TALES OF THE WAZEERIS

way to lagos

by @surayyahms

31...🦋🦋🦋

SURAYYAHMS

TALES OF THE WAZEERIS...

raunataccen kuka mai cike da tsantsan ruwan makirci sarauniya areesha takeyi ayayinda take bibiyar bayan mahaifyartan da wani kalar zazfr harara har saida taga ta lume cikin chambarta kafin nan tamiqe tsaye ta share hawayenta tareda jan wata arniyar tsaki aranta tana cewa babu yadda kuka iya dani dan dole ne ushna ta bar gidan nan gobe gobe bazan kuma bari tadawo ba har saina auri yarima...

abune datajima tanaji aranta cewa inhar ushna tana gidan bazaiyu azabeta a matsayin perfect cndidate na yarima ba sbd komi a fili yake, ushna tafita kyau da yanayin kasaita da kuma jinin mulki nesa ba kusa ba garadai in azo asamu ita dayace ƴa mace agidan.

A bangaren ushna kuwa tunda ta shige cikin dakinta tarufe kofa da karfi tareda jingina bayanta jikin kofar nawasu sakanni bata dena zubda ruwan hawaye tana sauke zzfar numfashinta dake fitowa da kyar ba dan sosai abun nan yaci mata rai sbd ko kadan batayi tsammanin arisha zatayi mata haka ba

gabanta ne ke wani irin bugawa cikin tsananin bacin rai da kuma takaici.

dan har yanzu muryar Areeshan ce ke yawo acikin kunnuwanta...

yadda ta kasance soo nice nd neutral sukayi hiransu na yan uwantaka acikin wasa da dariya snn ta tbbatar mata cewa bazata taɓa bari maganan mr abdul yafita waje ba..

ur secrets are safe with me....

ranta kara baci yakeyi inta tuna wann words din tareda irin innocence din da arisha tazuba ayayinda take kan fallasa maganar agaban babansu kmr bata san abunda takeyi ba

wani irin murmushi mai ciwone ya kubce mata slowly tashare hawayenta snn tabar bakin kofar ta taho tazauna akan gadonta ahnkli tareda sanyin jiki ayayinda idanunta suka kara cikowa da kwalla.

for the first time in years sai tafaji kamar ba zata kara iya yarda da addarta Areesha ba.

bakuma waidan saboda yau ta fallasa maganar mr abdl agaban babansu ba

kawaide sigar da ta fada din ne yafi ɓata mata rai tareda bata mamaki nd yet arisha is still pretending innocent kamar batama gane halin data jefata aciki ba.

ahankli ta dafe saman goshinta jin xafafan hawaye suna gangaro mata. sai ynxu ta fara fahintar abunda xiyada ta gaya mata na batun riqe wasu information din a zuciyarka kai kadai..bt if not for that phone call tasan da har abada dai bazata gaya ma arisha komi ba..cikin ranta tace amma babu damuwa, anyi nafarko anyi na karshe kenan sosai ta dauki babban darasi.

tadade ahaka tana kallon wani empty space dake gabanta cikin zuciyarta na dada rikicewa dan duk wani tunanin da zatayi arnta sai taji takasa gane asalin real intentions din addarta arisha....

tasan dai a matsayinta na babba she will dfntly mean no harm amma kuma tasani har abada arisha bazata iya fahimtar wanann murdadden alaqar tsana dake tsakaninta da mahaifinta ba.

da yuwar tayi tunanin cewa babansun zai iya taimakonta ne shiyasa harma ta gaya masa ita kuma tasan hakan bazai taba yuwa ata bangaren mahaifinsu ba. this must all be a huge misundstandings amma duk da haka aranta tajani gara dai kwata kwata tadena gaya ma arishan komi dan hakan ne kawai zaifi musu sauki gabaki daya.

saida tay nisan tunani akan lamarin snn taji ranta yay sanyi.

slowly tadaga hannunta ta share hawayenta sannan ta mike tsaye acikin nitsuwa

kai tsaye bathroom ta nufa ta cire kayan jikinta kafin nan takunna warm shower sannan ta tsaya karkashin ruwan idanunta alumshe.

ruwan dumin na sauka akan flawless skin dinta yayin da take kokarin controlling numfashinta for some minutes bata motsa ba harsaida duk wani nauyin dake kirjinta ya ragu daga bisani ta kashe shower din ta fito ta dauki white towels ta daura, daya kuma tafara goge jikinta dashi snn ta fito ta tsaya gaban mirror tana kallon reflection dinta cikin zurfin tunani.

