Ɗanɗano Book 2
by @legendspen
Cikin sanyin Ac da ke ratsa ɗakin, ina zaune a kan kujera mai laushi, na takure waje guda ina kallon dukkan motsinsa. Hasken daƙin ya kasance mai sanyaya idanu, wanda ya ƙara wa fuskarsa wani irin kyau da kwarjini na daban.
Yana tsaye a tsakiyar ɗakin, riƙe da remote ɗin Ac a hannunsa tamkar abun magana na makirofon, yana bin sautin waƙar da ke tashi a hankali. Idanunsa suna kaina, cike da wani irin murmushi mai taɓa zuciya, yana girgiza jikinsa kaɗan-kaɗan cikin ƙwarewa da kazar-kazar.
Muryarsa tana fita a hankali, yana haɗa ido da ni yayin da yake rera waƙar.
“In dai akan ki ne na yi nisa dan ba kiran da zan amsa.”
Wani irin daɗi na ji ya mamaye mini dukkan jikina. Na lumshe idona ina jin yadda kalmar “na yi nisa” take ratsa kowacce jijiya ta jikina.
Ina buɗe idona, na ga yana takowa zuwa inda nake, har yanzu idanunsa suna narke a cikin nawa, muryarsa tana daɗa zurfi.
“Tilas ganin mu tilas barin mu ƙaunarki tun da nai nisa.”
Wani gajeren kallo na jefa masa, wanda na san ya isa ya gaya masa dukkan abinda da ke ɓoye a raina na soyayyarsa. Na gyara zama, ina jin yadda shauƙin soyayya yake neman huda kowane sashi na jikina. Kalamomin da yake faɗa na kowanne baiti ba a iya baitin waƙa nake jin su ba, jin su nake tamkar suna bin jinina ne suna zazzaga a cikin zuciyata.
Murmushi ya suɓuce mini, na kasa ɓoye farin cikin da yake shirin fito mini da hawayen daɗi. Shi ma ganin murmushina, sai ya fashe da wata daddaɗar dariya wacca ta bayyana kyakkyawan hakoransa, ya miƙa mini hannu tamkar yana roko na na karɓe shi.
Yana daɗa matsowa kusa da ni, har ina iya jiyo hucin numfashinsa, ya tsaya daidai gabana sannan ya cike baiti na gaba cikin wani irin salon mai ratsa zuciya.
“Sam ba batun na fasa ko za a ce mini in ba da rai fansa.”
A lokacin da ya fadi kalmar “Rai fansa”, sai na ji wani irin shock ya ratsa ɗaukacin gangar jikina. Nima na fashe da dariyar. A daren nan, babu abin da zuciyata take gani sai shi, babu abin da nake ji sai kalaman sa, na sake tabbatar wa kaina cewa, babu wani abu a duniya da zai iya raba ni da shi na har abada.
*********
Dum! Haka na ji zubar sassanyan ruwan a jikina, ban kai ga gama tantance ko mene ba, na ji an ɗauke ni da wani azababben mari, da sauri na riƙe kuncina tare da ƙwalla uwar ƙara.
"Ahhhhhhhhhhhhh."
Idanuna har wani dishi dishi suke, amma haka na iya ganesu yana tsaye kiƙam, ita kuma ta dafa kafaɗarsa, hannunta riƙe da jug da alama ita ce mai watsa ruwan sanyin, shi kuma ya ɗaure fuska. ‘wai ni ce yau Sardauna yake mari wannan wace irin rayuwa ce?’
"Na sha faɗa miki ki fita sabgar mata ta da abinda ke cikinta kin ƙi ko, wallahi Nana ina jiye miki ranar da zanyi miki Ɗan bara uban duka a gidannan, jaka kucaka."
Wani irin abu ya toshe mini ƙirji, na ji kamar na faɗi ko zan samu faɗuwar ta zama sanadiyar da zan rasa rayuwata baki ɗaya, rayuwar da ba ta da wani amfani, a yanzu ba wai juya min baya da sardauna ya yi ba ne yake damuna ba, takaicin da danasin biyewa Sardauna da na yi, na zaɓe shi na watsar da 'yan uwana, na zaɓe shi na watsar da kowa, tabbas namiji ba Ɗan goyo ba ne, kuma duk wacca ta ɗauki miji uba zata mutu marainiya.
"Na faɗa miki dai, jaka ballagaza da bata da ilimi."
