka key ta waje ahnkli ta bude kofar ta leko kai cikin dakin tareda sakin gyaran murya ahankli

atake ushna ta juyo adan razane suna hada ido Areesha ta turo kofar gaba daya tana zuba wani calm innocent murmushi hannunta dauke da karamin fancy bag dauke da kayan sawa ajiki

sorry litle sis...am i interrupting smething?

ushna ta girgiza kai tace no...pls come in.

Areesha ta karaso cikin nutsuwa ta samu waje ta zauna kusa da ita bayan sun gaisa

for few seconds tay shiruu tanata kallon ushna dake kkrin shafa mai ajikinta kafin can cikin sakin azcyr zuciya tace soo..who is mr abdul?

kirjin ushna ya buga tace ohh..uhmmm he is our bootcamp supervisor how did u know his..

cikin katseta da sanyin murmushi Areesha tace ohh dont mind me i over heard everything daga kofa dake banasan na shigo ciki ne na katse ku shiyasa ban yi motsi ba, well, tell me abt him he must be a really terrible person huhn

..taking you to his house and trying to drug nd rape you???hmm gaskiya that’s insane.

ushna ta dan lumshe ido tana jin wani iri aranta dan ko kadan bataso da arisha taji wann labarin ba

kafin tagama nitsar da zuciya tadawo cikin hayyacinta taga Areeshan har ta matso kusa da ita tana cewa cmn karki damu ush,ur secrets are safe with me. i’m really sorry you had to go through all that alone.

slowly ushna ta sauke ajiyan zuciya tace its okay nagode big sis, thank god babu wani abunda ma ya hadani dashi..

murmushi areesha tay tace yeah, alhamdullh...shiyasa nake alfahari dake sosai, ure brave. nagode ma Allah da kika ci ubansa duk dama yanuna aiyana sonki who knows da nice hala dana fada cikin tarkonsa.

ushna tay dariya kadan tace "what?? haba big sis. Allah ya kiyaye ki fada cikin tarkonsa duk wani mai hnkli da tunani da wurwuri zai gane cewa gayen bbn mayaudari ne ..he is cute, bt he is bad news.

cikin kyabe baki arisha tace "well, i am not dat sure. kin tuna gayen danake ce miki zan aura??

ushna tace yess, the prince??

Arisha tace yess..he is already back home amma har ynxu kuma baizo nan garin ba gashi gaba daya yanxu na kasa samun wani nitsuwa azciyata ji nake kamar naje garinsu na jawoshi yazo ayi maganan aurenmu, he is damn cute, i love him since when i was this little. ive crush all over him, bana jin zan taba son wani namiji araina inba shi ba..

Cikin kyabe baki ushna tace wo*** u think he will feel the same??

da murmushi arisha tace ehh mana. i am sure of that. ke baki san royal matchmake yana da high chances of acceptance ba ne? kindai san tharim vale sune suke juya komi maybe untill they are ready zaizo dakansa nd i just cant wait to say yes to marrying him. kinga daga ranar kuwa kakanmu ta yanke saka we will all bounce back again

ushna dake kokawa da dogon sumanta tace "..ive neva been to that place

..kawai labarin su nakeji sama sama are they dat powerful nd rich...

Arisha tace "extremely, they are like the rothschilds of africa. they have their own private banks, millitary, so many lands, real estates,

agriculture, mining/mineral resouces, ga fin techs,.. for years... kinga kuwa suna da matsanacin power da kuma dukiya dan ance gaba daya yankunan nan akarkashin su yake..they have this long life nd prosperity.

ushna tace woww, i am happy for you sis inadai ba mayu bane?

atare suka kara fashewa da dariya..Arisha tace auko mayun ne ma i wll still

give my life to my yarima

dan duk duniya babu wnda nakeso kamar sa fatana dai Allah yasaka ya soni shima sosai sbd inbashi na aura ba zan iya mutuwa.

ushna ta rungumeta ahnkli tana murmushi tace in sha Allah zaiso ki big sis. yadda kika kula da su baba da masarautar nan ai ure a real defination of a future queen. babu wani yarima a duniya da bazaiso ya aureki ba koshi wayene.