she have been feeling nd surviving alone all her life, gani take babu wani sauran tsoro ko fargaba acikin ranta ynxu dan haka kawai gara tabar gidan nan tafara maida dukkan hnklinta akan abunda ya kawota kasar nan dan tasamu tagama program dinta a cikin nasara har ta koma dubai akan lkci, in Allah ya bata nasara tasan zata samu hanyar tsayawa da kafarta na har abada basai tasha takaici da walaknci anan gidan nan gaba ba ..

cikin raya wnn tunanin ta sauke ajiyar zuciya tace“i really need to take control of my life...

dan masarautar nan bai tabo zamowa safe space agareta ba ta lura kmr duk lkcin datake gida ba'a samun zaman lfya bare nitsuwa komi dayashafe ta yakan zame musu tamkar matsalane

ahnkli tajawo cream inta ta shafashi lighly ajikinta snn ta saka wani soft pyjamas maikyau datazo dashi cikin nitsuwa tagama yan shafe shafenta bayan ta gama ne tajawo apple laptop dinta ta zauna akan gadon tana gyara pillow bisa bayanta sannan ta kunna system din blue light din screen din ya haskaka kyakkyawar fuskrta yayin da dakin yayi shiru gaba daya.

kai tsaye ta bude browser tafara searching inda zatay special royal IT inta cikin nutsuwa gashi ba abu me sauki bane cos she need to find some Top real estate firms accepting internship in Nigeria...

garin abuja ta fara dubawa a karo nafarko tafara leka cikin manyan firms kala kala and some few real estate luxury development companies da commercial property groups ko urban housing firms haka da suka dace da requirement inta

tafi awa tana dubawa saidai mafi yawancin su internship dinsu ya riga ya cika ko taga requirements dinsu sunyi qasa dayawa tasan koda tay applying she wll just waste her time nd limit her chances na samun aiki a dubai.

ahaka dai ta cigaba da searching ta duba port Harcourt, Kaduna,kai harda Zamfara, katsina, duk dai inda taga akwai opening sai ta bude front page dinsu ta tsaya ta karance tsaf cikin nutsuwa, kowanne kamfani saida tayi analyzing dinsa daya bayan daya saidai duk professionalism dinsu are kind of below international standard wasu kuma dokoki ne bazata iya ba

tafi awa uku kafin nan ta dawo da dubanta lagos anan kam ta samu wajaje hadaddu da uban yawa amma babu wanda ya dauki hankalinta har saida ta biya kudi tabude wani encrypted paid article da yake magana akan top real estate corporations in africa.

tana lekawa atake kuwa idonta yasauka akan PRIME REAL ESTATE GROUP. kai tsaye ta bude exclusive company profile dinsu tafara bita kai within som minutes saigashi tay firgit ta mike zaune daga kwancen da take tanamai kara matsowa da laptop dinta kurkusa

gabaki daya tabi ta bada hanklinta akai cos the deeper she read the more familiar everything looked.

ga clear hotonan project dinsu ga komi da komi anan tagama kallon luxury developments,international properties,royal investment holdings da middle east partnerships.

tana ganin dubai affiliations taji kirjinta yawani irin bugawa da sauri sauri dan batasan sanda wani kalar murmushin farinciki ya kwace mata ba,... da sauri ta bude next article din sai taga ashe ma wanannn kamfanin is officially partnered with Royal Gulf na Dubai wato kamfanin da suka turota wnnan progrm din

tsabar dadi dataji harji take kamar an kwashe mata shirgin takaici da matsalolin dake cin zuciyarta ne atake

tana sakin wani irin sanyin murmushi tace Alhamdullh.

nan wani irin tunani ya fara yawo acikin kanta cikin kakalo ma kanta nitsuwa ta cigaba da karantawa.