Ya faɗa yana barin wajen, a take na tuna lokacin da Sardauna ya ce dani.
"Nana, ina da arziƙin da zan riƙe ki, bake kaɗai ba har da gidanku, muna da arziƙin da bazamu taɓa talauci ba, Nana a cikin gidan nan zaki zama kamar sarauniya ne, Nana bana son karatun boko nan, Nana bana son cuɗanya da maza, ina miki so mai tsanani, ina miki kishi mai zafi Nana dan Allah dan Annabi ki haƙura da karatun."
Wasu zafafan hawayene suka biyo kuncina, a fili na furta.
"Allah Yana ji Yana gani."
"Kutumar uban can, Baby ta zageka, wai kaine shege!”
Ni ban ma san tana wajen ba, dan ban kula da ita ba sai da na ji ta yi wannan maganar, ban kai ga gama kallonta ba na ji saukar wani marin a kunci na, tare da sa ƙafa ya kwarfeni na zube a ƙasa ya shiga duka na hannu da ƙafa, tun ina ihu har na sauti ya daina fita.
*********
“Nana, ki saurare ni da kyau. Mutanen da yawa suna kallonki a matsayin wawa ko dolowa da ba ta da zuciya, domin duk wulaƙancin da mutumin nan yake miki, har yanzu ƙoƙarin kare shi kike yi kina masa uzuri. Amma a matsayina ta likita, na san ba ke ce kike son sa ba... Wata cuta ce ta maƙale miki a ƙwaƙwalwarki, ba a zuciya ba!”
Na kurawa Dr. Na’ima ido, ina jiyo muryarta tamkar daga sama. Ta ci gaba da cewa.
“A ilimin likitanci, akwai abin da muke kira Obversive Obsession (ko Limerence). Cutar haukan son abu ce da take kama sinadaran ƙwaƙwalwa. Mutumin da yake ɗauke da wannan rashin lafiyar, ƙwaƙwalwarsa tana daina nuna masa gaskiyar abin da idonsa yake gani, ma’ana ba zuciyarki ke son Sardauna ba ƙwaƙwalwarki ce.
Duk lokacin da Sardauna zai cutar da ke, Kina masa uzuri marar iyaka ne domin idan ƙwaƙwalwarki ta amince Sardauna azzalumi ne, to gaba ɗaya za ki iya haukacewa, domin ƙwalƙwalwarki ce ke son shi, har takan mantar da zuciyarki sharrikansa!”
************
“Nana duk wani abu da ya faru na bibiya, kuma in sha Allahu komai zai zo da sauƙi, tun daga kan zaluncin da ya yi miki, har ɓata sunanki da ya yi a family, ya ja kowa da kowa ya tsaneki.”
Kallonshi na yi, a raina na ce.
‘Yanzu Sardauna har cikin ‘yan uwasa ya je ya ɓatani?.’
“Eyh Nana, lokacin da zai ƙara aure ya ɓata ki sosai a cikin ‘yan uwa da iyaye, amma na yi miki alƙwarin zan tsaya tsayin daka wajen ganin na dawo miki da kimarki da martabarki, Nana ki bini wannan bashin.”
“Hhhm, wace martaba.. wace kima? Kima da martaba ta sun tafi kenan har abada, tun da babu wani abu da zan iya tsinanawa a rayuwar nan, har abada fa bani da damar da zan iya haihuwa, tabbas Sardauna ya yi min Sartse me raɗaɗi a zuciya, wanda zai dauwama har abada yana bina, kaicon rayuwata.”
Tashi ya yi ya matso kusa dani, cikin tausasawa ya fara magana, muryarsa da take da banbanci da ta Sardauna nesa ba kusa ba, muryar da babu sautin yaudara ko ƙarya a ciki, zallar murya mai cike da kwarjini.
“Nana, abubuwa da yawa su kan lalace, wasu su fashe fatsa fatsa, kuma a iya gyarasu har su fi baya kyau da ƙarko. Ni Abubakar Turaki na yi miki wannan alƙwarin, Nana zaki ji daɗi, zaki san menene rayuwar aure, zaki yi farin ciki ki yi alfahari na har abada.”
*********
Falon ya yi shiru, kowa yana saurarena har na kai aya, ina direwa Yaya Rumaisa ta cafe da cewa.