Areesha ta dada rungumarta tana zuba murmushi tace thank you my little princess shiyasa nake sonki sosai. anyway., nazo na gaya miki ne cewa we are not allow go to shopping today dan dazu baba ya kira yace zai dawo anjima late in the evening kinsan idan yana nan baa fita koina inba da izininsa ba

kinga wadrob dinki is empty ba asaka miki kaya aciki ba sbd bamusan zaki dawo ba, you can take some of my clothes for now..i have plenty. inkinaso zaki iya dubawa kisa duk wanda ya miki kafin in baba ya dawo ya huta sai na karbi katinsa muje ki saya kaya.

cikin sanyin murya ushna tace thank you big sis

..i wll manage dis ones dama inaso nadan huta yau i have to attend to some files in my PC.

Areesha tace “its okay

nima akwai aikan baba da zanje na duba anan kusa bazan jima ba zan dawo.

nan da nan ta mika ma ushna fancy bag din ta bude tafara fiddo wasu hadaddun kaya masu tsada sosai aciki mostly pastel colours masu matukar kyau da daukar hankli kai zakace tsakani da Allah duk duniya babu wanda take mugun kauna aranta kamar ushna..

i think wannan zai miki kyau...tace tana mikawa ushna wani red colour flair skirt nd blouse.

ushna ta karba ahankli tana kallon kayan da murna...

Areesha ta saki murmushi sannan ta mike tace see u in abit sis, suna murmushi suka dan rungume junansu, daga haka ta juya ta fita daga dakin da dan sauri

saidai tana rufe kofar yanayin fuskarta gaba daya ya sauya da wani irin intense disgust tanamai cije labbanta ahankli.

can kasan numfashi tace " the clock is ticking, baba yana dawowa yau yau zaki bar gidan nan dan ban isa yariman tharim vale yazo yaga kyanki yace kece zai zaɓa ba nikuma na tashi a tutar babu, maganin bari karma afara dole ne kawai ki tattara kafafunki ki bar gidan nan..

bayan wasu yan lokuta Masarautar ya dauka da yanayin nutsuwa yayinda Areesha tafito bayan ta gama hadadden shirinta na fita zuwa yankin da ake rabon abinci da yarima ya aiko.

wani doguwar luxury black abaya ne ajikinta tai rolling veil dinsa mai matukar kyau hannunta sake da wata gold wrist watch dake kyalli taci uban kwalliya kamr ma itace matar sarkin yankin gaba daya.

tunda ta shiga babban motar gidansu personal driver nata ya nufi hanyar yankin kazurmi da ita

suna isa daga nesa tafara hangen yadda garin ya cika da jama’a saboda manyan trucks na abinci da kayan tallafi da aka aiko musu daga Prime Real Estate foundation karkashin umarnin sultan shamsan wazeeri.

kamar yadda ya musu alkwari da sasafe motocin abuncin suka taho mutane ne cike da farin ciki suna layi cikin tsari ana basu 5 good food bags each masu dauke da abinci irinsu shinkfa, masara cooking oil, flour, sai canned foods da irinsu cartoon na gishiri maggi, da omo.

komai na wajen yana tafiya cikin tsari ganan

manyan banners na Prime Royal Estate ne a manne da gefe da gefe yayin da workers din foundation ke ta zirga zirga cikin official uniforms suna kulawa da mutanen kauyukan nan da suka fito kowa yana zumudi...

motar Areesha na gama parking mutane da yawa suka juya suna kallonta saboda tsabar kyau da class din data shigo wajen dashi tana jan aji tana basarwa.

ta fito ahankli tana gyara black designer shades dinta cikin isa a ranta wani irin jin dadi takeji data iso akan lokaci dan ayi komi da ita. since she wll soon be yarima's wife yakamata ace ynxu anfara ganinta acikin lamaruka na rayuwarsa

yadda taga mutane suna murna suna masa addua yasaka tay murmushi tace

"perfect..talaka an samu na banza. waye kuwa zai iya deban dukiyarsa kamr baiso yana baku inba irin su yariman ba. well, this is exactly where i should be.

