BARRISTER SUHAIL
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
KUYI HAƘURI DA RASHIN SAMUN POSTING AKAN LOKACI MUNA FAMA DA RASHIN NEFA
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️----14
duk hararar da aunty Aisha kema naima bai hana ta karɓi kudin daga hannun aunty zaituna ba,suna tafiya ta hau yi mata faɗa ta ce"da tasan haka zata yi masu da baisu zo da ita ba"
Aunty Fauziya ce ta bata hakuri cewar har yanzu naima yarinya ce
"yarinya kuma Fauziya Shekara ta Ashirin da ukku fa har da diya kuma kice yarinta"
Aunty Fauziya ta ce"duk da haka kidai yi haƙuri" har suka karasa Gida aunty aisha bata daina yi mata faɗa ba.
driver na parking ta buɗe kofa ta fita tana gunguni Zarah tafi bayan wanda dan haushi da takaicin abinda tayi ma ya hanata magana a cikin mota
part mami suka nufa banda aunty Fauziya da ta wuce nata dakin
Mami ce zaune a falo ita da yar aikin ta tana mata list din food stuff din da likita ya rubuta mata
naima ta fara shigo waje ta samu kan kujera ta zauna sai haɗe rai take Zarah ta shigo
"gaskiya Naima abinda kikayi gidan surukan Suhail kwata-kwata baki kyauta ba wallahi sa nasan abinda zakiyi kenan baza mu tafi dake ba kuma sarai nasan suna lura da yadda kika nuna kamar ma ƙyarmar suke"
a fusy naima ta mike ta ce"so what idan su gane"
Mami dake kallan su ta ce"wai mike faruwa"
Aunty aisha dake shigowa ta zauna ta fara yi mata bayanin duk abinda ya faru Hajiya laila ta ce"ni ai banda laifin naima dan ta amso kudi naga dama ai ana badawa ko"
Zarah zatayi magana mami ta ce"ni ban tambaye ki kimin shiru"
jakar ta zage ta fito da kudin da naima ta saka mata ta wurga mata ta ce"ga shinan sai kiyi abinda zakiyi dasu ai"
ta wuce ta shige ciki Naima ta fita zuwa dakin yan aiki ta amso Ayla dake hannun nannyn ta
Aunty aisha ta miƙe tana gyara zaman mayafin ta ce"Ummi zan tafi"
"agaida gida"
Jikin Ammi ya riga ya gama sanyi tun shigowar su ganin yadda Naima ke ta kama jikin ta daki ta shiga ta bar masu ganin lefen a tsakar gida tare da aunty zaitun.
zama tayi baƙin gado ta rafka tagumi a haka aunty zaituna ta shigo ta taradda da ita
KUYI MANAGE DA SANNAN🤣 YAFI BAB