Prime real Estate group is one of the biggest real estate corporations in africa babban headquarters dinsu na Lagos.

bisaga online reviews na manyan investors tagane cewa wajen is extremely secured,highly competitive and strictly professional snn kusan duk executives dinsu international experts ne.

infact acikin articles din har an rubuta cewa companyn bata taɓa daukan interns ba saboda nature na aikin wajen da irin confidential projects din da suke dauka

ahnkli ushna ta dan cije lips dinta sanin cewa wnn wjen ba irin companyn da yara yara ko beginners irinta ke samun shiga bane is a whole empire on its own.

saidai Allah ya zuba mata taurin kai ko kadan sai bataji ta tsorata da komi ba cikin lumshe ido da budewa takara scrolling but the more she read about the company the more interest dinta ke karuwa akai sbd shikadai ne anan africa da yake da alaka da program din datakeyi a dubai, wanda tasan inhar ta samu shiga toh babu shakka babban burinta na tsayawa da kafafunta arayuwar nan acikin sauki zaicika nan bada jimawa ba

musmmn ma dataga yadda komai nasu yake nan soo organized ga wani irin elite standards kai kanka dole kaji ka zaƙu kagakanka acikin wann uban power, da structure da kuma intense control dake wajen

daga farko har karshe ta karance komi da komi gameda kamfanin dan saida ma taiyta biyan few dollars dinta online kafin wasu information dinsun ya budu mata fully tasamu har take karantawa ynxu.

har wajajen karfe daya da rabi na dare ushna na zaune tadan jingina bayanta jikin gadon tana kallon screen din cikin zurfin tunani

for some strange reason tafara ji ajikinta kamar wajen nan ne kadai zai iya bata babban opportunity datake nema a rayuwa.

matsalar daya ne dataga alama kamar Prime Real Estate group ba fa irin wajen da mutum zai iya shiga haka kawai bane especially ita da bata gama degree dinta ba tukuna.

da gigin bacci a idonta tarufe laptop din agjiye tanamai sauke ajiyar zuciya dan tasan ko da bala'i da tashin hankali sai ta nemi duk yadda zatayi ta cusa kanta anan, dakyar ta idar da adduar bacci wanda bada jimawa ba ma baccin yay awon gaba da ita.

washe gari da safe daga masarautar kano kuwa tun bayan sallar asubahi yau gaba daya palace din nasu ya dauki yanayin nutsuwa da tsantsar shiru..

bayi, gurds da palace servants na zirga zirga cikin uniform dinsu kowa ya dukufa akan abunda ke gabansa ayayin da securities suke sintiri acikin compounds din cikin nutsuwa.

daga private chamber sultan shamsan ne zaune acikin private living room dinsa sanye da plain simple royal jallabiya navy blue colour mai matukar tsada

hadadden hannunsa dayaji gyara yana rike da tablet ayayinda yake reviewing wasu reports na projects dinsa acikin nutsuwa.

duk dama ynxu hutu yakeyi amma har ila yau bai iya aje wasu responsibilities din da suke bibiyarsa ba.

sabida yanayin cold nd hot tempersa yasaka ba lallai kaga servants dinsa suna wulgawa a inda yake ba...

shi mutum ne daya fiye bukatar shiru kuma baida abokin wasa ba, he is eida ignoring u or thrashing u with a single look..

inka takura masa kuma anan ne zaga gane cewa yana da tsananin zafin zuciya

yajima anan azaune shikadansa yanata danne danne for few moments later wani respected hadimi ya nemi ixinin shigowa palon cikin girmmawa ya rusuna ya gaidashi kafin nan yace..

ranka ya dade hajiya nana ne takeson ganinka..

kallo daya baiyi ma mutumin ba bare yace masa komi ahaka har yagaji da tsugune snn ya tashi ya fita afalon cikin sassarfa.

abunda yake gabansa kawai ya cigaba dayi da alama baima saka ran zai tashi ba bare yaje wani amsa kira

sai can kusan bayan mintina talatin sai ga nan tsohuwar ta shigo cikin sashen dakanta cikin nutsuwa.

cikin daraja kai take tafiya ahnkli jikinta sanye da dogon hijabi da yay mata kyau ga wann hasken fatar nata namanyan mutane na haskawa

saida yaji dattijuwr sallamarta a kofa snn ya dago kansa cikin girmamawa ya kura mata ido yana kallonta daga nesa harsaida ta karaso kurkusa dashi kafin nan yaji aransa zai iya daurewa ya kulata...

baice mata uffan ba har saida ta nemi waje ta zauna snn ta masa sallama ahnkli ya amsata muryansa kasa kasa

kai tsaye takira sunan sa cikin murya mai cike da nutsuwa snn tace rankashi dade naji wai zaka koma lagos anjima ko.

batare da ya kalleta ba yagyada kai ahnkli yace yes, grand mother...