kai tsaye ta gyara zaman spec dinta snn ta nufi wajen wata mata mai dan shekaru amma cike take da authority ana kiranta

Mrs Hauwa Matazu.

ita ce overall shugaban distribution commitee a karkashin kamfanin charity foundations na yarima shamsan wazeeri.

sanye take cikin neat corporate suit nd hijab da ID card ajikinta yayinda take bada umarni cikin nutsuwa da tsantsar kwarewa.

Areesha ta karasa kusa da ita da dan murmushi irin na manyan mata da kasaita a muryanta tace "sannu da aiki mrs hauwa...mun gode da kokarin dakikeyi..

matar ta dago kai ta kalleta daga sama har kasa kafin na ta amsa atakaitace tace

yawwa.

sai ta shareta batace sake cewa komi ba

Areesha bata kula da cold response dintan ba ta dan yi murmushi kadan sannan tace

...honestly i just had to come down here personally after hearing what yarima arranged for the people...this is so thoughtful of him.

Mrs Hauwa ta gyada kai tanamai cigaba da duba clipboard dinta

Areesha ta kara matsowa kusa tanamai jin kanta sosai....nace ba??? bakwa tunanin rabon nan yadanyi yawaaa nasan yarima yana da soft heart musmn da yazo yaga talakawa suna wahala he really thinks deeply about these ppl but you guys shud have make ppl undertsnd the value of this things....kinsan talaka da son banza instead of 5 bags why not arage abasu 2 bags ai sun samu.

tana maganan ne tana dan murmusawa cikin wani salo mai nuna familiarity kmr itadin watace a rayuwar yariman.

still Mrs Hauwa bata wani kula ta ba sai ma daga kai datay tadan kalleta sosai can snn tace madam dan Allah kina aiki da companyn masarauta ne?

kai tsaye Areesha tace

oh no...family ce.

Mrs Hauwa ta hade gira sama tace "family ta ina kenan?

Areesha ta wani gyara tsayuwarta cikin barazana da nuna isa tace..“well...not exactly family yet...but..

cikin datsar numfashinta mrs hauwa ta hade rai snn tace malama dakata, idan ba aiki kikeyi da kamfani ba kuma ke ba official family dinsa bace meyasa kika tsaya anan kina hana mutane aiki? nd who told u we need ur unsolicited advices

take murmushin dake fuskr Areesha ya dan tsaya kusa da su wasu staffs ne suka tsaya suma suna kallonta.

cike da borin kunya arisha tace excuse me kinsan da wa kike magana kuwa?

Mrs Hauwa tawani shareta ta juya gaba daya tanamai cigaba da magana cikin baza authority ma workers batare tasan da wata banza awajen ba.

ran arisha ya mugun baci tace madam hauwa i am talking to u pls..

matar ta juyo da masifa da kuma karfi tanacewa "ke malama idan zakiyi distributing abinci ne toh ki tsaya acan ki taimaka idan kuma kallon aiki zakiyi toh ki matsa can gefe mutane suna jira.

wani irin kunya da bacin rai ne suka taru suka tokare zuciyar Areesha lokaci guda ta tsaya cak tana jin kmar an watsa mata ruwan sanyi a tsakiyar jama’a da suka juyo sunafa kallonta wasuma har sun ganeta wasu kuma basu santa ba

duk da haka ta wanye tareda daure fuskarta tana cewa i was only trying to support my ppl..