“Nifa shi ya sa bana son shiga al’amuran Nana wallahi, yarinyar nan gaba ɗaya bata da lissafi ko kaɗan, idan ba ki sake aure ba dauwama zaki yi a haka, da baƙin ciki da wancan mistiyacin ta dasa miki?”
“Ni bama wannan ba, Sardauna da kansa ya ce ba ke yake so ba, ƙuruciyarki yake so kuma ya samu, ya ce yana matuƙar kishinki fiye da kowace halitta a duniya, kuma wannan gaskiyya ne domin ko da mukaje ɗauko ki a gida, ina ganin kallon da yake yi wa Ridwan akan ya taɓaki, kallo ne me cike da kishi, haka ranar da mukaje kwashe kayanki, kinsan dalilin da yasa ya daki wancan mai motar?”
Na girgiza kai alamar bansaniba, Yaya Radiya ta gyara zama sannan ta ce.
“Sabida da muka zo shiga jikinki ya gogi nasa, ku duka baku sani ba, a lokacin ina ganin yadda Sardauna ya runtse ido, hakan ya nuna Sardauna yaba matuƙar kishinki fiye da yadda kike tunani, to kina tunanin idan ya ji kinyi aure ya zaiyi?”
“Baƙin ciki ne zai kashe mitsiyaci.” Ra’is dake tsaye ya faɗa, sannan ya ce.
“Ta wani ɓangaren ma, kinsan Sardauna ya tsani Yaya Turaki, a yanda kika faɗa mana ya ce ya tsani ya ga ya mallaki abu Yaya Turaki ya mallaki mai kama da shi, ki tuna gida ɗaya suke da Yaya Turaki, ki hango tashin hankali da rayuwarshi zata shiga idan ya buɗe ido ya ganki a matsayin matar Yaya Turaki Nana.”
********
“Wallahi Sardauna da ina da yadda zanyi ido biyu da zuciyar taka sai na sa mashi na cake ta, ko ta ƙarfi ne na fito da ita, na yayyanka ta na watsawa karnuka ita, dan dabbobi ne suka da ce da ita, Sardauna na tsaneka bana son ko haɗa ido da kai, Sardauna wallahi ina danasin mai girma idan na tuna wai a baya naso mutum mai kama da kai, kuma idan baka matsamin daga nan ba, sai na take ka da motar nan wallahi.”
Ina gama faɗin haka na buɗe motar na shige, ya yi saurin riƙe murfin motar.
“Nana Sardauna ne fa.”
“Mitcheww*** Na ja wani dogon tsaki na fisgi murfin mota ta na rufe.
***********
Ku gyara zama, yanzu za a fara asalin tafiyar labarin.
Ban ce babu marubutan da suka fini ba, amma na sani cewa alƙalamina yana da wani irin salo na musamman wanda muddin ka fara karanta shi, ba za ka so ka ajiye ba. Yanzu zamu fara asalin tafiya asalin labari,
sabuwar rayuwar da za ta girgiza ku. Komai zai sauya, domin abin da yake tafe BABBA NE! Kar ku bari a ba ku labari, domin zo muku da abin da ya fi kowane lokaci.
Ina roƙonku da ku ba ni kyakkyawar shaida da yaƙini, ni kuma zan ba ku nishaɗi da darussan da kuke buƙata in sha Allahu.
TSARIN TAFIYA:
• Book 2 : Zai fara zuwa muku ranar Talata 26/05/2026.
• Farashi: #700 kacal sai dai akwai special offer, zaku iya biyan naira 500 daga yau har zuwa ranar da zamu fara posting na Book 2 daga nan zai koma asalin kuɗinsa 700 (akwai tsarin small VIP, da zaku biya #1000 sai kuma Special Offer VIP ga masu bibiyaa Arewapen, tsari na musamman gare ku, 5 to 8 pages ko wacce rana.)
Babu jira a cikin tsarina; cikin ƙankanin lokaci za mu kammala wannan labarin cikin ikon Allah.
*Littafin Sartse na kuɗi ne 700 a whatsapp ake posting, ku tura kuɗin karatu ta wannan acc ɗin 8104743474 opay Hafsat muhammad lawan, shaidar biya ko tuntuɓa ta wannan lambar.*
***
Nagode da soyayyarku da amincewarku akan rubutuna. Allah ya haɗamu a Aljanna Firdausi. Amin.
#SARTSE
#LabarinSoyayya
#ZamantakewarAure
#MugunMiji
#SayyidLegendspen