ta dade tana kallonsa kafin nan ta sauke ajiyan zuciya cikin taushin murya tace

toh kafin ka tafi ina sone muje tareda kai wajen yaran nan marayu na foundation din kakanka shugaba khaleefa daya gina maka shekaru dayawa da suka wuce.

shiru yayi yana sauraronta cikin nutsuwa amma zaka iya rantsewa hnklinsa ba akanta yake ba

ahnkli ta cigaba da cewa duk wannan tarin dukiyar da Allah ya baka amanah ce dan mutum baya iya kai guzurin komai cikin kabarinsa sai kyaun halinsa da kuma addu’ar mutane...

kakanka khaleefa Allah ya jikansa da rahma,ya kasance mutum ne mai tsananin taimakon jama’a. akwai wasu yan kauyukan da har yau suna rayuwa ne saboda abubuwan daya gina musu tun kafin a haifeka.

wann kalaman data furtan shine kawai yasakashi har yadago kwayar idanunsa sama kadan ya zuba anata yanamai sauraronta cikin nutsuwa ba tare daya katseta ba

tausayi yaji ta bashi ganin yadda kwayar idanunta yacika da ruwan hawaye da basu sauko qasa ba tukuna

...even after so many years da akwai alama cewa har yau tanajin kewa da kuma mugun zafin mutuwar mijinta shugaba khaleefa..

shikansa haryau bai manta ba dacan daya ke karami yana yawan gaya musu cewa duk wani dukiyar da bazata anfani talaka ba tana iya zama fitina akan mai ita.

kallon kakarsa nana hafsa yakeyi ayayinda tagama shanye raunattun hawayenta cikin dauriya ta dan murmusa ahankli tace

sometimes i fear this generation has already started seeing wealth as power alone. kuma kai kasani cewa wealth without Allah's rahma becomes arrogance.

still baice mata uffan ba, yanayin idanunsa ne kadai ya dan sauya da tausayinta dayake dannewa taciki

abazata yaji tadan shafa laushin saman hannunsa ahankli tace nasan da cewa you are carrying too much rsponsibility already, amma kada ka manta da mutane marasa karfi,..will you pls grant my wish?...namaka alkwari bazamu jima ba.

hannunshi ya janye anata ahnkli muryansa kasa kasa yace okay...

da murmushi ta miqe tana gyada kai dan tasan bazai fadi wani kalma daya wuce haka ba.

tace toh sai naganka

baice komi ba har saida ta fice a sashen snn ya miƙe kai tsaye ya haura sama zuwa private room dinsa dan ya karasa kintsa kansa atsanake dan ya samu ya fito akan lkci, dan ya tsani yin wani abu da baya cikin schedules dinsa, badonma yana kallon grand ma din nasa da tsananin so da daraja ba da hala bazai taɓa iya zuwa koina ba saidai yayi aike.

he is a man of strict principle kusan komi na rayuwarsa a tsare take baya negotiating lokacinsa akan kowa

yana shigewa dakinsa ya samu har angama shirya masa ruwan wankansa da komi da komi dayake bukata a tsanake. wayarsa ya dauka ya tura sako wa pilot maza aka sauya time na flight din dazai kaisa lagos zuwa can da yamma..

daga nan wanka yafada bayan kamr mintina 25 ya fito, fresh healthy skin dinsa tana wani irin xuba sheqi ayayinda gabaki daya dakin ta dauka da wani irin azababben qamshi na tsadaddun sabulan dayay wanka dasu.

atsanake yayi yan shafe shafensa ya shirya kansa tsaf cikin kankanin lokaci kuwa ya gama yin kominsa acikin nitsuwa.

baqaqen motoci kirar lexus 800mph masu tsananin security aka shirya musu awaje da securities wanda zasu rakasu har can gidan marayun.

karfe 10am na bugawa sultan shamsan waxiri ya fito sarari yasaka wata perfectly tailored matte black fitted shirt wanda sleeves dinsa is folded slightly at the wrist showing part of his expensive patek philip watch. maturely yayi tucking in rigarsa into dark charcoal trousers sai ya daura wata long ash colour overcoat da tsayinsa ya tsaya dede knees dinsa da black italian leather shoes dinsa masu matukar kyau da nuna tsafta.

private qurds dinsa ne abayansa suna rufa masa baya har ya karaso harabar waje cikin sanyin kasaita yana takawa ahankli hadadden coat dinsa is moving slowly bhind him giving him that craxy royal aura...