Mrs Hauwa tace okay mutane nan yunwa ce take damunsu saiki hanzarta ai kifara aikata abunda ya kawoki....

tana fadin hakan ta shareta anan ta kama hanya ta kara da gaba.

duk da cin mutunci da maganar banza da arisha tasha awajen distribution din abincin nan ko kadan hakan baisaka ta hakura ba.

haka ta cigaba da yawo tsakanin workers din tana cusa kanta kmar wata important figure acikin project din.

wani lokaci harda tsayawa tana karbar wasu food items tana mikawa mutane da hannunta saboda kawai a dauke hotonta itama ace tay kkri

maatsalar kawai shine da taga kusan babu wanda ya wani damu da ita duk dama wasu sunsan ita sarauniya ce

mutane gaba daya sunfi maida hankalinsu ne akan yawan kayan masarufi da yarima shamsan ya bayar

kowa na mamaki ana cewa Allah ya saka ma yarima da alheri. Allah ya kara mai daukaka

...gaskiya yarima ya iya taimakon jama’a.. wnn shine ake kira da aslin taimako ba adauki kwano daya na abinci ana bamu kamar kaji ko almajirai ba

duk inda ta juya wannan kalman kawai takeji yana yawo...

wani irin zafi ya tokare kirjinta har ta fara jin aranta cewa ashe dama tuntuni mutanen kauyukam nan ba gode ma taimakonta sukeyi ba.

sai can da aka fara rabon kudi ta sake matsawa kusa da Mrs Hauwa tace hajiya maybe i can help you coordinate the women section kinga ai...

Mrs Hauwa bata barta ta karasa maganar ba tace kina cikn financial staff ne?

Areesha ta dan tsaya batace komi ba.

da bacin rai matar tace dan Allah ki matsa gefe kudin nan bazai shiga hannun kowa ba sai staff dinmu sbd amane ce aka bamu

da bacin rai arisha tace kawaide kin kasa fahimtar cewa i was only trying to support ne because as a family..mutanen nan namu ne bazamu cucesu ba

mr hauwa tace kowa fa anan wajen family ne idan akan taimako ne amma wasu matan suna zuwane ayi aiki dasu dan kawai suyi posing ace suna da kokari, nafa san mtsayinki madam ke sarauniya ce anan yankin but u have to let us do our job pls.

wasu mata da suke kkrin kwashe food bags dinsu suka dan sace dariya.

wani irin haushi da borin kunya ya tokare Areesha lokaci guda.

daga nan tay zuciya taje gefe ta tsaya tana huci har zuwa yamma tana nan tana a tsaye kamar mayya amma gaba daya wajen babu wanda ya bata wani muhimmanci.

karshe ma datagaji ta koma motarta sai taji wasu staff mata suna gulmarta suna cewa

hmmm haka wasu matar fa suke dagaji ance yarima yay aika saisu dinga yawo ackin mutane kamar suna da wani alaqa dashi...yan neman gindin zama.

sosai ranta ya mugun baci tasaka aranta cewa daga zarar ta aure yarima sai ta walakanta mrs hauwa da wayann staff din da sukay gulmanta gabaki daya sai ta nuna musu matsayinta anan gaba

late evening ta dawo palace din mahaifinta da bacin rai saidai koda ta shigo main hallway nan taji kmr muryar mahaifinta na tashi daga private parlournsa.

take ta dan tsaya snnan ta dada gyara fuskarta da sauri within seconds ta komar dashi na sweet elegant princess din data saba nunawa agaban mutane.

tana shiga parlourn taga sarki murad ya na zaune cikin hadadden dark blue royal attire yana dan danna wyarsa cikin kasaita yayin da gimbiya amani noorain ke zaune kusa dashi suna magana kasa kasa

babu wani sallama Areesha ta shigo tareda da sakin wani beautiful smile mai cike da nuna farincikin ganin babanta

da shagwaba ta fada kasa agabansa tafara gaisheshi da tsantsar nutsuwa da ladabi shima yadan murmusa yanamai shafa kanta ahankli...“my princes kenan...Allah ya miki albarka

tana murmushi ta zauna kusa dashi nan da nan kuwa tafara bashi labarin activities dinta na ranan tareda nuna masa cewa tay taimako yau sosai

gimbiya amani dake gefe ta dan yi shiru kafin can tace ranka shi dade ushna ma fa ta dawo gidan nan jiya wani schll internship ne ya kawo ta nigeria.

sarki murad bai wani nuna interest dinsa sosai akai ba kawai yace "that’s fine..

xuciyar gimbiya amani ya dan yi nauyi da irin amsar da yabata sai batace komai ba ta mike tsaye ahnkli tana cewa toh bari naje na kirata taxo ta gaidaka nasan batasan ka dawo ba

basuce mata uffan ba har ta fita. nan da nan arisha tadawo gefensa tanamai cigaba da jawosa cikin mgangnu masu muhimmanci shikuma ya bada duka hanklinsa yanata sauraranta musmnan datake bashi labarin abubuwanda yariman tharim vale ya aiko dashi a yankunan kazurmi da kewaye

ata bangaren ushna kuwa zaune take akan gadonta tanakan gyara hannun dayan rigar da Areesha ta bata.

riga da skirt din data saka ajikinta sosai ya kara fitowa da soft curves din jikinta ya mata kyau sosai

koda gimbiya amani tazo dakin kiranta sai da taji gabanta ya dan fadi kadan saidai bata

yi kasa agwiwa ta mike tabi bayanta cikin yanayin nutsuwa.

suna shigowar falon gabanta ya fadi ganin sun hade idanu da mahaifinta da ya kare mata kallo bada sakin fuska sosai ba

gabanta na faduwa ta karaso dan har yanzu yanayinsa yana da wnn intimidating look din dayake tsoratar da ita tun tana karama.

ta karaso ahankli ta tsugunna agabansa cikin girmamawa tace

ina wuni baba..fatan ka dawo lafya

sarki murad ya daga idanunsa ya kalleta for some seconds kafin nan yace lafiya...ina fatan dai karatun kawai kikeyi ba wani matsala bane ya dawo dake gida

ushna ta hadiye wani gulluton abu dake makale a makoshinta cikin ladabi tace eh ba wani matsala bane

yadan gyada kai can ya kalleta yace tell me abt the internship

ushn ta bude baki kenan zata amsa sai caraf taji Areesha har ta cabe maganan da sauri tace laaa baba,

...ban baka labari ba

atake gimbiya amani ta dago kai da sauri tana kallon Areesha.

Areesha ta cigaba cikin nitsuwa tace

wai imagine, some creepy man waishi mr abdul a camp dinsu ushna, yakaita har cikin dakinsa da tsakar dare and he drugged her with his own tea sabda ruwa ya mata duka tay bacci akan gadonsa..hmmm, but thank God nothing serious happened, da wani abu ya faru da ita da bansan ya zaayi ba

atake fuskar ushna ya sauya ya dawo jaaaa ta tsaya cakk tanata kallon areesha da wani irin baqar mamaki

gimbiya amani tay shiru jin gabanta yana fadi da wani irin yanayi saboda tasan halin mijinta sarai

Areesha kuwa sai cigaba da zubo masa labari take kamar bata fahimci gravity din mganar datake fada ba.

she make it sound nd look like ai mr abdul din dan iska ne amma kuma saurayin ushna ne a schll din

sarki murad ya dago kansa ahankli yanata kallon ushna da wani irin cold expression.

saidai kafin yay magana wayarsa ta fara ringing cikin jan tsaki ya dauka ya saka a kunnensa yanamai sauraro can kafin nan ya mike yabar musu falon.

yana fita maza gimbiya amani ta mike da sauri tabi bayansa

ushna dake ganin duhu duhu nan ta mike tsaye a fusace idanunta sun cika da ruwan hawaye da sauri sauri ta kama hanyar ficewa zata koma dakinta

tafara tafiya kenan tana Allah Allah ta shige dakinta sai taji anwani jawota baya muryan arisha taji daga bayanta tana cewa ushna wait...

meya faru jikinki take wani ɓari????

kirjin ushna na bugawa dakarfi tajuyo a fusace dan batasan sanda ma tafara mata ihu cikin kuka ba

"why would you tell him that????