qamshin limited turarensa na Sovereign XIII da ake masa shi na musmmn daga middle east ya cika iska da dadin qamshinsa

tun bai karasa zama cikin motar da zai wuce dasu ba saiga nan kakansa ta fito itama sanye da wani neutral coloured lafaya me tsananin kyau da tsada amma baida hayaniya ko kadan

daga ita sai kuyanginta da kuma katon jakarta data riko kai tsaye aka bude mata motar dake bayan nasa ta shige ciki

nan aka fara jansu har zuwa orphanage din dake daya daga cikin anguwani da yake dan nesa da su wanda tun kafin su iso wajen an riga shaƙe koina da security da staffs.

babban building ne da akay tsarinsa kamar boarding school ga hostel, ganan class rooms da sick bay da refectory gidan sama ne maihawa uku saidai kuma an zagayesa ne da babban katanga sbd tsaro.

yara yara marayu da nakasashu from age 0 to 17 sune kawai ake rainonsu anan gidan daga zarar ka kai 18yrz za'a turaka karatu ko a baka wani sana'a me karfi da zai isheka kayi rayuwarka tanan gaba.

yan matan kuma ana kulawa dasu ne har iya lkcin da Allah zai basu miji suyi aure.

convoy na baqaqen motocinsu suna tsayawa wajen ya cika da hayaniyar workers da kuma yara, sultan shamsan wazeeri bai wani ciki son yawan magana da mutane ba amma presence dinsa kadai yasaka wajen ya kara rikicewa da dmbin murna dan kowa yana sone ya gansa sbd duk abunda ake musu da sunanshi da dukiyarsa ne wanda shikansa bai gama sanin yawan dukiya da uban gatan da kakarsa shugaba khaleefa ya bar masa kafin ya rasu ba.

tun da ya sauko kasa bai daga idonsa sama ba yana tahowa ne agefen kakansa with dis calm authority ayayinda manyan officials na wajen ke binsa abayansa cikin nutsuwa

duk inda suka wuce mutane sai miko musu gaisuwa suke cikin girmamawa.

bayan sun zaga ko ina kafin nan aka barsu da yaran orphanage din kowa yafara tahowa suna kallonsa cike da murna

duk dama bai iya nuna emotions dinsa a fili ba amma zuciyarsa sosai tay taushi ya tsaya yana sauraran yaran with composed expression

wasu yaran suna fadin abubuwa masu ratsa zuciya wasu suna da abun dariya...

sun kuwa shirya masa abubuwan nishadi da yawa kmr su sweets, sweaters, caps, t shirt, flowers, arts, drawings daga cikin skills da ake koya musu anan.

can wata yarinya yar karama blck beauty mai suna surayya ta karaso gabansa ahankli.

sanye take cikin simple flower dress idanunta cike da wani irin pure innocence hannunta na dauke da wata yar karamar mage irin pure white cat din nan masu blue eyes

security har sun matso zasu dakatar da ita dan sunsan doka ne shida kansa baya karban komi a hannun strangers.

da ido ya dakatar dasu

yarinyar ta karaso har gabansa tana baza murmush sannan ta daga cat din sama ta mika masa tace...this is for you sir....her name is husna.

sultan shamsan ya sauke idanunsa kasa ya kalle yarinyar snn ya kalli cat din slowly sai ya mika hannu ya karbi cikin nutsuwa..

ya shafa kan yarinyar lovingly batare da ya furta uffan ba yarinyar tafara murmushi sosai da alaman taji dadi..

kakarsa dake gefensa itama tayi murmushi ahankli tana kallonsa

sometimes the purest gifts come frm people who have nothing...

bai mikawa kowa cat din ba kuwa ya riketa dakansa harsaida suka gama abunda zasuyi a gidan marayu ya kara musu signing din welfare donations yayima yaran sallama daga karshe snn suka tafi..

ata fannin ushna kuwa washe gari da safe kusan wayar kawarta xiyada ne ya farkar da ita da gigin bacci a idonta ta lalumi wayar tasaka akunnenta da kyar ta kwace baccin a idonta snn suka fara magana saidai tsabar tanaji kamar bata ydda da kowa ba yasaka bata iya sanar da ziyada komi da komi daya faru da ita ba

she just brief her sama sama akan komi data gano akan kamfanin prime real estate lagos, ziyada tana kan zugata akan taje ta gwada sa'arta awajen kenan suna cikin magana sai taji heavy knock a bakin kofarta, tace come in. wata palace servant ne ta shigo tace mata ana nemanta a falon mahaifinta

gabanta taji ya fadi da sauri tay excusing din ziyada snn tasauko kasa agurguje ta nufi bathrom ta kimtsa kanta snn tasaka dogon hijabi ta bude kofarta ahnkli ta fara tahowa dayan sashen with each step sai taji gabanta na masifar tsinkewa...