Areesha ta tsaya cak kamar bata fahimci komi ba."tell him what? i was only...

hawayen ushna na zuba sosai tace wann maganan tsakanina dake ne, nd you know exactly how he thinks about me...still kika budi baki kika gaya masa kuma kinsan ba gaskiyar kika fada

da wani irin fake panic attack Areesha ta dan matso kusa da ita cikin daburcewa tace whaat innalillh wa inna ilaihi rajiun,..no no little sis its not a big deal i swear...i was only looking out for you. a tunani na baba ai zaiyi wani abu akan mr abdl din nan he try rape u

da wani irin tsananin takaici da kuka ushna tace amma ai bata sigar haka kika gaya masa ba..you are nog looking out for me..you just got me into fresh trouble

take Areesha ta dafe kirjinta tawani fashe da kuka har jikinta na rawa rawa tace little“i didnt mean to hurt you

da ihu ushna tace mta just stop talking...bfr i kill you...

daganan ta juya da sauri ta shige dakinta tana kuka sosai

Areesha ta bita har bakin kofar tana cewa “ushna please open the door...innalillahi wa enna ilaihi rajiun i’m soo sorry little sis..

kuka takey daga nan kamar dagske amma cikin zuciyarta wani irin sanyi takeji dan tasan dolene babansu zai dauki mataki sosai

ta dan lumshe ido tana murmushin mugunta ahankli cikin ranta tace this will destroy you slowly gobe dai nasan dole zaki bar gidan nan.

dagata bangaren sultan shamsan wazeeri kuwa rayuwanshi ya kasancene a cikin hutu saidai in yagaji yaje dakin motsa jiki,yau kusan kwana biyu kenan da zuwansa kano amma babu inda yake takawa yaje face sashen iyayensa da kakansa da kuma masallaci.

Mahaifyarsa kuwa kullum itace take kawo masa abincin datake dafa masa dakanta domin yaci.

Inda haryau itama bata zauna tay wani nisan hira tare dashi ba saboda tsantsar kiyaye dokan mahaifinshi dayace a kyaleshi ya dan huta kafin nan ya koma lagos

ita kanta tasan samun isashen hutu yana da matukar muhimmanci ga shamsan ayanxu musmn in tay la'akari da tarin ayyuka da kuma responsibity dake jibge a gabansa yana jiranshi son samu ne ya dan huta din,snn ya warware gajiyar jikinshi duka kafin ya soma daukan duk wata nauyi dake rataye a wuyansa anan gaba.

dukkan wani gata da tarairaya da kulawa,da kuma girke girke masu dadi da armashi shita dinga mashi a iya wayann kwanakin don kawai yasamu cikakken nitsuwa ajikinshi.

******gimbiya amani noorain tana tsaye cikin zullumi har mai martaba yagama amsa wayarsa

yana sauke wayar akunnensa Cikin tsananin bacin rai ya tsaya daga inda yake yana kallonta da jajeyn idanunsa masu cike da takaici.

zatay magana cikin katseta yace“...Ke yanzu wannan shine irin tarbiyyar da ushna take rayuwa dashi?

shaye shaye da shiga dakin namiji? saura kuma afara kawo gulmanta da irin wnan maganan acikin garin nan sai mutunci na kuma ya zuba

gimbiya amani noorain dake tsaye gabansa jikinta duk yay sanyi cikin tashin hankali tace ranka shi dade ba haka bane...maganar bata kai haka ba am sure ushna has her own explanations dan Allah kayi hakuri kbata dama tay mana bayani da bakinta bawai dan arisha ta ari bakinta tafada maka gatsau kawai saimu dauki mataki ba.

da hannu ya dakatar da ita cikin kakkausar murya yace “enough amani karki maida ni mutumin banza mana arishan ba dadarta bane zata cutar da ita ne? ai tun farko dama na fada miki wannan yawan samun waje da sangarta da akeson nuna wa yarinyar nan shine zai lalata ta toh yanzu ba gashi nan ba tana rayuwa babu kunya babu tsari.