cikin tsananin faduwar gaba ushna ta karaso har private royal parlon mahaifinta tanata kokarin controlling numfashinta kafin daga bisani ta daga hannunta ahankli ta tura kofar fargaba ya gana cike mata zuciya

atake wani irin sanyin AC yabugi rikitaccen fuskarta fararen kwayar idanunta suka sauka akan sarki murad dake zaune cikin royal dark attire dinsa data masa kyau yana dubawasu yan takardu ahankli

ummu hareera ke zaune gefe daya tana sipping herbal tea a daya bangaren kuma gimbiya amani noorain ce zaune cikin nutsuwa saidai yanayin fuskarta ya nuna sarai cewa itama bata wani samu sukuni arantaba

akaro na farko kenan dataga babu alamar Areesha acikin falon

atake kirjin ushna ya kara bugawa da karfi cikin nutsuwa ta karaso tsakiyar falon sannan ta tsugunna kasa cikin ladabi ta fara gaishesu daya bayan daya

mahaifiyarta da ummu hareera ne kadai suka amsa mata da sakin fuska cikin katsesu sarki murad yay gyaran murya ya dago mnyan idanunsa ya kalleta na wasu dakiku ba tare da yace komi ba

wajen gaba daya ya dauki wani irin nauyi da shiruuu kafin daga bisani ya dan gyara zamansa ya sauke wayarsa agefensa

cikin muryarsa mai cike da kwarjini yace ..ke yaushe ne zaki tafi?

ushna ta hadiye wani abu dake makale a makoshinta muryanta na dan rawa rawa cikin nutsuwa tace yau.. yau ne baba...dama akwai wajen placement ina da zan je..

kafin ta karasa karyan yace a ina kenan?snn wa zai kula dake acan...ko zaman kanki kikeyi..

ushna ta dan yi shiru na wasu seconds kafin nan tace “a lagos ne baba. dama an turo ni ne nay wasu yan watanni zanyi aiki ne akrkshin wani kamfani sune zasu kula da komi

bai amsa ta ba saida ya jingina bayansa da kujera yana kallonta da idanunsa masu tsauri lokaci guda taji cikinta ya tsure har tadauka ko harya gano karyan datayin ne ynxu dan harga Allah itama batasan meyasa ta kirkiro wnn uban karyan ba, she have neva been to lagos..snn bata da tabbacin cewa intaje can za'a kulata ko a karbeta a kamfanin nan.

kawai maganan ya kwace mata ne batare da ta shirya masa ba

can cikin wata cold voice sarki murad yace “tunda yanzu ke kin girma kina ganin kin isa kiyi duk abunda ranki yakeso sbd ana goya miki baya, ni bazan hanaki aikin ba duk inda zaki je kije kiyi duk abunda kika ga dama amma wannan shine warning dina na karshe. bana son sake jin wani magana na zubar da mutunci daga gareki dan kuwa ranar dana sake jin wani abu makamancin wannan danaji jiya akanki toh wallahi aure zan miki da duk wanda naga dama dan ba ke kadai Allah ya bani ba ina da ƴata me nutsuwa wcce tafiki anfani.

wani irin abu mai zafi taji ya tokare zuciyarta kwayar idanunta suka cika da kwalla batare da daga kai ta kalleshi ba ta kara sunkuyar da kanta can kasa cikin rawar murya tace..i really am sorry baba in sha Allah bazanyi wani kuskure ba.

hannu ya daga mata da alaman ta tashi ta bashi waje..

daga haka ta mike ahnkli cikin sanyin jiki ta fita daga cikin falon batare datasake jin sha'awar juyowa ba

ahnkli take tafiya ga wani irin dumbin tsoro da fargaba daya gama lullumeta taciki na snin cewa dolenta ne ta tattara inata inata yanxun nan ta wuce garin lagos ta kuma tabbata tasamu wajen aikin akan lkci tunma kafin babanta yagane cewa karya kawai ta masa..

#SURAYYAHMS

AYI COMENTS AYI SHARE SABIDA ASAMU POST GOBE DA JIBI

TALES OF THE WAZEERIS.....

2026

SURAYYAHMS

***