numfashin gimbiya amani ya tsaya cak jin yadda yake magana akan ushna da tsauri kmar ba yar cikinsa ba.

da sanyin murya tace mai martaba don Allah nide ka saurare ni muyi magana karka yanke wani hukunci batare da munji bakin ushna ba dacan in ita yarinya ce yanxu ai ta girma

cikin katseta da wani irin kallon takaici yace banda wann lokcin, ni zan fita, naji ance wai yariman tharim vale yariga yabada umarnin aikin tituna akauyukan garin nan batare da an nemi izinina ba zanje wajen aikin da akace anayi idan na dawo zan san irin hukunci da zan dauka akanta

yana gama fadin haka yafita daga dakin yanayinsa cike da iko.

gimbiya amani ta tsaya cak jikinta yayi mugun sanyi gaba daya

tsillin hawaye suka gangaro mata ahankli tashare tana jin zciyarta na tashi da wani irin fargaba dan batasan mezai yi wa ushna idan ya dawo ba

ta jima tsaye kafin daga bisani ta juya ahankli ta fito daga sashensa tana tafiya ahankli cikin nazarin abunda zatayi

tahau kan hallway kenan sai taga arisha tana tahowa daga bangaren ushna cikin wani irin takun kasaita kamar babu abunda ke damunta aranta

atake fuskar gimbiya amani ta sauya tun bata karaso ba tace “Arisha..come here immidietly.

da sauri tace yes mummy.

gimbiya amani ta kasa hakuri bata jira arishan ta karaso ba ta daga kafa da sauri ita ta taho gab da ita lkcin idanunta sunyi jajur

wani irin daure fuske tay tace...meyasa kika furta irin wann kalamn agaban mahaifinki?

arisha ta kwalo ido da salon rashin fahimta cikin nitsuwa tace wane magana kuma mummy?ohhhh is it abt ushna,.toh what is wrong dan nagaya ma baba halin da ushna take ciki da maza

da tsananin bacin rai tace “you didnt see what is wrong?

arisha ta matso kurkusa tana kifi kifi da ido kamr ma batasan metayi ba ahnkli tace yes mumy, i was only trying to explain to him what happened...

a bazata taji mhifiyrtan ta fixgota tare da sakar mata wani irin shaharn mari mai masifar karfi wanda saida ta kifar da ita kasa dashi

arikice arisha ta dago tana kallon mamarta in shock bakinta dake bude yana fidda jini

jikin gimbiya amani har ɓari yake numfashinta yana fita da karfi ta nuna ta da yatsa tacee you think this is a joke?

arisha ta yaya zaki tsaya agaban mhaifinki kina fadar irin wanann magana akan kanwarki alhalin kece kikafi kowa sanin yadda yake daukarta aransa?yarinyar nan jiya tazo gidan nan tana kuka she was trying to settle down after everything daya sameta amma kika runtse idonki agaban ta kikara jefa ta cikin wani matsala..did you even care abt her at all?

a mugun rikice idanun arishan suka ciko da hawaye muryanta na rawa rawa tana kuka ta sunkuyar da kanta kasa cikin rawar murya tace im really sorry mummy...dan Allah kiyi hakuri ni wallh bansan abun zai bata muku rai nafada ne sbd baba ya taimaka mata...what is wrong with that?

da wani irin bacin rai

gimbiya amani tace

dan Allah ki kyaleni nide banason jin wani magana daga gareki kuma duk abunda yas ame ushna agidan nan i swear to u zan dauki mummunn mataki akanki..yadda kika furta wnn magnn agabansa kisan yadda zakiy kije gabansan ki wanketa tasss if not don't expect me to talk to u any sooner. ai kin girma kinsan abunda kikeyi sarai...

tana fadin hakan ta wuce hanyar sashenta da sauri....

Arisha dake kasa tana hawaye hannunta dafe da kuncinta ta juya tana kallonta da wani irin harara mai zafi

#SURAYYAHMS

***

TALES OF THE WAZEERIS

2026